Showing 3001 words to 6000 words out of 241571 words

Chapter 2 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14688

kome!" "Yanzu ina Inna da Abba?" "Abba yaki cewa kome! In fact ya ce kada na kawo mishi su gida, na san yadda zan yi!" "Gani a hanya" wasa wasa tunda Safiyudeen yazo ake tufka da warwara har Safiyudeen ya iso, ga Yaran sun fara galabaita da kuka, Hajja Gaanah tana kallon yadda Aliyu yayi wujiga-wujiga domin tashin hankali, a cikin Yan uwansa Maryam ce kawai a tare da shi. "Inna don Allah ku kai Yaran nan, ni zan kai Aliyu ta shirya lokaci yana ta tafiya!" A fusace ta b'alla mishi harara Hajja Gaanah tayi ta juya cikin Yaren shuwa ta ce mishi.
"Yar banza ba kince ke ba zaki zauna da shi ba? Kin zata ke ce kawai mara mutumci? Anan kika ce ko yaron nan Ummu Hadiyyah ya haihu ba zai bawa Yaranka nono ba, don uwaka ba zan saka dan uwana ya je ba, ka ja mana abin kunya ana bikin rantsar da Gwamna amma tana asibiti tana cutar da marayan Allah, Anya Aliyu kina tsoron haduwa da Allah? Ka ga ni daga nan ina gama bikin zan koma garin mu can miki da mugun nufinki Gara da Yaron nan Ummu Hadiyyah ya bar ka Yaranka ki je can mara kunyar karya. Ni dai ba zan tafi na kara zubar da mutuncin na ba!" Ta fada tana kauda kai.
Kwanciya nayi amma na kasa jin dadin rayuwata, ita uwa a kodayaushe Uwa ce na haihu a rayuwata amma na ajiye Yaran a can tow me yasa na bar mishi Yaran? Me yasa ban kwaso abina ba? Lumshe idanuna nayi wanda ba barci nayi ba, amma fa ina cikin tashin hankali. Har kusan karfe sha daya da naji gabana yana faduwa, karfe sha biyu za'a rantsar da shi amma tow waye ya sani ko ya tafi abin shi ya bar min Yaran a can? Ban san yadda aka yi ba sai ji nayi na tashi zaune ina zare idanu. Idan kuma Aliyu ya kaiwa Hajiya Shuwa Yarana fa? Kenan Sa'adiya ce zata ci gaba da yadda taso a kaina da Yarana kenan? Shigowa Mama tayi ta kalle ni. "Lafiya?" "Kaina yake ciwo!" Na mata karya, don naci karya na kwana da yunwa na gayawa Mama cewa Yarana nake tunanin kada su fada hannun Shuwa da Yarta. Tab'e baki tayi ta janyo locker gadon ta ciro Panadol ta ajiye min ta fita, karfe sha biyu saura minti ashirin, naji hayaniya a gidanmu da Unguwar bakiÉ—aya, sai da naji kamar zuciyata zata diro waje........
For more info...
08130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*


*🚫 Gargadi da kashedi! Wannan labarin hakkin Mallakar Mai_Dambu ce! A kiyayye tab'a abin da ba naka ba kuskure ne kowa yayi nashi🔞*






FATAN ALKHAIRI GA DUK WATA SINGLE MOTHER WANNAN LITTAFIN NAKU NE💕🌺


Paid book
_Zuwa yanzu na fahimci nayi kuskuren barwa Tafida Yarana tabbas kowacce mace ba ce ta cancanci zama uwa sai wacce Allah ya so ta da rahama_


02
Mikewa nayi jikina yana rawa domin haka kawai nake ji kamar Aliyu ne da tawagarsa suka biyo sawuna. Shigowa dakin Mama tayi tana faÉ—in. "Bismillah ku shigo mana!" Tun kafin ya iso kamshin turarensa ya cika dakin gabana sai dukan uku uku yake, yana baya safiyyudeen yana rike da baby macen domin daga yanayin abin daukansu na fahimci haka, komawa bakin gadon nayi na zauna tare da saka hijab dina. Cikin wani munafukin na nutsuwa ya zauna yana sunkuyar da kai wanda a da can wani gani gani yakewa dakin idan muka zo, sai yau naga akasin haka. "Mama don Allah ki ce ta amshi yaran wallahi an kusan!" "A'a ba sai kun had'a ni da Alla ba ai bata kyauta ba, kawo su ku tafi kada a makara." Ta amshi yar hannun Safiyyudeen din ta kwantar da ita sannan ta mika hannu ta amshi Namijin da yake kwance a faddadar kirjin shi. "Don Allah ki roke ta, ta koma kafin ayi bikin shiga gidan gwamnati!" Ya fada yana mikewa cikin sanyin halin da ban san yaushe ya dauko shi ba yo ai ba halinsa ba. Kasa-kasa nace. "Sai dai a kai gawata gidanka, wallahi ba xan koma ba!" Nasan zai ji kuma bakiÉ—aya ma nasan zasu ji, na dauke kai kamar bani nayi maganar ba. Wayar Safiyyudeen ne yayi kara ya ga Mahmud tsaki yayi yana faÉ—in. "Muje!" Dakyar ya iya fita yana jin kamar an sauke mishi nauyin da yake kanshi. A gurguje suka nufi filin da za a rantsar da shi, daga shi har Safiyyudeen babu me damar magana hankalin kowa a tashe yake domin gani suke kamar an mishi wani ne. Gyara murya alkalin alkalai yayi sannan ta shiga maimaita alqawarin da rantsuwa da Aliyu Muhammad Jadda zai dauka, ya sha fararen kaya kanshi sanye da wata bakar hular zanna Bukar da tasha aiki me kyau, ana gama rantsar da shi ya shiga motar gwamnati kamar yadda kowani gwamna yake.
A fusace Mama ta nuna min Yatsa, "kada ki sake fushina ya kwace akanki, kika sake raina ya b'aci zaki ga ba daidai ba" a matuƙar tsorace na hadiye duk abin nake ji na koma na nutsu tare da kame kaina Mama bata daukar reni tana cikin iyaye marasa daukar iskancin Yaransu. Fita tayi amma bakiɗaya ranta a b'ace yake haka ta hado ruwan zafi ta kawo dakin Allah Sarki Uwa me dad'i, hatta sabulun wanka ta hada, "Assalamualaikum, Hadiza ashe an kawo Yaran?" Inji Umma, murmushi tayi tana me faɗin. "Eh gasu nan zan wanke su." Waye bai san halin Umma ba wurin had'a wuri da son bin didigi, "Kai Hadiza ina laifin ki ce ni ko Yaya wata tazo ta wanke Ummu Hadiyya da jarirai ke da kanki zaki yi haka?" Cikin ko in kula ta ce mata mata. "Yanzu aka min jika abin cikin kwai, yafi kwai dad'i!" Daga haka Umma tayi turus, "Allah ya huci zuciyarki!" "Ai ba fada ba ne!" Mama ta fada tana cirewa Macen kaya, ta fara shafe ta da lalle da ta kwab'a da tazargaje, ta maida ita cikin abin ɗauka ta rufeta, sannan ta koma wurin wurin namijin shima haka ta shafe shi tas, har lokacin Umma ta gagara jan kafa ta bar dakin. Domin bata tab'a kawowa Mama zata gaya magana haka na. "Ummu babu inda yake miki ciwo?" Girgiza mata kai nayi sannan ta juya yana faɗin. "Sannu da arziki ashe har yan biyu ne." Gyada kai nayi a kunyance, fita tayi can bayan fitarta Mama ta dalla min harara. "Wallahi da kin sake wani ya san bar mishi Yaran kika yi da na sab'a miki!" Shiru nayi ban ce kome ba, saboda nasan zata iya nad'a min duka wallahi. Tana rufe bakinta sai ga makota sun fara shigowa. "ashe Ummu Hadiyyarmu ta sauka lafiya?" Murmushi Mama tayi domin Mama me Jama'a ce kuma Allah ya bata jama'a don haka ta ce musu "Eh wallahi!" Ta nuna musu Yaran da take gyara su, yadda Mama take hidima kawai ya saka ni jin tabbas ta jima tana shiri ba na wasa ba, domin tsakaninta da Allah take kome, kafin zuwa azhar gidanmu ya cika da yan barka da yan Allah ya sanya alkhairi. Wato a a tayani murnar samun nasarar da Tafida yayi har yau an rantsar da shi. Murmushi nake domin basu san me ke faruwa ba, da an buga ni a jarida. "Assalamualaikum!" Mama da take tsakar gidan ta amsa tana faɗin. "Malam Mudan!" "Na'am Mama, ga kayan Hajiya Ummu da wayarta." "Masha Allah, ka kyauta wallahi!" Zata amshi kayan Zakiya da itama shigowar kenan daga kofar gida ta amshi kayan tana faɗin. "Mun gode, Mudan yanxu dai zaka koma Government House kenan?" "A'a Hajiya Zakiya ina nan daram a tare da Hajiya Ummu!" "Lallai na zata can zaka koma ai." Dariya yayi yana faɗin. "A'a babu inda zani!" "Mudan kyale magananiya ga abincin nan!" "Hajiya Mama kin san gidan ana ta hidima Hajiya Maryam ta haɗa min kayan naci abinci." "Tow shi kenan." Sallama yayi na leko ina faɗin. "Mudan ka rufe min store dina!" "In sha Allah" ya fada yana me barin gidan. Mika min jakata Zakiya tai na na amsa ina bude jakar,wayata ce Samsung series X ina kunnawa na ga babu charger. "Zakiya?" Na kirata. "Na'am Aunty Ummu!" "Don Allah bude akwatin nan akwai power Bank a ciki bani!" "Tow!" Ya zuge akwatin na ciro, ta mika min ina sakawa a charger kamar abin munafunci sai ga kiran Tafida. Kamar ba zan dauka ba. Jin wayar tana ta ringing ban dauka ba, ta shigo dakin. "Kanki daya kuwa? Ba kiranki ake ba?" "Ayya Mama kin ga abin da nake yi basu mama nake fa!" Na fada kamar zanyi kuka, "kowa rai ya amfana baya ga me shi ne!" Daga haka ta fita wayar ya kuma ruri. Dauka nayi a fusace na ce mishi. "Me kake bukata?" "Ko ki kira ni!" "Akan me zan kira ka meye matsalata da kai da har zan damu kaina da kiranka!" Murmushi yayi sannan ya ce min. "Matsala ai babba ce tsakanina da ke, dama na kira naji yaushe zaki dawo ayi suna a government!" Ya fada a cikin sanyin murya da ni bako ne a gare ni. "Da bance ka zo ka ɗauke kayanka da ka kawo min ba?" Wani shiru yayi kamar baya rike da wayar na cigaba da cewa. "Idan ka sake raina ya b'aci kotu ce zata raba ni da kai." "Ummu Hadiyya duk akan me yayi zafi?" "Na gaya maka zama da kai ne ya kare ka fahimta mana!" "Ummu Hadiyya ni fa ban san me nayi kika dauka da zafi har haka ba." "Zaka sani daga baya!" Na kashe wayar har yanzu wani irin b'acin rai nake ji domin kaf wayata babu wanda ya kira ni a gidansu Aliyu Tafida ya min barka haka ya tabbatar min suna tare da Dan uwansu da Yar uwarsu, kuma nasan koda ina gidan haka zasu cigaba da harkansu babu wanda ya damu da ni. Murmushin takaici nayi ina kallon Yaran, wayata tayi ƙara dauka nayi ganin Kulsum. "Aunty Ummu Hadiyya ashe kin sauka." "Hmm eh Kulsum!" "Wayyo Allah nan nesa bata maganin kusa kamar nayi tsuntsuwa na zo na ga Aunty baby da Jaririnta kin san ma a ina na gani?" "Sai kin fada tsikallazi!" " A status din Mai girma gwamna, ya saka tare da cewa My beautiful kids from first lady!" Tab'e baki nayi ina cewa. "Sai dai wata faisi ladyn ba dai jinin Baburawa ba!" "Kai Aunty Baby!" "Meye nayi? Daga fadar gaskiya wallahi kuwa zai aiko min da takardana!" "Ba ruwana!" Jin ana kiran wayar nace mata. "Kashe Father inlaws yana kirana!" "Tow Maman twins daga Aunty Baby zuwa Maman twins!" Tana kashewa ina daukar kiranshi. "Abba kayi hakuri!" "Yarinyata ke xan bawa hakuri ashe babu wanda ya zo ganinki? Babu abin da aka kawo miki? Yarinyata wacce irin rayuwa kike yi ne haka? Kin ga haka abokiyar zamanki take yi ne?" Kafin nayi magana Hajja Ganaah ta ce mishi. "A'a Jadda kar ki ga laifin Yaron nan Hadiyya mutum ce guda, Yaron yana da kawaici kawai iskancin yan gidanka ne su ya dace kiyi musu fada ba Yaron nan Hadiyya ba, kuma kin ga hankalin kowa ya tafi wurin bikin rantsar da Tafida shi yasa aka manta.", ai kuwa ina ji ya juya mata kanuri shiru yayi domin a fusace yake, "Ga sako nan na turo zuwa an jima xan zo da kaina.;" "Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, Allah ya biya da gidan Aljanna!" "Zan zo na ga yaran kin ji!" Nan ya shiga bani hakuri dama fa haka yake, Tafida da laifi shi da bada hakuri. "A'a Abba wallahi babu kome!" Kai mutumin nan da girma yake. "Na gode sosai! Allah ya muku albarka sai na zo!" Haka muka yi sallama na ajiye wayar kenan sai ga Kiran Aunty Maryam na dauka. "Ashe kin sauka lafiya!" "Eh wallahi!" "Tow sannu!" Ta fada a dakile kafin ta rufe baki na ce mata. "Yawwa!" Na kashe wayar, sake kirana tayi na dauka tare da cewa. "Kin yi mantuwa?" "Ban yi mantuwa ba, kada ki ga don Abba yana wani ji da ke ki dauka wata tsiya ce, domin talaka bai iya samun wuri ba!" Dariya nayi irin na cusa haushi nace mata. "Ke Yayar Aliyu ce shi yasa ba xan gaya miki me zafi ba, amma idan da gaske kina tare da dan uwanki don Allah ki ce mishi kafin faduwar rana zuwa hudowar na gobe ya sauke igiyoyin da ya zame mishi alak'ak'ai ya huta kuma ku huta da bakar kaddara!" Kafin ta gaya min abin da zai hana ni barci na katse kiran tare da sakata a blacklisted kowa ya huta, nasan ba irina suke bukata ba, shi yasa duk abin Tafida yayi min basu gani asalima gani suke kamar an tauye mishi hakkinsa na aura mishi. "Mama Amarya ga wata a kori kura da kaya wai an kawowa Aunty Hadiyya ne!" Shiru nayi ina zare idanu, bankado labule tayi na fara kokarin ajiye Jaririna zan mike. "Ban fahimci me Yaron nan yake faɗa ba?" "Dama-dama, Abban babansu twins ne ya ce za a kawo kayan abinci." Wani kallo ta zuba min na fara rantsuwa. "Wallahi ban roka ba." "Kada ki tara min mutane." Ta ja mayafinta, ta yafa sannan ta ce min. "Kika sake wani abu ya dawo daga hukuncinki wallahi zan saka kafar wando daya dake." Hadiye yawu nayi na wuce ban dakin da yake cikin dakinta na dawo dakin na tsiyayyi ruwan flast na wuce, Tabbas Abba ya turo da kayan abinci, babu abin da babu kama giron kunu, buhun sugar, katon din madara da Ovaltine, shinkafa, alkama, man gyada manja, da Naira dubu hamsin, wai a gaya min gobe za a kawo nama.


Koda aka shigo da kayan, Hajiya Balki da Umma suka shigo. A fuskar Hajiya Balki da na hango sanyi na gaisheta. Cikin kulawa ta ce min. "Sai gashi har biyu kika haifa da kanki?" Komawa kujera nayi na zauna, domin girman Hajiya daban ne. "Kin zama Maman Yan biyu, bana nan tun asuba muka tafi gidan Taima kin san abin sai a hankali zama yaki dad'i kuma Babanku yaki magana akai shi yasa naje tun lokacin ina can. Ina dawowa Kawu Gwani yake gaya min kin haihu. Ikon Allah muna ta al'ajabin wannan cikin naki ashe kyautar Allah ne awurin." "Ya su Taima din da Yaranta?" "Suna lafiya, al'amarin sai a hankali uwar mijin taki a zauna lafiya yanxu haka dakyar aka shawo kanta!" Naji babu dad'i sai dai ita sharri haka take, "Allah ya kyauta ya daidaita tsakaninsu." "Amin Ummu ki yafe mana, sannan ki zauna a dakin Mijinki wallahi Allah ne ya d'aga darajarki amma tabbas halin ki da na mahaifiyarku abin koyi ne!" A hankali na d'ago kai na kalleta kafin ta ajiye Yaran ta ce min. "Daga yau zan cigaba da musu wanka, jin Yaran nake kamar Yaran kawu gwani!" Hawaye ne ya cika min idanuna. Nasan Allah ya haÉ—a ni da kawu gwani tun farko amma da Allah bai nufa ba haka kome ya tafi da tarin zunubi marasa dad'i, "Ba kome Ummi!" Yadda Yaranta suke kiranta. Har zata fita Mama ta shigo da ruwan wankan Yaran. Ta ce mata."kiyiwa ma mijinki da kishiyarki ni zan yiwa Y'ata." Murmushi Mama tayi tana faÉ—in. "Oho wato ke nan me gudun dangi har zaki guji miji da kishiya ki gyara yarki!" Abin da daure kai yaushe Mama da Ummi suka shirya? Wai meke faruwa ne a gidanmu waye zai gaya min wannan labarin? Ummu Rooman, tabbas ita ce zata bani labari haka Ummi ta kwashe ruwa ta kai ban daki ta saka na fito tayi min wanka tas, har da jijiiga min cikina sai ga jini da yake damuna. Kafin na fito ta koma bangarenta, ina ga girkin daren da tayiwa Baba shi aka zuba min yaji man shanu gijib, aka Mahira ta kawo, sai sannan ta ga Yaran dake irin yaran nan ne masu rawan kai, amma.tana tsoron Ummi, ta shiga daukar Yaran a hoto sannan ta daura a story dinta, da faÉ—in. *Alhamdulillahi Masha Allah tuburkallah, Yaran mai girma Gwamna Aliyu Muhammad Jadda Bro Tafida!* Kafin wani lokaci an cika mata waya da kira ana tambayarta da gaske Matarshi ta haihu? Komawa Whatsp tayi ta ce Yes Aunty Baby ta haihu. Ta faÉ—a tana murmushi. "Aunty Baby ni fa xan iya dawowa nan da dama saboda Yaran nan, wai ma ya sunansu ne?" "Mahira kina babbar Uwa ina ruwana da su!" "Ok bari mu zabi suna masu dadi!" mama da take shafe su da turare ta ce mana. "Oho garin saye sayen suna sai kun sakawa Yara suna cokali!" Dariya Mahira tayi tana faÉ—in. "Wannan sunanshi Mufid ita kuma Mufidah. " "Oho idan kunso ku saka musu muzuru da magege!" "Kai Mama kishinki yayi yawa!" "Idan ban yi waje dasu ba ku ba dame ni da maganar kishi!" Ta fita tana murmushi. "Aunty Baby kiyi hakuri ban shigo ba na tafi school ne kuma na dawo na kama aiki kiyi hakuri!" "Ba kome Mahira!" Shigowa Mama tayi da tukunyar miya, ta ajiye ta zubawa Mahira tace. "Ki kaiwa Umminku da Umma!" "Tow Aunty Baby sai gobe don karatu nake sosai mun kusan Exam!" "Allah ya bada sa'a!" "Amin Ya Allah!" Ta fada tana me barin dakin, zuba min nawa tayi can su Zakiya da Uwani suka shigo. Suka baje a dakinta. Nan muka shiga hira, muna haka Baba yayi sallama. Duk suka mike tare da komawa can gefe, ciki ya shigo yana faÉ—in. "Haka kawai naji ina cikin farin ciki ashe Ummu Hadiyya ce ya sauka, Masha Allah Alhamdulillahi Ubangiji me kyauta da kari." Ya taka har bakin gadon ya dauki yaran yana musu addu'a. "Wato kun zo ayi bikin Babanku ko?" Kaina a sunkuye ya kalle ni kafin ya ce min. "Sannu Ummu!" Ni dai kaina a sunkuye. "Dazun Alhaji Muhammad Jadda yake gaya min, Ummu Hadiyya ta sauka sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login