Showing 75001 words to 78000 words out of 241571 words

Chapter 26 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14723

ga nata rabon!" "Amin Ya Allah! Bari na shiga na sake alola, Sunana Alhaji Junaid Yashi, daga jahar Bauchi." Mika mishi hannu Tafida yayi yana faɗin. "Aliyu Muhammad Jadda Tafida!" Shiru Alhaji Junaid Yashi yayi yana faɗin. "Kamar nasan sunan nan amma na manta inda na sanshi." "Haka ne Allah yake lamarinsa, sai ka.ga kasan abu amma sai ka iya manta inda kansan shi zan shi, zan tafi masallaci nima!" Suka rabu kowa ya kama hanyar shi, akwai wani darasin da bai tab'a tsinta ba sai yau labarin Matar Alhaji Junaid Yashi ya tsaya mishi a rai, ya rantse ba zai dauki duk wacce ta mata gori ba, sannan ba zai zauna da duk wanda ya wulakanta mishi mata ba, "kut!" Ya fada yana jin aranshi wannan kuskure ne, ai wannan kuskure ne taya don an yi mata laifi zai hukunta wanda bai ji ba bai gani ba. Tsaki yayi yana faɗin. "Ummu dole ki dawo dakinki wallahi!"
**
*Abba*
Zuwa yanzu Abba ya kara fahimtar waye Tafida, domin Ummu tana ta kan bayyana musu asalin siffarsa. Inda yake ƙara godewa Allah yadda Tafida bai bar kowa ba, bai kyale duk wani wanda yake ganin zai iya kyalewa. Shi yanzu abin da yake ganin zai taimakawa Tafida zai yi ba wanda zai kara nisanta shi da Tafida ba, don haka ya kira wani abokinsa babban Malami ne, wanda shi yake taimaka mishi da wani abu addu'a da sauran su, sannan akan Tafida ma Malam Zailani yayi ƙoƙarinsa domin shi ta bawa Abba shawaran kada ya sake ya bar Tafida ya fara auren Saadiyyah, wannan shine babban abin da zai yi danasani. Bayan sun gaisa ya ce masa. "Malam Zailani! Barka da asuba!" "Alhamdulillahi Alhaji Muhammad Jadda, ina ka boye mana mai girma Gwamna!" "Yana Umara malam kayi hakuri nayi maka laifi Yarinyar nan ta haihu ban gaya maka ba!" Murmushi yayi yana faɗin. "Hasken gidanka da na gaya maka ya fara bayyana ba, baka yi laifi ba nima bana kasar yau sati guda da dawowata!"


"Masha Allah! Ya hanya da fatan ka dawo lafiya." "Alhamdulillahi, sai godiyar Ubangiji, lafiya tayi karanci. Amma da sauki." Sannu Abba yayi ta mishi sannan ya cewa Abba. "Ina jinka bakinka da magana!" Nan Abba ya gaya mishi kome, shiru yayi kafin ya ce mishi. "Aliyu bawan Allah! Kamar yadda na gaya maka gaskiya kuma kamr yadda na gan shi a cikin Yaranka bakiɗaya shi na musamman ne, Aliyu gadanga kusar yaki. Alhaji Muhammad Jadda, Aliyu yana tare da makiya dayawa, Aliyu yana tare da makiya kadan da suka bayyana kansu basu da illa kamar wanda suka boye kansu. Alhaji Muhammad Jadda, tun yanxu ka fara sadaka kayi yanka a zubda jini, a ciyar da miskinai da mabukata. A rabawa Yara fura da nono, a basu alawa da gyada da aya. A basu bakinsu ya amsa da Allah ya biya bukata, kasan inda kaddara ta kai shi. Wuri ne da ko yana da marasa imani da nutsuwa suka gina, Allah kuma ya kawo wanda yake bukata a cikin bayinsa. Alhaji Muhammad Jadda,kada ku tilastawa Yarinyar dawowa ita da kanta zata ga yiwar haka." "Batun Yaran fa! Ina tsoron kada a kara samu irin Aliyu a cikinsu." "A'a wannan lamarin Ubangiji ne, Aliyu yana tare da kariyar Allah. Yaran a kawo min su da Mahaifiyarsu." "In sha Allah!" Godiya sosai Abba yayi sannan suka yi sallama. Shiru Abba yayi kafin ya kira Deen duk da garin yayi sassafe ya ce mishi. "Ina son don Allah ka je gidansu Ummu zan kira Alhaji Bulama na gaya mishi ka kai su gidan Malam Zailani." "In sha Allah Abba bari na shirya!" "Allah ya maka albarka!" "Amin Ya Allah!" Kashe wayar yayi ya kira Alhaji Bulama ya gaya mishi zai turo Deen ya kai Ummu da yara a duba su. Tow ya ce mishi. Suka yi sallama.
**
*UMMU!*
Ina kwance Mama ta shigo tana faɗin, "Yaran nan ki shirya su yanzu haka Baban Tafida ya kira Alhaji wai ku shirya zaku fita." Gabana ne ya fadi na ce mata. "Lafiya kuwa?" Harara ta watsa min, "ina zan sani, Ummu ki koma dakinki na gaya miki." "Don Allah Mama kamar kin gaji da ni!" Ware idanu tayi tana faɗin, "lallai fa! Gajiya kan ai na gaji da ke." "Ni kuwa Mama don Allah me nayi da zafi?" Ware min yatsunta tayi tana faɗin. "Kaniyarki kika min, idan nazo sai na fasa miki baki!" Tura baki nayi ina faɗin. "Don Allah yaushe mutum zai samu nutsuwa ace kai da Mamanka amma tana gaya maka ta gaji da kai, gaskiya ba ayi min adalci." Mafificin gefen gadon ta dauka zata buga min na fada toilet da gudu, ina dariyar. "Ja'ira dole ki koma dakinki" wanka nayi na fito na samu tana yiwa yaran tea na hada na sha, sannan na dauki Mufid da aka gama mishi wankan na gyara shi, kafin ta miko min Mufidah itama na gyara mata jikinta, kayansu na saka musu iri daya, sannan na kalli Mama. "ko za a kira min Nana!" "Tow bari na tura a kirata" haka Mama ta fita aka kira Nana, tana zuwa ta gaishe ni. "aunty Baby! Kawo Mufid yau mun b'ata da Mufidah!" "Yau kuma!" Ta amshi shi muka fita ina kallon Uwani tana faɗin. "ke dai Aunty Baby gaskiya kin takura mana, Mama ta koma gidan Mijinta!" Ta fada tana komawa Bayan Mama. "Bani da lokacinki!" Na saka kai muka fita ina faɗin. "Mama sai mun dawo!" Sai da na fara shiga bangaren Ummi muka gaisa sannan na tafi Bangaren Umma. "Wai ke yaushe zaki koma dakinki ne?" Shiru nayi Nana yarinyar ce amma nayi mamakin yadda ta bata amsa. "Hajiya Umma yan rakiya take nima, idan zaki shiga cikinsu mu saka ki a list!" "Yar banza mara kunya ke kan Amina tana da aiki." "Oho dai ai aikin naku ne, idan tayi nata a cikin gidan ku kuma yan yad'awa kun karasa mata Aunty Baby muje ki gaida sweet Bulama!" Make ta nayi, ina hararanta muka fita, to suna wasan jika da kaka, su gaya mata magana ta gaya musu musamman Umma da bata ganin zarrau sai ta tsinka, a parlour baba muka hadu da Deen. "ina kwana baba!" "Lafiya Lau uwar Yan biyu, Amarya ta ya dai kike wani murmushi ko soyayyar mu ta naira goma ce ta motsa!" "Kai ina Sweet Alhaji Bulama, ka ga nayi kama da mai soyayyar Naira goma indai ba class zaka zubda min ba." Sake Baki Deen yayi yana kallon Nana yar yarinyar da bata wuce cikin cokali ba. "tow ku je kasan gidan Malam Zailani akwai a jama'a, ke kuma Amaryata zan kawo miki Naira gomanki har gida na tambayi Malam Yakubu nawa yake baki ne!" Dariya tayi tana me faɗin. "Shi kenan!" Deen yana gaba da nake gaishe shi, Nana tana bayana. Baya na shiga ita ta shiga gaba. "Ya Madam Yaya Deen!" "Tana lafiya itama kwana biyu nan bata jin dadi!" "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah!" Ya fada yana jan Motarshi, "Ummu ya maganar abokina ne?" "Wa kenan?" Murmushi yayi yana faɗin. "Baban twins!" Hade rai nayi ina faɗin. "Shi ya turo ka?" "Ko daya bai turo ni ba, ina me son na baki hakuri ne!" "Hmm ya wuce kawai ya bashi shawara ya sauke nauyin da yake kanshi ya huta." "Tow Allah ya kawo mana mafita!" Daga haka yayi shiru don ya fahimci bana son maganar tayi nisa yasa nace ya sauke nauyin ya huta, kuma maganar gaskiya ban ga abin burgewa na sake jiki kana tattaunawa da abokin mijinka ba, indai ba dole ba. Gaskiya ba haka na ga Mama tana yi ba kuma ba zan ɗauki al'adar wasu na daurawa kaina ba.
Tun kafin mu isa kofar gidan, na fahimci inda muka zo domin akwai motoci sun kai bakwai a kofar gidan, kuma ba kananun ba irin na alfarma na manyan mutane. Parking Deen yayi ya kashe motar muka fito, zauren gidan muka shiga, mutane ne suna zaune a gaban wani dattijo fari kyakkyawa da shi, "Safiyyudeen! Rabona da kai tun kafin aurenka yau gashi domin yiwa Aliyu hidima ka kara zuwa!"
"Haka ne malam barka da asuba!" "Barka dai, Ummu Hadiyya!" "Na'am!" Na amsa a hankali, koda yake ban yi mamakin yadda ya kira sunana ba. "Ku shiga wancan parlour bari na sallame su" haka muka shiga dakin, Deen y amshi Mufidah da nake rike da ita. Yana kallon yadda take barci. Dukkan mu shiru muka yi aka rasa me magana a cikinmu, bayan minti goma aka kawo mana abin karyawa, Nana ce ta ci daga ni har Deen bamu ci ba. "Barkanku" ya fada yana shigowa dakin. "Yawwa malam" Deen ya fada yana mikewa, nima haka. "Zauna abinki!" Zama muka yi ya kalli Deen. "Amintarku da Yarda ku, abin burgewa ne kai dai ka cigaba da tsayawa a gefenshi, domin kalubalenku tafi ta kowa girma, ita wannan nata me sauki ne kai ne za ayi ƙoƙarin ganin an cimma nasara akanku. Ban da iyayenku mata suna hana idanunsu barci a kanku ai da tuni an murkushe alakarku. Tow Allah ya hada ne kamar yadda ya haɗa na Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da Abubakar haka ya haɗa naka da na Aliyu! Kaf duniya baya jin kunyar kowa sama da kai." Sannan ya zauna yana murmushi ya cigaba da cewa. "Kanata samun promotion saboda Aliyu ka ki tafiya ka ki amincewa, kai mutum ne me matukar muhimmanci a rayuwar Tafida!" Kunya duk ya lullube Deen, domin yaƙi yarda wani yasan da haka, har kona takardan yayi kada wani ya gani, baya son barin Tafida a wannan yanayin da bai tsaya da kafarshi ba.
"Yaushe zaki koma dakinki?" Ware idanu nayi bakina yana rawa. "Ummu Hadiyya yaushe zaki koma dakinki?" Hawaye ne ya shiga zuba min. A hankali ya ciro goro a aljuhun babban rigarshi ya fara ci yana faɗin. "ba kuka zaki min ba, Deen cirewa yarinyar nan rigar jikinta, kema cire mishi rigar jikinsa. " "Idan ke da Deen kuka nisanci Tafida garkuwar da yake da shi ya rasa, ban ce ko ne kuke kare shi ba, sai dai kowani mutum da irin baiwar da Allah ya masa, Tafida yana da shi amma naku da ya hadu da nashi Allah ya saka mishi albarka, kuna kyautatawa iyayenku da nashi, wannan albarkan da suke samunku yana rab'anshi. Idan kuka matsa s jikinshi wannan darajar da yake ci zai rufe kamar yadda ake saka toka akan fa a, Tafida zai rushe kuma za ayi nasara a akanshi, ku tsaya mishi Deen ka kula da hannun damanka." Ya fada yana jan wani allon karfe ya fara rubutu a jikinsa da zuma, murmushi yayi sannan ya kalli Nana. "Sarkin tsiwa. Shekarunki nawa?" "Sha uku!"
"Masha Allah! Ubangiji ya albarkaci rayuwarki!" "Amin Ya Allah!" Kuma amsa bakiɗaya. Goran zam-zam ya dauka ya dibi ruwan ya wanke rubutun ya ce mana. "Bani namijin domin Alhaji Muhammad Jadda yana tsoron kada su gaji mahaifinsu!" Ya fada yana kallona, Deen ya mika mishi Mufid. "Tafida bai kyauta ba, amma qaddara ta riga fata, idan aka yi hakuri. Kuma sai kome ya zama tarihi." "A'a Malam ban da Tafida, a barshi ya san ciwon kanshi." Murmushi yayi yana faɗin. "Deen kamar ka koma bayan Ummu!" Dariya yayi yana faɗin. "Kanwata ce duk da naga tana fushi da ni!" Shafe Mufid yayi da ruwan rubutun ya dura mishi haka yiwa macen ma.
**
*TAFIDA*
Tare kofar tayi tana huci, kamar wata macijiya. "Bani hanya na wuce kada na rasa sallah azhar!" "Hakkina zaka bani....https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Hakki?" Ya tambaye ta, kafin ya fara duba aljuhun rigarshi da wandon shi yana niman hakkinta. Inda ya ajiye amma bai gani ya d'ago kai fuskarshi babu annuri ya ce mata. "Matsa ki bani hanya na wuce!" Ciki ciki ta ce mishi. "babu inda zan matsa ka bani hakkina kawai!" "Ba zan bayar ba, ke din wani hakkin ne dake, bakiɗaya mace babu dandano kina tsaye mace amma a zahirin cikinki gara a baka dafaffen kaza mara hadi, domin zaka ci shi haka da akan ke." "Wannan matsalarka ce, ita matarka da ka iya ci meye banbancinta da ni?" Kallon renin hankali yayi mata daga sama har kasa ya ce mata. "Ita ni na fara yanka kazar na fige sannan na dafa da hannuna babu wnada ya taya ni daga gefe. Kin ga ba tare da ajinamota da gishiri ba. Na cinye kazata, kuma har yau marmarin kazata nake!" Ya wuce ta abinshi yana jin ranshi fess. "Allah zai saka min!" D'aga kafada yayi yana faɗin. "Can miki!" Idan tana jin asalin zaman doya da manja tow kuwa shi suke da Tafida, domin bawan Allah nan baya kunya ya gaya mata magana anyhow. Ranar da suka cika sati biyu suka fara shirin dawowa gida, sannan ya shiga manyan store yayi ta sayayya kamar hauka Yaranshi da Ummu kawai su yakewa sayayya, yana gamawa ya wuce gida. A bakin kofarshi ya hango Sa'adi. Murmushi yayi mata yana faɗin. "Matar Governor!" Banza tayi mishi tana faɗin, "Aliyu ka bani hakkina mana, tun ranar da ka kai ni asibiti baka kuma bani hakkina ba ana maganar wata kusan uku." Gyara tsayuwarshi yayi da kyau sai kuma ya shiga cikin dakinshi yana faɗin. "Ke hala Aljanu ne dake masu jaraba?" "A"a Ifriqai nake dasu ba Aljanu ba!" Banke kofar yayi yana faɗin. "Ki je can ni bani da lafiya, basir yana damuna!" Shiru tayi kamar zata yi kuka tayi ta buga kofar Amma yaki.
***
*Ummu Hadiyya*
Tun lokacin da muka dawo daga gidan Malam Zailani, maganar da muka yi ya tsaya min a rai. Amma na tattara ba ajiye a gefe Tafida ba kamar sauran mutane ba ne, da zan sake waiwayarshi cikin sauki, dole ina bukatar sanin halin rayuwa da kuma yadda mata irina suke tafiyar da mutum irin Tafida, ba wai ban san halin Tafida ba ne, sai dai bana fatan na koma mishi har ga Allah domin yan uwanshi ba kaunata suke ba, gara na rufawa kaina asiri. Nayi zurfi cikin tunani wayata tayi ƙara, Hajiya na gani cikin farin ciki na dauka ina faɗin. "Hajiyata!" "Na'am yata, bayan ƙoƙarin da kika yi amma kin kasa zuwa duba Mamanki? Kodai baki son na miki maganar Baba Ali ne?" "A'a Hajiya ban samu fita ba ne, amma idan na samu fita zan zo in sha Allah." "Allah ya nufa na gode sosai, Allah ya miki albarka, yasa kema Yaranki su miki abinda kike mana, Ummu Hadiyya Ubangiji ya shirya bayanki da gabanki na gode sosai!" Idanuna ne suka cika da kwalla tabbas Hajiya ta gama min kome irin wannan addu'ar. "Amin Ya Allah, Amin Ya Allah, Allah ya baki lafiya Hajiya." Na fada kamar xan yi kuka don bana son yadda suke min godiya. Kashe wayar nayi ina sauke ajiyar zuciya. Na kalli Yarana sai naji sanyi a raina tabbas Allah ya min ni'ima da ba kowa yake da shi ba. Alhamdulillahi da wannan damar da Allah ya bani.
*Shuwa*
A gaban Malamin take kamar zata yi kuka ya ce mata. "Ita yarinyar a tsaye ake kansu, na gaya miki sai an tashi tsaye domin ko muna aiki zamu samu masu warwaresu." Idanunta sun kad'a jajjur ta ce mishi. "Malam babban tashin hankalina shine uwarshi ta dawo taya zan samu biyan bukatana!" Zane yayi kafin ya d'ago kai yana kallonta kafin ya ce mata. "Yarinyar ta dawo da ita, sannan babu wata hanyar da zamu iya kulla wani abu, sai mun samu hanya." Ya cigaba da zane kafin ya d'ago da mamaki ya kalleta ya cigaba da cewa. "Akwai hanya amma ba nan kusa ba, abu daya zan gaya miki shine ga wannan hayakin ki tabbatar an saka ya sha shima dan banza yana da taurin kai, wannan kuma a jefa a rijiya mu ga me zai faru nan gaba! Tabbas hanya biyu ne na farko ki tabbatar ranar da ya dawo ranshi a bace yake na biyu kuma gaskiya za a iya rasa rayuwar wani ko.wata akan aikin idan kuma kina ganin haka zai zama mafita to!" "A'a ban da kisa Malam, a barshi xan san yadda zan yi da shi." Zufa ne ya karyo mata, kafin ta ce mishi. "Allah yasa a dace domin yaron nan na sha fama akanshi yanzu da zan huta amma kowa yana niman hanani! Yan uwansa da nake amfani dasu ma sun fara ja da baya." Murmushi ya yi ya ce mata. "Ga wanann ki tabbatar kin saka musu, ba zasu tab'a miki gardama ba, sannan zasu zama masu miki biyayya!" Kudi ta zuba mishi, tana godiya ta fito.
---
Tunda tasan abin da ta kulla, ta nufi bangaren Abba da ta dawo tana me kai karar Tafida. Domin idan ta fara da Abba tafida na zuwa Abba ya mishi magana zai fusata. Tana komawa bangarenta ta kira Saadiyyah, ta gaya mata duk rintsi kada su tawo Najeriya bata fusata Tafida ba. Ita kuma yayi mata alkawarin haka zai faru. Shirin da Shuwa take ba karamin shiri bane don haka ta kira Rukayya domin tasan ita ce zata fi bata haɗin kai, don haka tayi amfani da ita ta kirata da sunan ranar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login