Showing 141001 words to 144000 words out of 241571 words

Chapter 48 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14735

mishi ba yayi ya kawo wacce zata wanke mishi gwamnatinsa duk me sauki ne a gare ni!"


"Ayya Rukyy ashe islamiyya tayi! Shi yasa nata san go da come ba!" Suka kwashe da dariya. Maganar yayi min zafi yau daya naji me yasa naki mai da hankali akan boko ma ne? "Eh islamiyya nayi shi yasa aka samu tazaran dabi'a tsakani na daku! Sannan Allah ya taimaka dukkanku babu wacce boko ya mata rana domin kuna zaune ne sai abin da aka baku gara ni ina da abinyi yi." Na fada ina dariya suma su ji yadda nake ji yan iska kawai sun dame ni. Ai kuwa suka fusata. Hajiya da take kitchen tace min. "Sannu Ummu ai kin yi kokarin kula dabbobi nan, na gaya musu gaskiya amma sunki ji su meye bokon ya musu rana ina kowacce biyo ki take tana cin arzikin yar islamiyya! Sannan daga Maryam har rukayyan babu wacce tayi makarantar gaba da secondry, suma ai daga secondry aka aurar dasu ha gara ke kin yi high islam!" Daga haka suka yi shiru basu kara magana ba, na godewa Allah da ya bani Hajiya a gefena idan ba haka ba takaici ya ishe ni. Haka suka gama iskancinsu har suka bar gidan.
*Asiyah*
Tunda suka bar gidan take cikin farinciki domin ita burinta na farko ya cika, ta bawa Ummu maganin kuma ta rike, sannan tsakanin Ummu da Saadiya babu shiri haka zai bata damar shiga jikin Ummu kafin ta samu biyan buƙatarta. Amma wani irin sauri aka yi har suka dawo ga juna. Har aka kawo su gida bata kula hiransu ba, tana jin su kamar zasu kashe Ummu a ranta tayi murmushi. Bayan sun sauka Nabilah ta ce mata. "ban san me Aunty Baby ta tsare musu ba suka tsaneta amma koma meye ai duk wanda zai zauna da naka ya maka kome kawai suna da wani irin ra'ayi ne!" "Ayya Allah ya daidaitasu!" Ta fada tana murmushi don ita nata shirin ya ci Uban na kowa.


Tunda suka bar gidan Asiyah ta sake kama kafa da Inna yadda take mata yasa Inna take tausayinta, sannan a wurin Nabilah ta amshi number Ummu don ranar tana jin ta fada mata numberta. Haka yasa yasa ta jira itama ta amsa a wurin Nabilah. Bata taɓa gwada kira ba, don haka da yamma bayan sallah la'asar kwana biyu da dawowa ta kira Ummu, bayan sun gaisa ta ce mata. "Aunty Baby Asiyah ce!" "Ayya sannu Asiyah ya kike?" "Lafiya Lau, Aunty Ina Mufid Dina!" "Suna lafiya!" "Allah sarki na yi missing dinsa na kwana biyun nan aunty xan zo ki bani aron shi." "Wai babu ruwana Daadi zaki tambaya don baya bari a fita da su!" "Ayya Aunty Baby ki mishi magana mana!" "Sai dai ko idan ya dawo na mishi magana!" "Tow shi kenan,"


Haka Asiyah take kiran Ummu su gaisa sannan ta tambaye ta Yaran, har ranar da ta ga labarai Tafida ya dawo. Haka yasa ta kudiri aniyar ranar Lahadi da yamma ta kira Ummu. Bayan sun gaisa ta ce mata. "Aunty Baby zan zo an jima ganinsu Mufid!" "Tow shi kenan!" Murmushi tayi ta dauki turaren sannan ta goga, kafin ta yiwa Inna sallama ta bar gidan.
***
*Ummu*
Ance mai d'a wawa ne tow ya yarda a kaina musamman yadda Asiyah ta gama zagaye ni da kaunar Yarana, a hankali nake hango hankalin yarinyar, tausayinta da ban san yaushe na fara ji ba, ya cika min raina. Haka tayi ta kirana tana nuna min kaunar Yarana, amma ban yi wani abu akai ba sai dai ina matukar jin dadin haka.
Kaina a saman cinyarshi, ya daka laptop a gefen kujeran da yake zaune yana aiki. "Ya naga yanayinki ya sauya?" "Daadi yarinyar nan tana da mutunci!" "Wacce kenan?" "Asiyah Yola!" Daure fuska yayi yana me aikinsa. "Daadi baka ce kome ba?" "Tow me kike tsammani nace dama? Don tana da kirki bari na fara rawa da girgiza Ummu ta yabi wata a gabana!" "Wuuh" na fada ina tashi zaune. "Allah ya baka hakuri, amma ya rayuwarka da haka?" Shafa kaina yayi yana faɗin. "Yarinyar sona take, ni kuma nayi rejecting dinta, idan kina son karamin matsala sai na aurota!" Jan hancinsa nayi nace mishi. "Kai da bakinka ka gaya min ai ba don ni daya aka halicce ka ba, kai mijin mace hudu ne idan ka manta na tuna maka idan baka auri Asiyah ba zaka auro wata ai, don haka ni ban ga wani abu na laifi ba don mutum yana son Yaranka!" Na fada ina tura baki, ni har ga Allah na fada wallahi ban fada da wata manufa ba, haka yasa shima ya bar zancen. Can kuwa sai ga Nana Asma'u ta buga kofar da sallama. "Waalaikumunsalam!" "Mami kizo kin yi bakuwa!" "Tow gani nan zuwa!" Na fada ina mikewa, mai da ni yayi na zauna yana min wani irin kallo me tattare da zautarwa. "Amma kasan!" Janyo ni jikinshi yayi yana faɗin. "Hm! Wato don kin gaji dani ana cewa ga bakuwa shine kika tashi zubur!" "Me xan maka kuma dai? Me kake bukata?" Shiru yayi ya cigaba da aikinsa yana rike da ni, yau ne zai sake ni kai har dai da na shafe awa daya cif a jikinshi, ban san saa'da na fashe da kuka ba, sharewa yayi ya cigaba da aikinsa. "Daga yau idan kina tare da ni, wani yazo wurinki matukar ba daga danginki ba ne wallahi sai na b'ata miki rai, oya ki je ki sallame ta ki dawo nan, idan kuma kika bari na zo da kaina a gaban Hajiya xan ɗauke ki cak." Ina tashi na harare shi ina share hawayen da yake zuba min na ce mishi. "Ba zan dawo ba, ka jima ba ka ɗauke ni ba!" Bai ce zai min kome ba dan gyara zama yayi na fasa ihu tare da tsayawa cak, na zata zai biyo ni ne. Tab'e baki yayi yana faɗin. "Haukar tsufa rashin ganin jika!"
Ya fada yana cigaba da aiki, ai kuwa na tura baki ina faɗin. "ba xan kara zuwa ba" na fita, murmushi yayi yana faɗin."yarinyar nan zan kama ki!" Duk wani burin shi naso ganin ya kyautatawa Ummu yana kokarin cika shi, asalima gani yake kamar bai mata yadda take so ko hakuri take da shi, a bangaren Mu'amala aure yasan tana kokarin daukar laluranshi kuma haka ya mishi dadi musamman yadda take jure bukatarshi, haka ya cigaba da aiki.
-
Na samu Asiyah a parlour Hajiya tana hira da yaran, sai tsalle suke akanta. Murmushi nayi itama ta sakar min murmushi. Muka shiga gaisawa Hajiya tana kitchen. Nana Asma'u da yaran suna ta wasa , shine ta zauna a cikinsu. "Aunty Baby Ya Ali ya ki barinki, kizo gashi nan xan tafi." "Allah sarki, mun gode kiyi hakuri na tsaya gyara mishi daki ne shi yasa." Nan muka shiga hira sama sama, ta fito da wasu kayan Yara, irinsu hankchef da sauransu da turaren Yara, masu kyau da tsada ta mika min daya blue daya pink! Har da ribom na kitso irin na yaran nan! "Duk su ɗaya?" "Ai Aunty Baby kin ji girma sai yaran kawai!" Ta fada murmushi nayi nace mata. "Gaskiya sun gode sosai, Mum dinsu tayi musu sayayya!" "Kai Aunty Baby babu yawa." Hajiya da bata kula mu ba, sai da na mata magana ta ce min. "Sun gode! Ummu bari na shiga sallah!" Ta wuce nasan Hajiya bata yarda da kayan ba, haka yasa na ki tab'awa na cewa Fanna. "Ya Fanna zo ki kai dakin Hajiya ki ajiye," "dake Yaran sun koma hannun Hajiya sai nima hidimarsu ta min sauki, haka ta dauka tana ta godiya itama, hira muka sha na manta da Tafida na can yana jirana. Ganin shiru ban dawo ba balle na saka mishi ruwan alola, sai gashi nan ya tawo don Tafida irin Alhaji ne haka kawai daga dawowarshi ya zo da wani butar karfe daga India wai ina zuba mishi ruwan alola da farko cewa nayi ko butar tsafi ce, hade rai yayi ya ce a'a na bokanci ne karewar tsafi don idan ya yanko magana kamar bashi ba, baya gajiya da bakar Magana. Tura kofar parlour yayi muka hada idanu, washe hakori nayi domin nasan ba mamaki ya kunyata ni....
*Ban so nayi magana ba amma bari na goge muku lissafin da wasu suke yi har da masu karanta bati! Labarin nan ba daga farko na dauke shi ba! Daga tsakiya na dauki labarin Ummu, kamar kowani marubuci yana da side din da yake daukar labarinshi! Tow ni daga ƙarshe karshen rikicin Ummu da Tafida na ɗauka! Labarin Ummu idan baso kuke na yanke labarin ba ku bar ni nayi abin da yake cikin labarin amma ko ina cewa ake ya labarin bai yi ba yo dama ai nasan ba zai yi ba, idan kuma kuna ganin na kammala shi kamar yadda ake tatsuniya ce daga wannan pagen din sai nace Alhamdulillahi! Don haka a bar ni nayi abin na tsara a labarin idan kuna ganin da matsala! Sai ku ajiye ku jira idan na kammala sai ku karanta amma bakiɗaya kuna dagula min lissafi! Sai nayi gabar kuce yamma zan yi me Ummu ta gani a kaidin kishiya da dangin Miji! Me Mahmoud yayi da za ace an gama sai na kama shi nace na bayyana asirinsa ya tonu gaskiya wannan shine short story, bayan da kanku kun san Deen yana kwance don Allah kuyi hakuri a bar ni nayi yadda na tsara sunan Mahmoud kuwa sai fa hakuri gaskiya don na tafi da labarin sosai. Ba zai yiwu a dakatar da jirgin kasa a gudun dubu dari uku a duk kowacce dakika dari da tamanin! A bar min kayana nayi sama sama da shi😀🏃🏻‍♀️*


🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7644
"Karfe nawa?" Ya kalli agogon hannunshi, kafin na bashi amsa ta bashi amsar. "Shida saura minti goma!" "Ummu karfe nawa?" Juya idanun nayi na mike tare da cewa. "Dama dama na manta amma!" Na juya zan nufi dakin Hajiya da wani irin zafin nama ya cabkoni yayi sama dani. "Wayyo Allah Hajiya ki ce ya sauke ni!" Na fara ƙoƙarin kwace kaina. "Hajiya kada ki fito ɗaukarta nayi rashin jin Ummu yayi yawa!" "Sauke ta dan gidanku ka manta ciki ne da ita!" "Hajiya me yasa kike min haka!" "Hajiya ki ce ya sauke ni Allah xan bishi!" "Ai tace Allah sauke ta!" Ba musu ya dauke ni, yana zungure goshina. "Wayyo Allah zai fasa min kai Hajiya ki ce ya bari kada ya fasa min kai!" "Babangida baka jin magana kai ma." "Gaskiya kam Hajiya Daadi baya jin magana ki gaya mishi ya daina rashin ji!" Matse hannuna yayi tare da cewa. "Hajiya ki tafi kawai ki barmu don Allah ya gani zan baki kunya!" Ya fada yana kokarin rungume ni! Juyawa tayi ta bar wurin tana faɗin. "fitsarare!" Tana barin wurin nace mata. "Hajiya cin zalina zai yi!" "Ai kema rawannki yawa ce da ita!"
Murmushi yai ya saka kaina a gaba muka wuce bangarenshi daga ni har shi mun manta da wata Asiyah,
*Asiyah*
shiru tayi tana kallon kofar. *Ummu* ta furta a kasan makoshinta, ji tayi idanunta sun cika da kwalla, tabbas zata gyara mata zama, mikewa tayi ta fita tana me kallon bangaren Tafida a hankali ta bar gidan, a hankali take tafiya ita ba damuwarta kawai Tafida yasan tana nan da rai. Kiran Mamanta tayi a waya. Kuka ta saka mata a hankali take kuka kamar zata shiga wayar. "Mama Tafida idanunshi akan Matarshi ya ke baya tunanin kowa yake ba sai ita, mahaifiyarshi da mahaifinsa damuwarsu Ummu basu tunanin ko me, idan ban samu Tafida gara na mutu, ni ban da amfani!" Uwar ta rasa yadda zata yi da ita ta ce mata tayi hakuri kome zai wuce.


Haka tayi ta kuka har ta isa, koda ta isa kwanciya tayi a kan kujerar dakin Inna. Haka ya cigaba da murkususu. Har kusan asuba, saboda rashin barci da safe tana tashi da ciwon kai, haka ta fadi a wurin domin jiya tayi ta shan kayan maye amma basu sakata barci ba, sai a lokacin sai da ta farka ne ta ji jiri ya kwashe ta, a wurin ta zube salatin Inna ya taso yan gidan, aka kwashe ta zuwa asibiti. A ranar aka kira Mamanta.
**
Sa'adiyya.
Cikin tsananin zafin marin da Mahmoud ya kwashe ta da shi, yasa take kallon shi bakinta a sake ta ce mishi. "Mai nayi maka? Na gaya maka gaskiya ba zan kara ba, idan ka sake ka kara dukana sai na gayawa duniya waye kai! Na gaji ka hanani zaman lafiya a gidan aurena, ka bar ni na tafi nayi rayuwata, kada ka kara min magana ko na gayawa Mahaifiyarka abin da kake min, kana tsammanin." Shake wuyarta yayi yana faɗin. "Ni zaki yiwa rashin kunya? Sai kashe ki na kara ganinki a wurin nan sai na lalata miki kafa jaka!"

Cikin kuka ta ce mishi. "Eh na yarda a haka amma ka sani ni aurena na tab'a, kuma a shirye nake na gyara tsakanina da mijina amma kai fa? Amanar Abokinka ka ci, kai baka samu Ummu ba ni ban samu Tafida ba, tun basu son zama da juna yanzu kuwa duk abin da muke Allah ta nuna mana cewa Ummu da Tafida ba me raba su, ka gama haukarka tun daga ranar da kace min ka kasa mata fyade na gane baka da ss'a har abada Ummu Hadiyya tayi maka nisa, ka bar nayi nawa rayuwar." Juyawa tayi zata tafi ya riko Hannunta cikin fushi ta juya ta watsa mishi harara. "Sake ni kafin na gaya maka magana, yadda ka cutar da igiyar aurena haka Allah zai tozartaka Mahmoud wallahi sai kayi danasanin abin da kayi. Azzalumi macuci! Na dawo daga karyanka ka dawo daga zalincika na daina na daina na daina ka bar ni kada ka kara shiga rayuwata idan kuma ka dame ni sai na gayawa kowa waye kai!" Daga haka ya bar gidan tana tafiya tana wani irin kuka, jin tayi ta tsani kanta, ba zata kara yarda ta rasa Tafida ba. Gara ta samu Alhaji ya bashi hakuri zata koma gidanta.
Har ta fito bakin hanya ta tuna ta bar motarta a can, haka ta kara juyawa ta koma ta bude motar ta shiga, sannan ta bar unguwar gidan ta wuce, bangaren Abba ta wuce ta samu yana shan shayi, akan gwiwarta ta zube tana kuka me cin rai. Zuba mata idanun yayi kafin ya ce mata. "Halimatu gaya min me yake faruwa?" "Abba na shirya zama da Tafida ne,Abba ka bashi hakuri ya zauna da ni!" Murmushi yayi yana faɗin. "Tow ai Halimatu ke da Mijinki babu wanda ya isa shiga fadarku, sannan ni nayi alƙawarin shiryaki da Mijinki don haka ki je gobe zamu yi magana da shi!" Tayi ta godiya sannan ta fita tana share hawayenta. Ba zai ce Tafida ya rabu da ita ba, amma zai bashi shawara ya saka idanun akanta, don yasan duk wani takunsu akan Ummu. Sannan ga Asiyah. Shiru yayi yana jin labarin ciwonta da alakantashi da dawowa daga gidan Tafida.


Yarinyar tunda Uwarta tazo take kuka ita dai Tafida take so, ya rasa yadda zai shawo kan rikicin Tafida.
---
Tun safe ya gaya min zai dawo ya ci abinci, sannan zai je gidan Abba bayan sallah isha. Haka na gama hada kome, tunda ya dawo nake maida hankali akan abinda zai ci, ina gamawa naji kar'ar saren dinsa, murmushi nayi sannan na tsaya a bakin kofar ya buɗe ido hudu muka yi da shi. Yadda na ganshi rai a b'ace, "barka da dawo hasken rayuwata! Ubangiji ya ƙara maka hakuri da juriya, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana yadda zaka kula da mu, Allah ya jagoranci lamarinka!" "Ki bani Ruwa na sha!" Riko hannunshi nayi bai min musu ba, ya biyo ni ya zauna Kamar yadda nace mishi, na wuce kitchen na dibo ruwa na kawo mishi. "Kayi ta ambaton Allah yana tare da kai!" Karba yayi yana sha kafin ya juyar da kan shi. Zama nayi a dan nesa da shi, kaina a kasa zuwa yanzu na fahimci me ake kira da Shugabanci. Domin wani lokaci zai shigo ranshi a dagule tunda Deen ya samu matsalar nan, "Ummu!" "Na'am Baban Mufid" murmushi yayi yana faɗin. "Sadiya ta kai karar na wurin Abba, sannan ya bukaci na haɗaku a government house, tunda nan." Hankalina ne ya tashi na kura mishi idanun. "amma!" "Kada ki damu zan akwai bangarenki!" "Da nan ka dawo da ita tunda akwai fili sai ka sake daukar wani aikin, idan ka duba gaba mulki zai kare dole nan zamu dawo! A ce yau muna can muna nan duk ba yi ba ne, zaka iya fa na yarda da kai!" Kallona yayi kafin ya ce min. "Kina ganin babu takura?" "In sha Allah babu takura sannan ni mace ce, kuma Uwargidanka idan ban rike gidanka ina zan riƙe?" Jinjina kai yayi. "Amma kace min sai isha zaka gidan ya aka yi haka?" "Eh zan tafi don yarinyar nan bata da lafiya ma!" "Wacce!" "Kawarki!" Sai na rasa wacece. "Wacce take kawo miki kaya mana!" "Ai Asiyah! Allah sarki Allah ya bata lafiya!" Na fada domin ban san meke faruwa ba. Sai da yamma ya ce min n shirya muje asibitin bayan sallah Magariba. Haka na shirya ban dauki yaran ba, muka tafi asibitin tunda aka sanar da Gwamna zai zo asibitin ake kome cikin nutsuwa, tare muka zo dashi ina sanye da riga da skirt ne na saka hijab har kasa sai face mask da ya ce na saka, haka muka shiga asibitin, rike hannuna yayi muka shiga kowa sai kallonmu ake, ina ta son cire hannunshi a cikin nawa amma yaki, koda muka isa kofar dakin haka ya rike hannuna gam, muka shiga dakin da sallama. Kanta kwance akan cinyar Mamanta. Tashi zaune tayi tana faɗin. "Maman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login