Showing 180001 words to 183000 words out of 241571 words
Chapter 61 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
me juyawa yana kallon Ummu yasan akan Ummu ce. "Cewa yayi!" "Nadrah" ya furta a hankali, sai lokacin "Muje!" "Kai magana nake maka!" A hankali ya zuba mishi idanun kafin ya ce mishi. "Ka bani hanya na wuce!" "Waye kai!" "Ina da abin yi!" "She is my wife! Kada ka kara kuskuren da kayi!" "Idan har matar kace bai dace ka barta a wurin ba!" "Matarka? Matarka for my Foot yarinyar da ka saka Tafida? Ummu kake faɗa hahaha matar da ka kama da Abokinka!" "Ke ki iya harshenki! Kina mace kina ihu kamar mahaukaciya, Yaya muje!" "Nadrah, ki kira security su kula da yarinyar can kafin na fito!" "Ok Yaya!" Sannan ya rab'a zai wuce ya ce mishi. "Perfect thanks! Allah ya turo ni ne domin na samu abokiyar gwagwarmaya! Na gode da jin sweet words na ka sake ta, Mahaukaciya meye sunanta?" "Ni ba mahaukaciya ba ce, sunanta Ummu Hadiyya! Ni dai idan kaso ka sace ta ka tafi da ita!" Tas Tafida ya dauke ta da mari, har mu da muke kokarin shiga motar sai da muka tsaya. "Matata ce Ummu Hadiyya, kuma dauke take da cikina wata uku, Uwar Yarana ne Muhammad da Aisha, kada kayi kuskuren shiga tsakaninmu na gaya maka!" "Yaya don Allah mu tafi!" Bai amsawa Tafida ba ya wuce cikin hall din, da sassarfa ya isa wurin motar kafin ya iso na shiga na saka lock na juyar da kaina. Dafa motar yayi da karfi tare da kallona, "Tinah bude min kofar!" Ba musu ta bude ta inda yake bata taɓa ganin shi a irin wannan temper din ba, ya bala'in tsorata. Shiga yayi ya ja murfin motar ya rufe, ai kuwa na fara ƙoƙarin buɗe na tafita. "Kika sake kofar nan ta bude wallahi da kalma daya zan wuce dake Maiduguri gidana, kin san me nake nufi!" Ji nayi cikina yayi wani irin murdawa sai da na rike cikina. "Na kara ganin wani ya kula ki da iddana sai na baki mamaki, na miki adalci ne yasa ban ce zan furta kalmar kome ba, idan kika sake kuwa haka ya kara faruwa!" Wani murmushi yayi yana kallon yadda nake zufa. Abu naji kamar yana zuba a pant dina, na rike rigarshi da ƙarfi. "Zan mutu!" Na furta da karfi ina rike shi gam, "Tinah!" Ya kwala mata kira, bayan ta shiga. "Lafiya!" "Abu na zuba a jikina, mara na cikina Wayyo Allah na Mama!" "What! Ba dai bari zaki yi ba?" Ta fada tana kara da cewa. "Ka taka mota mu wuce asibiti!" Bai san iya adadin gudun da yayi ba, shin gudun ceton cikin ne ko ka ceton rayuwar Ummu, sun isa wani asibitin da yake can gaba da unguwar yan majalisu. Yadda yayi parking zaka fahimci baya cikin nutsuwarshi, ta ciki ya bude inda nake, ina jingine da set ɗin, ya fito ya bude tare da daukata, jini na zuba a jikina kamar an bude pampo. "Oh My God! Tana bleeding out!"ta fada da karfi, ganin takalminta zai bata wahala tuni ta watsar dasu tayi cikin asibitin tana ihu. Haka ya janyo nurse suka rufe akanmu. A hankali nake ganin Tafida bibiyu, kafin ka daina ma fahimtar kome, emergency aka wuce da ni, aka shiga bani taimakon gaggawa. Zama yayi yana kallon Tinah. "Dama bata da lafiya ne?" "Eh amma ni a tunanina laulayi ne!" Ta fada tana kallon kofar. "Allah ya bata lafiya!" "Amin!" Can sai ga nurse sun fito daga cikin ER ɗin, suna zuwa aka cigaba da abin da suke sai dai ana bukatar jini, haka ya tafi aka dibi nashi bayan an gwada jininshi, haka yasa tunda ya kwanta ya huta.
"Doctor! Babu wani cigaba ko zamu gayawa sakatariya ce ta gayawa Yallabai?" Kallonta daya likitan yayi kafin ya ce mata. "Ku kirata tow!" Haka suka yi ta ƙoƙarin ganin Ummu ta farka amma abin ya ki, haka yasa suka kira Sakatariyar wacce ta ce gasu nan zuwa dama an tashi. Kamar minti goma sha biyar suka iso, mamaki ya cike Tinah sai dai bata yi mamaki ba, sauya kaya suka yi daga shi har matar suka shiga ER. "Me ake ciki?" "Doctor bari ne, amma gudan yaki fadowa duk da placenta din ya fita amma shi gudan yaki fadowa har yanzu. Kalaman Tafida ne yake yawo akanshi. _Matata ce da cikina_ bai gama nazarin kalaman ba maganar Sa'adiyya ya kara fado mishi. *Babu aure a tsakaninku tunda zarginta kake me zaka yi da Matar da abokanka ya kwanta da ita* murmushi yayi ya amshi kayan aikin da allurai, sannan ya yi duk abin da ake ya kalli Nadrah. "Ki mata aikin !" "Why Yaya?" "Kawai ki mata!" A hankali ta koma gaban Ummu ta zauna ta haska gabanshi sannan ya ce mata. "Sauki wancan!" Ya dauka tana jiranshi. "Ki saka mata a hankali, sai ya shiga zaki bude shi!" "Ok!" Haka ta dinga bin abinda yake faɗa, tana yin yadda ya ce har aka samu nasarar fitar da dan tayin, ya amsa a hannunta. "So cute! It's baby girl!" Ya fada idanunshi na cika da kwalla, shi ko b'arin ma ayi a gidanshi Allah bai nufa ba, shi yasa duk lokacin da aka samu matsalar b'ari shi yake aikin domin Allah ya jarabce shi da son haihuwa. Haka ya gama goge jikin dan tayin, sannan ya amshi wani farin kyalle aka nad'e shi, ya saka a cikin wani karamin kwali. Ya fito sai lokacin ya ga Tafida yana rike da kanshi. "Gentle Man!" Ya d'ago kai suka haɗa idanun suna kallon juna. "Gashi a kai ta a bisineta, Allah yasa me ceto ce! Uwar tana bukatar hutu!" Ya fadi haka yana juyawa. "Kai uban waye ya baka damar kallon Matata!" "Matar mai rabo dai! Ai wannan matar ta gaya min kun rabu." Ya fada yana murmushi, sannan ya juya. "Kai!" "Shiiii! Muna da marasa lafiya please ka iya sarrafa kanka mana!" Ya fada mishi yana murmushi. Irin na cusa haushin nan. "Ki nuna min inda take ba zata zauna a asibitin nan ba!" "Matsalata da kai baka da hakuri sam baka iya bin kome gentle ba, babu inda Ummu zata. Kai yanzu abin da kake shi zai saka Ummu ta fahimce ka? Kasan yadda zargi yake destroying aure ai? Sannan kana ta kokarin kara cusa mata kiyayyarka idan ka yarda da kanka ka yarda da matsayinka no need kayi ta shirme haka, idan Ummu taka ce har abada babu wanda zai burge ta sai kai, idan ba taka ba ce kana ji kana gani zata tafi ta shimfida rayuwarta da wani don Allah ka iya sarrafa kanka!" Ta fada tana jin haushi kamar ta mare shi, can Nadrah ta fito tana faɗin. "Mss ko zaki je ku yi magana da Doctor!" "Ok thank you!" Ta wuce tana kallon Tafida da yake ta huci, tab'e baki tayi tana cigaba da tafiyarta, Office din doctor din ta nufa da tambaya ta isa office din duk da dare ne amma yadda ake gudanar da ayyuka a cikin asibitin zaka dauka rana ce. Knocking tayi tana faɗin. "Excuse me! Zan iya shigowa?" "Yes!" Ya fada daga cikin office din. "Sannu da aiki!" Ta fada tana zama, "yawwa!" Ya fada shima yana aikin shi. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu. "Kayi hakuri da abin da ya faru dazun!" Murmushi yayi sai da dimple point dinsa suka lubba. "Ba kome!" Ya cigaba da aikin kafin ya ce mata. "Bugun zuciyar Babyn ya daina bugawa tun safe which mean, tun safe ya mutu ina ga da zaki tambaye ta sau nawa ta ga discharge kafin faruwar haka? Sannan akwai damuwa da gajiya sun taimakawa cikin wurin lalacewa, sai ban san alakar da yake tsakaninku ba, but zuciyarta yana kumbura!" "Excuse me!" Ya fito ta hango Tafida da yake tsaye har zuwa lokacin. Kiranshi tayi da hannu, ya zo tana tsaye suka shiga cikin office din. "Mu shiga!" "Ba inda xan shiga!" "Kayi karya kenan!" Ta fada tana cikin fushi da b'acin rai, ta ja hannunshi har cikin office din, kallon juna suka yi kafin ya cigaba da aikinsa. "Doctor please ka mana bayanin daga farko!" Nan yayi musu bayani har inda ya tsaya ya juya musu kan computer dinshi yana nuna musu. "Wannan shine zuciyarta, likitocin mu na bangaren zuciya suka dauki wannan hoton, domin mun ga yadda jininta yake hawa babu control, mun zata ko gishiri ne yayi yawa a jininta sai muka ga ba haka bane, bugun zuciyarta ne yake bugawa sama da kima, shi yasa basu wanke mata cikin ba sai da nazo domin gujewa hatsari, ban san kome akan ciwon zuciya ba amma ina ga ya kamata ku kyaleta idan ba haka ba zaa iya rasata." Ya datse kalman bakinshi bawai don ya gama ba, sai dai abin da zai fada zai iya fusata Tafida sai ya share yana kallon yadda yayi shiru. "kana nufin idan aka daina takura mata zata samu lafiya?" Gyada kai yayi yana faɗin. "Akwai abinda take gani wnada yake daga mata hankali, include Kai kanka domin matarka ta gaya min baku tare why not ka rabu da ita idan kayi haka zata samu lafiya!" "Eh na rabu da ita ka aure ta." Murmushi yayi yana. "A yadda nake hango kishinta a idanunka, tabbas zaka iya warewa ka yi dambe don na ga kamar dan dambe ne kai. A lokacin da aka kawo ta nurse biyu da suke kanta sun ji tana cewa. Ni banci amanar aurenka ba, ka zarge ni Allah ya gani ina sonka amma zan hakura da kai ba don naso ba! Haka yana nufin idan da zaka gyara kuskurenka zaku koma rayuwarku na baya, sai dai ita zuciyar mace tana iya rike abu me kyau da mara kyau, kayi kokarin bata lokaci sosai ba wata daya ba, ba biyu ba, ba uku ba kai ba shekara ba ka bata shekaru biyar har zuwa goma, sannan ka hakura da wannan zafin kan. Kayi ƙoƙarin ganin ka dauke kai akanta yadda zata samu zuciyarta ya huta. Amma ka sani matukar ka cigaba da tafiyar da ita kana barin wani abu yana faruwa a tsakaninku zaka kashe ta ne. Mata dayawa suna mutuwa da tarin takaici da bakinciki, saboda damuwar da tayi yawa a ransu. Idan da zaka bata damar nutsuwa da kanta zata amshi kaddaranta, ko na bata magani matukar zaka na tinzura ta ba zata warke ba Please domin yaran da suke tsakaninku ka barta ta huta!" Gyad'a kai yake yana ji kamar yayi hauka ne ko kuka ne oho, a hankali ya mikawa Tinah takardan magani. "Ku saya mata zuwa gobe da yamma idan ta ji sauki zamu iya sallamarta. Wannan maganinta ne! Sannan wannan takardan na wani Doctor Amjad daga lagos yake zuwa Maiduguri ganin masu irin matsalarta, ba kowa nake bawa katinsa ba, sai wanda na ga ya dace, yana babban asibitin Maiduguri ne yana zuwa duk karshen wata." Gyada kai Tinah tayi tana . "Zata tafi ganinshi kenan?" "Eh saboda ya ga yadda zuciyar take ne, kuma zai taimaka mata kwarai wurin bata drugs masu kyau da kula da lafiyarta sai dai kuma zata yi hakuri sosai domin!" Ya kalli Tafida kafin ya yi Murmushi. "Kawai shi kenan zata ganshi kuma xan mishi bayani!" "Mun gode!" Tinah ta fada tana, murmushi suka fito daga office din, wayarshi ya dauka yayi ta kiran Layin da ya rubuta *worst than death Dr* tsaki yayi bai dauka ba ya tura mishi sako kome sannan ya kashe wayar shima yana nazarin matsalar Ummu. Idan har ya fahimci maganar Sa'adiyya tabbas akwai soyayya da yayi had'aka da kishi, sannan gajen hakurin Tafida, idan bai ya kara fahimtar maganar Saadiya, da sunanshi da ta fada ya gano Gwamnan Maiduguri ne, haka yasa ya tuna rigimar da ake ta gulmar matar gwamna da abokinsa sun aci amanarshi idan har Tafida ne da Ummu tabbas an zalince ta, sai duk yaji tausayi Ummu ya cika mishi zuciya amma baya ganin zai samu damar shiga domin Allah bai bashi haihuwa ba, amma baya jin zai iya raba soyayyar da ya hango a idanun Tafida. Sannan ko bai raba su ba yadda Ummu take maganar tana sonshi zai matukar wahala ta karbi soyayyar wani da namiji cikin sauki da dad'i, Allah ya daidaitasu kawai.
Kudi Tinah ta biya da fadar sunan Ummu da kome aka cika mata file, Tafida ya kalleta cikin sanyin murya ya ce mata. "Nasan na lalata kome, bana son ta kara ganina ciwon ya zauna a jikinta, don Allah ki kula da ita, idan da hali ki zama shadow dina, yadda xan na sanin kome akanta ba sai na nime ta ba, please Tinah ki min wannan aikin Please girgiza kai Tinah tayi tana faɗin. "amma me yasa ka bari kome ya tafi a haka!" "Saboda tana bukatar hutawa, na cutar da ita amma ina son ta dawo gare ni ba tare da alfarma ko tausayi da jin kai ba, ta dawo don ni don ra'ayinta i know Ummu she love me har yau, amma bana son soyayyar ta cutar da ita ne, akwai abubuwan da idan tana tare da ni ba zan iya, amma idan ta nisance ni maybe zan iya don Allah ki kula da lta!" "Zan yi kokarin haka amma kasan mun yi nisa bai zama dole na san wani abu ba." "Na sani yadda ta sake da ke bata sake da kowa haka ba, zaki fini jin wani abu a tare da ita!" Haka yayi ta rokon Tinah da ta zauna da Ummu. Karshe babu yadda ta iya dole ta shiga lamarin Ummu ko don dawo da martabar ta na baya, dole ta taimaka.mata domin sanin ciwon kanta, ita ba zata tsayawa Aliyu ba domin kuwa yayi kuskure yanke hukunci cikin gaggawa zata tsayawa Ummu Hadiyya ne ta zama mutum itama kamar yadda take ganin son nasara a rayuwarta zata yi kokarin ganin haka ya faru, tana kallonshi ya shiga motar da aka zo daukar shi ya bar asibitin.
"Aliyu kuskurenka zaka girba, idan har kai ne soyayyar Ummu tow ba makawa zaka zama ajalin Ummu, zan tsayawa Ummu ba zan kara barin kayi nasarar nakasa mata zuciya ba!" Ta koma cikin asibitin ER din ta isa ta ga Babu Ummu a wurin, wata nurse ta ga tafito daga dakin ta tambaye ta. "Don ina ina mara lafiya nan da tayi b'ari?" "Tana can dakin an tura ta can." "Ok na gode!" Ta nufi dakin, ta tura. Ta samu tana ta barci hankalinta kwance.
***
Tafida
A bakin kofar masaukin ya sami Saadiya tana dariya, ganinshi kawai da tayi duk jikinshi ya b'aci da jini ta ce mishi. "Allah yasa ba kisa ya fara ba!" Shiga cikin dakin yayi ta bashi, kamar dama jira yake ta shiga ya saka ki. Yayi ta marinta domin ranshi yayi bala'in b'aci, sai da ya mata mari ya kai sau goma har sai da hancinta ya fara zubar da jini, cikin kukan wahala ta ce mishi. "Don Allah kada ka lalata min fuska, kayi hakuri wallahi zan fita a rayuwarka na rantse da Allah ka kyale ni don Allah!" "Ba zaki fita cikin sauki ba, kamar yadda kika iya cin mutuncina da na ummu a gaban Jama'a haka nake fatan na ci naki. Kazama jaka kin zata zan cigaba da kwanciya da ke ne? Wanda nayi na Allah ya yafe min, yanzu ma ina tare dake ne domin biyan buƙatar kaina, idan na gama zan baki mamaki. Kamar yadda kika kunyata min Ummu sai na saka uwarki ta ji me yasa ta haife ki jaka mara tarbiyya!" Marin da yayi mata yasa mata wani irin tsoron shi haka yasa ta koma gefe can ta takure. "Zan cigaba da azabtar dake yadda zaki na rokona na sake ki, amma ina kin haka domin sai na saka ki cin kashin da kika yi, kun yi kuskure ke da Mahmoud da Kaltuma da Hamza Goza na shiga rayuwarmu da Ummu kuka cusa min kiyayyar Aurena........!
What?😲 Wasa farin girki me kuka fahimta? Shin me zai faru gaba...... Something out like 🔥🔥🔥
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_GYARA SHINE MACE_*
*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327
*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,
Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍
Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍
Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃
Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya