Showing 225001 words to 228000 words out of 241571 words

Chapter 76 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14704

kai ina matsa maka wata rana ba zama dole na tuna maka girma da daraja na zumunci ba! Na koshi!" Rike hannuna yayi yana tab'a shi a hankali, kuka Asiyah ta saka tana faɗin. "Me yasa kike fada har haka!" Murmushi yayi yana faɗin. "Shi kenan ku shirya muje!" Nayi mamakin saukowar shi,.amma nasan daren yau sai dai na hakura da barci da asuba zan yi domin duk lokacin da muka yi irin haka sai ya fanshe a shimfidarmu.
Bayan mun gama aka shirya har da Fanna muka.nufu asibitin, tunda muka shiga muka samu yarinyar tana zaune a tsakiyar gadon. "Nazy!" Ya kira sunanta, tana ganinshi ta cire karin ruwan hannunta ta nufe shi tana faɗin. "Uncle don Allah kada ka tafi ka barni zasu zo wallahi sun ce zasu zo, don Allah ka tafi da ni!" Ta juya kaina tana faɗin. "Aunty Baby ki tafi dani don Allah ki tafi da ni, wallahi zasu zo " yadda ta rikice mana sai jikin kowa yayi sanyi. "Zaki zo ki zauna a wurin Dodonkin ko sai na zabga miki mari!" Uwar ta fada fusace, duk da ranta tayi farinciki da zuwansu amma kuma maganar gaskiya taji takaicin zuwa dasu Ummu da yayi domin tasan tazo ne ta ga yadda Naziha take ciki, "Ya mai jikin?" "Da sauki!" Ta bawa Asiyah amsa fuska a sake, ina bude baki nayi magana ta wani dauke kai, taki amsawa, yadda tayi min haka shima yayi mata domin bai tambaye ta ba, gaban yarinyar ya je ya durkusa yana tambayarta me ya faru, kuka ta fashe da shi ta ce.."Uncle yunwa ga duka, bana zuwa school Baba ya hana ni fita, shine Aunty Dayyiba ta aike ni wurin kawayenta a hotel, tunda naje.suka kwace wayar hannuna suka bani wani abu daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba, na rantse iya gaskiyar kenan!" Ta fada tana kuka, d'ago kai tayi tana faɗin. "Uncle wallahi suna zuwa na gansu sun zo!" Shiru yayi yana faɗin. "Ba zasu kara zuwa ba, za a saka miki security a bakin kofar kin ji!" "Uncle ba zan koma gidan Babana ba ko? Aunty Dayyiba!" "Ba zaki koma ba!" Ya fada yana shafa kanta, a hankali ya mike yana faɗin. "muje Ummu! Baby zan ga likitan sai mu ga yadda za'a yi kinji!" Mika mishi hannu tayi ta ce mishi."promise!" Juyawa yayi yana kallon Uwarta. "I promise!" Ya haɗa hannunta, ya tuna lokacin tana yarinyar idan ya je gidansu zai tafi sai ta tambaye shi zaka je ka dawo ne promise zaka dawo! Fita yayi ya samu duk likitocin asibitin ga su nan, "Matori ka turo wasu su kula da yarinyar, Ummu ku jira gani nan zuwa." Sannan ya nufi likitocin ya ce.."ina bukatar bayanan Yarinyar nan da awa daya, a turawa Kwamishinan lafiya, zai kawo min sannan a kula da masu shiga cikin dakinta tana razane har yanzu." "In sha Allah za ayi haka." Juyowa yayi ya saka mu a gaba muka dawo gida. Tun a hanya na kalli Mufidah bakiɗaya sai naji jikina yayi bala'in sanyi. Yarinya kamar Naziha ace wani ya wasu sun mata haka abin da tashin hankali, haka muka isa gidan , ban san meye shirinsa ba, amma da sassafe sai ga Deen, yana zuwa suka shiga tattaunawa, anan ya karya sannan ya fita shi kuma ya tafi office. Yaran na wurin Fanna, shiru ban ga Asiyah ba na tafi wurin. Na buga kofar Amma shiru kuma naji ya zo wurinta amma kamar bai shiga na ne, ko ya shiga oh. Ina shiga naji kar'ar ruwa, na ta zuba leka dakin nayi naga ruwa har cikin dakinta. "Asiyah!! Asiyah!!! Asiyah!!!" Na kara buga kofar ban dakin. Daga karshe na bude kofar ban dakin, a kwance na ganta a kasa da sauri na isa gare ta ina kiran sunanta amma shiru, waje na fito na wuce dakina na dauko wayata, kiranshi nayi. "Don Allah duk abinda kake ka dawo yanzu nan Asiyah!" Na kashe wayar, na fito na koma dakinta, kayan ta na ciro na saka mata, doguwar riga zan iya cewa ban tab'a kula da wani abu na musamman a rayuwata kamar asiyah ba, ana kishiya kishiya amma Asiyah kishiya ce da naso ta da dukkan rayuwata da zuciyata, jingina ta nayi, na cincibota zuwa waje, ban san da na fashe da kuka ba, ina janyo ta tsakar dakinta. Ina me rungume ta, ina jin karar saren dinsa, na kara rungume ta. Haka ya shigo yana ganin mu ya sa jikinshi yayi mugun sanyi, yana isowa ya ce. "Sako hijabta mu tafi!" Ya dauke ta, hijab dinta na dauka muka fita, wato Aliyu ba iya shi kaɗai yazo ba har da likitoci suka zo, haka yasa muka nufi asibitin, tunda muka isa cire babban rigarshi yayi aka bashi kayan aikin ya shiga dakin Emergency, zama nayi jin kamar zasu fito ace ta rasu, Deen yake bani hakuri har tsawon awa uku kafin suka fito. Aka wuce da ita ICU. Zama yayi a kusa dani, na daura kaina a kafadarshi. Ya rike hannuna yana faɗin. "Idan sun kaita dakin ki shiga ku yi bankwana domin bai zama dole ta kara bude ido ba, Asiyah tana mana bakwana, ashe abubuwan da take yi tafiyar ta ce take mana bankwana,ko kafin na fita tana fada min kanta na ciwo, na bata magani ta shiga wanka. Har zata shiga ta juyo ta rungume tana faɗin. Ina sonka Ya Aliyu ka so ni mana, don Allah ko akan gawata ka furta min kana sona nima, idan kayi min haka Allah zai amintar da ruhina! Ina sonka ina sonka ina sonka!" Yayi shiru, ya rike hannuna ya cigaba da cewa. "Rabona da tarayya da ita tun kafin mu tafi Saudiya, amma yau ta bukaci haka na juya mata baya. Bata yi fushi ba sai ce min tayi iya haka ma ya min wallahi na gode sosai, ni dai ina sonka!" Shi yake bani labarin ni ce nake kuka ina faɗin. "Me yasa baka bata abin da take so ba, me yasa baka mata yadda take so ba, wallahi da ace wani abu ake bukata domin Asiyah ta tashi na rantse zan bada xan bata tana son rayuwa tana son rayuwa da mu, Ya Allah ga baiwarka Ubangiji ka tashi kafadarta...75
Na fada cikin shashekar kuka, wani irin tausayin Asiyah na kara cika min zuciya," me yasa? Me yasa sai wanda muke fatar mu rayu da sune suke tafiya su bar mu?" "Kada ki tuhumi Allah da abin da ya tsara mai kyau ko mara kyau!" Kifa kaina nayi akan kafadarshi, ina shashekar kuka domin na rasa yadda xan yi idan har Asiyah ta tafi tow daga ni har Tafida zamu zama abin tausayi, shima zuwa yanzu na fahimci son da yake mata, ba na wasa ba ne, duk da yana boyewa amma nasha ganinsa yana zama yayi zurfin tunani idan na tambaye shi akan me yake zaune har bai yi barci ba, murmushi yake ya ce myanzuin. "Kwanta kawai, Asiya nake tunanin inda xan kaita ta samu lafiya, ina son ganin ta samu lafiya itama!" Ashe ba lafiyar bace, abokin tafiyarta ce. Har aka fito da ita suka wuce ICU, na kasa binsu dan adam ba a bakin kome yaƙe ba. Musamman idan Allah ya jarabci lafiyarshi. Tunda na isa bakin kofar daga bakin kofar nake hangota domin dakin ba a cika shiga ba, nima abin da yasa aka bar ni na shiga don matsayin Tafida ne, zuwa yayi ya rike hannuna ya shigar da ni dakin, gaban gadon naje na tsaya, hawaye na zuba min. Tsayawa nayi ina kallon Asiyah, Allah mai kyauta da ƙari. Wata Nurse ce ta zo ta ce mana. "Yallabai ko zaka fita da Madam!" Juyawa yayi ya kalleta, ta sunkuyar da kai. "Muje Ummu!" Ya kara riko hannuna muka fita, a ranar nayi kuka kamar kaina zai fashe, karshe ciwon kai ne ya kama ni babu ji babu gani, haka ya wuce da ni gidan Mama, a can na wuni, da dare suka dauko ni a lokacin yake gaya min Asiyah Mahaifiyarta tazo kuma dama Mama sun tafi dubata. Sai dai an hana kowa shiga, koda muka dawo gida ranar raba dare nayi ina fadawa Allah matsalar Asiyah, shima a bangaren shi haka ce lallai Asiyah ta tab'a rayuwarmu ta shiga rayuwarmu tayi mana kane-kane ta shiga yadda babu wanda zai iya cire ta. Wurin karfe uku na kwanta shima barci da jiri ya dame ni na kwanta. Barci me nauyi ne ya dauke ni. Hajiya na gani zaune akan wani kujera ga korayen ciyayi sun lullube inda take, hannunta daya riƙe da casbi, sanye take da fararen kaya, fuskarta tayi fayau sai dai murmushi, "Hajiya kina huta ne?" Murmushi tayi ta mika min hannu. Na mika mata na zauna a gefenta. "Ummu Hadiyya!" "Na'am Hajiyata!" "Na gode sosai! Kada ki daina kada ki fasa! Allah zai kare ki da Yaranki, ki yi hakuri na tafi ban karasa abin da ni ce musabbabinsa. Ki kula da Tafida kin ji shine abin da zan kara rokonki akai." Tashi tayi tana faɗin. "Allah ya albarkaci rayuwarku!" Zan bude baki nayi magana, shiga sallah asuba ya farka da ni, bude idanun nayi ina faɗin. "Hajiya !" Tashi zaune nayi ina tuno murmushin da na gani a kan fuskarta, kamar zan yi kuka na tashi zaune ina me nufar ban daki, tsarki nayi tare da sake sabon alola, na fito na tadda sallah, ina idarwa na wuce gado na kwanta, zazzabi ne ya rufe ni. Na kwanta ban farka ba sai karfe sha daya na safe, kallon Tafida nayi gabana ya fadi. Tashi zaune nayi ina zare idanu. "Lafiya? Ya jikinta?" Zuciyata tana kara tsinkewa ganin yadda na ke wurga idanuna akan fuskarshi ina jiran naji me zai ce min ya saka shi dariya.."Alhamdulillahi jikin da sauki." "Saukin gaske ko sauƙin hausawa?" Jan hancina yayi yana faɗin. "Saukin gaske mana, Allah da sauki sosai jikinta!" Daura kaina nayi a tafin hannunshi ina murmushi.."Alhamdulillahi!" Na furta, "kaina yana ciwo ne na kwanta shi yasa ban farka da wuri ba, amma yanzu Alhamdulillahi." Na fara kokarin sauka."Ummu ina zaki?" "Abincin asibiti!" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Ki huta na saka a kawo me girki namiji zai na abinci, dazun Sagir yazo kina barci. Domin naga barcinki ba na lafiya ba, shine ya duba ki yace jininki yana hawa ne, damuwa tayi miki yawa Ummu, kina cire wasu abubuwan don Allah. Rashin maganarki bai da amfani kina gaya min damuwarki ko zamu ba magance matsalarmu, daukar matsalar ke daya akwai damuwa." Murmushi nayi ina faɗin. "kawai laluran Asiyah ce kawai ya dame ni amma ba wani abu!" Duk yadda yaso nayi magana naki tow me zance mishi. Haka nayi wanka ya kawo min abinci na ci, na shirya a parlour na same shi, yana zaune yana aiki. "Matori zai ajiye ki a asibitin!" "Tow kai fa?" Na tambaye shi, murmushi yayi ya ce min. "Na je dazun ne!" Gyada kai nayi ina faɗin. "Tow! Wurin su Maryam ka leka su kuwa?" "Bani da lokacin zuwa idan na samu lokacin zan duba basu." "Tafida Hajiya tana bukatar kuyi zumunci Daadi, kuyi zumunci kafin lokaci ya kure wallahi nayi mafarkin Hajiya kayi zumunci Tafida."


Murmushi yayi yana shafa fuskata, "zan yi Ummu." Haka ya fada min, sannan na raka shi ya fita, nima na leka su Fanna. Sannan na wuce asibitin, ban san me yasa yace ba zai je ba, sai da naje na fahimci dalilin kin zuwa da ni, domin Mahaifiyar Asiyah bata da kyau, yadda take fade-fade da cewa an gaya mata ya fara shan jinin domin mulkinsa, a gaban kowa ta kunyata Tafida ta ci Mutuncin bawan Allah da babu ruwan shi, na tausayawa Asiyah domin bata samu uwa ba, uwar da take gabanta ba uwa bace monster ce take raye a matsayin Uwarta, yadda take fadar da hadin bakina za a sadaukar da Yarta yasa na bar asibitin , muka wuce babban asibitin Maiduguri, duba Naziha. Sai dai lokacin da naje ana ta fama da ita tana ihu, tare da saka hannunta dukka biyu tana sosa gabanta tana ihu da a cire mata kaikayi yasa naji wani tashin hankali da firgici. Danneta aka yi suka mata allura. Na sunkuyar da kai kasa ina jin wani irin tausayin Yarinyar. "Munafuka kin zo ganin halin da muke ciki ne? Kin zo ganin yadda kika mata asiri ne?" "Allah sarki tausayi kike bani, wallahi kina ba ni tausayi domin." Kai hannu tayi zata tab'a ni, Dora ta sha gabanta. "Maam muje!" Abin ya bata mamaki domin bata tab'a zaton zan iya samun kariya ba, zuwa wurin Naziha nayi na shafa kanta. "Allah ya baki lafiya!" Sannan na kalleta. "Kiyi hankali da rayuwa ba mata dole!" Na fada ina murmushin baƙin ciki, domin rayuwarsu Maryam abar tausayi ce. Bata gane hakan ba kuma ba zata gane ba.


** An samu kusan sati guda ana.fama da jikin Asiyah, wanda zamu ce kawai sai godiyar Ubangiji, domin tunda ta faɗin nan bata kuma bude idanu ba, asalima kawai mun cire rai ne da ita, wannan abin ya ƙara kashe mana jiki, ga mahaifiyarta da ta sako Tafida a gaba sai da aka hanata shiga karshe aka dawo da ita asibitin gidan gwamnati, aka hana kowa zuwa inda take domin kuwa tana bukatar kulawa. Rukayya ma naje na gaishe ta, da sauki iskancinta domin ta daku, kuma zuwa yanzu babu wani abinda take da shi, Abba ya kore su, Abubakar da suke takama da shi ya hanata zuwa gidanshi. Umar bai mata alkawari ba domin tunda ya samu nasarar wani aikin da ya samu ta hannun Tafida bawan Allah nan ya fece Abuja. Yanzu idan ka cire Alfah, Sharifai sai Umar sune suke jikin Tafida ba don kome ba sai don sun yarda haka Allah ya nufa ya kuma ware daya a cikinsu ya azurtashi. Sun kuma kara godewa Allah akan Ni'imar da yayi musu.


Ciwon Asiyah sai da ta kai da dole aka fitar da ita, duk da bai so Mahaifiyarta ta shiga lamarin ba, haka Abba ya dakatar da shi ya barta aka tafi ita, domin yadda take nunawa kamar Tafida zai kashe mata yarta, don haka yasa shi ya barta suka tafi tare da Deen, Har abada Tafida ba zai tab'a mantawa da Halaccin Deen ba, domin shi yayi musu kome aka kaita babban asibitin ƙwaƙwalwa na kasar America, Tafida da wulakanci har da matarsa suka tafi, ya ce suyi honeymoon, suka sha soyayya lafiya.


Satinsu biyu Deen ya dawo yayi shar da su. Gwanin ban sha'awa, Ni ce nayi musu abinci Matori ya kai musu, Naziha ta ji sauki amma kuma Ubanta yace ba gidanshi ba, don dole Maryam ta daukata suka dawo gidan, dan sauran abincin lokacin da yiwa Rukayya duka ta boye, shi suka yi ta ci har aka sallame Naziha, a hankali wasu abubuwan suka yi ta faruwa, musamman Abubakar da gobara ta kona mishi kome na gidansa. Sai da Abba ya bashi daya bangaren da muka zauna, Tafida yayi banza da shi, sannu Allah sannu Annabi Tafida ya taimaka mishi da wani karamin aiki sai da ya roki. Alfarma aka dauke shi, a matsayin karamin ma'aikaci, shima koyarwa ce a wani kauye can. Aka bashi asist headmaster, Wai kada ace yana Gwamna guda, amma Allah yana gani ba karamin wahala nake ciki da Tafida akan yan uwansa ba, domin zuciya ce da shi kamar kuturu, haka nake fama da shi, akansu amma su ganin suke kamar na mallake shi na cusa mishi kiyayyarsu,


Bayan wata biyu na shiga watar haihuwa na, a lokacin Asiyah tana da wata biyu da tafiya, aka fara shirin bikin Alfah da Jalilah, ba zama don ma cikin ya hana ni sake , haka nayi ta faman kai gwauro da mari, har aka gama bikin, kwana biyu da da bikin da sauka lafiya. Inda na samu da namiji, yaron kato da shi kamar Tafida, duk wanda ya ganshi har Mamaki ake yi idan aka ji ni ce na haife shi, gashi fari tas har yafi su Mufidah, lokacin da na cika sati daya aka yi suna Yaro yaci sunan Safiyyudeen an yi shagali takwara kuwa yayi bajinta, domin katon rago ya kawo da bankara shi aka yi ta ci akan abincin, a bakin Jalilah nake ji wai ashe Maryam ta je tayi ta ihu da hauka, wai na cika gida da Yara maza, Tafida yana gidan suka yi ta gayawa Juna magana sai da Abba ya kore shi. Bayan mun yada wanka muka tafi biu bikin Hafsa kanwar Raliya, an sha biki sosai sannan muka dawo satin mu bakwai ya shirya mana tafiya ganin Asiyah, Hmm Asiyah lokacin da muka je sai dai mu mata fatan Allah ya bata lafiya, domin kuwa har yau bata gane kome, bata gane wanda yake kanta, haka yasa nayi ta kuka domin yadda aka kawo ta haka take babu wani cigaba. Sai uban kashe kudi da ake yi wanda babu wani cigaba, mahaifiyarta kuwa tayi kyau tayi shar da ita sai yawo take zuwa, tana baza capacity iya capacity. Kallo daya Tafida yayi mata yaji gara a dawo da Asiyah gida, domin babu amfanin kashe kudi ita tana moran kudin, ita wacce ake yi domin ta tana kwance bata sani ba, don haka yayi ta shige da fice bata sani ba, sai da wata rana ta dawo ya mika mata ticker dinta, ta fara masifa da ihu da tarawa kanta mutane yayi tafiyarshi ya barta. Haka muka tattaro Asiyah muka dawo Maiduguri da ita, Hajiya Turai bata san Tafida ba, sai da ya haukace mata dakyar aka shiga tsakaninsu, ganin da gaske zai iya maketa yasa ta shafawa kanta ruwan sanyi, shi abin da ya bashi haushi ita ba zama take a jikin Asiyah take ba, sannan tana yawo sauran wasu magungunan da aka rubuta taki saka hannu ta a kai, sai dai tayi ta kashe kudi, domin duk bayan wata kudi yana tura mata kudin magani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login