Showing 66001 words to 69000 words out of 241571 words
Chapter 23 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
tafi nace!" Na fada ina bude ban dakin na shiga. Tunda na shiga na jima a ban dakin, kafin na fito. Yana tsaye kamar an dasa shi, "nace ka tafi!" "Me yasa kike ture ni daga jikinki!" "Saboda bana son ganinka." Daga haka na nufi inda ya shimfida min abin sallah, wani irin b'acin rai nake ji kanshi. Haka nayi sallah ina sallah kuka nake, domin na fahimci yana nan har yanzu. Koda na idar hade kaina da gwiwata nayi na cigaba da kuka. Shigowar Abba da Babana tare da baba bulama, yasa shi mikewa yana me gaida su. "Ummu lafiya kike kuka kuma?" Cak kukan ya tsaya min sakamakon muryan Babana da na ji, "babu kome!" " akan me zaki ce babu kome bayan Muryanki har waje!" "Baba kayi min addu'a na mutu!" A wani irin razane Tafida ya nufo ni, "kada ka zo inda nake!" Na fada ina kara k'amkame jikina. "Kada kazo don Allah ka tafi nace bana son ganinka don Allah!" Yadda nake maganar yasa bakiɗaya iyayenmu suka shiga kallona musamman Babana. "Kul na kara jin haka, Mijinki kike kora haka." "Kyaleta Alhaji Kabiru tayi ba mamaki bata son ganinshi ne! Jeka." Inji Abbanshi, "ina zai je? Idan bai zauna kusa da ita ba a ina zai zauna? Matarshi ce Jadda kyale ta bana son fitina irina su na mata." Babana ya fada, shigowan Doctor Sagir yasa suka fita. "Ummu tashi ki kwanta!" "Kyaleta na ga gudun ruwnata! Ummu ki gaya min me nayi miki da zafi kike min irin wannan tozarcin?" D'ago kai nayi zan yi magana a hankali naji bakiɗaya duhu ya mamaye idanuna. Ji nayi na tafi bakiɗaya can nesa nake jin kamar ana kiran sunana daga nan ban kuma sanin me yake faruwa ba.
Daga asibiti gida ya wuce a matuƙar fusace, a parlour ya samu Sa'adiyya ta cab'a kwalliya, ta mike cikin tarairaya tana faɗin. "Welcome back His Excellency!" Dama haushin Ummu ta b'ata mishi rai ya zuba mata idanun. So yake ya gano inda Sa'adiyya ta fi Ummu. So yake ya hango, "hancinki yana da kyau amma da yazo nan dai yayi tukunya, ita kuma hancinta premature ne saboda yanayinta da bata da girman jiki, haihuwa daya tayi amma kamar yar shekara shida ke idan kika haihu sai dai a bude kofar gida domin zaki koma kamar saniyar hud'a" kamar bashi yayi maganar ba, ya wuce dakinsa daren jiya fa sun kwana lafiya,har yau garin Allah da ya waye amma yanzu ji yadda ya banka mata bakar magana.
Yana shiga dakinsa ya zauna shiru, tabbas idan bai yi da gaske ba yana ji yana gani Ummu zata subuce mishi. Babu abinda ya kara b'ata mishi rai kamar yadda Dr Sagir ya ce mishi. *Ranka ya dade! Idan da hali ka daina zuwa ganinta domin jininta mun samu ya sauke jiya har zuwa yau, yanzu tana ganinka jininta ya kuma hawa muna tsoron kada ya tab'a mata zuciya nayi tunani kodan Yaranka!* Shi fa yanzu tunda Ummu ta haifa mishi yara yake ji kamar kaf duniya babu abinda za'a ce ya kasa amincewa. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wayarshi tana tsiwa amma bai d'aga ba. Sake kiran aka yi ya dauka yana faɗin. "Deen!" "Naje asibitin baka nan!" "Deen Ummu bata son ganina!" "Kamar ya?" "Wallahi Ummu taki jini na ban san me nayi mata da zafi ba! Don Allah ka san me na mata?" "Kai da kake tare da ita baka san me ka mata ba, sai ni da nake waje zan sani kai dai ka binciki kanka!" Zare hular kanshi yayi yana faɗin. "Na rantse maka ban san me nayi mata ba, yarinyar nan ko ana saura kwanaki ta haihu sai da ta min dambu yanzu dambu ya kare, sannan miyar da take yi ta ajiye yanxu babu, wallahi rabona da naci abinci me dadi na manta!" "Ok yanxu saboda yunwar cikinka kake son Ummu ta dawo?" Deen ya tambaye shi, "Tow ya kake son nace? Yarinyar nan tasan yadda nake son zama da ita fisabiilillahi ita!" "Tafida tambayarka nake saboda yunwar cikinka kake son ta dawo?" "Eh a'a!" "Ok akan me kake son ta dawo?" "Har ga Allah akwai nutsuwr da nake samu a tare da ita ne, sannan." "Aliyu na fito maka zahiri mutum? Tow ai lamarinka idan dai akan haka ne Ummu ba zata dawo ba, domin abu biyu ya bayyana a maganarka! Na farko don kasan kaf duniya abincinta zaka ci cikin natsuwa da yarda da kai, na biyu ita ce macen da ka fara sani, sannan ta rike maka darajarkanta. Idan akan wannan ne tow kayi hakuri Ummu zai yiwu ta dawo gare ka!" "Deen dole ta dawo ai tana jin maganar iyayenta da manya!" "Nayi maka alkawarin idan ta dawo don dole sai nayi azumin kaffara na wata gudu!" Ai kuwa ya fara masifa kamar Deen din yana gabanshi. "Ban da iskanci taya na kiraka ka gaya min magana, Ummu kanwarka ce da zaka tsaya kana min munafunci munafuki waye ya sani ko kai kake zugata." "Eh ni nake zuga ta nace kada ta sake ta dawo gidanka mutumin kawai!" "Ni kake gayawa Magana kasan da wanda kake magana?" "Da wanann mara jin maganar me shegen taurin kai da rashin kunya Tafida nake nufi da kai nake magana Look ka ajiye iskanci kayi facing reality dinku." Tsaki yayi ya ajiye wayar Ummu zata ga iskanci Umara zai tafi ma da Sa'adiyya. Kiran Mahmoud yayi ya gaya mishi abinda yake bukata da kuma rigimarsu da Ummu, cikin takaici da baƙin ciki. "Wallahi da ni ne saketa zan yi haba da girmanka da darajarka sai wani baka wahala take kamar ta samu wani danta! Ka yarda kwallon managoro ka huta da kud'a." "Ai kasan Alhaji ba zai yarda na sake ta ba nima ai na gaji wallahi!" "Ok shi kenan zan yi abinda ya dace." Daga haka suka kashe wayar.
Mahmoud.
A lokacin da Tafida ya kira shi, yana parlourn gidanshi ne, yar aikin matarshi ya saka a gaba yake ta lalata da ita. Jin kiran Tafida bai saka ya tsagaita wuta ba, sai da ya gaya mishi rigimarshi da Ummu tuni ya zare. Kallon yarinyar yayi yana hango yanayinta da Ummu, dama abinda ya sa shi fara lalata yarinyar kenan yanayinta kamar Ummu bata da tsawo gata yar siririya. Shafa fuskarta yayi yana faɗin "ki nutsu mu mori juna, babu abin da zai faru." Ya cigaba da abin da yake yi.
Da sauri ya sauka akan yarinyar yana me nufar ban daki, Maza fita kada na same ki a dakina!" Ya shiga yayi wanka idan har Tafida basu shirya da Ummu ba tabbas abin da zai faru saki zata bugata idan ya sake ta haka zai bashi damar niman soyayyarta. Murmushi yayi a karo na uku yana ban dakin ya gama ya fito, ya shirya sake kiran Tafida yayi cikin kame-kame ya ce mishi. "Naji kana cewa Ummu bata da lafiya ko?" "Eh tana asibiti!" Ya fada mishi. "Ok dama zan kai Madam ne ta gaishe ta!" "Ba damuwa!" Ya faɗa, murmushi yayi yana faɗin. "Shege Allah yasa kun rabu kenan har abada." Ya fada yana shiryawa sannan ya fito daga dakin cikin shigar kananun kaya ya nufi bangaren iyayenshi. "Ammyn zan tafi na duba matar Tafida bata da lafiya?" "Allah ya bata lafiya, sannan ina Yarinyar nan take ne ba halin na tura ta wurinku aiki sai ta tafi nata yawon!" Cikin ko in kula ya ce mata. "Oho ni ai na jima da gaya muku bana bukatar yar aiki amma kuka ƙi yaran da ko an dauke su basu da wani aiki sai rashin ji!" "Ni dai ka rufa min asiri kada na ji kada na gani wani abu ya sami yar mutane, aiki na dauke ta kuma marainiya ce bata da kowa sai yar Uwarta don Allah kada labarin da nake ji a waje ya zo gidana!" Inji Hajiya Haulatu, mahaifiyar Mahmoud, saboda tasan halin danta kud'a baka haramun ne, cikin borin kunya ya ce mata. "Fisabiilillahi Ammyn da ace Rayyan ne ba zaki fadi haka ba, sai ni saboda kawai abin da mutane suke fada " yadda yake maganar zuciyarshi na tsannanta bugawa domin tabbas idan ya sake Ammyn tasan yana lalata da yarinyar me suna Khairat ya mutu ya lalace domin sai ta masifar bata mishi rai. "Ni xan tafi Allah yana gani!" Ya fada yana kokarin barin dakin, shigowar Khairat din ta nime wuri ta zauna. A hankali kallonta Hajiya Haulatu tayi a tsannake. "Ke Khairat daga ina kike?" "Ammyn na tsaya wanke kayan Aunty ne!" Shiru Hajiya Haulatu tayi tana faɗin. "Allah ya kyauta!"
Zama yayi cikin motarshi yayi shiru, gabanshi yana tsannanta bugawa. Domin lissafinshi sai yanxu ya zo mishi dole ya iya takunshi idan ba haka ba duk ranar da Ammyn ta samu labarin abinda yake sai ya yi danasanin. Shi kuma abin da zai bata mishi ran iyayenshi yake gudu, yasa yake mamakin yadda Tafida bai dauki iyayenshi da daraja ba, shi ai ko Iyayenshi yanka namar jikinshi suke ba zai tab'a kinsu ba. Balle shi Tafida hatta rike Matarshi iyayenshi suke mishi. Tsaki yai yana jan Motarshi. Koda ya isa asibitin Mama ya samu dakin tana jijiga Mufid da yake rikici. "Sannu Mama ya me jikin?" "Da sauki Malam Mahmoud! Ya mutanen gidan?" "Suna lafiya!" Ya fada yana zama a kujeran dakin, turo kofar dakin aka yi Deen ne dauke da basket da bakar jakar leda. Wani haɗe rai yayi yana me gajeruwar sallama. "Sannu Malam Safiyyudeen! Sannu da kokari." "Yawwa Mama, Mufidah tayi barci ko?" "Eh tayi Mufid din ne dai yake rikici uwar bata cikin nutsuwarta balle ta basu nono." "Ai lalura ce, Dr Sagir ya ce min yawan rikicinsu har da yunwa shine na kawo musu madaran gwangwani a fara basu kafin uwar ta samu lafiya!" "Allah ya saka da alkhairi!" Sannan ya ajiye mata basket din abincin yana faɗin. "sakon Ammah ne wannan!" "Kai Masha Allah mun gode Allah ya saka da alkhairi!" "Amin Ya Allah!" "Kazo ne?" "Eh ya kake?" "Alhamdulillahi? Tow Mama zan tafi idan ta farka a gaya mata Ammah tana gaishe ta." "In sha Allah!" Inji Mama, "Mahmoud sai mun sake haduwa!" "Ok nima fita xan yi!" Shima yayiwa Mama sallama suka fito. "ban gane ba ne, Matar Tafida ce ko Matar Safiyyudeen? Domin naga hidimar kamar na matarka ko kana zaga Tafida ne?" Dariya Safiyyudeen yayi yana faɗin. "Allah ya min tsari da kallon abincin da guba ne a gare ni, Ni Deen Allah ya haramta min shiga gonar wasu. Iya nawa ya wadatar da ni."
Mahmoud zai kara magana Deen ya ce mishi. "Shawara daya zan baka, kada ka sake Tafida ya samu labarin ka tab'a kokarin hakewa Matarshi, don na lura akan Ummu zai iya taka uban kowa ya kwana lafiya!" Fisgo shi Mahmoud yayi yana faɗin. "A ina ka ji labarin nan?" Dariya Safiyyudeen yayi yana faɗin. "Ka zata kowa banza ne irinka?" "Ummu ce ta gaya maka?" "Baiwar Allah ta rufa maka asiri a yawon barbadarka ka gayawa mutane aka gaya min." Fuskarshi ya maida kamar ta yara ya nuna shi da yatsa yana faɗin. "na gaya maka duk ranar da ya samu labarin hatta yankaka tayi domin ta zare mutuncinta, Wayyo!" Deen ya rike bakinshi. "Ta kare maka!" Ya fita daga kofar ward din yana me nufar inda Motarshi take, yana shiga motar ya zauna yana tuna wanda ya gaya mishi. Wani Yaronsu ne mai suna alguburo, Yaron shi yake kawowa Mahmoud matan banza tow ya kai masa wata yarinyar yayi kome da ita amma yaki biya shine yarinyar tayi ta kiran Alguburo tana gaya mishi magana ya kashe wayar kashe ta biyo shi tana mishi tijara, Deen ya kashe rigimar ta hanyar tura mata kudin Mahmoud da yake wurinsa, domin suna hada kudi haka kawai ana sadaka da shi kuma Deen yake haɗawa. Shine Deen yake yiwa Yaron fada. Ya ce mishi. "Fisabiilillah kai kaga wannan rayuwar da kuke ya dace? Baka tunanin za a yiwa iyalanku haka!" "Oga Deen wallahi ba aikina bane Oga Mahmoud yake tura ni na dauko su,sannan gaskiya ku saka idanun akan Matanku da kannenku domin Oga Mahmoud bai da kyau haka lokacin da ya nime matar Oga Tafida shine ta yanke shi a cikin don Allah ka saka idanun akan kanwarka Jalilah domin ya sha fada min duk wani abu me kyau da daraja kune kuka hada, sannan akwai wata mata da bansan wacce ita ba,tana da alaƙa da ku suna tare da ita gaskiya ban san ta ba domin baya waya da ita a gabana. Idan zai yi ma baya yarda na fahimci wacce ita!" Tun daga ranar kiri-kiri Deen ya hana Jalilah zaman gidansu ya mai da ita gidanshi sannan ya mata wani irin kashedin da tasan tabbas zai aikata domin yace koda wasa ya samu tana da alaƙa da Mahmoud wallahi sai ya kashe ta har lahira kuma ba zai nadama ba. Tana mugun tsoronshi Matarshi ma ya hana ta alaka da Matar Mahmoud domin itama Matar ba wani tarbiyyar ce da ita ba.
Shi yasa a wannan lokacin baya bukatar Tafida ya ce zai yi wani abu da Mahmoud zai fahimci ainihin abinda yake faruwa a tsakaninsu da Ummu. Domin yin haka kamar bada kofa ne,yasan waye Mahmoud yasan idan yasaka abu a gabanshi sai ya cimma, sai dai bai kai Tafida tijara ba, shi fatan shi kada Tafida ya gano abin da yake faruwa, duk ranar da haka ya faru a yadda ya fahimci Tafida ya fara gano amfanin Ummu a rayuwarsa tow gaba yana fatar idan har ya fahimci wacece Ummu a rayuwarshi anan ne zai tsaya mishi da yakin dawo da ita.
-- Shafa kai Mahmoud yayi yana kallon Motar Deen da ya fitar da ita daga asibitin. Murmushi yayi yana faɗin. "Deen baka isa raba ni da abinda nake so ba. Ummu Hadiyya mallakar zuciyata ce, tabbas idan ban samu Ummu ba to sai dai Mutuwa nayi matukar ina raye Ummu tawa ce." Haka ya nufi wurin Motarshi ya shiga, ya nufi office din hukumar mahajjata, yayi duk abinda zai yi sannan ya kira Tafida ya gaya masa ya gama kome.
---
*TAFIDA*
Juyawa abincin yake yana kallonshi kafin ya ajiye cokalin, ya mike tare da nufar cikin gidan. Kowa yana ta sha'aninsa. Parlourn Abba ya nufa da sallama ya shiga cikin parlour. Zama yayi yana kallon abincin Abba. "Sannu Abba!" "Yawwa Tafida!" Abba ya amsa mishi. "Yaushe zaka tare a gidanka na gwamnati?" Shafa kanshi yayi yana faɗin. "Ina jiran Ummu ne?" "Ai tow shi kenan ai!" Gyara zama yayi yana faɗin. "Abba dama nazo ka saka baki!" "Baki a ina?" Cike mamaki Tafida yake kallon Abba. "Akan lamarina da Ummu, Abba ta kusan arba'in ta dawo dakinta haka." "Wannan tsakaninka ne da ita idan ta ce zata dawo ai shi kenan sai fatan Alkhairi."
"Abba ba zata dawo ba!" "Ai haba?" Yadda Abba ya mai da lamarin wasa yasa Tafida ya harzuka. "Abba!" "Kaga lokacin da na nima maka ita ka aike ni ne? Daga lokacin da aka bata aurenta nayi maka wani abu ne acikin gidanka? Aliyu ka je kai da matarka da kake so babu ruwana." Cikin haushi da zafin rai kamar zai fasa ihu. "Shi kenan idan na dawo daga Umara xan bata abin da take so " ya mike ya fita daga dakin a fusace, har yana kwallo da butar karfen Abba. Sunkuyar da kai Abba yayi idanunshi yana cika da kwalla. "Ya Allah kai ka bani Aliyu ya Allah kada ka kawo sanadin da zai rabu da yarinyar nan, Ya Allah kada ka sani nayi kuka akan Aliyu, Ya Allah ka shirya Aliyu tafarkin addinin Muslunci, Ya Allah ina jin ciwo da zafi Ya Allah kada ka.dauki rayuwata Aliyu bai shiryu! Ya Allah!" Ya fada a raunanane, har ga Allah Aliyu shine rauninsa. "In sha Allah Ubangiji zai amshi addu'arka, Allah ya shirya mu bakiɗaya!" Inji Hajiya Salamatu da ta zo ta zauna a gefenshi. Zata iya cewa ita ce silar lalacewar Tafida, ita ce ta raba shi da Uwarshi, amma bata tab'a zaton lalacewarshi zata kai har haka ba, ta godewa Allah da bata wanke hannunta da datti ba, domin a lokacin har Hajiya Shuwa tana faɗin ya saubanta rayuwarshi tow ba ayi ba kenan.
"Duk yan uwansa suna cikin nutsuwa, da kwanciyar hankali amma shi da ya kasa rike mace daya ne da rigimar auren Mace biyu, hmm!" "Allah ya taya shi riko!"
**
*SA'ADIYYA"
"Ni wallahi ba xan iya rashin mutunci Tafida ba, haba fisabiilillahi wai yau matarshi ta fini kyau!" Tsaki shuwa tayi tana zaga dakin, "shegen Yaro duk yadda nake kashe kudina amma dan banza babu abinda yake aiki akanshi. " "Hmm ai na gaya miki mutanen kudinki suke ci fa." Wayarta ta janyo tana me kiran wani Malaminta da yayi mata aikin da aka matso da maganar auren Sa'adiyya aka ayi akan lokaci. "Malam yaron nan fa sai kara haukace mana yake wallahi, yarinyar ya bar gidan yanxu haka." "Ok rike wayar da fatan kina da kudi a wayar!" "Akwai malam!" Ya fada tana ajiyar zuciya. Tana rike da wayar har bayan minti goma ya ce mata. "Shuwa Yaron nan Uwarshi tana akan shi, Ubanshi yana kanshi. Yarinyar kuwa tun kafin ta haihu muka yi aiki akanta amma ya warware kuma yaron ya warware shuwa Yaron nan ya san me kike bukata a gare shi, idan kika matsa dayawa zai iya baki mamaki!" "Tow Malam maganar Matarshi fa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Zan saka aljanu su kara dagula al'amarin amma akwai aikin da xan yi shine a rufe bakin yarinyar yadda ba zata tab'a amince ta dawo dakin ta ba. Amma maganar gaskiya wannan aikin yana bukatar kudi, sannan kafin nan ki tabbatar an nimo miki kudin da ya fito hannun Kuturu da wanda ya fito hannun makaho da wanda ya fito hannun Bebe, da wanda ya fito hannun kurma, ki hada bakiɗaya