Showing 117001 words to 120000 words out of 241571 words
Chapter 40 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
min. "Ki shirya zan mai dake gidan!" Yadda yayi maganar sai naji hankalina ya tashi, haka na wuce dakin na zauna ina jin kuka yana zuwa min.
"Kana burge ni Tafida, kai tsaye kake lamarinka. Na ji dadi da kake fadar gaskiya ba ƙaramin aiki bane fadarta." "Deen tafiya zata yi fa!" "Ba zata tafi ba, yanzu ka je kace ta shirya zaka fita. Sallah juma'a zaka ajiye ta a gidansu!" Ya kuwa mike, ya nufi dakin Deen sai dariya yake mishi yana wasa da Yaran kaunar da yakewa Iyayen Yaran ya shafi yaran sosai, don yana jinsu kamar na shi.
A bakin gadon na zauna ina shashekar kuka, domin nasan ba wani sauyawan da yayi, yayi min laifi kamata yayi yazo ya rarrashe ni amma yace wai na shirya zai ajiye ni a gida, wato yaci moriyar ganga, duk sai naji na tsani kaina da ban biyo shi ba da ba zai min haka ba, haka na cigaba da kuka, ban kawo a raina zai zo din ba sai gashi ya turo kofar, wani irin sanyi naji ya tsirga min, na d'ago kai ina kallonshi shima kallona yaƙe. "Allah ya huci zuciyarki, nayi laifi a yafe min dama can ni tsohon mai laifi ne, kuma na kara aikata bayan laifi ayi hakuri ba zan kuma ba." Ban kalle shi ba, na cigaba da share kwalla da yake zuba min, "Tow tunda ba zaki min magana ba, bari na hada kayanki na kai ki gida!" "Dama ka kawo ni ne ka min koran kare!" *Yes i hit the point!" Narke min yayi cikin rarrashi ya ce min. "a'a tashi na kai ki gida don Allah, wannan abin da nayi ina jin kunyar kallon idanunki!" Ya fada yana me durkusawa a gabana ya zuba hannunshi akan cinyoyina. "Ni dai kada garin son zama dani kayi ta aikata kuskure bayan kuskure, ka rufa min asiri kada kayi wani abin da zai tab'a rayuwarmu bakiɗaya." Na fada ina kuka, "ita mahaifiyata ce, dole naji wani abu na ga kamar ba sona kake ba, dama can na san Babu so kawai muradi ne ta zuciya...." hannunshi ya saka ya rufe min bakina. "Don Allah ki daina fadar haka wallahi bana jin dadi, nima Uwata ce, yanzu haka na saka za a maida mata wayarta ba zan kara wasa da rayuwar wani saboda ke ba, amma kiyi hakuri ba zan kara ba kin ji!" Gyada kai nayi ina share hawayen da yake zuba min. "Kiyi hakuri xan tafi sallah kada na makara!" "Allah ya tsare muje na tayaka shirya." Gaban closed din shi muka nufa na cire mishi wani babban kaya shadda ce fara sal, sai hular da zai haka da kayan, sai takalmi da links zamana da shi a abuja, baya saka babban kaya dai ranar Juma'a. Amma kusa na haddace shigarshi. Yadda yaga ina taya shi saka kayanshi ba tare da na damu ba, ya ce min."Ina tunanin ko idan kika dawo na barki a nan ne ba sai kin je government house!" Shafa kumatunshi nayi ina faɗin. "Duk yadda kace yallabai na!" Jan hancina yayi yana faɗin. "An gama yarinyar nan hancinki Mufid ya dauka. Mufidah nawa!" Ya fada yana haɗe rai. Dariya nayi ina faɗin. "Kuma laifi ne don haka ya faru?" "Kawai dai kishi nake da kika raba shi Abba ya dauki hancinki Ita Uwata kika barta da irin nawa hancin!" "Ba ka ga yadda yaran suka zamo kalanka ba!" "Hmm kuma haka ne kin fini gaskiya!" Ya fada yana rike hannuna, "ki so ni koda dan ne, ni dai nasan ina miki mahaukacin so ne! Ummu Hadiyya ina sonki sosai, irin son da nake jin ban yiwa kowa irinsa ba." Girgiza kai nayi ina faɗin. "'Lokaci yana tafi kace fada zaka je sallah!" "Eh anan nake zuwa tunda na zama gwamnanku!" Jan kumatunshi nayi ina faɗin. "Ka kyauta!" "Gobe asabar zamu shiga Biu ki shirya da wuri fa." Kallenshi nayi kafin na ce mishi. "Gobe kace amma kana ce min na shirya da wuri!" Na fada ina yaƙe. Mika mishi hular da yake hannuna nayi ya kansa ya kafa, wurin turaren shi na nufa na ciro na fara fesa mishi yana murmushi. "Na gode zan tafi mai xan sayo miki!" "Duk abin da ka gani ya maka kyau ina so nima zan min kyau!"
"Hmm ji nake kamar kada na tafi!" "Muje maza Yayana yana jiranka, ka wani bar mishi renon Yaranka!" Muka fito ina gefenshi, "Nanny sannu da kokari ka ji!" "Kam uban can ni ne Nanny?" Deen ya fada da karfi yana nuna kanshi. "Lallai tafiya daga dan iska sai kai, a rashin mutunci ni zaka kalli tsabar idanuna kace min Nanny ka ɗauke ni dan daudu ne!" Yadda Deen yake tijara sai naga sam haka bai damu Tafida ba, asalima sumbatar goshin yaran yayi yana faɗin. "Kuyi hakuri Abbanku yana ta ihu, sai na dawo Yarann Daadi da Abba! Idan ka gama basu dariya muje don Allah!" Wayarshi ce tai ƙara ya kalla yana sake tsaki yayi ya ce. "Deen ya zan yi da Asiya ne?" "Ina ruwan sly Queen!"
Juyowa yayi ya kalle ni, "wata cousin dina ce!" " ka gaya mata me kama fatalwa kin san an bashi mace dan iska ya ce baya so!" "Deen kada ka ja min bala'i don Allah!" "Yaya Deen kace dama can amanata kuke ci?" "A'a ban dani dan iska dai yake cin amanarki!" Ya nuna tafida da hannu, "Ka aurota!" Na fada zan juya, "Ni fa ba dan iska ba ne, kuma abu daya gare ni kin ga ya wuce daya ne? Da zaki ce na aurota!" "Yallabai ko bance ka aurota ba, wajibi ne auren mata sama da daya, Allah ya baka budi da rufin asiri in dai ba son zuciya ba, ai kana da damar rike mu mata hudu!" "Ummu Hadiyya ki fita idanuna na rufe. Auren ce miki aka yi da sauki ne da shi da zan rike mace sama da daya Hadiyya ki fito Ki gaya min bakya bukatar zama da ni mana!" Murmushi nayi na wuce shi don nasan ya cika haka suka fita, a waje ya amsa wayar yana me bude mata tsohon littafinsa na tijara, jin tana kuka yasa shi sasauatawa ya tambaye ta me ya faru, bai karasa ji ba ya kashe wayar ya nufi massalaci yana zargin Deen da hada mishi husuma me Deen zai yi ban da dariya.
Bayan fitarsu nayi alola na zo nayi sallah, sannan na kunna wayata na kira Uwani na gaya mata ba zan dawo ba, ta ce min ai Baba ya gaya mata. Murmushi nayi sannan na kashe wayar na ja Yarana muka shiga kitchen, mamakin yadda aka zuba kome na zamani nayi, ina cikin aiki wurin karfe biyu da arba'in da biyar, ya kira ni. "Ummu Hadiyya! Akwai matsala!" "Ina tare da kai babu wata matsala gaya min me nene?" Daga can na ji Deen yana faɗin. "wallahi billahi azim ba zata zauna a inda Ummu take ba, ka kaita gidan Abba ko ko gidan Hajiya ba zata zauna ba, Ummu tana buƙatar ka kana bukatar Ummu, meye amfanin kebewan da kayi ba don ku huta ba ne, Yaran nan wallahi ban da suna shn mama da na rabaku dasu, ko ka kaita gidan Maryam amma ban da Ummu."
"Wai me ke faruwa ne?" Kashe wayar yayi.
Mamaki ya kara kamani na kira Tafida, "zan kira ki!" Kashe wayar yayi..
**
A can kuwa Abin da ya faru, Asiyah ta sab'a lamba, domin ta tabo Saadiya a daidai lokacin da take cike da Tafida, abun da ya faru kuwa, tun da Tafida ya bar gidan bai gaya mata zai tafi bude sabon titi a wani kauye ba, take cika take batsewa domin a bakin yan gulmanta take jin labarin, har dare aka sha ruwa babu Tafida, ta kira Deen lokacin yana waya da ya gama ya kashe wayar domin shi dai bai da amsar da zai bata, wurin karfe hudu na asuba kamar ance ta fito ta hango Asiyah ta fito kamar daga ɓangaren Tafida, haka yasa ta kara kallon sosai ganin ta ga sun sake rungumar juna, kafin ta wuce inda take zama, tana ganin ya shiga Mota ya bar gidan. Jikinta yana tsuma kawai ta fito da gudu lokacin Asiya ta shiga bangaren da take ta rufe kofarta, komawa tayi ta shirya har karfe daya na rana Asiya bata fito ba, sai wurin karfe biyu ta fito. Ai kuwa Sa'adiyya tayi wuf da ita tayi ta bugata da kasa, tana bata kashi. Sannan ya yakushe mata fuska tana ihu karuwa kwartuwa me bin mijin wasu. Yadda kuka san mahaukaciya haka aka dauke Sa'adi baby akan Asiyah, duk abin ba dadin gani. Da ta samu ta shige dakinta ta kira Tafida tana kuka, shiri tayi amma bata zata wannan me kalar samudawan zata mata mugun duka haka ba, sai gashi ta yakushe mata fuska, sai da tayi kukan bakin ciki, bayan sallah juma'a Tafida yazo gidan ganin har lokacin Sa'adiyya tana ihun sai ta kashe Asiyah yasa Tafida kallon Deen. "Ku sake ta ku je!" Suna barin wurin ya nufeta. Aikuwa farar shaddan jikinshi ta damke wuyar rigarsa da ta yaga har kasa. "gaya min me nayi maka zaka ci amanata, ashe karuwa ka ajiye a gidanka, shine ka hanani hakkina, wallahi ba zan yarda ba muje ka bani hakkina nima na haihu kamar Ummu." "Kin ga nan ba kamar da can baya bane, ko ina akwai jami'an tsaro Please mu shiga daga cikin gidan!" Dake tana ganin girman Deen haka suka shiga rarrashinta da tambayar me ya faru bakincikin ya hanata fadar abin da ya faru sai kuka da rantsuwar matukar bai d'aga Asiyah a gidan ba zai samu gawarta, dakyar Deen ya kwantar da rigimarta, sannan yazo ya ga Asiyah sai da yaji babu dad'i. Yarinyar fuskarta ya kumbura. Shine yake tunanin ya kawo ta wurin Ummu ta yi jinya, Deen yace karya kenan. Ba zai yiwu lokacin da ya samu zai kula da kanshi da iyalinsa yace zai karawa kanshi yan sa'ido ba, don haka yasan yadda zai yi da ita......
#Tafida
#Deen
#Ummu
#Sa'adiya
#Asiyah
#Mahmoud🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
*Tafida*
Kasa magana yayi yana kallon Deen baki sake. "Na tambaye ka wani abu?" Tafida ya tambaye shi, "ina jinka dan iya!" "Da ni da Ummu waye ka fi so a cikinmu?" Murmushi yayi yana faɗin. "Kai waye ya damu da kai, kato shirgeggen mutum irinka, nafi damuwa da Ummu akanka!" "Mtseew! Amma ita yarinyar!" "Indai ba cikin Hajiya kuka kwanta ba ka kara kira min sunan Yarinya sai na zage ka!" Tunda Deen ya fada mishi haka ya rufewa kanshi asiri, yana me lumshe idanunshi. "Yanzu me?" "Daman-daman!" "Kada ka fita idanuna sai na zage ka!" Haka suka isa gidan. Abba sun iso tun sha daya na safe, cikin nutsuwa da ya samu a kwana ɗaya, ya shiga gidan sai gaishe shi ake. Da fara'a a fuskarshi yake amsawa. Yana isa parlourn Abba ya samu su Maryam da Rukayya, cikin girmamawa ya zube a gaban Abba, tare da cire hular kanshi. "Gwamna da kanshi!" "Barka Abba ka sha hanya!" "Lallai Babangida ya kara girma, Deen me kake bawa Babana ne haka?" "Abba me zan bashi kuwa Ummu take cika mishi tumbi da daddar abinci, don bakinciki nace ya nima min daya kanwar Ummun gayen nan ya hade rai, gashi sai tara tsokaki yake kamar tsutsa!" "Abba kace ya fita idanuna!" "Tow kai Deen fita a idanunsa!" "Abba ina zan fita bayan yana auren kanwata! Bari na shiga wurin Ammah!" Ya mike yana gaida su Rukayya. Banza suka yi da shi kamar basu ji shi ba, "Man idan ka gama ka min magana, akwai sakon Ummu zan kai mata hannu to hannu, Abba ka kara yiwa Ummu godiya fa, Allah ya mata albarka yar aljanna!" Ya mannawa Rukayya da Maryam hauka. Ya fita suna gaisawa da Inna da take tambayar shi me ya faru da Asiyah Mamarta ta kira tana cewa. "Deen me ya samu wannan yaron Asiyah, Mamanshi ya kira ni yana ta cewa an kashe mishi fuskar Yaro, shine nace mishi nasan zaki zo!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Fada suka yi ita da Sa'adiyya amma da sauki tana asibiti!" "Na shiga uku ni jakan Umaru, Yaron nan Sa'adiyya ta fada ta'addanci ne? Ya daki mutum har gadon asibiti. Maza a kira min shuwa yazo ya ji abin da yaron nan ya aikata, Ita Tafida tana ina wannan abin ya faru?" "Baya gari Inna?" "Oho haka yasa ya kashe Yaron mutane, wannan masifar da me yayi kama da zai kashe yaron mutane." Yadda Inna take maida Sa'adiyya namiji yafi kome bawa Deen dariya, a nan ya barsu. Har parlourn Abba ta shiga da fada tana masifa, zuwa Tafida idanu. "me ya faru?" "Ina zata sani ita da bata gari." Inna ta kwace tambayar ta shiga rabto bayanin Saadiyyah zata kashe Asiyah tana asibiti, ciro wayar shi yayi da yayi kara. Sakon Barka da juma'a aka tura shi. Murmushi yayi yana kallon Inna da take ta bayanin yadda Sa'adiyya ta kashe Asiyah. "Inna da kike wannan maganar wai a kan idanunki aka yi ne?" "Ungo naka Mairamu nace ungo naka, ka fita idanuna munafiki, ko an gaya maka ban san kome ba ne wannan yarinyar Deen ta gaya min!" Murmushi Tafida yake yana faɗin. "Innata bayan sallah zaki fara zuwa wurin bita ajin bana ke da ni da Ummu Hadiyya da Hajiya Kaltuma zaku tafi, ki kira Yar uwarki Hajja Ganaah muje mu sauke farali." Bata son lokacin da ta fashe da kuka ba, tana faɗin" Alhamdulillahi! Allah na gode yau da yarinyar da Muhammad da Aisha suka haifa ta biya min aikin hajji, Allah ya saka ki gama da duniya lafiya ya rabaki da iyayenki lafiya!" Zani a hannu ta fito tana rangad'a gud'a tare da kiran Alhamdulillahi, maza a sayo gyada a rabawa Yara sadaka.
Kallon Abba Tafida yayi yana faɗin. "Abba kasha Madina!" "Eh Aliyu na ji kamar kada na bar garin!" Murmushi yayi, sannan ya cigaba da cewa. "Yan uwanka sun kawo karanka!" "Tow Abba laifin me na aikata?" "Maryam ina jinki!" Nan ta shiga kame-kame kafin ta kawo zancen ya biyawa Maman Ummu Umrah amma ga Hajiya shuwa da ta sha wuyarshi, yanzu baya kyautata musu, sai Ummu da danginta. Murmushi yayi ya ce mishi. "Abba yanzu daga dawowarka hutawa ya dace kayi ba Muhawara ba!" "Eh haka ne amma me yasa kake musu rashin kunya? Yayunka ne fa!" Kura mishi idanun yayi har Abba ya kai Aya kafin ya ce mishi. "Abba ba zan taimaka musu ba, Abba kune kuka zama dole na muku hidima, su kuwa suna da wanda zai musu suna da Mazaje da ya xama wajibi akansu!" Yadda yake maganar Abba ya fahimci ranshi a b'ace yake. "Me suka maka!" Kasa magana yayi yana sauke numfashi, tunda yayi haka Abba yasan tabbas yafisu gaskiya. "Kai musu don Allah, Allah zai maka sakamakon alkhairi. Sannan kayi hakuri sosai na sani kai meyi ne kuma kana badawa ba tare da ka damu da jiya ka bada ba. Kayi hakuri kayi musu Allah zai tsarkake rayuwarka da zuri'arka!" Hakuri Abba yayi ta bashi yana rarrsshinsa. "Kana tare da Ummu ne yanzu?" D'ago kai yayi da idanunsa suka cika da kwalla ya ce mishi. "Eh ina tare da ita, kafin ta dawo." Murmushi Abba yayi hawaye na zuba musu dukkansu biyu, kuma suna murmushi, "Abba kuka kake?" Girgixa kai yayi yana faɗin."kukan farin ciki da jin dadi nake yi, yau gaka ga Ummu a tare. Ji nake kamar kome nawa ya cika yau gaka ga Ummu." Shima share kwalla yayi yana sunkuyar da kai a gaban Abba, yana murmushi ya ce. "Abba ina sonta sosai! Abba ban san wani irin so nake mata ba, Abba ina son Ummu sama da yadda nake jin bugun zuciyata. Abba ina sonta sosai, Abba ba zan yafewa duk wanda ya shiga tsakaninmu ba!" "In sha Allah babu me shiga tsakaninku duk wnada yayi ƙoƙarin shiga zai yi mummunar karshe, na roki Allah ya kare aurenka da Ummu duk wanda ya shiga cikin aurenku, sai yayi mummunar ƙarshe!" Yadda yake gayawa Tafida irin mugayen addu'ar da yayi yasa Rukayya tsoro don dama tana da mugun tsoro, Maryam ta razana amma bata yarda ta an ga haka a kan fuskar. Sai da suka gama hira tsakanin da da Uba, sannan ya juya kan Maryam yayi musu tas akan Umara da ya biyawa Maman Ummu, sannan ya ce su b'ace mishi daga parlour. Sun ji tsoro amma haka.suka nufi bangaren Shuwa suna ta zagin Tafida da jin haushin Abba yana goyawa Tafida baya.
Anan ya sha ruwa yayi sallah Magariba, sannan ya baro gifab..
*UMMU*
Tun fitarshi da kuma kiran da yayi min, yasa na tattara hankalina akan aikina da sauraron dawowarshi, ina gama aiki nayi wanka tare da Yarana, yau daya sai naji na gaji sosai, domin idan daya yayi barci zaka samu daya idanunshi biyu, haka nayi ta fama da su har na gama, mun fito ras kamar ba, na basu madara sun sha sannan na kara musu da nono, har aka sha ruwa babu labarin, bayan nayi sallah na kara gyara jikina, nasan yanzu yana hanya, dakin na kara gyara dakin nayi na shiga ban dakin duk da na gyara da nayi wanka sake gyara shi nayi, sannan na fito parlour na zauna kenan naji alamar ya dawo motar rakiyarshi. Bakin kofar na tsaya, yana turo kofar da sallama. Na kalle shi cikin kulawa ina amsa sallamarshi, "sannu da zuwa, barka ka sha hanya ya Ibada?" Zuba min idanun yayi yana murmushi, "Alhamdulillah na gaji." "Masha Allah, sannu sadauki!" Na riko hannunshi muka tafi har dakin shi, na zaunar da shi a bakin gadon, na fara cire mishi takalmin kafarshi da safar kafar, na wuce ban daki na hada mishi ruwan dumi, sannan na