Showing 21001 words to 24000 words out of 241571 words

Chapter 8 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14690

Mama, domin idan ka cire mazan gidan duk sun sauke Matan ne sai a hankali domin suna da shegen kyau fa farin fata. Wannan kyan nasu yasa suke min izgilanci bai taɓa damuna ba, domin bani nayi kaina ba, abu daya na sani duk da wannan kyan nasu kafin su saka suturar da nake sakawa sai an shekara, ba wai ko lokacin bikin sallah ba a'a, akwai wata bayarabiya da take zuwa daga Lagos, wurin aikin Mama take duk karshen wata uku tana zuwa ta kawo kayan sayarwa daga kwatano haka yasa Mama take saya mana kaya, Mama har Kano wani lokaci tana zuwa ta sayo mana kaya ta ajiye a gidan Hajiya Amina sai dare yayi ta saka ni da su Ummu Kulsum da Ummu Rooman mu je mu kwaso kayan, wani ma daga can muke kaiwa wurin tela wata yar kalaba me suna Maman Chioma, haka yasa duk iskancin yan matan suke d'aga min kafa, kuma babu yadda suka iya dani, koda nazo na gama high Islam na kara rungumar, gashi mun shaku da kawu gwani wanda haka yasa aka.fara zargin soyayya muke.


A wurin aikinsu aka kawo tallar wani makarantar girki, kafin ya dawo ya saya min Form ya cika min sannan ya kawowa Mama ta gani, ban ji dadi ba amma kuma ganin shine ya kawo min na mai da hankali na shiga makarantar, tabbas akwai inda zaka rena kanka, domin ina shiga makarantar na hadin gwiwa wasu mutanen kasar waje ne, larabawa da turawa, sai Hajja Yaana wacce ta bukaci so tayata budewa, ita din Yar shehun Borno ce. Haka yasa muka mai da hankalinmu. Shekara daya muka yi akan girki amma kafin na gama na samu satifiket a bangarori na makarantar da dama, saboda kwazona da mai da hankali akan abinda ya shafe ni, haka yasa muna gamawa na kara mai da hankali na rike baiwata gam.


Ana haka aka yi bikin Bakura da Sadika. Muka sha biki sosai amma sai da aka yi ta girma domin kawai Baba ya dauki hidimar abinci ya bamu, karshe sai da Mama ta dauki kayan abincin ta maidawa Baba case ya mutu, sai dai Baba da yayi walima mune muka hada mishi kome sannan muka samu kanmu. Haka rayuwar gidan yake. A hankali aka yi ta bikin yan matan gidan har aka zo ɓangarenmu. A lokacin ne aka yi bikin Ummu Kulsum da Ummu Rooman, hankalin Mama ya tashi domin lokacin da Baba yayi maganar hada ni da kawu gwani hankalin Hajiya Balkisu ya tashi inda tace ko a fada auren ko ta tsine mishi albarka, haka ya bar ni ya auri wata yarinya Mariya, bayan nan aka yi auren Salman Bamai, babu kowa sai yayan rikon Umma da Ummi.


Nasan Mama tana cikin damuwa amma Allah ya gani ba ni ce na hana kaina miji ba, domin ana haka nayi ta samu manema sai sun zo zasu gudu, wani ma sai anyi maganar aure rimi-rimi har manyan sun shiga an kawo sadaki za a fasa, sau uku ana haka kawai sai na daina bawa kowa fuska. Akwai wani taro da aka yi a unguwarmu, wanda ya janyo aka yi ta zuwa sayan abincin, maza ne guda uku suka shigo shagon abincin nasan dayan yana yawan sayan abinci da safe. "Barka dai Hajiya kwana biyu bana ganinka!" "Aunty Baby nayi tafiya ne!" Dariya nayi ina faɗin. "Har da kai a cikin masu kirana aunty!" "Eh mana!" Ya fada cikin dariya. "Me za a zuba maka!" "Shinkafa da wake, da soyayyen kifi ayi min hadin kullum dai!" Shinkafa da wake yake saya, sai salat da kifi, sai tsimi. Haka kullum yake saya kuma za ayi mishi takeaway guda ɗaya. "Jamilu anan nake cika cikina!" "Hmm na ga alama!" Ya fada yana bin inda nake da kallo. "Me za a saka maka ka fada?" "Idan akwai tuwon alkama miyar kuka! Sai mana wani iri suke da shi!" "Aunty Baby wani irin nama kuke da shi!" "Akwai na kaza, na rago da na saniya!" " A saka min kirjin kaza!" "Tow!" Shigowa Uwani tayi tana faɗin. "Aunty Baby an gama dan waken da alalen!" "Tow zo ki mika musu, na dauko." Shigowa tayi ta mika musu na shiga cikin gidan na kwaso kayan na kawo. Ina kawowa kuwa aka.fara shigowa ana karban abinci, Mudan yana ta zuwa yana kaiwa kasuwa musamman wadanda suka yi booking. " "Alawan anan suke abincin ne?" "A cikin gidan nan mana, gidansu ne kuma ko yaushe ka zo zaka samu abinci da dumi. Babu abinda basu sayarwa domin local food ne amma kuma luxury restaurant ne da sai ka jijjiga aljuhunka!" Ya fada yana shan ruwan tsimin. "Aunty Baby a bani takeaway na ga kudin abincin!" Ya mika mata kuɗin su bakidaya.


"Na gode sosai!" Na saka mishi wanda yayi guzirinsa, haka rayuwata take tafiya. Sannan a gefe guda wannan Jamilun a nan yake karyawa, abincin rana da na yamma da Uwani take yi. Wasa gaske sai gashi yana niman shigo min da zancen soyayya. Duk yadda na kaucewa soyayyarshi haka ya takura min, ban san ya aka yi ba wata juma'a bayan an sako masallaci ina ta fama da almajirai da wani ya saya musu abinci ina raba musu, dan gaba da mu, ana daurin aure ne. Unguwar an cika sannan wasu na ta shigowa na sayan abinci, sannan duk ranar juma'a an fi yin abinci dayawa saboda sadaka. Sannan an fi cika gaskiya. Kaina yayi zafi ina fama da jama'a. "Assalamualaikum ina niman Aunty Baby!" "Na'am gani nan!" Na d'ago ina kallonta. "Jidda ki fito mana da shegiya karuwa!" Kallon wacce aka kira da jidda nayi na ce Mata. "Ki ce musu tayi hakuri zuwa gobe yau ina da jama'a ne!" Ihu ta wajen tayi ta fara zage zage da cin mutuncina, ban kulata ba sai da na ga haukar tayi yawa na fito an cika ga yan aurin aure sun fito ana ta tsayawa. Zakiya da bata da hakuri ta nufe su na riko hannunta. "Uwani ita ɗaya ce kyale su!" "Baiwar Allah ban san wacece ke ba, amma kiyi hakuri idan na b'ata miiki rai." Na juya riko rigana tayi ta baya. Na juya zan kwashe da mari sai kuma na fasa musamman yadda na ga an cika a wurin ana bata rashin gaskiya. "idan akan Alhaji Jamilu ne ki je bana bukatar shi, domin bai isa da ke kuma kin nunawa duniya cewa ke mahaukaciya ce, wacce ta fi karfin Mijinta. Ban tab'a rigima da kowa ba a unguwar nan tun tashina, idan don shi ne ba zaki mai da ni karya yar uwarki ba, ki je da Mijinki Allah ya baku zaman lafiya!"
Na juya ina me komawa shago, rintsa idanuna nayi,ina kallon mutumin a cikin idanuna wanda girmanshi da kwarjininsa ya hana ni marinta, "Malam Inuwa wacce yarinyar nan?" "Agolan Bulama ce." "Amma tana da tarbiyya sosai!" "Ai don ma baka zauna da ita ba ne, yarinya ce matuƙar hankali da sanin ya kamata." "Hmm ko ban zauna da ita ba zan bada labarin haka a gaba, yadda ta d'aga hannu zata mare ta kallonta nayi ta sauke hannun. Irin wannan yarinyar nake ta nimawa Tafida wacce ta san idanun da darajar na gaba, Alhamdulillahi na samo mishi ita."


Kwana biyu a tsakanin muna cin abincin dare aka kira ni wai Jamilu yana kirana, na san ina son nayi aure duk da ba wani jimawa nayi kawai hankalin Mama da yake tashi ne yasa nake ganin gara nayi auren, tunda na fita yake bani hakuri amma ban ce mishi kome ba,.yana gamawa na ce mishi. "Kayi hakuri kawai, Allah ya baka wacce ta fini." Na juya na koma gida, ni a zatona zai bar ni ne a'a haka ya cigaba da zuwa shigona. Bana kula shi abinci yake zuwa ya saya ya tafi. Bayan kamar wata biyu ya daina daga nan na sakawa raina hakuri babu amfanin saka kaina hakuri da mai da kome ba kome ba, duka-duka shekarunta ashirin da biyar ne zuwa da shida kawai ganin kannena duk sun yi aure yasa Mama take cikin damuwa. A duk shekara akwai wani Alhaji Mu'azu yana daukar nauyin girka abincin bude baki da na asuba ana rabawa sadaka. Sai da ya rage wata daya za fara azumi Allah ya mishi rasuwa, a wurin rasuwa mabukata ke ta kukan rashin da aka musu, bayan anyi jana'izar shi wasu daga cikin Yaranshi suka dauki nauyin abincin kamar yadda Babansu yake yi, bayan sun gama kome da aka share makoki suka ce sun fasa. Domin basu gayawa mana sun fasa ba sai da azumi ya rage saura sati biyu a lokacin yake bada kudin kayan abincin wata guda. Abin ya dame ni sosai domin raina yayi masifar b'aci, ana cikin wannan yanayin aka ce an samu wani ya dauki nauyin abincin. Kuma yazo yana wurin Baba. Sai a lokacin Mama take ta zolayata. "Ummu ina zaki kai son kuɗi ne haka?" "Allah Mama ba wai don kudin da nake samu ba ne kawai sadakar yana da amfani. Sannan ina shan addu'a a wurin Mutane." "Allah yasa mu dace!" "Amin nace mata!" "Hadiza!" Muka tsinkayo muryan Baba yana kiranta, mikewa tayi ta fita can ta kuma dawowa suka fita da shi. Koda ta dawo ban kuma bin ta kanta ba, sai dai na ga ta fita zuwa gidan Mama Amina. Ban san me ya faru ba na ga dai sun dawo tare suka tasani a daki ana ta min wani irin bayani da ban gane kanshi ba. Ni lissafi idan ba na abinci ba ai gani nake kamar bata lokaci ne. Ni dai washi gari na shiga kasuwa nayi sayayya sosai sannan na dawo muka ci aiki kamar ba gobe.


Har ana gobe za a fara azumi bamu daina aikin ba, da yamma muna busar waje aka shigo mana da nama, wai Alhaji da ya dauki nauyin abincin azumi ne ya turo da namar, ni dai haka muka gyara aka saka a firji, washi gari aka fara azumi duk fadin duniya muka yi kunu da kosai, sai shinkafa da mita wanda yaji nama. Idan aka gama muna sakawa makota da mutanen gidanmu, duk da Mama ta gaya min nayi harkan gabana kada na damu da kowa nayi abin da na ga xan iya shi yasa ban tab'a kallon yan gidan mu a cikin rayuwata ba. Duniyata da Uwata da kannena sune a gabana domin ko lokacin da kanina Ahmad ya samu scholarship ba karamin artabu aka yi ba wai Baba yana fifita yan dakinmu. Haka ya zuba musu ido. Ahmad ya tashi a tsakaninmu duk abinda ya gani na hidimar gida da kome sai ya kira ya gaya min sannan ta tura min ta facebook din Uwani domin ni dai irin wannan haukar bai dame ni ba, sai daga baya wani zuwan shi hutu ya zo min da waya waya. Anan yake turo min da kayan kitchen mu kuma da mama muna tura mishi kudi, idan ya saya dayawa sai ta turo min ra cargo. Idan aka kawo gidan Hajiya Amina muke kaiwa tana da extra daki da take zuba min shirgina. Hatta kayan gado a can ya saya min aka kawo min. Sannan a gidanmu ana ganin duk wahalar da nake yi ba mamaki idan bikina ya tashi nauyin zamu daurawa Baba shi yasa ake yawan samun rigima akai na. Azumi yana kawai goma da safe na je gaida Baba yake gaya min. "Hajiyar tuwo da miya, bayan tarawi akwai bakon da zaki yi don Allah a tsaya a mutunta shi kamar yadda na san ki da halin ƙarammaci!"


"In sha Allah Baba!" Daga nan na dawo daki ko Mama ban gayawa ba, haka muka yi ta aiki bani da kuzari, bayan ana sha ruwa ina kwance yaro ya shigo . "Aunty Baby ana sallama da ke!" "Tow gani nan zuwa!" Na fada ina kwance. "Tashi ki je mana!" "Tow Mama!" Ma fada ina jin damuwa, haka na shirya na fita akan zan musu iso zuwa parlourn baki. Ina fita na hango su a jikin Motarsu, domin nace haka ne saboda dayannsu da ma gani cikin motar karasawa nayi zan musu sallama daya ya ce min. "Kanwata don Allah ki shiga gidan can ki kira mana Ummu Hadiyya!" Sai naji na diririce, baki na yana rawa na ce musu. "Ai ai ni ce!" Yana latsa waya ne bai san lokacin da ya d'aga kai yana kallona ba. Karewa kunna torching wayar yayi yana haska ni daga kasa har sama kafin suka kwashe da dariya, su biyu shi wanda yayi min magana bai yi dariya ba, sai cewa yake. "Meye haka Tafida Mahmoud Meye na biye shi kuna dariya." Idanuna ne suka cika da kwalla san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Ina tsaye sai dariya suka tare da faɗin. "Wai Tafida kayi kamuwa wai ina ruwan kashi da rai! Ka ga hancinta kuwa ina ruwan mitsil!" Wani irin kuka ne ya zo min. Har jikina yana rawa, na juya xan tafi shi wanda ya haska ni ya ce min. "ke Ummu kike? Tow ki gayawa Mutumin da ya zo gidanku idan ya sake zuwa ki ce ni tafida ban miki ba." "Dalla me yasa kake yin haka ne? Mahaifinka ne fa kake cewa mutumin da yazo kamar wani sa'anka!" "Deen babu ruwanka da ni, ya ga Yan mata kalar gari a hada ni da wata kucaka wacce bata da bambancin da yar kauye. Idan kai haka ka shirya rayuwarka ni tawa da banbanci....
#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


09


"Kyale shi Tafida idan kana niman bagidaje ka samu Deen ai magana ya ƙare, banza ko shi aka hada da wannan me magana busashen kifi ba yarda zai yi ba, don Allah duba ta kamar wacce aka gama rabon halitta aka manta da ita sai daga baya aka yi karo-karo..." Bangaje kafadarshi mutumin da yake musu fada yayi yana faɗin. "Sannu Ubangiji da ya iya tsara halittar kowa!" "Kada dai ka fita musulunci don na lura ba Tafida aka turo ganin yar baby ba kai ne" ya kwashe da dariya, yana.nuna Deen din. "Kanwata" ko sauraronsu ban yi ba na nufi gidan a zaune na durkusa na fashe da wani irin kuka, na kai minti ashirin a wurin kafin na mike zuwa cikin gida sai da na wanke fuskana, sannan na shiga dakin Mama na ce mata. "Na dawo Mama" na fada zan fita daga dakin. "Ya kuka yi?" Na ji ta tambaye ni. Bakina yana rawa dake ban saba mata musu ba na ce mata. "Allah yasa haka shine mafi alkhairi!" "Alhamdulillahi Ubangiji ya tabbatar da alkhairi." Juyawa nayi zan fita ta ce min. "Ummu Hadiyya Yaron yayi miki?" A hankali na kara juyawa hawaye na zuba min. Na ce mata "hm!" "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah lokaci yayi da zaki tafi dakinki,masu ganin ba zaki yi aure ba su sha mamaki." Hawaye ne ya kara zubo min Mama bata damu da nawa damuwar ba bukatattar nayi aure ta huta da maganar har yau na ki aure. Bani manta lokacin da Ummu Rooman ta haihu ranar sunan da muka je gidan sunan haka wasu daga cikin dangin Mama suka yi ta min magana wai ina nan ina ruwan idanun. "Ina zata yi aure tana jin kudi na shigo mata, sannan har da laifin Hadiza da ta rike mata kan maciji tana wasa da wutsiyarshi." Ni dai ban ce kome ba, haka suka gama mita wai naki aure. Haka na shiga dakinmu. Na kwanta sai na fahimci barcin ba zai min ba, kawai na tashi ma nufi waje nayi alola na zo na gabatar da sallah nafilla, ban tab'a ganin daren da yayi min tsawo kamar wannan daren ba, sam barci ya kaura ce min, domin har karfe biyu da rabi yayi muka daura abincin sahur bana jin ko gyangyadi, haka na yi ta aiki har muka gama hudu saura Mudan yazo yayi ta fita da shi ana rabawa mutane. Uwani ta lura da bani da kuzari ta ce min. "Aunty Baby ko zan zubo miki tuwon ne?" "A'a zan sha lipton ya isa!" Haka muka yi sahur sannan muka kama aiki sai da aka yi sallah asuba muka kwanta, musamman ni wurin karfe daya na farka. Dakin Mama na nufa da na leka na ganta da Aminiyarta, "Mama Amina ina kwana?" "Lafiya lau Ummu kin tashi lafiya, sai nake jin abin arziki Allah ya tabbatar da alkhairi!" Gyada kai nayi kawai na dawo dakinmu na kwanta. Ban san me suke ta yi ba sai dai azumi na da goma sha biyar suka sake dawowa, da yamma bayan sallah la'asar. Tunda aka gaya min na kasa fitowa, Mama ta ce min. "Wai baki ji baki kika yi ba?" "Na ji!" Na saka hijabi na fito a parlour Baba na same su dake yana gida, "gaida da shi na fara yi sannan na gaishe su, ashe yau har da Babansu suka zo!" Hadiye yawu nayi domin na ga shi daya ne. Babu abokanshi. "Kasan yayi dan majalisar wakilai kafin ya dawo, ko nace suka dawo da shi yanxu yana tare da shugaban kasa ne, Alhaji Bulama ka ganshi talatin da bakwai yake so nake ya samu macen da zata rufa mishi asiri, yar mutanen kirki wacce zata haska mishi gidanshi da na Yaranshi. Shi yasa na ce maka xan turo shi ya ganta, jiya nayi magana da shi ya ce min na tambayi Yarinyar shi tayi mishi sai dai wai ita ta ce bata amince ba!" Mutumin ya zuba min idanun da nayi kasa da kaina, ina jin kwalla na cika min idanu. "Ummu ce ta ce bai mata ba? Amma yadda nasan Ummu ba zata fadi haka ba, domin ranar da suka zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login