Showing 6001 words to 9000 words out of 241571 words
Chapter 3 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
da na kusan shigowa gari yake gaya min yana ta bani hakuri yanxu ma yace bayan Isha yana hanya. "Tow Masha Allah!" Haka ya gama maganar sannan ya ajiye su ya fita after kamar minti talatin sai ga Amiru da katon leda, gasashen kaza ne har uku inji Baba. "Amma Alhaji ko? Zai gamu da ni!" Ta fada tana me faɗin.."Uwani dauko min tire da flat." Fita Uwani tayi sai gata da su, ta baje mana sannan ta zuba min nawa naci sosai don ma bakina ba dad'i. Wurin karfe takwas sai ga Sako Baba ya turo a gayawa Mama Alhaji Muhammad Jadda yazo. Sai da tayiwa yaran addu'a sannan ta dauki daya Zakiya ta ɗauki namijin, Uwani da katon tire an saka ruwa da kayan sha. Aka kai musu Yaran, dake ya saba duk inda zai shiga da Kannen shi nan guda biyu. Ba'agwe da Abbalawan, sune suka amshi Yaran yana zaune a kusa Baba da ya ajiye mishi kayan marmari gabanshi. "Ina Yarinyata ba wurin wadannan naxo ba!" Abba yana cikin mutane masu dattako da daraja, shi hankaka ne mai da dan wani naka, kuma har yau haka yake. "Bari na kirata!" mama ta kuma fita muka tawo tare na sha uban lafayya. Ina shigowa na zube zan gaida shi ya ce min. "Kul koma kan kujera, danyen jiki ne dake zauna a sama, Hajiya shigo mata da takalminta!" Kallon Abba Mama tayi yayi murmushi ya ce mata. "ki shigo da shi mana!" Haka ta fita ta kawo takalmin, ya ajiye min sannan ta cewa Abba. "Alhaji baka bukatar wani abu ne?" "A'a Hadiza me zan bukata yau ango nake nayi sabuwar Amarya shar ke da Balki da Yahanasu na ja muku layi." Ai kuwa farlon aka saka dariya ta fita tana murmushi, "Alhaji Bulama kayi dacen mata, haka nake mafarkin Aliyu ya dace da Hadiyya,matukar wancar matar da ta fita ita ta haifi Hadiyya tabbas Aliyu ya dace. Alhaji ka bawa Ummu Hadiyya hakuri na sani,.kuma nasan zata cigaba da yi. Murmushi Baba yayi ya ce mishi. "Alhaji sha'anin Yaranmu sai Allah amma nasan zuwa yanzu kome ya wuce ai, tunda gashi har da zuri'a." Wai ma tukun bikon Aliyu aka zo yi wato gani nan sakarya shine da zo a bani hakuri ban gama nazarin haka ba naji Abbanshi yana faɗin. "Nayi mata alkawarin kuma zan sauka akan alkawarina ba, Allah ya mata albarka ta kuma cika yar halak, ta nuna min ita haifafiya ce, Ummu Hadiyya ki tsaya akan kalamanki Allah zai tsaya miki, zan kuma koma gefe na zuba idanu. Idan Aliyu Tafida yayi nasara akanki zan baki boye kaina idan kika kai shi kasa da shi da yan barandanshi nayi miki alkawarin tsaya miki kai da fata, amma ki sani sai kin zama jajjurtacciya akan kome da kowa, Alhaji Bulama kayi hakuri amma akwai banbanci da can baya da yanxu domin ina bayanta ne a yanzu. Wannan shine dalilin zuwa ta. "Na zata kome ya wuce Alhaji!" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Yanzu ne mafarin.... Anya Alhaji Muhammad Jadda Uban Aliyu Tafida ne kuwa.... Me yayi zafi har da zai hada kai da Matar dansa? 🥺
08130269641YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
03
Duk da dai ban san dalilin Abba nayi haka ba, amma naji a jikina tabbas ko Abba da Baba su tsaya min ba, wannan shine karshen zamana da Tafida domin a duk lokacin da na tuna abun ya faru a baya tabbas Tafida yana buƙatar space me girman gaske, yana bukatar na bashi wuri ya sha iska, don haka na sunkuyar da kaina kasa, har Abbanshi ya gama bamu hakuri ya cewa Baba. "Ka kira Mamanta su maida su daki." Ya fada yana kallon Yaran da yake jin wani kaunarsu kamar ya tafi da su. "Tow Alhaji Muhammad, ayi ta hakuri dai domin shi rayuwar bakiɗaya akan hakuri yake." Haka ya kira Mama a waya suka tawo suka dauki Yaran ni kuma nayiwa Abba da Baba da yan uwan Abba sallama, koda muka koma dakin Mama ruwan zafi ta had'a min na danyen gasarar kunu da ta zuba sugar da garin yaji, ta dauko min namar da Baba ya kawo ta kara dumamin, sannan ta ajiye min tana faɗin. "Kafin ki kwanta ki sha ana bukatar yaran su wadata da ruwan nono kafin gari ya waye." Gyada kai nayi na cire kayan jikina, sannan na maida wanda na saka dazun na fara shan ruwan zafin ina cin namar, hira suke tun ina jinsu har barci yayi gaba da ni, dake na manta da wayata ban kashe ta ba, wurin karfe daya na dare naji wayar na ƙara, a matuƙar gajiye na dauki kiran. "Ya kike?" "Gaskiya ka shiga hakkina akan me zaka kira ni daidai irin wannan lokacin? Fisabiilillahi baka gane kana cutar da rayuwa ne? Ka je Allah yana nan baya barci." Na kashe wayar bakiɗaya na kwanta. Dakyar nayi barci don ma Mama tana dakinsu Zakiya.
*Aliyu Tafida*
Yau duk wani hayaniya da aka yi tare da bidiri a kasan ranshi Ummu Hadiyya ce, domin a matuƙar dame yake ya rasa yadda zai yi ne, amma dake Allah ya daura mishi zurfin ciki da juriya yasa bai wani nuna damuwa ba, amma tsakani da Allah yana hautsine akan abinda Ummu Hadiyya take nima, wunin yau bai da nutsuwa ga bikin da aka yi, bayan rantsar da shi. Duk yadda yaso ya yi magana Safiyyudeen ya hana shi, koda ya kira Ummu Hadiyya ma yana cikin mota zasu koma gida ne su uku Tafida, Safiyyudeen da Mahmud. "Ummu!" "Tafida zuwa karfe biyu na rana zan zo na hada maka kayanka!" "Deen!" "Na'am!" "Ka wuce da ni gidansu Hadiyya!" "Dare yayi kai ka gaya min tun karfe daya na daren jiya take abu daya yanzu ta samu zata huta kace a tafi a tadda ita kai ka ce baka tab'a sanin haka Mata suke shan azabar haihuwa ba, ka san me? Allah yana sonka da rahama ne har ya nuna maka yadda mace take nakuda." "Amma me yasa.!" Kafin ya kai Aya Safiyyudeen ya dakatar da shi da cewa. "Kada ka manta yanzu kai ne gwamnar Jahar Borno wai ma Tafida yaushe ka fara kananun magana?" "Tun ranar da aka aura mishi wancan me siffar dodon wasan Yara!" Inji Mahmud, kalamansa sun yiwa Aliyu zafi saboda ya san cewa shi ya bada damar haka amma bai taɓa kawowa zai iya cin mutuncin Ummu a gabansa haka ya basu damar fadar abin da yayi musu. "Wannan wacce irin hauka ne? Taya zaka fadi haka?" Inji Safiyyudeen yana tuki. "Kambu da kai nayi? Dan shigigi ko ance babu wanda bai san halinka ba ne." "Gara ni ba munafiki ne ne, gara ni bani da fuska biyu idan har bana son Abu bana wahalar da kowa sannu shugaban munafukai. " "Kai ya isa haka, don Allah meye haka ne? Tun muna Yara kuke wannan haukar har yau baku gane gaskiya kun girma ba ne!" "Shi zaka gaypawa dan matsiyata!" "Na gode sosai tunda arzikin ba ubanka yake rabawa nace ya manta da gidanmu ba, gara na zauna a tsiya da na zama me irin halinka!" "Zanci bura uban mutum!" Ya fada da karfi haka yasa bakiɗaya suka yi shiru. Wato shi Safiyyudeen kokari yake ya hana Tafida fadar sirrinsu yayi da Mahmud yake son yaji meke faruwa tsakanin Tafida da Ummu. Dukansu abokan Tafida ne tun suna Yara shi yasa kaf duniya bai da sama da su, amma don sirri da tattauanawa me muhimmanci bai da sama da Safiyyudeen domin shi Deen irin mutanen nan ne masu zafi da fada, yanxu sai ya iya kwaabewa ayi dambe da shi babu ruwan shi. Yayinda Mahmud baka tab'a sanin halinshi idan ka cire jaraban bin mata tow magana ya kare duk suna da kirki sai dai tsakanin Mahmud da Safiyyudeen shirinsu na lokaci ƙalilan ne zuwa wani lokaci sun hautsine don shi Mahmud yana da wani irin dabi'u saurin gori da nunawa yafi kowa yayinda Safiyyudeen bai da irin wannan halin sam, sannan shi kanshi Tafida yasan halinsu ya san abin kowanensu zai aikata. Kuma dukkansu babu wanda yake jin zai rabu da shi don halinsa sai dai kai ka rabu da Tafida don kanka. Sai da aka fara sauke Mahmud a gida ya tsaya a gefen motar ya ce. "Allah ya isana duk wanda yayi gulmana!" "Kai can ci ubanka!" "Na dai faɗa!" Ya juya tare da shiga get din gidansa. Murmushi Safiyyudeen yayi ya ja motar suka yi gaba. Tafida ya kwantar da kanshi. "Deen me yasa kake hanani magana!" Banza yayi mishi tare da mai da idanunshi kan hanya, wannan halin na Deen yana matuƙar burge Tafida domin Deen Allah ya mishi baiwar iya shariya musu ka tambaye shi abin da yasan ka sani ba zaka kulaka ba sai dai ya bawa banza ajiyarka banbancinshi da Mahmud shi a kodayaushe cikin zargi yake ana munafuncinsa. Sai da ya shigar da shi cikin gidan Mahaifinsa security da masu tsaron da suka hana binsu suka taso tare da lullube su. "Aliyu!" Juyawa yayi yana kallon Deen yana da kyau ka mutuntata darajar Ummu Hadiyya ko babu kome yanzu an zama d'aya, idan da hali kada ka bawa kowa damar cin mutuncinta, yarinyar nan ta rufa maka asiri sama da yadda zamu rufa maka, ta boyewa duniya waye kai ta kuma maida ka mutum sama da kasa, don Allah ko ba don ita ba ko don albarkacin Yaranka ka girmama lamarinta, ba ina gaya maka haka don akwai wani abu ba, kai mutum ne da yayi approaching siyasa yanxu kada ayi amfani da abinda ka aikata akanta ayi kokarin b'ata maka siyasar ka." "Nagode sosai Deen in sha Allah zan kiyaye kuma ina son idan na samu lokaci zamu je gidansu." Murmushi Deen yayi ya ce mishi. "Sai da safe!" Daga haka Aliyu ya fito a motar ya cewa Security din. "Ku Kai shi gida!" "Yes sir!" Suka fada tare da bin motar Deen. A hankali yake takawa jikinshi na matukar mishi ciwo, ya shiga har cikin gidan ya samu babu kowa bangarenshi ya nufa ya samu Sa'adiyya tana zaune waya a hannunta, sanye take cikin kyakkyawar shigar kayan barci. Sau daya ya kalleta sannan ya dauke kai kamar bai dangata ba. "Ya Tafida!" Kallonta yayi kafin ya ce mata. "Au kina nan ne ashe?" "Zaman jiranka nake?" "Ni kuma? Ai da kin kwanta abinki!" "Wani irin kwanta na gama shirin na tayaka murnan samu nasarar zama Gwanma kace nayi barci." Yadda take surutu ba karamin haushi yake bashi ba, Sa'adiyya ita ce irin choice dinsa amma yawan maganarta yasa yake jin babu dad'i akanta ta bude baki zata yi magana ya ce mata. "Please na gaji hutawa zan yi!" Ya wuce dakinsa wanda yake kusa da na Ummu Hadiyya, sai yanzu yaji bakiɗaya kome ya tsaya mishi. Gabanshi ya shiga faduwa da gaske Ummu Hadiyya tafiya tayi? Kurawa dakinta idanun yayi sannan ta wuce dakinsa, duk yadda yaso ya samu hutu ya kasa dole dakin Hadiyya ya dawo ya kwanta. Kamshin turarenta da yake cike a dakin kamar yanzu ta saka ya sashi lumshe idanu. Yana kwance a wurin har aka kira sallah asuba, dakyar ya tashi yayi sallah anan ya baje bai farka ba sai wurin karfe daya na rana. Shima kiran sallah azhar ya farka. Ban dakinta ya nufa yayi wanka sannan ya dauro babban towel dinta. Ya nufi waje sake da baki Sa'adiyya tayi da take waya da kawarta ganinnshi daure da Towel din Hadiyya, bata san lokacin da ta kashe wayar hannunta ba. "Tafida meye haka? Ko tsari babu." Banza yayi mata ya wuce dakinsa, tana biyo bayanshi ya ce mata ya ce mata "Get out!" Juyawa tayi babu shiri, tasan ba karamin aiki bane ya maketa kamar zata yi kuka ta kira Uwarta. "Ammi anya kuwa mun samu Tadda yadda muke so kuwa?" Ta fada kwalla na cika mata idanu. "Kul ki sake fadar haka ki zo muyi maganar mu biyu ban da waya." Kashe wayar tayi tana jin wani zafi da kishin Tafida a ranta, bata gaya masa ba ta shirya ta nufi cikin gidan. Shi kan yasan abincin gidan tunda Ummu ta bar gidan shi kenan ta kare mishi. Don haka ya nufi bangaren Inna sanye yake da gezner skyblue shaddar har wani sheki take takalmin kafarshi hafcove ne na kamfanin Dolce de Gabbana, sai hular da ya murza akanshi tangaran ce tayi bala'in mishi kyau. Ta babbar kofar gidan ya shiga cikin gidan, kamshin turarensa ya sanarda yan gidan da masu aikin gidan ga Tafida nan ya shigo, wani uwar gud'a da Mama indo ta buga yasa shi sake fuskar shi. Ta shiga mishi kirari. "Mama indo bakya gajiya ne?" Dariya tayi tana faɗin. "an gaida Uban Yan biyu, Uban Mutanen Borno. " Hannu ya saka aljuhunsa bai san iya adadin abin da ya ciro ba ya mika mata, ya wuce sai godiya take. Yana barin wurinsu ya haɗe rai kamar bashi ba, ya nufi bangaren Abbanshi. Da sallama ya shiga farlour ya samu Yayunsa maza suna zaune a kasa Abbansu yana kan kujera. Cikin nutsuwa ya zauna bayan yayi sallama. "Ina kwana Abba!" "Lafiya lau, ya aka ji da Jama'a?" "Alhamdulillahi!" Ya fada yana sosa giransa ya kalli Yayunsa cikin dan sake fuska. "Ina kwana ya Abubakar? Ina kwana Ya Umar!" "Lafiya lau Mai girma gwamna!" Murmushi yayi suka su bakiɗayansu. "Aliyu!" Alhaji Muhammad Jadda ya kira sunansa"Na'am Abba!" "Jiya Allah ya nufa an rantsar da kai a matsayin Gwamnan jihar Borno ko?" Cikin nutsuwa ya gyara zaman shi. "Eh Abba." "Masha Allah!" Abban ya furta a hankali, sannan ya ce mishi. "Nasihata gare ka ka ji tsoron Allah, ka tuna abun da ka dauka na kamar matsayin senata ba ne a baya, ba matsayin wakilin shugaban kasa ba ne, Aliyu ka tuna nauyi ne na al'ummar jahar Borno bakiɗaya, ya zaka ji idan Allah ya tsayar da kai karkashin alarshinsa yana tambayarka shin ka sauke nauyin da ya daura maka?" Sake sunkuyar da kai yayi yana jin wani irin yanayi yana rab'arshi. "Aliyu ni mutum ne da nayi aikin gwamnati tun daga matakin karamar hukuma har zuwa matakin federal nayi gwagwarmayar da yan boko da yan siyasa, kuma an waye da ni lafiya Aliyu kada ka shiga rigar gwamnati ta yi abinda zai saka ni jin kunyar kaina da a Mutanen da suka yarda da ni! Aliyu shugabanci yana da matukar wahala, na rike shugabancin jami'o'in kasar nan, na rike shugaban jami'a, na rike shugabancin hukumar zab'e, na zama me baiwa shugaban kasa shawara, nayi aiki da ofishin jakadanci, Alhamdulillahi duk wannan aikin da nayi ban tab'a dukiyar gwamnati da na Al'umma ba, Aliyu kada ka sake wani ya tab'a dukiyar al'umma da saninka ba tare da ka janye shi a tafiyar ka ba. Aliyu zuwa yanzu zaka ga masoya da makiya ka tuna da abokan da kuka tashi tun Yaranta kada duniya ta sa ka manta da su. A cikin hakkinka kayi kyauta kayi sadaka kada ka tab'a hakkin Al'umma, kada ka yarda wani ya baka shawarar gina kanka domin masifa ce idan kayi hakuri, wannan albashin da ake biyanka ya ishe ka kai da iyalinka da sauran dangi. Aliyu yan uwanka da sauran dangi kada don ka samu duniya ka manta da su, Aliyu kada don ka zama wani abu ka manta da kamsuna salawati, babu babban tashin hankali kamar kayi ta wasa da Allah, domin daga nan ne ake fahimtar waye mutum, Aliyu ka rike Allah cikin lamarin ka Allah zai tsaya maka kana nan ko baka nan, babu wanda ya isa cutar da kai face Allah ya rubuta a kaddaranka! Aliyu bakiɗaya shekarunka Arba'in ne cif a duniya kada ka yarda ka lalata alakarka da Allah, domin shine abu mafi muni da tashin hankali. Abubakar Umar ku zama shaidana ba bawa Aliyu Shawara akan rayuwa da mulki, Allah kana ganin na sauke nauyin da yake kaina. Duk abinda yayi na sauke nawa, saura shi ya sauke nauyin da Allah ya daura mishi, Allah ta tayaka riko, ka ga dai yadda kuka yi da Alhaji Mansur Goza!" Yayunsa ma suka mishi nasiha kafin suka shiga taya shi murnar samun karuwa da yayi na haihuwar da aka mishi, abinci aka kawo mishi daga ɓangaren Inna. Anan ya ci yana faɗin. "Gaskiya Inna tayi kokari." "Yawwa ya batun suna ne kayiwa Yaran suna ne?" Gabanshi ne ya fadi yana kallon Abbanshi. "Ban yi musu suna ba, rabona da su tun jiya." Ya zaci fada daga Abbanshi sai ya ga akasin haka ya nuna ma bai damu ba. "Yaushe zamu je a gansu? Ko zasu dawo ne?" Umar ya tambaye shi, "Hmm ban sani ba ko zata zo ayi suna anan ko a can zata yi sunan." "Abba baka ce kome ba?" Inji Ya Abubakar, "da aka yi me?" Ya tambaye su, "Akan matar Tafida, za ayi sunan ne nan ko a can?" "Ya je ya same ta a can su shawararsu." Shiru Tafida yayi domin ya fara shakkar Abbansu nan, don haka ya mike jiki a sanyaye ta nufi bangaren Inna ya shiga ya gaida ita tana karyawa Ita da Yar uwarta. "Tafida kin kira Yaron nan Hadiyya?" Zama yayi yana kallon Hajja Ganaah ya ce mata. "Ban kira ta ba!" "Baki kira Yaron nan Hadiyya ba? Anya Tafida kina tsoron haduwarki da Allah Yaron nan ya haifa miki Yara biyu shi ne ba zaki kira shi amma Tafida zaki ci mutum har buzunsa."
Gajiya yayi da maganar Hajja Ganaah ga Inna taki cewa Uffan, haka ya ƙara saka shi cikin tashin. Muryan Deen yaji yana dariya a tsakar gida Hajiya Kaltuma tana faɗin. "Yanzu fa kuna tarewa a government house ba zamu kara ganin ku ba, sai an cika wasu takardu da sharuddan ko?" Dariya yayi ya ce mata. "Baba ina ba muda inda yafi nan, don haka ki kwantar da hankalinki. Muna nan fa babu inda yallabai zai koma." "Masha Allah, sai gashi an samu karuwa bana nan wallahi daren jiya