Showing 15001 words to 18000 words out of 241571 words

Chapter 6 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14751

alamun jego ya amshe ni. "Ke dai ta wurin saibi kece za a bawa lambar yabo, fisabiilillahi ke ba yarinya ba amma kullum kece a karshen shiri." Inji Mama da ta shigo dakin. "Ga Nana jikar Hajiya Amina zaku tafi tare!" Ta dasa aya tana kallona, domin kuwa ban yi mamakin kallon da take min ba, "duk zuwa asibitin ne ya kawo wannan shigar?" Kallon kaina nayi kafin nace mata. "Kin san zan kai Mufidah ta ga likitan idanu! Kuma kin san yadda al'amarin yake ana ganina tagajam magajan za a fara surutai a kaina!" Na fada karamin murmushi tayi sannan ta ce min. "Na fahimta Allah ya tsare!" Haka muka fito ni da yaran, dakin Baba muka fara shiga na gaishe shi sannan ya ga Yaran yayi musu addu'a, kafin na wuce bangaren Ummi da Umma. Sannan na fito, ina zuwa waje na samu har Mahmud din ya iso, wani haɗe rai nayi na nufi bayan motar na shiga na cewa Nana. "Ki shiga gaba!" Murmushi yayi yana me jan motar bayan mun shiga. Kin yarda nayi na zauna inda zai na kallona, na koma gefe na zauna ina kallon gefen hanya. "Hajiya Ummu ya kwana biyu, da fatan ba ayi fushi da rashin zuwanmu ni da Madam ba ko?" Magana yaƙe son nayi da shi, amma fir naki ma cigaba da kallon gefen hanya, asibitin koyarwa na garin Maiduguri muka nufa, tun kafin mu isa inda suke security suka tari motarmu. Sam haka bai min ba, amma na share ni ban tab'a mafarkin irin wannan rayuwar ba. Tun kafin na isa inda suke manyan staff na asibitin suka yi ta fitowa ana min Barka da zuwa, MD na asibitin ya amshi Mufidah, yayinda mataimakinshi ya amshi Mufid a bayan Nana. Muka shiga cikin asibitin bayanshi na hango yana duba marasa lafiya. "Ina Hajiya?" Na tambayi Safiyyudeen. "Tana office din MD." "Tow ka kai ni wurinta!" Kasa yayi da murya yana faɗin. "Akwai yan jarida sosai, sannan wannan abin kin ga kowa zai dauka yazo ziyarar bazata ne so please ki ɗan kame kanki!" "Jinyar mahaifiyarshi sai ya siyasantar da shi sannan zai samu yadda D sVo? Anya kai mutumin kirki ne? Idan da kai mutumin kirki ne ba zaka zo ya siyasantar da jinyar mahaifiyarshi ba, ka je kuyi yadda kuke so da nasan zuwana ba zai yi amfani ba tow babu me kawo ni nan!" Na juya zan fita daga bayana Tafida ya ce min. "My Love kin iso ne?" Wani kululun bakinciki ne ya cika ni, na juya ina kallonshi fuskana dauke da murmushin takaici. "Ih yallabai!" "Muje mu ga marasa lafiya!" Kallonshi nayi ido cikin ido. "Hmm bar min wannan kallon my love!" Takaici ne ya kama ni. "Muje!" Kafin nayi magana ya riko hannuna, wai Tafsstida ya haukace ne? Taya zai na irin wannan abin kunyar a gaban jama'a. Sai daukar mu hoto ake yana ta washe baki shi nan ga gwani. Muna tafiya ina duba agogona, har zamu wuce office din MD. "Na gaji ba ziyara na kawo ba, wurin Hajiya nazo." Murmushi yxyayi yana faɗin. "Yarinya kenan, ai Hajiya tuni ta tsufa a garinta, domin tun jiya daj dare ta ga likitan aka sallame ya yau da safe. " a hankali naji kamar numfashina zai bar gangan jikina. "Mahaifiyarka cewa kuwa?" Murmushi yayi yana faɗin. "Idanun media yana kanmu, nayi kokarin nayi rayuwa ko babu ke a cikin kwanakin nan, amma na fahimci mutane suna yawan tambayana shin da gaske muna tare? Ni kuma ina son nayi amfani da hakan domin na nunawa duniya ina tare da yar ƙaramar guntuwar matata.." ya fada yana zungure ni, yadda ake daukar hotonmu yasa na buge hannunshi ina dariya. "Wannan abin ba sabo ba ne. Amma kuma i think yazo karshe, zan bar Aliyu Tafida amma taya? Haka muka zaga asibitin aka kuma kai ni office din MD, na zauna na bawa Yara nono sannan aka kawo mana abinci bakinciki da b'acin rai ya hanani kallon ko abincin ma, Nana ce taci sosai har tana faɗin. "Aunty Baby na kwashi abincin na tawo da shi gida?" Daidai shigowar Aliyu dakin. "Idan kina so ba, ki dauka ." Na fada a hankali ina kauda kaina. "Bata ci bane?" "Eh!" Idanunshi naji a kaina, ta mike a hankali ta fito waje. Tunda ta fita yake son magana amma naki kula shi. Wayata na duba zan dauka babu ita babu labarinta. "Wayarki kike nima?" Y ajiye min akan cinyata. "Ina son mu samu lokaci na gaya miki waye ni." "Ai ban bukata ba!" "Ummu Diyyah!" "Zan tafi!" Na mike a hankali, "Ummu!" "Don Allah ka bar ni na tafi!" "Yaushe zaki dawo dakinki?" Dauke kai nayi tare da cewa. "Ina son zan tafi gida!"


"Ki bani lokaci!" "Ka dauki duk lokacin da yayi maka Malam bada case!" Shiru yayi yana kallon yadda nake kokarin daukar Yaran bakiɗaya ya amshi Mufid yana faɗin. "Hajiya ta isa lafiya!" Boyayen ajiyar zuciya na sauke, tare da cewa "ban tambaye ka ba!" Daga haka na wuce ina me nufar kofar fita. jin shi nayi ya fisgo ni yana me faɗin. "Idanun duniya yana kanmu, ina ta kokarin nayi yadda ba zan cutar dake ba ki saurare ni!" Yadda yayi maganar kamar ba shi ba. A hankali na dan kara tsawona na ce mishi. "Duk yadda kayi duk daya ne Tafida kuskure na shine shiga rayuwarka, kuma cikin ruwan sanyi na fita ina ga karama gidahumar yar Mace me ya rage? Na ce me ya rage?" Kasa magana yayi yana kallona. "Zan tafi nace na sake maimata maka!" "Muje a ajiye ki!" Ban san ni ba ko kalaman da nake amfani da su yana tab'a shi, amma nasan shi da taurin kai ba zai damu ba. Haka na wuce yana me bin bayana, har wurin motar Mahmoud. Lokacin da na isa wurin motar Nana ta buɗe shi kuma yana rike da Mufid ni kuma Mufidah tana hannuna, shiga motar nayi ya kalle ni. "Ki cire number na a blacklisted kin ji!" Yadda yayi maganar sai da na d'ago shi nace mishi. "Yaushe ka zama haka? Na zata har yau hayakin na kanka bai sauka ba." "Ku huta lafuya." Ya fada min yana me rufe min kofar motar, dauke kai nayi ina kallon can gefe guda.


Muna barin asibitin Mahmoud ya fara magana amma nayi banza da shi, tunda babu dalilin da zai saka yana min9ps7dzas magana son ranshi, ganin yayi naki cewa cikanka yasa shi yin shiru da bakinshi. A kofar gida ya tsaya na fito tare da Nana, ban kalli inda yake ba balle ya saka ran zan mishi magana. "Yan mata ga sakonki!" Ya mika mata irin ledar abincin. "Aunty Baby!" "Karba!" Amsa tayi na wuce na barta, muna shiga cikin gidan na samu mutane a cikin gidanmu. "Lafiya?" "Ummu yanxu muka kalle ki a hoto!" Inji Mahira, murmushi nayi da bai kai zuci ba, na wuce zuwa dakin ina ajiye Mufidah Nana ta shigo tana faɗin. "yau gani ga gwamna!" "Don Allah!" Inji Zakiya, "wallahi kada ki ganshi wai Aunty Baby ta cab'a!" Suka kama ihu kowa yana jin ina ma shi ne, matsalar da ake samu kenan a rayuwarmu baka san yadda mutum ya sha azaba ba, kawai burinka ina kai ne a wurin. Ni yanzu na daina damun kaina da rayuwar wani domin akwai abin tsoro a cikinsa. Ina zaune Mama ta shigo ta kawo min abinci.
Sauka nayi kasa na zauna akan pillow ina sauke ajiyar zuciya. "Aunty Baby ga abincin nan;" "a'a na koshi nima yanzu zanci nawa, ki gaida Mamanmu, "zata ji!" Har zata tafi nace mata. "Zo nan Nana!" Na bude jakata na ciro kudi dubu biyar na mika mata, ta amsa tana godiya, har tana kara nunawa Mama. Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Kai Masha Allah kawata yau a wurinku xan kwana sai kudinmu ya kare zan dawo nan!" Dariya tayi tana me barin dakin. Ina cikin abincin Mama ta ce min. "Ya jikin Hajiyar?" "Da sauki sosai, har ta koma gida!" " Yau kuma?" "A'a tun jiya ta ga likitan ashe fitarsu ya kaita Asibitin." Na cigaba da cin abincin. "Tow idan kika yi arba'in zaki koma dakinki ne?" Hadiye abincin bakina nayi ina kallon yadda take kallona cikin damuwa. "Mama kin gaji da ni ne?" "A'a Ummu ban gaji dake ba, bana son a fahimci cewa kina son ki kashe aurenki ne, zai zame min abin kunya ne!" Ta fada cikin sigar lallashi. "Mama na gaji ne!" "Har yau baki dauki auren ibada ba ne?" "Na dauka amma akan Tafida na fahimci babu amfanin yin ibadar da kasan babu lada a cikinsa. Ki fahimce ni!" "Na fahimce ki amma ke yanxu ba abin kunya bane ace kin samu damar hawa sama lokaci guda a ji kin dirko kasa? Ummu ba zan hanaki rayuwarki ba, amma zawarci yana da nashi kalubalen fa." Ban san me yasa iyayenmu suke hango mutuwar auren mace kamar tonuwar asirinsu ne. "Yanzu kin ga Taima duk da halin da take ciki Hajiya Balkisu bata mata fatan kashe auren, balle kuma Samira duk yadda take fuskanta matsala Umma taki yarda da maganar mutuwar aure, ina tsoron kada ayi ta." Hawaye ne ya zubo min tabbas Mama bata yi kuskure ba, amma kuma mai da ni rayuwar Aliyu Tafida shine mafi girman kuskuren da zata aikata! "Yanxu ki duba Yaranku haka zaki barsu? Ina ga ya kamata ki koyawa kanki zama mace kuma jaruma ba wacce zata gudu ta bar sauran aikinta ba. Da ace shekarun baya na samu wnada ya min wannan karatun da ban baro gidan mijina na auri Bulama ba. Amma dake rabon su Ummu Kulsum da Ummu Rooman yasa dole na hakuri da kome na dawo nan, kuma ina zani? Anan nake da sauran Rayuwa. Kiyi hakuri kada ki kashe aurenki akan abin da bai da hujja, dayawan iyaye mata muna hakura da abun da muke dashi ne domin ku, kuma sai ki ga kome ya wuce." Kasa magana nayi domin wani abu da naji ya tsaya min a kirji wanda ya kasa wucewa kasa yana tsaye a wuyana, hawayen da nake dannewa ya zubo min tabbas, idan na fahimci mama da kyau burinta na koma gidan Tafida. "Kiyi hakuri kin ji!" Ta kuma fada ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, kaina a sunkuye na ce mata. "Me yasa? Me yasa kika bari aka bashi aurena? Me yasa ko don bani da gata ne? Mama nima mutum ce kamar kowa nima ina son farin ciki. Idan na koma gidan Aliyu har abada bani da fata da farin ciki sai dai nayi rayuwa domin Yarana. Amma shi kenan idan aka kawo miki gawata kada ki zargi Aliyu." Na tashi ina me nufi ban daki.


Jikinta yayi sanyi domin kuwa gani yadda nake kuka yana tab'a mata rai, idan har ta bar ni za iya cigaba da zaginta na ta bar ni na kaso aurena, amma kuma farin cikina yana gaba da kome tow me zata cewa Mutane? Da ko a gidana nake tasan magana zasu cigaba da yi.


Koda na fito na samu bata dakin tana ɗaya dakin, sai da naji dariya na fahimci aminiyarta ce tazo wato Hajiya Amina. "Hajiya Amina shigo." Suka shigo dakin bakiɗaya, "ke Ummu dubu ashirin da biyar kuka bawa Nana fa, a cikin ledar abincin da dubu ashirin kin ganshi yayi mata yawa wallahi!" "A'a rabonta ne fa bani na bata ba, Babansu Mufidah ya bata!" "Amma!" "Kai Amina sai kace wacce aka bata miliyan don Allah ki sawa ranki nutsuwa rabonta ne!" Zama suka yi ta kalli Hajiya Amina tace mata. "Gata nan ban san meye ribar da zata ci ba, idan ta kashe aurenta. Don Allah ki fahimtar da ita illar zawarci." Kallona Hajiya Amina tayi kafin ta ce mata. "Kada mu ga laifinta, bayan kema kin san yanayin da suka zauna da Yaron nan, bana fatan Ummu Hadiyya ta dawo gidan nan, amma maganar gaskiya shine ta nimawa kanta yanci, sannan shi yaron kin ga danginshi sun damu da ita ko kula da ita? Kin ga Hajiya Hadiza mu kowa Yaranmu kwatan kansu kada ki maida ita lusara mana kishiya take da shi fa, yar uwarsa kuma Yar dangi na zata an wuce wannan zamanin da mace zata zauna zaman alfarma, Ummu ki ja zarenki da kyau ki nunawa danginsa kema mutum ce kada ki zama.wacce Tafida zai naja yadda so!". "Wai Amina me yasa kike biye mata ne?" "Na gaya miki tabawa kawata a gidan take aikin tuwo, ita ta ke bani duk labarin abinda yake faruwa ban da Allah ya nufa Ummu Hadiyya tana da nisan kwana aka ce miki bakinciki bai isa kashe ta ba har lahira kawai idan kin ganta a damuwa tayi hakuri ta zauna gudun kada aurenta ya mutu a mata gori ko?" Ta juya tana murmushi ta ce mata. "idan kika so yarki babu wnada zai wulakantata idan kika juya mata baya, akwai irin Aliyu dayawa zasu ta wulakantatta shawara na gare ki, ki barta ta tsaya da kafarta ko kuma kina ji kina gani wata rana za a kawo miki gawarta, ban san me yasa mu iyaye muke tsoron mutuwar auren Yaranmu ba, idan don maganar mutane ne da zawarci tow kinyi kuskure......
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*






*Assalamualaikum don Allah kada a tura payment ta GTBANK babu network zan saka Opay dina*
Paid book


07


Shirun Mama babu alkhairi a cikinsa, domin kuwa girman Hajiya Amina take gani yasa tayi shiru wanda nasan Hajiya Amina tana barin gidan Mama ba zata daura maganarta. Don haka na ce mata "Mama Amina zan koma." Ba iya ita ba hatta Mama naga mamakina a fuskarta. "Zaki koma fa?" Suka tambaye ni bakinsu a haɗe, cikin wani irin shashekar kuka na ce musu. "Eh zan koma!" "Ummu babu inda zaki kome, ranki baya son gidan Tafida yanzu idan kika koma kamar cutarwa ne ga rayuwarki!" "Babu abin da zai same ni!" Na fada ina kuka, sai kallona Mama take ita dai bata ce min dole ba, amma kuma a ranta tasan bata kyauta min ba. "Kiyi tunani Hajiya Hadiza tunda kika haifi Ummu ta tab'a miki musu? Duk abin da kike ce shi take miki, akwai hisabi a tsakaninmu da Yaranmu." "Hajiya Amina ni fa bance mata dole ba, kin ga na mata magana ne?" Ta fada kamar ranta ya b'aci, murmushi Hajiya Amina tayi tana faɗin. "Shi kenan, Ummu ki yi duk abin da ya dace. Wanda zai gyara miki yau ɗinki da domin kuwa shi rayuwarki na gaba. Ita mahaifiyarki!" Sai kuma tayi shiru tana kallona kafin ta mike tana faɗin. "Allah yasa haka shine mafi alkhairi! Ni zan tafi." "Amina kamar ranki ya b'aci?" "A'a raina ba zai b'aci ba, Ummu Hadiyya yarki ce ni kuma makociyarki ce kina da yadda zaki yi da ita. Ni kuma babu yadda zaki yi da ni, sannan ina ga mu bar zancen nan kawai Ummu Hadiyya mun gode sosai fa, kamar kin san ina niman kudi ido a rufe, sai an jimanku!" Ta saka kai ta fita nasan Mama Amina ranta ya b'aci sosai, tana fita ko minti goma ba ayi ba, Mama ta sabi mayafinta tana faɗin. "Amina ita ce bangon da nake jingina na ji dadi, ita ɗaya take tayani kuka lokacin kuka, gara na shirya kafin a fara mana dariya." "Sai kin dawo!" Na fada ina jijiga Mufid. "Kawo shi na goya shi!" Goya shi tayi suka fita, hawayen da suke ta zuba min na goge, ban san ta kuma dawowa ba sai ce min tayi. "Kuka ba zai miki magani ba Ummu Yaran nan zaki duba, ya rayuwarsu zata kasance idan baki tare da mahaifinsu. Dama Allah ya baki kada kiyi wasa da shi wurin lalata aurenki, Allah ya buda miki kika gidan aurenki ma bai saka kin rasa kome ba shawara nake baki fa ban ce dole ba." Share hawaye nayi ina kallon Mama da ina ga kamar dole take min na koma gidan Tafida, fita tayi tana faɗin "kowa rai ya amfana baya ga mai shi ne." Kamar Tafida yana jiran ta fita sai ga kiranshi. Kallon wayar nayi kafin na dauka. Dariyarshi na ji tare da yan iskan abokan shi. "Ummu!" "Hmm!" "Uwar gida Sarautar Mata, dama na kira na gaya miki ko zaki samu lokaci zuwa wata sati zamu je Umra da ke!" "Tafida!" "Na'am Matar so!" "Bana son aurenka! Kayi hakuri ka rabu da ni." "Amma Ummu baki ga kamar yayi sauri ace mun rabu da juna duka-duka shekarar mu nawa da auren da zamu rabu da juna?"
"Ai ko kwana ɗaya ne nace ba zan zauna ba!" "Ba zaki zauna da ni ba, tow me nake miki da kike jin haushina." "Ba kayi kome ba, ba zaka tab'a min kome ba saboda bana bukatarka yasa nake son rabuwa da kai." "Ummu Hadiyya kin ga ina ganin girman Iyayenmu yasa nake bin ki cikin lumana idan kika bari wani abu ya taso ba zan miki da dadi ba!" "Ni dama bana son ka min dad'i" daga haka na kashe wayar ina ganin yana ta turo sako amma fir naki budewa. Tunda na fahimci ni ce matsalarshi na saka a raina zan rabu da shi, amma shi ya kasa fahimtar haka.
**
SA'ADIYYA.
Amarya Tafida wacce suka sha alwashin dole ta zama first lady, ana ta gyara ciki da waje domin tun barin Ummu Hadiyya gidan har yau bata gane kan kusar yakinta ba, duk wani abin da suke karbowa na barbadawa da turarawa, bai yi tasiri akan Kusar yaki ba domin kuwa yana da matukar taurin kai, sannan Tafida duk rashin jin shi ya tsare salloli biyar nan baya wasa da su, Allah yayi alƙawarin kuma yana cikata akan wadanda ya daukawa, shi yasa duk haukarsu baya tab'a sh, sai da suyi ta asara wanda kowa yasan bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login