Showing 9001 words to 12000 words out of 241571 words
Chapter 4 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
na dawo!" "Ba kome Allah ya raya mana su tafarkin addinin Muslunci." "Naji ance ya shigo cikin gidan nan ko?" "Eh!" Hajiya Kaltuma Amarya Abbansu ce kafin ita akwai Hajiya Hawwa tana nan itace Uwargidan Alhaji Muhammad Jadda, sai dai dukkanninsu Mahaifiyarsu Tafida ita ce Babba amma aka samu rabuwa, tana Njamaina na kasar Chadi. "Inna baki ce kome ba?" Harara ta watsa mishi ta ce mishi. "Ke Tafida ki fita idanuna na rufe wallahi kika sake raina ya b'aci sai na miki shegen duka." "Assalamualaikum! Dama nasan za ayi haka kazo wurin uwargida sarautar mata ne?" "Hmm!" Ya fada yana mikewa ya ce . "Muje ka kai ni gidansu wancan yarinyar!" "Wacce kenan?" A hazuke ya dannawa Deen zagi. "Bana son kutma uba, Black gidansu zaka kai ni!" "Ai kuwa ban san hanyar gidansu ba!" A fusace ya sa kai zai fita Deen ya riko shi. "Kada ka sake ka fita wani ya kai ka gidansu Ummu a wannan lokacin, ka san waye kai yanzu? Ya kamata ka iyawa kanka haba don Allah, wai me Ummu ta tsare maka ne?" Buge hannu Deen yayi yana faɗin. "Zanci ubanka wallahi xan maka rashin mutunci ni zata hada da iyayena?" Ya fada da karfi, "matsalarka kenan baka da hakuri, kowa ya raina matarka saboda a gaban kowa zaka ci zarafinta." "Safiyyudeen zan maka rashin mutunci wallahi!" Ya fada cikin fada kafin ya daura da cewa. "Don ina binta ba yana nufin ina sonta ba ne, Yarana ma da ta zuba min zan je na amso su wallahi na fasa bar mata su, har Ni zata hada da iyayena!" Kafin kace kwabo an taru a tsakar gidan, ran Alhaji Muhammad Jadda ya kara b'aci amma yayi murmushi irin nasu na manya ya kalli Hajiya Kaltuma ya ce mata. "Dole sai ya biya abin da yayi Kaltuma." "Aliyu bai da laifi fa, har yau ina kan bakana da ace lokacin da ya rasa Uwa Inna tana nan da zai samu sauƙin haka, kai ka yanke hukuncin rabuwa da Aisha, sannan ka kwace shi kasan illar da ka mishi? Ka saka ya tashi mara hakuri, Eh Aliyu yana da zurfin ciki domin babu wanda yasan irin ukubar da ya sha a hannu Hawwa da shuwa, don haka bai tab'a gayawa kowa ga damuwarshi ba, akan Ummu Hadiyya ne baya iya hakuri, akan Ummu Hadiyya ne baya boye b'acin ransa, domin duk abin da ya faru kai ne sila, ban da Allah ya taimaka Uwarshi bata barci a kanshi har yan uwansa ai da abin da Aliyu zai zama sai yafi haka tow Allah baya barci kuma shi ba azzalumin sarki ba ne. " ta fadi haka tana fitowa waje, ganin yadda aka tsatssya yasa ta cewa. "Da alamu matsalar gabanku bai ishe ku ba ko ? Har sai kun kara da na Tafida!" Tuni kowa ya watse, ta shiga dakin har lokacin bai daina fada da masifa ba. "Deeni kyale shi ya je, tunda har Ummu Hadiyya ta iya tsallake Yaranta a gadon haihuwa babu abin da zai bata mamaki ko tsoro ya je ya tunkare ta, har yaushe zaka girma Baba Ali? Yaushe zaka yi hankali? Tow zuwa yanzu Borno da Al'ummar borno suna kanka sai ka cigaba daga inda ka tsaya, Amma hargowa da hargagi ba zai kara maka kome ba, sai dariyar waɗanda basu son kayi gaba. " daga haka ta juya ta bar dakin Inna, a can bangaren Shuwa daurawa suke suna kuncewa domin Aliyu dai irin mutanen nan ne da yau aka yi aiki kansu gobe zai iya yin sanyi ko ya lalace. Don haka koda Samha ta gaya mata Ya Tafida yana can yana fada akan Ummu taki zaman dakinta tayi jego wani murmushi ya kwace mata, "Alhamdulillahi ta nan muka yi nasara......🤔YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
04
"Ke tashi aikinmu yayi kyau!" Girgiza kai Yarta Sa'adiyya tayi tana faɗin. "Ba dai akan Tafida ba, na san waye shi na kuma san me yake yi a cikin kashi goma na aikinmu dakyar daya yake kama shi, tow bari na gaya miki a dakinta ma ya kwana karewa kenan kin ga kenan babu batun wani aiki yayi kyau. Ni na gaji da zubawa yan iska kudi ki nimo wata hanya amma Tafida baya cikin mazan da asiri ko tsafi zai kama su, domin nayi imani da Allah kaf gidan nan babu wanda ya kai shi ibada da tsayuwar dare, lalacewa da ake kallon yayi yafi wadanda ake musu kallon kintsatsu sannan ke kanki shaida ce yadda na gama lalacewa da bin maza ina amsar kudi tow Tafida a idanunku yake mutumin banza amma a zahirin gaskiya yafi kowa samun Allah, sannan ban da sharrin da muka mishi bana jin har akwai abin da zai kama Tafida tunda kowa ya ga abin da ya faru hatta matarshi ta gani amma ta kare tana zama da shi a haka ne dai ki nimo wani hanya idan har haka zai saka ya rabu da ita wallahi bar ganin yana ihu na rantse da Allah son da yake mata ya wuce baki ya faɗa, domin kuwa na gani akan idanuna."
"Ke kada ki mai dani yar iska, kina nufin Aliyu yana son wancan bakar Yarinyar?" "Kwarai da gaske, baya sonta zai dinga hawa kanta yana sauka? Baya sonta zai dirka mata ciki? Baya sonta zai haukace ta ce ta dawo dakinta tayi suna? Jiya fa har na shirya zan bishi ya ce kada na sake yaga kafata a wurin bikin rantsar da shi tunda bai min alƙawarin nice first lady ba, gaya min wacece First Lady?" "Ke mana, ai ya gayawa Babanki tuntuni ke zai bawa wannan matsayin." "A'a ba dai haka aka yi ba, sai dai idan kune kuka roka min ya bani!" "Ke ki min shiru yarinyar da kike magana akai ko jami'a bata shiga ba balle ayi maganar wani matsayi. Nasan nan duniya babu wata first lady sai ke!" Mikewa tayi zata fita domin ita kan Sa'adiyya bata jin zuwa yanzu zasu sake samun kan Tafida don yayi gaba. "Ina zaki bamu gama magana ba!" Juyawa tayi idanunta cike da kwala ta ce mata. "Watannin baya kin san dalilin da yasa Tafida ya kora Hadiyya gida?" Girgiza kai tayi tana kallon yarta da take ciki da mamaki. " murmushi Sa'adiyya tayi tana faɗin. "Nice nan na saci kudinsa na yi amfani da shi, kuma nasan bayan shi da Hadiyya babu wanda yasan inda yake ajiye kuɗi, na kwashi sauran na kai dakinta na boye." Goge hawaye tayi tana kallon Hajiya shuwa da kyau, "amma kin san me? Da yazo yana bincike na ce ban sani tunda ban san inda yake ajiyar ba, hmm kiran Hadiyya yayi ya ce ta tafi gidansu sai ya zo da kanshi. Bayan yasan ko me zai ajiye ba zata tab'a dauka ba. Tana barin gidan ya turke ni sai da na gaya mishi gaskiya ya kyale ni kin san me ya ce min? Kin ga wancan yarinyar da muke renata ko me na ajiye idan ban ce ta ɗauka ba da shi da banza daya ne, wallahi kin yi na karshe kada ki sake raina ya kuma b'aci wallahi kika sake na kuma kama ki sai na wulakanta ki!," murmushi tayi tana share kwalla ta cigaba da kallon Hajiya Shuwa. "Kina tsammanin zan kyale ni ne idan ya gano abubuwan da nake aikatawa na son rai!" Daga haka ta juya huci Hajiya Shuwa take tana jin lallai koda zata yi yawo tsirara sai yarta ta zama first lady na Maiduguri.
---
*Ummu Hadiyya*
Cikin barci naji wayata tana kara, a hankali na lallubeta na saka a kunne. "Assalamualaikum!" "Waalaikumun salam, Ummu Hadiyya!" Bude idanuna cikin nauyin barci nace. "Na'am?" "Maman Ilham ce, gamu a unguwarku ban san inda xan fara ba ne!" Tashi nayi zaune nace mata. "Aunty Saimah! Ki ce a nuna miki gidansu Aunty Baby'sMama kitchens!" "Ok!" Tashi nayi zaune ina me tattara sumar kaina, domin na wanke dazun da safe, na saka ribom na kama shi, sannan na shiga ban daki na kama ruwa na fito, ina kokarin zama naji sallamarta. "Assalamualaikum! Ikon Allah matar nan ashe har kin haihu? Ni da nace ki gaya min idan haihuwar tazo muje asibiti." Murmushi nayi ina sosa kaina, ina kallon Yaran. "Ikon Allah dama biyu ne Abban Ilham yaki gaya min, lallai zai sani." Ta fada tana shigowa dakin. "Aunty Saima zauna mana!" Na fada ina kokarin saka hijab xan fito waje. "Idan ta ni ce koma ki zauna sai da naci abinci kafin na fito kin san ba don rantsar da Tafida ba ni da borno sai kin haihu!" "A'a bari a kawo miki ruwa!" Haka na fito na samu Uwani ce a tsakar gida tana tattan kunun yamma. "Uwani ki had'a min kome ina da bakuwa!" "Tow Aunty Baby!" Na koma ciki, ina hada faɗin. "Kawai sai kuka ji labari ba!" "Wai kawai ashe ke da Aliyu kuka tawo asibiti!" "Eh wallahi kin san Hajiya Kaltuma bata gari tafi bikin yar Yayarta kuma kin san hidima baya karewa a familynta. Kin ga Inna kuma girma ya cimmata town waye zan kira a wannan daren?" "Hajiya Hawwa da Shuwa fa!" Murmushi nayi bance kome ba domin bana fatan na fadi kome har abada tsakanina da su idanu. "A'a kawai Ni ce nace muje asibitin idan ban haihuwa ba a nimo su." "Amma Ummu baki dauki kasada ba?" "Salamun alekum!" "Uwani oho Assalamualaikum ake fada fa!" "Tunda kin gane ba shi kenan ba, ke dai akwai son gyarawa mutum abu!" Dake abokiyar wasata ce yar Kanin Mama ce na kuwa ce mata. "Ai kuwa kina yin kuskure zan gaya miki katuwa kawai!" "Eh na yarda ke kuma Yar mitsila!" Dama can tun fil azal haka muke da ita. Ta juya tana kallon Yaran ta ce min. "Allah yasa kada kuyi halin Aunty Babyn roba!" "Allah ya taro mana ke!" Na fada ta juya ta gaida Aunty Saimah. Dalilin shiririnta Uwani aka share batun haihuwa, muna cikin hira sai ga Yayun Aliyu mata da biyu, Aunty Maryam da Aunty Rukayya, kallon Maman Ilham suka yi. "Eh ba dai Ya Abubakar ya baki labari ba ?" "Eh ai kunsan haihuwa da mutuwa bata boyiwa kafin ya gaya min makotana daga Abuja suka kirani suna min barka ashe har IG an daura yaran Baby'sMama kitchens." Tab'e baki Aunty Rukayya tayi tana latsa wayarta. "Ina wuninku!" Na gaishe su, a lalace suka amsa. Ban damu ba itama kuma Maman Ilham abin ya bata haushi tuni ta hade rai, ta dauki zobo tana sha. Taki mika musu Yaran. "Uwani!" Na kirata. "Aunty Baby gani nan ba sai kin fada ba, the first lady of Borno state." Kallon juna muka yi da Maman Ilham muka saka dariya. "Wato Uwani nan taku yar gari ce." Shigowa tayi da katon ture ta ajiye musu cikin zolaya ta ce min. "Banda mugun hali irin naki, kiri-kiri kin hanani ganin kyakkyawar mijinki, ki rage kishi, sai dai ya kashe shi da soyayya da shagwab'a. Don Allah kada ki saka yaje office yana kasa aikin al'umma." "Uwani zanyi zagi!" Tab'e baki tai tana faɗin. "Idan kin zage ni ma kin yi a bawo, domin nice zan shiga gidan mai girma Gwamna a ta uku!" Ko su Aunty Rukayya da Maryam basu yi niyyar dariya ba, suka kwashe da dariya. Yarinya ce Uwani amma ta iya mu'amala da mutane ga kayan saka dariya. "Kada ki damu indai tafida ne kamar kin ganshi."inji Maman Ilham, murmushi tayi ta fita kamar ba zasu sha ruwan ba suka sha Aunty Rukayya ta ce min. "Sai mun roka ne zaki bamu Yaran!" "Amma a bisa alada ba ita ya dace ta mika muku Yaran ba" ta fada tana mikewa ta dauko yaran ta basu. "Ikon Allah! Maryam yaran nan kamar lokacin da Hajiya ta haifi Tafida sak-sak da shi,.ina da hoton har yau." "Wai ni kuna jin labarin Hajiya kuwa?" Inji Maman Ilham, kallona suka yi suna jiran karin bayani. "Baby ya labarin Hajiya?" Hmm kusan wacece Hajiya? Mahaifiyarsu ce fa, idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Hajiya tana lafiya sai dai kuma bata jin dadi gaskiya." Na fada ina dauke kaina. "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah!" Na fada bayan sun hade baki sun mata fatan sauki, hira suke jefi-jefi Mama tayi sallama ta shigo. "Oyoyo Mamana!" Dakin ta shigo tana me sallama. " Sannu ku da zuwa. Uwani baki kawo musu alele ba sai kayan ruwa ba kome a gabansu baya akwai alele da dan wake da doya da kwai maza a kawo musu ga babba me shiririnta da ta kasa magana, a zuba musu farfesun kajin nan maza don me Alhaji da Babanku suka kawo ba don a ciyar da masu zuwa Barka ba, maza a kawo musu abincin." Ta fada tana me kallona. "Kin ci abinci? Jego ba zai yiwu ba sai ciki ya dauka musamman wancan cinye du din don yafi yar uwarsa cin abinci. Maza hada shayin kisha." "Mama nasha fa bakina ne ba dad'i." "Ayya Ummuna daure kisha idan baki ginu ba, ba zaki iya daukar wani laluran nan kusa ba, amma idan kika ginu nan da wata shekara wani labrin ake." Mamaki ne ya maka su yadda suka ga Mama tana ritita ni, haka Uwani ta shigo musu da abinci, tana ajiye musu Mahira tana kawo min tuwon alkama miyar kuka danya wacce aka daketa kamar karkashi ta sha kayan kamshi, ta ajiye." "Aunty Baby Yan grp suna gaida ke, wai sun yi kewarki don Allah yaushe zaki cigaba da sanwata alfaharina!" "Ke Mahira yafi can kyaleta da wayarnan!" Dariya tayi tana faɗin. "Sweetheart kuna barci ko? Sai kun tashi xan zo muyi wasa;" "Sai ki hada har da kasa da yashi a bude muku fili Sabuwar uwa ta fara hauka!" Ta fita tana dariya, duk kin Allah aunty Rukayya sai gashi ta sake suna cin abinci hankali kwance. Fita Mama tayi ta bamu wuri can sai gata da wani kofi dauke da dafaffen madara. "Mama yanxu nasha tea." "Ungo naki, gyaran jiki babu ruwansa da kin sha ko baki sha ba, maza sha." Haka na amsa ina kallon madaran har mai mai yake yi kamar zan yi kuka na fara sha. "Wallahi kin more, irin wannan kulawar waye zai samu ji yadda Mamanki take kulawa dake!" Inji Maman Ilham, dariya nayi kaina a kasa na sha rabin madaran na ajiye. "Kin san nice Babba kannena duk ba ita tayi musu jego ba, asalima ba a dauko wanka a gidan nan, nice dai nazo da kaina!" "Assalamualaikum Mama ga sako daga Baba wai dafawa Aunty Ummu Baby!" "Sai dai Uwar baby yanxu ta tashi daga baby ta koma Uwar baby." Murmushi Aunty Maryam tayi tana faɗin. "Kanwarki nan akwai abin dariya!" "Uwani ba, ai ba ita ɗaya ba ce a kofar shiga kun wuce wata tana sayar da abinci a shago. Zakiya kenan Yaranta ne anan suke zaune abinci suke sayarwa idan sun yi aure ko kafin su yi aure za a kawo mata wasu." Ware idanun suka yi. "Kamar Ya?" "Kusan dake mu talakawa ne amma muna da burin mu cigaba idan har zaki iya hakuri ki kuma kame kanki zaki nime kudi Mama bata da matsalar kome, yanxu ita Uwani public health ta karanta, kuma next year zata gama, tana abinci da safe na karyawa an fara maganar aurenta idan tayi aure Akwai kanwaart zata zo ta fara karatu da sayar da abinci." "Kuma ya batun kayan daki?" Dariya nayi ina na saka hijab na dauki Mufidah da take dan rigima na bata ruwa ta sha sannan na bata nono. " kayan dakina waye yayi min? Ita tayi min haka suka kayan dakinsu da kome hatta garan da zata miki na shekara daya duk ita ce! Ai mace ce me kamar maza." Na fadi haka ne saboda yadda suke ganin kamar nauyi aka daurawa Dan uwansu. "Ummu ni gas cook ɗinki nan Amma ba a Nigeria aka saya ba?" "Eh kanina Ahmad da yake Turkiyya ya gani ya turo min na tura mishi kudin ya kawo min an karshe hatta kayan kitchen dina da furniture duk a can muka saya." "Amma aka ce mana Abbanmu ne yayi!" "Wai da gaske?" Inji Maman Ilham, murmushi nayi nace mata. "A'a kayana ne da Uwata tayi min da guminta domin yar kasuwa ce kuma a gidanta nake sayar da abinci." "Amma mu kuwa aka gaya mana duk abin da aka kawo miki Abba yayi miki!" "Eh zasu fadi haka saboda yadda Abba ya dauke ni kamar yarsa!" "A bar wannan zancen yaushe zaki koma domin mun fi son ayi suna a can!" Murmushi nayi ina kallon Aunty Rukayya da tayi maganar nace mata. "Ina ga mun magana maganar nan da shi ai, ba zan koma gidan Aliyu ba, ai yanzu ya isa matakin da yake bukata suna kuma zaku iya zuwa ku dauki Yaran ku tafi dasu babu matsala, amma yadda na dawo dakin Uwata babu me fitar dani sai gawata!" Na fada ina murmushi. "Wai me yayi zafi ne? Naga dai kuna zaune lafiya zaki dauko tashin hankali, daga haihuwa da rantsarwa sai ya zama tashin hankali da niman rabuwa yanzu haka yana can yana ta faɗa." Cikin girmamawa nace mata. "Ko me zai yi yayi kawai amma na zan koma ba." "Kamar ya ba zaki koma ba?" "Akan me kike tambayarta? Kada ta koma ya ce anjima idan yazo zaki bashi Yaranshi." Gyara zama nayi da kyau nace musu. "Ku bari na hada muku har da kayansu ku tafi da su!" Na mike tsam na fara hada kayansu tsaf, sannan na ajiye musu. "Gasu nan, idan kun isa ku ce ina jiran sakonshi." "Ummu Hadiyya ban san ki da wannan halin ba!" Murmushi nayi mata nace mata. "Maman Ilham, baki sanni da wannan halin ba, amma yanxu zaki sani ai sun san waye Tafida don haka su dauke Yaranshi su kai mishi bani daga cikin Matan da namiji zai yiwa barazana da Yara kafin na same su sai da na shekara ashirin da