Showing 162001 words to 165000 words out of 241571 words

Chapter 55 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14726

mata da takardanta don tana rufa mishi asiri. Ai kuwa Mijin ya ce bai san wannan zancen ba ba zata ci mutuncin Uwarshi ya kyaleta ba, ya sake ta tare da korata sannan ya kwace yar shi karamar. Ya korota, tunda ta dawo kullum suna kasuwa su hudu, don sun dan sadiya ba mutunci ne da ita ba, kiran Maman Ummu kuwa Hajiya bata son shirin Yaranta akan Ummu ba ita dai don jikokinta tayi kiran amma kuma ta lura Maman Ummu bata da sauki akan lamarinmu, kuma ba don ya tafi da ita ba da haka zasu cutar da Ummu, hawayen da ya zubo mata ta share. "Ina ga ba sai an kai wannan case din ga hukuma ba, matsalar cikin gida ne a magance shi a anan!" Yan sanda suka koma bawa Abba hakuri, a nan kuwa Tafida ya kira ya kai sau goma. Lokacin da suka nace da buga kofar gidan Hajiya ta ce musu. "Uwarta tazo ta dauke ta."
Yadda Abba ya fusata yasa ta fadi abinda ya faru, tana tsoron kada ya kore ta a gidan Tafida bayan bata da inda ya fi nan, "ina baki shawara ki bar gidan nan a mutunce idan ba haka ba wata rana abinda kike ganin zaki iya tunkarar shi, shine zai tunkare ki, hankalinku ya kwanta Ummu ta bar dan uwanku, sai ku zuba ruwa ki sha, amma ku sani daga yau na cire ku cikin Yayana!" Ya kalli matar Uwar da Abubakar. "Ku kuma mazajenku zasu san yadda zasu yi da ku!" Daga haka ya juya zai fita, Hajiya ya ce mishi. "Kayi wani abu Ummu ta dawo idan ya dawo bata nan ban san yadda xan fuskance shi ba don Allah!" Murmushi yayi irin na manya ya ce mata. "Tafida kike so ba? Uwarta tayi namijin kokari da ta dauke Yarta kafin a cutar mata da ita, ni abin tambayar anan shin dama kin shiga jikinta ne domin ta janyo miki Tafida a gare ki ne ko? Domin kuwa ban da haka babu yadda za ayi ku hada kai da Yaranki da surakanki zaku kashe yar mutane cikin jikinta da Yaranta. In sha Allah Ummu kuka saka a gaba Allah sai ya saka mata in sha Allah!" Ya fada yana barin gidan. Duk sun ji haushin Abba saboda Ummu zai kai su wurin yan sanda.
**
Tafiyar Tafida Sudan, tare da Ammah da Matar Deen sai Jalilah aka yi tafiyar yaso tafiya da Ummu amma ta bata mishi rai, akan me zata saka baki idan yana magana ta bala'in rena shi. Haka yasa ko ta tafi da ita, zai ta jin zafinta ne sai dai tun da ya bar gida ya rasa nutsuwarsa. Kuma ya kasa sake jiki su tattauna da Deen, ya gane halin da Tafida yake ciki, karshe sai ya rasa yadda zai mishi bayani akan Mahmoud, ya bar zancen tare da ganin wata rana zai gaya mishi. Sannan ya gayawa Tafida kudirinsa don yasan matukar yana tare da Tafida Mahmoud zai ta bibiyarshi. Haka suka ta shige da fice har Deen ya samu aikin koyarwa a kasar. Deen bai tab'a boyewa Tafida abu ba, sai wannan karon sai dai ya mishi hannunka mai sanda ya ce mishi. "Kada ka bari kowa yasan Ummu ce rauninka domin akwai masu jiran haka su yi amfani da rauninka! Sannan bana nan ka saka idanun akan dukiyar al'umma da ka dankawa Mahmoud. Kada ka sake ko da wasa ka barwa Mahmoud Ummu, ka saka idanu akan gidanka Ummu tana buƙatarka kuma tana buƙatar kulawarka, Tafida ka saka idanun akan Ummu don gaskiya wannan karon idan ka bata rawanka da tsalle ba zan iya saka baki ba." "Tow ya zanyi?" "Ya zaka yi? Dole kowa ya bar maka gidanka Hajiya kuwa kayi hakuri da ita ba kai kaɗai ta haifa ba dole zaka na ganin irin wannan lamarin, musamman da su Rukayya basu da lissafi!" Kamar zai fashe da kuka haka yake kallon Deen, ajiyar zuciya ya sauke yana jin kamar ya fasa ihu, haka suka rabu satin shi daya ya kira Number Ummu ya kai sau nawa kullum bata dauka, asalima sai yake ji kamar bata raye ne an boye shi, babu shiri ya bar sudan, ranar da ya dawo kai tsaye gida ya ya ce. Yana shiga ya ga window bangarenta a fashe, jikinshi ne ya fara bashi da matsala a hankali ya isa bangaren ya tab'a kofar yaji a rufe, "Aunty Baby!" Ya kira ta kamar yadda kowa ke kiranta, yaji shiru juyawa yayi yaga Rukayya ta fito hannunta ɗauke da manyan jakanka leda, hadiye yawu yayi ya kalleta daga sama har kasa. "Meye ya kawo ki gidana?" "Hajiya nazo dubawa bata da lafiya!" A hankali ya nufi bangaren Hajiya, ita kan da gudu ta bar gidan bayan ta kwashi kayan abinci da wasu kayan auren da suke hadawa. Yana shiga babu kowa a parlour. Ya nufi dakin Hajiya tun a bakin kofar dakin yaji muryan Fanna tana kuka. "Eh Allah bai bani haihuwa ba, kuma bawai baya sona ba ne, ya daura min ƙaddaran aure ke da yake sonki ai kin kasa zama a gidanki, sannan kin hana matar zama a gidan kin ga ashe bani da laifi, kuma da kike cewa kwadayi ya kawo ni, na fi karfin kwadayi gidan Tafida, zan bar muku gidan ku ci yadda ranku yake so hakkin Ummu sai ya tambaye ku!" Ta fada tare da bude kofar zata fita tana kuka, Hajiya tana ganin abin da suke amma ta kasa magana, kwana biyu nan da suke gidan abincinta da take ciki saboda diabetes dinta, Maryam ta hana sai dai ayi daya wai ai tuna tana shan magani zata iya cin kome. Daurewa take amma sugarta kasa yake a madadin yayi sama, "Maryam! Kada ku kore min Fanna ita take taimaka min da wasu abubuwan, Ummu bata nan balle naji sauki a gare ta. Idan kuma kuna son na mutu ne tow shi kenan!" "Hajiya ba fa abin da zai same ki domin Ummu asiri tayi miki, kuma ba zan yi kaffara ba tayi haka ne don rabamu da ke da Tafida." Bata yi magana ba, kallon juna Fanna da Tafida suka yi ya juya abinsa yana jin kamar yayi kuskure na yarda da Hajiya zata dawo gare shi. Lokacin da suka fito waje ya ce mata. "Ina Ummu?" Sunkuyar da kai Fanna tayi tana share kwalla da yake zuba mata. "Ina Ummuna?" "Ummu ta tafi mahaifiyarta ta tafi da ita!" Lumshe idanun yayi yana faɗin. "Na gode Fanna! Yanzu ki tafi gidan Abba ki zauna a can kafin ta dawo domin dawainiyyar zai mata yawa " "Na gode amma gaskiya ban da kai da yau na koma gida na gaji da halin Maryam Hajiya bata iya magana, sannan bata da lafiya. Gashi ba a gama abinci akan lokaci ga ciwonta yana kokarin tashi, don Allah ka kula da ita." " shi kenan!" Haka ya saka aka kai Fanna gidan Abba, bangaren shi ya nufa yayi kura alamar Ummu bata nan kenan, hadiye b'acin rai yayi ya shiga dakinshi ya ga zauna shiru, ya rasa me zai yi a hankali yake sauke ajiyar zuciya, bakiɗaya kome ya tsaya mishi ya fahimci yanzu Ummu gata ce a rayuwarshi sannan rashinta kamar asara ce a tare da shi. Haka yasa yayi ta nazari, ban daki ya shiga yayi wanka da alola sannan ya dawo , daki ya dauki kayanshi ya saka, kafin ya drower din da ya ajiye mata kuɗi ko tana da bukata, ya samu bata tab'a kome ba, dakinta ya nufa ta rubuta mishi sako ta ajiye a saman mirror.
_Ina son zama da kai amma igiyar ƙaddara tana ta walagigi damu! Ina son zama da kai ina son kasancewa da kai! Amma danginka sune rike da makomar aurenmu! Kayi wani abu kafin dangina su fusata don Allah_
*~MatarAliyu~*
Rike takardan yayi kamar hannun Ummu yake rike da ita, haka yasa yaji hankalinsa yayi bala'in tashi.
**
*Ummu*
Har ga Allah na saka rai Tafida zai zo gare ni, haka yasa koda muka sauka a dakin Mamawo, ban yarda da na sake jikina da gidan ba, don gani nake Tafida zai iya zuwa a kwana na daya amma ina sai gashi yau ina kwana na hudu, duk da kome aka min, sannan Yarana takas Babana ya ɗaukar min me kula da su wata babbar mace ce, bata tab'a haihuwa ba tana da kirki. Ni kuma aka bar ni da laulayin da na fara, me matukar wahala. Kana ganina kasan na ƙaramin wahala nake sha ba, har gida Baba ya kira Sagir shi yake zuwa ya duba ni, ranar da na cika kwana biyar na kalle shi. "Bro baka ji labarin ya dawo ba ne?" Kura min idanun yayi, "Ummu ya dawo jiya!" "Me yasa yaki zuwa duba ni? Ko ya daina sona ne?" "Me yasa kike fadar haka?" Ya jefa min tambayar da ya sani naji kamar zan yi kuka. "Nasan idan har ya dawo ya ga bana nan zai ta kira na, ni ban ma san inda na ajiye waya ta ba." Wani irin tausayi ne ya rufe shi . "Ummu Mijinki yana sonki kuma zai dawo gare ki!" "Ina jin tsoron kada ya rabu da ni ne, ina jin tsoro kada yace ba zai zauna da ni ba ne, Yaran mu uku da shi. Idan na bar mishi yaran zai kula da su amma bai da lokacin zaman gida. Bakiɗaya lokacinsa na al'umma ce " murmushi yayi yana faɗin. "idan na gaya miki gaskiya zaki yarda?" Gyada kai nayi ya sakar min murmushi yana faɗin. "yana sonki kuma yana can yana niman kwarin gwiwa da zai nime ki, Ummu Hadiyya baki cikin matan da mazansu zasu daina so domin kina da kyau da hali me sanyi wanda duk wanda ya zauna dake zai fahimci haka!" "Na gode sosai!" Gyada kai nayi ina faɗin. "me yasa danginsa basu sona?" Murmushi yayi yana faɗin. "Ra'ayinsu ne su so ki ko su ki. Sannan wayarki tana hannun Babanmu, idan kika kwantar da hankalinki zai baki!"
Godiya nayi masa sannan ya fita, ina zaune a wurin cikin damuwa.
**
Tafida bai ce musu cikanku ba, yana dawowa ya fuskanci aikinsa, yadda zaka san yana cike da b'acin rai, mutumin nan da kanshi yake bin aikin da yabawa yan kwangila, yana dubawa. Sannan ya saka aka kawo mishi wata motar da haɗaka mata karfe a gabanta, idan ya bada aikin gini, zuwa yake da motar ya daki ginin yana zubewa zai saka dan kwangila sai ya biya kudin da ya bada sannan ya cigaba da aiki. Wasa wasa Tafida ya tashi hankalin ma'aikata, domin sai baku tsammanin zuwan shi ba sai a ganshi, an dakatar da ma'aikata dayawa, ya kuma kori wasu musamman idan ya fahimci yadda kake aikinka. Sai gashi kowa ya shiga hankalinsa, a wannan lokacin hadda Mahmoud sai da Tafida ya zabga mishi mari a gaban jama'a, sakamakon kama shi da yayi yana lalata da wata ma'ikaciya, wacce yar bautar ƙasa ce da ta zo daga Edo, mari uku yayi mishi sai ya ga yadda Mahmoud yake mishi wani irin kallon reni, cikin fusata ya fara ɓalle botirin rigarshi na hannu da cire agogon hannunshi. Yana faɗin "kutumar Uba Ni kakewa wannan kallon?" "Anyi maka lusari kawai kanata hauka a gari, bayan Matarka da kake haukar akanta cin amanarka take da Abokin sirrinka, me zai saka na maka kallon mutumin da zai bani tsoro, idan baka yarda ba ga shi nan!" Ya nufi laptop dinshi ya danna sai ga hoton Ummu tsira... Daukar laptop din Tafida yayi wurgi da shi da ya fashe, cikin bala'in fushi da mugun kishi, Tafida ya rufe shi da mugun duka kamar zai kashe shi, yana hango Ummu ba kaya. Sai da aka janye shi daga jikin Mahmoud don ya kasa ko motsi, sannan ya ce. "Kun gani ne?" "A'a!" Huci yake kafin ya ce musu.." an kawo min report din cin hanci a cikin ma'aikatan nan, ku turawa EFCC." Ya juya yana kallon Mahmoud. "Ka soke ni ta baya, kasan da haka ka cigaba da kallona." Ya kai mishi naushi da kafa. "Deen kashe shi zan yi, itama Ummu Hadiyya na b da Allah." Mahmoud da ya farfaɗo yana dariya ya ce mishi. "Kana sake ta shi zai aureta, waye ya sani ko Yaran da kuke kira naku, na sune su biyun!". Sake kai mishi naushi yayi sai da ya sake suma. Kwashe kayanshi yayi ya bar office din. Yana shiga mota ya kifa kanshi yana jin kamar zai mutu. "Kai ni gidan Abba!" Haka suka wuce sauran motar suna bin shi, lokacin da ya isa rikice ya nufi bangaren Abba, ya zauna a gabanshi yana me fashewa da kuka, yana jin kamar zai mutu saboda zafin kishi. "Abba kai ka bani Ummu, Abba na dawo maka da ita, amma ka rubuta ka ajiye idan nayi idanun biyu da Safiyyudeen zan kashi, ita kuwa Ummu Haddiya Muhammad Kabir, na sake ta saki daya na yafe mata abin da tayi min kada ka ce zaka.min dole domin zan iya mutuwa. Zan mutu kada ka min dole!" Ya fada yana kuka. "Abba taya abokaina zasu ci amanata? Me nayiwa Deen zai kebe da matar sunnah ta..." Tass Abba ya wanke shi da mari, ya kara marin shi ya ce mishi. "Saki ya tabbata ka rabu da ita ko?" Murmushi yayi mishi ya dauki wayarshi ya kira number Malam Zailani ya kira ya gaya mishi Aliyu ya sake Ummu, sun jima yana magana. Kafin ya bashi shawara guda daya sannan ya ce mishi. "Aiki yana gabanka, ka ɗauketa tayi nisa da inda yake a yanxu zai kara gane faidarta, ka kyale shi da sauran yanzu zaka gane waye shi da kyau sannan ka gayawa Deen, amma yanzu Mahmoud zai san ya tab'a masu tsada."


Kallon Tafida Abba yayi, ya kashe wayar ya kuma kiran Deen ya ce mishi. "Allah ya maka albarka, na gode sosai sai dai Tafida ya sake Ummu, burin danginsa ya cika burin Mahmoud ya cika, sauran bayanin zan turo maka ta email zan maka bayanin sauran aikin da baka rasa min ba!" Sannan ya sakewa Tafida murmushi ya ce mishi. "Sati me zuwa za a daura maka aure da Matan da danginka suke so, sannan Sa'adiyya zata dawo gyara mata bangaren ta, Tafida idan ka sake ka rabu da sauran matanka baka da hujja sai na tsamme hannuna akan. B'ace min jahili, dabba wanda sauran dabbobin suka fishi hankali ina sha Allah Ummu tayi maka nisa, da nasan cewa saboda Mahmoud zaka sake Ummu da na saka an baka guba kaci ka mutu, wanda baya kishin kasa idan Ummu ta ci amanarka kai me rufa mata asiri. Ko don Yaranka!" "Abba ya ce min ba Yarana bane?" Tasss Abba ya kara kifa mishi mari. "Fita min a gida, kafin na fusata na tsine maka, fita kafin na saka maka baki a kanka da rayuwarka!"
"Abba me kake boye min!" "Fita kafin nayi maka maganar da zai dame ka." Fita yayi yana kuka wiwi, ya rasa me ya aikata, bai tab'a zama yana kuka haka ba sai yau da ya sake Ummu.


Yana fita Abba ya Baban Ummu, bayan sun gaisa ya ce mishi. "Gobe ina hanya zaka bani y'ata fa!" "Alhaji Muhammad Jadda yarka ce, sagir zai kawo maka ita yana gari."
"Na gode zata tafi Sudan ce ta haihu a can!.kayi hakuri Aliyu kasan!" Dariya Baban Ummu yayi yana faɗin. "Allah sarki ai dukkanmu, mun san haka Allah ya bawa zaman lafiya!"
Haka suka rabu, bayan sun kashe wayar ya kira Deen ya gaya mish gata nan zuwa idan ya sake ya bari Tafida ya san tana wurinshi zai fusata. Sannan ya kira Malam Zailani da yake aiki kamar ba zai dauki wayar ba ya dauka. "Ina aikin wannan ublishin ne!"
"A'a kyale shi, kyale shi Allah yana ganinsa, Ubangiji zai mata sakayya kada ka damu lokaci na zuwa, mu barshi da Allah, Malam kai kake gaya min haka yau kai zaka fusata haka"


"Raina ne ya b'aci!"
"Ka kyale shi, Allah yasa Yaron bai boye mana kome ba!"
Da wannan suka yi sallama


**
Ran malam Zailani ya b'aci kwarai ba a tab'a cin mutuncinsa irin wannan ba, tashin wani almajiransa yayi ya dauko kayan aikinsa bai cika aiki irin haka ba, sai idan an yi abin da ya fusata shi. Yau saboda Tafida da Ummu zai yi shi. Wata allon azurfa ce, ya fara rubutun yasin yana yi yana tari, yau Mahmoud ya takalo bala'i."
Suna gama waya da Alhaji hawaye ya zuba mishi, haka yayi ta zubar da Hawaye ya kara kiran Abba ya ce mishi. "Kada ka amshi sakin ka ɗauketa kafin labarin yaje kunnenta."
***
Zazzaɓi ne ya rufe ni, kamar zan suma duk da na sha magani, ina kwance Babana ya shigo ya ce na shirya na tafi da sagir. Haka na shirya muka bar gidan, ina jin kewar Mamawo, muna isa airport ya kai ni, a daren muka wuce Kano, daga can aka wuce da Ni khatum na sudan, da asuba muka isa Deen ne ya zo daukata, yana me ɗaukar Mufidah, yana kauda kanshi hawaye na zuba mishi, "kuka kake Yayana? Tafida ya juya min ko saboda danginsa ko?" Sai ya rasa bakin da zai min magana, taya zai gaya Ummu an sake ta.


A can Maiduguri labarin ya karad'e ko ina, da har ya fado gidan Mama da safe tana aiki Ummu ta shiga tana murmushi ta ce mata. "Hadiza hala baki ji labarin, abin da ya faru ba Mijin Ummu ya kamata da laifin cin amanarshi!" Sake abin hannunta tayi tare da riƙe kirjinta....


🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76






🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾


*_GYARA SHINE MACE_*


*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login