Showing 237001 words to 240000 words out of 241571 words
Chapter 80 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
matukar son kanshi da son zuciya, kuma ko yau na samu dama zan cutar da Ummu amma wallahi ban san yadda zan gaya mata kome ba, ina godiya ga Allah da ban saki Ummu ba."
"Hmm" kawai Deen ya fada mishi, Hajiya Kaltuma kuwa kamar zata hauka domin kashe mazajenta da Mahaifiyarta tayi ta cewa gasu nan, ita bata yi hauka ba ita bata zauna a mai lafiya, Maryam kuwa kamar ta zare a garin Maiduguri domin duk inda ake tsammanin Naziha tana nan babu ita, har cigiyarta aka yi tayi babu labarinta.
Duk wani Yawon campaign da ake yi Tafida bai je ba. Domin ya matsu ya bar musu mulkin ya huta. Baban Ummu ya kira Abba ya gaya mishi Naziha tana wurinsu, amma maganar ba ta waya.ba ce, idan ya samu lokaci yazo, a satin Abba ya je, da Inna da hajiya Salamatu, aka tattauna akan matsalar Ummu da Tafida, yayinda Mama da suka same ta a nan, ta ce musu. "Rabuwar Ummu da Tafida mai sauki ne, amma yan iska ba zasu iya rabuwa da juna ba, idan kuna ganin karya ne ku barshi da ita su zo na gaya muku, Ummu tana bori ne, yana zuwa zasu shirya." Haka suka yi ta tattaunawa. Karshe aka tsayar da cewa matukar suka bukaci komawa tow kofa a bude yake idan kuma Ummu tace bata bukata babu dole, amma maganar gaskiya kowa yana son Ummu da Tafida.
Haka suka watse Alhaji ya bukaci a bashi Naziha ya tafi da ita. Amma tace a'a ba zata bishi ba idan ba Ummu ce zata koma gidan Uncle Tafida ba, domin da haka zata kaucewa fitinar mahaifiyarta. Don zata iya lalata mata kome da ta samu. A lokacin da Maryam ta ji labarin Naziha tana wurin Ummu, ta hauka ce ita sai dai a bata yarta Abba kuwa ya ce ya ji labarin ta je wurin Naziha, Sai ya tsine mata, dama bai tsine mata ba tana cikin masifa domin kuwa bashin da ta tarawa kanta yasa aka yi ta zuwa kotu.
*Ummu*
Naso Naziha ta koma wurin Mamanta amma Yarinyar taki, don haka na kyale ta, na cigaba da Binta da addu'a. Da fatan Alkhairi. Nima zaman da nake ba jin dadinsa nake ba haka yasa na fara koyar da yadda ake cake, Allah ya kuma dafa min, sai gashi ana yi musamman Christian waɗanda muke dangi na kusa da na nesa, suka shiga zuwa ana musu na birthday da biki da suna, a hankali na zama yar gari ana kawo min ko ina. Alhamdulillahi domin iya wannan ba karamin nasara nayi ba. Kuma naga amfanin sana'ar hannu akwai yar Baffana mai suna Atikah tana gaban Mamawo ga Kanwar Dr Sagir, mai suna Hafizah, tare muka yi aikin sai yaran makota kafin kace kwabo mun bude babban shago a kofar gidan Babana. Ko lokacin da aka yi campaign na su Tafida, naji labarin bai zo ba. Amma akwai mabiya party dinsu, sun yi odar cake da snacks. Naji dad'i sosai, yayinda wasu suka bani wani odar musu girkin abinci aka zuba a takeaway. Bayan an gama suka caske min kudina. Tuni na manta da Tafida na rungume Sana'ata.
A yanzu ina niman shekara ɗaya, Baba ya kira shi ya tambaye shi meye nufinsa akan ajiye ni da yayi, ya ce zai zo shi bai sake ni ba, hmm ban san me ya gayawa Baba, na ga Baba ya koma bayan Tafida. Haka ma Mama da Baba Bulama, babu wanda ya koma ce min wani abu sai dai sun bani tabbacin idan nace ba zan koma ba an gama magana, ashe dan waken zagaye suka min, ina zaune a gida aka yi zabin da ya girgiza kowa domin party dinsu ya sha kayi.
Bayan zab'en ne party Alhaji Hamza Goza, suka sako Tafida a gaba da cewa yayi rubda ciki akan dukiyar mutane, a wannan yanayin na ji tashin hankali da damuwa, domin sau biyu yana kirana yana cewa na yafe mishi, makiya sun mishi rubdugu, addu'a sadaka, babu wanda ban yi ba, ban san me yasa ba a tsawon shekarar da nayi a gida da haushin Tafida nayi shi, amma ranar da ya kirani naji yadda muryanshi tayi sanyi na fahimci Tafida yana cikin wani hali.
Deen da Tinah suka tsaya mishi, wani abun mamaki sai ga Abubakar tare da masu son ganin Bayan Tafida, haka yasa akan abinda ake zarginshi da shi, suka yarda yayi sata, sannan aka kuma kara rub'anya tashin hankalin da yake ganin da sauki. A lokacin Mahmud yazo, ya bada duk abinda ake zargin Tafida da shi. Ya wanke Tafida da shaidarshi ya kuma fitar da wanda yayi satar Abubakar ne tare da Alhaji Hamza Goza. Sai Hajiya Kaltuma da ta sato takardun a wurin Abba. Takardun Tafida ne ya bawa Abba ya ajiye mishi na wasu hukumomin ne na local government, sanin takardan yana da muhimmanci yasa shi bawa Abba ashe Kaltuma ta ɗauke, da wannan takardun tayi ta blackmail din Abba da cewa da iyasu sai ta ga bayan Tafida.
Allah ya wanke Tafida, bayan haka gwamnatin da ta samu shugaban kasa har lokacin party dinsu ce, take aka nad'a shi a jakadan Nijeriya a South Africa.
***
Wata asabar ina tsaye muna aikin cake, kana ganina kasan ina cikin nutsuwa tunda naji abin da ya samu Tafida na cigaba, sai naji kamar nafi shi murna, ina aikina na ji an ce min. "Mammy!!" Juyawa nayi na kalli yar yarinyar da na tafi na barta bata gama tsayawa da kafarta ba, ita ce s gabana an mata gyaran gashi gwanin ban sha'awa. Sai ga dan uwanta shima ya shigo yana kallona. Durkusawa nayi ja bude musu hannu, hawaye na zuba min. "my apples!" Na fada ina rungume su da kyau ina jin kamar an yanta ni daga azabar da nake ciki. Shigowa tayi yana murmushi. "Finally na zo niman gafara!" Mikewa nayi na bar shagon da Yran a hannuna muka shiga cikin gidanmu. A parlourn Baba na zuba mishi harara. "ka zo min da sakina?" "Ai ke tsakaninmu ba saki ba yaji, ba mugun kallo!" "Ni ba zan zauna da kai ba aure zan yi! Gara ka sake ni!" "Waye ya aike ni, ba fa zan sake ki ba wallahi!" "Na rantse!" Hmm mugu kullum yasan hanyar da zai cuce ni, ban yafe ba dai. Da iya kiss ya dawo da matattun kuzarin da nayi alƙawarin na kashe su, koda kuwa zai mutu akan sona sai gashi yayyafin da yayi ya tado min su, Nasan ina matuƙar son Tafida amma yadda muke samun rashin daidaito a tsakaninmu yasa na ke ganin Gara mu rabu, tun da ya kawo min yara ya tafi can yayi wata uku, sannan ya dawo yayi ta bibiyata yana bawa yan uwa da dangina hakuri kai Tafida mugu ne hatta Naziha sai da ya hada kai da ita, tayi ta min fushi da bori. Ga Mama da Mamawo suma bina suke har Tinah da naji labarin wai ashe sun jima suna dating da Deen, hmm amma kuma tana son shi kuma.zata zauna a bisa ka'idarshi. Mama da kanta ta kawo min me gyaran jiki, tare da rarrsshina na koma kan Yarana, sannan wanann karon dai an saka Tafida a gaba da yarjejeniyar matukar yaga ba zai iya zama.dani ba ya sake ni sun gaji. Yayi ta rantsuwa ba zai kara ba, waye ya mutu waye ya dawo, haka iyaye suka taushe ni na koma gidan Tafida karshe kasan ma muka bari. Unguwar mu ta manyan mutane ne yan boko da attajirai ce. Mun tawo da Fanna da Naziha, wacce Tafida ya mai da ta makaranta, tare da saka idanun akanta. Ana ce bayan wuya sai dad'i. Na ci azaba akan Tafida.
#RamlatManga80
Azabar da na sha a hannun Tafida da danginsa ko Makiyana bana fatan ya fuskanci haka, amma kuma yanxu zance Alhamdulillahi, sannan gefe guda daga ni har shi mun fahimci rayuwarmu ba zai tab'a cika ba, sai da dayarmu. Watanni mu goma Rayyan kanin Mahmoud ya kira Tafida ya gaya mishi rasuwar Ammyn, da aurenshi da aka yi da Khairat yarinyar da Mahmoud ya lalata mata rayuwa, Tafida yake gaya min haka, nayi mata Addu'a da fatan rahama. Sai bikin Rayyan din shima Tafida ya kira Deen ya gaya mishi yayi mishi alkhairi, kuma da alamun ayin domin yaron ya kira yayi ta godiya kamar zai yi kuka.
An yi haka da kwana biyu, muna kitchen da Naziha. Wayarta yayi kara, Fanna ta kawo mata tana faɗin. "Ke dai wallahi baki da hali, kin ajiye min waya kamar ba naki ba!" Amsa tayi tana faɗin. "Allah ya baki hakuri Nannynmu!" "Zaki sani!" Wayar ta duba, tana faɗin. "Waye?" A hankali tayi karo da wani sako da aka ce mata. _ina ta binki amma kina guduna, na gane kawai bakya bukatar mu'amala da Ni ne, amma nasan ke yar hannu ce_ goge chat din tayi, ta cigaba da aikin da muke. Na yarda babu abinda yafi addu'a, idanuna na kan Naziha, haka yasa kowani motsinta na sani, sannan ina lura da goge sakon da tayi, a hankali na ce mata. "Waye ya turo miki sako?" "Wani Yaro ne, Mammy nayi kamar da yar iska ne? Don Allah Mammy gaya min me yasa maza suke bibiyar sawuna?" Ta fada hawaye na zuba mata, jan kumatunta nayi ina faɗin.."Anya kuwa? Idanunsu ne yaƙe ganin haka" na shiga bata misali da yadda rayuwa take, da ni kaina. Sai jikinta yayi sanyi.
Bayan mun gama, muka yi wanka da Mr Man ya dawo ya huta ya ci abinci, a hiran na bashi labarin yadda muka yi da Naziha, shima nasiha yayi min na mata, bayan ya gama ya ce min. "Gobe muna da bako fa, ba zan gaya miki." "Cin amana!" "Eh na yarda!" Muka yi ta hiran kashe tv yayi ya dauke ni, ina zillewa haka ya wuce da ni dakinmu. Sai da ya zane ni da bulalansa kafin ya hakura. Bayan mun fito wanka na ce mishi. "Wai ni ya Asie ne?" Hade rai yayi ya kwanta bai kara min magana. "Wai tambayarka nayi ka share ni." Fisgo ni yayi yana zungure goshina. Tura bakina nayi na ce mishi. "Ka ji tsoron Allah, da Hajiya tana raye ba zata barka ba!" "Eh albarka Hajiya kike daukewa da cin amanarta Hajiya tana son mu cika mata gida da Yara ke kuma Yar renin hankalin kin hana faruwar haka, ki cire roban nan ko ki na gayawa Uwata!" Wato Mama karfi da yaji Tafida ya kwace min iyaye sai ya bar ni da Inna da Abba da Hajiya Salamatu. Daga haka ya mantar da ni Asie da take can tana fama da jinya, ita ba ga Tafida ba ita Baga aure ba. An sake Abubakar saboda Tafida, sai dai da alamu rashin rabuwa lafiya da Hajiya ya janyo yayi ta fama da wasu irin jarabawar rayuwa kome sai an taimaka mishi, hatta Tafida da baya son ganin cigaban shi, ya fi kyautata mishi, addu'ar da Tafida yake sha ba kaɗan ba ne.
Washi gari.
Tun asuba na tashi nake aiki, ya kai Naziha makaranta tare da niman Yaron, aka nimo iyayen Yaron, hakuri aka yi ta bawa Tafida domin ya ce zai yiwa hukumar tsaro magana a shiga lamarin shi aiki ya kawo shi ba tashin hankali ba. Jin haka iyayen suka saka d'ansu a gaba ya bar makarantar. Sannan ya bar makarantar shima.
Wurin karfe daya Naziha ta dawo da farin ciki, kitchen din ta shiga ta ga na gama kome, ai kuwa ta saka hannu ta ɗauka, Fannah ta buge mata hannun. "Mammy ki ce Aunty Fannah ta daina." "Fannah bana son haka!" "Tow Mammynmu!" "Maza ku gaya gyara parlourn Daddy, sai ku zo ku dauki abincinku!" Haka suka gama aka saka turaren wuta, kafin karfe uku mun gama kome wurin biyar sai Tafida da bakonshi. Yana gaba bakon a baya, tsayawa nayi na sake baki kafin na kira sunanshi. "Auta! Ahmad Tijjani!" Tawowa yayi da sauri ya rungume ni, na make kirjinshi ina faɗin. "Kai ne Auta?" "Aunty Baby ni ne amma kada ki manta ni!" Make kanshi nayi ya cewa Tafida. "Yaya ka gani ko? Haka take min su ta cin zalina!" "Mammy me haka!" Tsaki nayi tare da cewa. " da na san girkina wa Tijjani xan uwa da nayi mishi kanzo da garin kuli-kuli?" Aka saka dariya, daga nan aka hau gaisuwa da maraba. "Daga Turkiya kake?" Girgiza kai yayi ya ce min. "yaya bai gaya miki zuwana ba ne?" "Hmm ya kwace min dangina taya zai gaya min, je ka yi wanka sai ka zo kaci abinci kayi sallah ko?" "Eh nayi a office din Yaya Aliyu!" Na nuna mishi dakin da muka ware don baki, na bi Tafida daki. "Me yasa baka gaya min shi zai zo ba? Na ji dadin zuwanshi wallahi kamar nayi ta ihu!" Cak yayi sama da ni yana faɗin. "Ihun nake son kiyi Ummu, ina son nayi ta baki mamaki " "sauke ni tow!" Ajiye ni yayi na wuce na hada mishi ruwan wanka, sannan na saka shi gaba ya shiga. Na cire mishi kayanshi daga shi har Tijjani babu wnada ya gaya min abin da ya kawo shi, haka muka kasance har dare, sannan muka kwanta a wurin kwanciyar ne ya zuba min idanun. "Ummu!" "Na'am!" "Nasan Maryam bata sonki, amma me yasa baki cire Naziha a cikin rayuwarki ba." "Saboda da ita da Mufidah kallo daya nake musu, bana jin akwai dalilin watsa da ita bayan kaf duniya ita ce ta zo gare ni domin mafita! Gaya min wurare nawa ta je aka ki amsarta? Ni uwa ce ina sane da wannan ciwon." Rungume ni yayi yana mai saka kanshi a kafadata. "Idan na ce miki, Mama ta turo Tijjani ne ya ga Naziha zaki yarda?" "Mai zai hana na yarda ai d'a da dukiya baka san waye zaka mora ba, sannan bana tunanin musu mugunta, idan Tijjani Naziha tayi mishi. Alhamdulillahi babban burina ta samu mijin da zai kula da ita ta so ta, idan har Tijjani ya min haka ya kyauta min." Gyada kai yayi, ashe a Maiduguri can Maryam haukarta har gidanmu ta je tayi ta rashin mutunci, Mama ta kuwa gaya mata ai yadda muka mallake Tafida haka zamu mallake mata y'a, sannan mu bata mamaki. Lokacin Tijjani yazo yake tambayar meke faruwa ne, anan Mama ta gaya mishi kome, budar bakinshi ya ce mata. "Mama ni kan ku bani aurenta mana, ina son mace me wayewa kuma da alamu lalacewar ba a ranta yake ba, shi yasa ta koma wurin Aunty Baby." Kallonshi mama tayi ta ce mishi. "Ina fatan ba zaka mata gori wata rana ba? Ina fatan ba zaka juya mata baya don abin da ya same ta ba? Ni dai idan kasan zaka ci mutuncinta, ka bar musu yarsu don Allah kada ka kuma jefa Ummu a cikin tashin hankali." "Mama in dai kece kika haife ni, nayi miki alkawari da sunan Ubangijina, ba zan tab'a tozarta Yarinyar ba, domin kamar Haram Aunty Baby na tozarta!" Da wannan Tijjani ya gayawa Baba Bulama, ya samu Abba ya gaya mishi, kai abu kamar wasa sai ga shi har anyi tambaya da kome, saura aji kome daga Naziha. Don basu son a samu irin matsalarmu da Tafida.
**
Naziha
Washi gari da sassafe, ta shirya ta tafi makaranta, a can ta kira Mamanta da ta turo mata sakon matukar ta amince da auren dan Uwan Ummu ta sake uwa. Koda ta kirata dakyar ta dauka. "Mama me yasa kike kin Mammy? Mama tasan cewa kune kuka mata kome amma ta zauna dani da haka, ta mai dani kamar babbar Yarta, ban san dalilin zuwan Kaninta ba, idan har aurena zai yi tabbas ya ceto rayuwata daga hallaka, idan ban aure shi ba zina kike so na cigaba da yi? Mama ki tuna akwai Allah kuma abin da kika yi bai tsaya akan iya ni ba, ki saka idanun akan Kannena." Daga haka ta kashe wayar tana kuka, bayan an tashi tana zaune wata yar Nijeriya da suke haduwa Wurin sallah, ta zauna a kusa da ita . "Kamar daga Nijeriya kike ko?" "Eh kema daga can ce?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Eh! Sunana Rahmatullah Habib Jimeta, ana kirana Maama!" Isowar wata mota yasa ta mike tana faɗin. "See you baki gaya min sunanki ba." "Naziha Abba Aji!" "Ok sai mun hadu " dawowa gida tayi, tayi a tsarge kamar tayi wani laifi, wanann yanayin ba ita ɗaya ba hatta ni. Sai naji babu dadi na rike hannunta zuwa dakina, kuka take ba kaukkautawa, kukan yasa na kira Sunanshi a waya, can kuwa ya zo muka sakata a gaba da tambayar meke faruwa. Bata cutar da kanta ba, ta gaya mana abin da yake faru, shiru nayi kafin na bude baki zan yi magana ya ce mata. "Ya kin ganshi yayi miki?" Rike hannunsa tayi cikin kuka ta ce mishi. "Uncle, waye zai ki ɗan uwan Mammy, Uncle ko bana son shi yadda yazo don ni na amince amma Mamana!" Ta fada tana kuka. Murmushi yayi ya ce mata. "Yana aiki a kamfanin hada motoci ne a Turkiyya yana amsar albashin Naira miliyan goma a duk wata, zai miki hidima zai yiwa Mamanmu, zai yiwa dangi hidima. Yana da shagon da ya bude na sayar da takalman yan kwallo da kayan yan kwallo, a ƙalla kowani yaron shagonsa yana daukar dubu dari bakwai a wata. Yana da babban shago Maiduguri yana sayar da kayan wuta, yaranshi na nan suna daukar kudi sama da dubu dari huɗu da hamsin gaya min akwai wani matashi irinsa da zaki samu?" Girgiza kai tayi tana shashekar kuka, "Ummu ba zata miki gori ba, Yan uwanta baza su miki gori ba, dukkanmu muna sonki da gaskiya kuma ba zamu yarda ya miki wani abu ba.", rike hannun shi nayi. "Ba zan miki alƙawari ba, amma