Showing 93001 words to 96000 words out of 241571 words

Chapter 32 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14735

tana da murmushi. "Babangida! Kai ne haka?" Murmushi yayi yana shafa kanshi. "Hajiyar Abba muje ina Innata?" "Ai baka da kirki tunda ka dawo nan ka barsu ita da yar uwanta zasu zo gobna has!" Dariya yayi ya mata jagora har bangaren shi waya yayi aka fara kawo mata abinci da abin sha, kafin wani lokaci gabanta ya cika da abinci . "Ina zan kai abinci haka? Allah ya yi albarka " ruwa ta sha tana kallonshi yadda ya faɗa. "Tafida!" Kallonta yayi kafin ya sunkuyar da kai. "Ka daina saurin hasala idan Sa'adiyya tana maka abu ka koyawa kanka hakuri." "Hajiya tasan kome akan Ummu, Hajiya sune!" "Duk mun sani Ummu tana nan, amma kayi hakuri." "Hajiya Ya zanyi? Ummu taki ta bayyana kanta ita kuma wancan yar iskar yarinyar tana sane!" "Kana son Ummu ne!" Numfashi ya sauke a hankali yana dafe kanshi. "Allah yana sane da kai!" Jinjina kai yayi, "Kasan Hajiya Turai?" Gyada kai yayi yana kallonta. Rasa yadda zata mishi magana tayi kafin ta ce mishi. "Kasan yar rikon Inna ce, tayi aure a Yola." "Eh Hajiya na sani amma na manta saboda bata zuwa akai akai." "Alhaji bai kiraka bane?" "A'a!" "Ya Aisha Fa?" Girgiza kai yayi ya kagu ya ji me zata ce, "Tow Allah ya kyauta ka tafi wurin Ya Aisha zata gaya maka meke faruwa!" "Hajiya gaya min me ya faru Ummu ne wani abu ya same ta!" Yadda ta birkice da tambayoyi yasa ta fahimtar, Tafida yana ganiyar kaunar Ummu! "Aure zaka yi!" Zubur ya mike yana me girgiza mata kai. "Akan me? Nace muku ina sha'awar wata mace ce? Ni Ummu nake bukata a rayuwata idan babu ita zan ajiye kome na tafi niman Matata!" " zauna Tafida! Shima Alhaji babu yadda ya iya ne, da yana da yadda zai yi ba zai amsa ba, ta baka auren Yarta son zo tare." "A ce mata ni Aliyu Muhammad Jadda Bana son Yarta ni matata ta wadace ni ko Saadiyyah jiran dawowar Ummu nake amma bata bukatar zama da ni! Hajiya ki gaya musu ni Tafida bana bukatar yarinyarta." Yadda Tafida ya gigice zaka ɗauka mutuwa aka kawo mishi. Amma ina ita kanta Hajiya Kaltuma bata da yadda ta iya haka ta bar gidan, Deen ya kira yana gaya mishi abin da yake faruwa. Yazo maza su tafi gidan Abba domin al'amarin ya wuce lissafinsa.


*Mama*


Zubawa Mudan idanun tayi ta rasa me zata ce mishi, dakyar ta dauki wayarta ta kira Baba Bulama. "Alhaji don Allah ka zo gida ka ji...... (Kuyi hakuri Maybe na kara muku wani update din yanxu ina busy ne...)🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


Mudan


Duk sai yaji kunyar duniya ta rufe shi. Har zuwa lokacin da Baba Bulama ya iso, kan Mudan a sunkuye yake bai d'ago ba saboda tsabar kunya da jin ina kasa zata bude ya shige cikinsa. Bai tab'a danasani irin yau ba, "Mudansiru me ya faru?" Baba Bulama ya tambaye shi. Kamar wanda yayi sata muryan shi yana rawa ya ce mishi. "Ni ne na dauki Aunty Baby daga nan na kaita Bauchi." "Kasan inda take a Bauchi ne?" Cikin rawan murya da rudewa. "Wurin motar lagos ta tafi bata yarda na kaita ba yadda aka yi na sani bin bayan napep din da ta shiga nayi na gano inda ta nufa." Cikin rikicewa Mama ta ce. "Ban gane ba?" "Ba a Bauchi ta tsaya ba babbar motar nan ta shiga zuwa lagos!" Wani irin zufa ne ya shiga karyo mata daga ko ina na jikinta rawa yake. A hankali ta fashe da kuka don ita ta jefa Ummu a wannan yanayin, "Alhaji ni ne na cillata cikin wannan yanayin, ta gaya min na fuskance ta amma naki, na dage gidanta zata koma!" "Kiyi hakuri zan saka a cigaba da saukar qura'ani Allah zai dawo mana da ita. Allah ya kyauta jeka ka ji!" Haka ya mike yana ta basu hakuri suna nuna mishi babu kome, bayan ya tashi Mama ya cigaba da kuka domin zuwa yanzu yan unguwa sun fahimci Ummu ta b'ata, haka ma Umma sai magana take yada mata a wasa.
***
*Tafida!*


A parlour Abba suka hadu bakidaya, tunda ya shiga cikin gidan Deen sai tausarshi yake da kalmai amma ya kasa nutsuwa, a tsakar gida suka hadu da Hajiya Turai. Ta ci sunanta Turai domin fara ce tas kamar baturiya, tare da wata baturiyar Yarta, ga kyau kamar tayi kanta abin ya haduwa yarinyar biyu Ubanta Fulanin Yola ne kuma fari Uwarta shuwa ce, abin ya mata yawa wai shege da hauka. Tsabar kanshi yayi zafi bai ma ganta, parlourn Abba ya fada kamar an wurgo shi, a tsakiyar dakin yayi musu sallama. "Abba na ji sakonka!" Jan shi Deen yayi ya zauna. "Baka da kai ne?" "Ina take da kai ta shigowa mutane kai sannan tayi sallama,wannan hali naki Tafida bai da kyau ki daina wannan abin bai dace ba!" Hajja Ganaah yayi idanu. "Inna ki ce ta daina mai da ni na mace!" "Idan naki fa? Kin zo kina mana ihu!" Shiru yayi yana jin takaici, shigowar Turai da yarta Asiya yasa shi kallonsu. "Ashe Tafida ne haka ko gaisuwa babu!" Banza yayi da ita, shi yake abinshi Deen ne da jin kunya. "Ki zauna!" Zama duk aka yi sannan aka gaisa da juna, kafin Abba ya bukaci ta maimaita abin da yazo da shi, nan kuwa ta faɗa. Kallon Abba Tafida yayi ya juya kanshi yana kallon Yarinyar ya ce mata. "Kanwata, ina da matar nake jira, kada ki fada dayawa, domin ni inuwar giginya ne. Wacce nake jira ita ɗaya ce zata sha dadin inuwata. Daga kanta na gama aure ki je ki auri wanda yake sonki ni tawa ta ishe ni!" "Tafida!" Deen ya rike shi, "Ba karya da gaske bana sonta ne, babu macen da nake muradi da son zama da ita sama da Ummu, ko na aureta ba adalci xan mata ba." Daga haka ya mike zai fita, "Har yau baka cancanci zama da Ummu ba, domin baka san darajar Ummu ba, kana niman Ummu ne don bukatar kanka." A matuƙar gajiye ya juya ga Abba da yake wannan maganar ya koma gabanshi. "Abba ka bani dama ta biyu, ka bani dama na gyara zamana da Ummu!" "Idan na baka dama ita ta ce bata bukatar zama da kai fa?" Lumshe idanu yayi ya bude, gwiwar shi a ƙasa. " zan amshi ƙaddarata a duk yadda ta zo min, zan rungume ta hannu bibiyu sannan zan zama Adali akan kaina da ita din."


Tsakanin d'a da mahaifi sai Allah, Tafida ya narkawa da Abba zuciya, "ka je Allah ya bayyanata!" Tashi yayi zai fita Hajiya Turai ta ce mishi. "Asiya yar uwarka ce, idan da hali ka bata aiki mana!" Bai bata amsa ba ya bar parlour. "Ya jadda baka ce kome ba!" "Turai kina ji ya ce Matarshi yake so, shi yasa nace miki ni ba zan kuma saka Tafida ya kara aure ba domin na sha ciwon kai akan Ummu, yanzu kuwa ban isa ba" kamar tayi kuka ta ce mishi.."Ko bai aureta ba ai Kanwarshi ce zata zauna a wurinshi." Haka aka bar zancen Baba Bulama ya kira suka kara tattauna akan batun Ummu. Sannan ya kashe wayar ya cewa Inna. "Maganar yarinyar nan ne, ana ta samun haske akanta!" "Allah ya bayyana wannan yaron yana ganin rayuwa waye ya sani ko matar saleh ne ta tura shi ya bi duniya."


"Allah ya kyauta!" "Amin Ya Allah!"
--
A kofar gidansu ya nime faduwa sai da Deen ya rungume shi. "Kai ni gidan Hajiya!" "Tow!" Haka ya wuce da shi. "Na kira Doctor ne?" "Bar shi kawai!" Haka ya wuce ga shi gidan Hajiya, security sun cika unguwar, Deen yana rike da shi har parlour Hajiya. Kwanciya yayi yana haki, "Babana ya dai?" "Hajiya wai auren wata yarinya aka bashi " "Asiya ko?" "Eh!" "Na gaya mata ta fara nimanshi ya ga yarinyar ni ba zan mishi dole ba." "Eh ya gaya musu gaskiya baya sonta!" "Alhamdulillahi! Tunda ya gaya musu! Tow shine ya koma haka?' "muna fitowa ne ya nemi faduwa a kasa." Murmushi tayi tana faɗin. "Allah ya baka lafiya kai Deen Allah ya baka ladan aikinka." D'ago kai Tafida yai yana faɗin. "Hajiya ni fa?" "Allah ya baka lafiya mana ai baka da lafiya ne!" "She Deen din me yayi da sai an mishi addu'ar lada!" "Tow dan hassada ashe kuma ba ciwo kake ba. Tashi ka zauna ka hana Allah bani ladan da ake min fatan samu, kai dai Tafida bakinciki ka dayawa yake yanxu don Allah ladan kake wa mita har da tashi zaune!" Ita kan Hajiya tana kallonsu fadar nasu gwanin ban sha'awa. Komawa yayi ya kwanta dole Deen ya kira Deen Sagir yazo ya duba shi, sosai yayi mamakin yadda jininshi ya haura. "Yallabai meke damunka haka?" "Kanwarka ta gudu ta bar gari, gaya min idan jini na bai haura ba ina zan cusa kaina." Girgiza kai Sagir yayi yana faɗin. "Allah ya baka hakuri ya daidaita tsakaninku!" Lumshe idanun yayi yana faɗin. "Amin Ya Allah! Ubangiji ka raba ni da yan sa'ido, masu farin ciki da halin da na shiga!" "Wallahi ba Amin ba!" Deen ya fada yana dariya. Haka suka yi ta drama har Sagir ya tafi. A gidan Hajiya Tafida ya rage dare dake Doctor Sagir ya bashi magani har da na barci, sannan Deen ya rako shi gida, har cikin gidan ya rako shi.
Washi gari. Bai fita office ba domin jikin ya matsa mishi, Saadiyyah tana can bangarenta bata san bai da lafiya ba, haka Deen da Sagir suke ta shige sai yamma da su Abba suka zo aka san halin da yake ciki, a lokacin ta fito zata je mishi tijara ta ga motar gida, a tunaninta Ummu ce ta dawo hankalinta a tashe ta nufi bangarenshi. A parlour ta samu yana kwance da karin ruwa a hannunshi. "Dama baka da lafiya ne?" Bude idanun yayi ya kalleta, hankalinta kwance sai kiba take. "Taya kuna gida ɗaya Sa'adiyya ace Mijinki bai da lafiya baki sani ba?" Kame-kame ta fara tana zare idanu. "ban gaya mata ba ne!" Mikawa Deen kunun da Hajiya ta dama mishi tayi. "Sannu da kokari Hajiya!" "Yawwa kafin ruwan ya kare yayi daidai shan shi ba." "Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana!" "Amin Ya Allah!" Wayar shi da yake hannun Deen ya karba yana faɗin. "Deen bani na gwada kiran Tinah kona abuja! Haka kawai nake jin like Tina tana tare da Ummu." "Wacece ita?" Hajiya ta tambaye shi da sauri don a wannan yanayin bata ki ta ga Ummu ba, ta roke ta ta zauna da danta idan ma ta kama har kwanciya tayi. "Kanwarshi ce tazo bikinshi ma." Kiran layin Tinah yayi ya saka a kunne. "Titina!" "Yes Aliyos ya kwana dayawa!" "Sai godiya!" "Teeminatina! Alfarma nake nima a wurinki" "Tafida ina jinka!" "Idan Ummu tana tare da ke ki ce mata tayi hakuri ta kawo min Yarana mu gana ina kyautata zaton rayuwata ya zo karshe!" "Ban gane ba!" Kwarewa yayi Deen ya kwace wayar yana faɗin. " idan tana tare da ke ki ce mata ta dawo kowa ya damu da halin da take ciki. Please."


Kiran Doctor Sagir akayi domin tari yake tayi kamar zai mutu, haka Sagir yazo da kayan aiki aka saka mishi abin numfashi, Hankalin Hajiya yayi mugun tashi. Karshe dai asibitin da yake cikin gidan gwamnati aka wuce da shi, ba iya Doctor Sagir ba har da wasu likitocin suka zo daga babban Asibiti tare da Kwamishinan lafiya da aka nad'a. Duk suka rufa akanshi, Maryam da Rukayya sun tawo, hankalinsu a tashe har yayunsa maza. "Yaya Jadda kayi wani abu!" Deen ya kalli Abba cikin kwantar da hankali ya ce mishi. "Zan tafi da wayarshi zuwa gobe da yamma zan shigo inda in sha Allah akwai wani ganawa da zan yi da wasu turawa idan na sake na rasa ganawar yau Tafida zai rasa wani babban abu ne bana son a rasa abin." "Tow! Allah ya baku sa'a!" Inji Abba, babu wnada ya iya mishi magana har ya bar gidan, kiran Layin Tinah yayi tana dauka ya ce mata. "Kina ina ne a abuja?" "Look ban san inda Ummu take ba!" Shashekar kuka yaji yayi yar dariyar takaici ya ce mata. "Bata wayar!" "Nace maka!" "Bata wayar nace!" Ya daka mata tsawa, "ok!" "Ummu!" Kukanta kawai ya ji ya ce mata. "Kina ina ne?" "Ibadan!" "Ok ki shirya kome dare xan kira Aliyu Tafida yana cikin wani irin yanayi bamu sani ba zai tashi ko zai mutu, ba zan ce ki dawo gare shi ba amma ki kawo mishi yaranshi." "Kazo ka ɗauke mu! Ka ji don Allah ka zo ka kai ni wurin Mamana!" "Good girl gani Safiyyudeen nan tafe!" Ya kashe wayar a lokacin yayi booking flight to abuja, karfe shida suka bar Maiduguri. Wurin goma yana zaune a airport din sai lokacin ya samu jirgin Ibadan.
"Ummu*
Tunda tafida ya kira yana tari domin ni ce na dauka, ta bar wayar a dakin yana kira ni kuma na dauka, da sauri na fito waje na mika mata wayar nayi na ji tana kiran sunanshi, sai na kasa tafiya. Sakawa da Handsfree tana magana da shi, ban san lokacin da na kura mata idanun ba. Da farko na zata drama ce sai da naji Deen ya amsa yana mata magiyar idan muna tare ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Domin ba karamin tashin hankali na shiga ba da yace na kawo mishi Yaranshi. Kuka nake ina jin a raina ban mishi adalci ba, da ni yake rigima ba da Yaranshi ba. Na saka yaran a rigimarmu! Haka na shiga haɗa kayanmu. Tana taya ni murmushi take tana faɗin. "Zaki koma ne?" Girgiza kai nayi na ce mata. "Yaranshi suna da hakkin ganinshi!" "Good amma dole ki koma ga Tafida kina buƙatarshi yana bukatarki." Shiru na mata, har na gama a ranar nayi sallama da mutanen gidan, wurin karfe daya Deen ya kira ya ce ya iso yana airport zai jira mu. A daren muka isa airport din, ta rike hannuna "Please ki nutsu ki yanke hukuncin da ya dace dake, kina buƙatar nutsuwa sosai, amma the best solution ki koma ga Tafida. Akwai abin da sai kin koma zaki kara ganewa." Hawaye ne yake zuba min nayi ta mata godiya. Muna isa Deen ya iso yana hararanta. "Kina da hankali zaki rike matar mutane? Sai na mare ki!" Ya nuna mata yatsa. "Shi mijin da gaske ya shirya zama da ita ne?" Kamar ya mangare ta ya kalleta. "Ka ce yayi hakuri kada ya mutu ga kayarsa nan dama tashi ce." Kaina a sunkuye ya ce min. "kin kyauta da kika tsallake har nan, idan gudun hijiran zaki yi me zai saka ki zo nan ga gidana." Ya fada da Yaren Babura, "Kayi hakuri!" Na fada, amsar kayan yayi ya mana booking jirgin kano, a daren muka wuce cike da kewar juna. Karfe uku na asuba muka sauka kano. Karfe shida bayan sallah asuba jirgin yan kasuwa da suka zo jiya yau zasu koma da safe, muka isa karfe takwas ya mana a gidanmu. Mama tana zaune akan abin sallah, ta ji ihun yara suka faɗin. "Oyoyo Aunty Baby!" Sai naji kunyar yadda na gudu ya kama ni, dakin Baba Bulama na shiga na zube a kan gwiwata, na fashe da kuka. "Alhamdulillahi Barka da zuwa Ummu Hadiyya, Allah ya miki albarka kin zo lokacin da ya dace, kai kuma Deen Allah ya tsarkake lahiranka da duniyarka!" "Amin Ya Allah! Zan tafi Baba don Allah kada ku gaya musu ni na dawo da ita." "Ummu Hadiyya!" Juyawa nayi ina kallon Mama da Ummi. "Allah ya shirya ki ke da zuri'arki, me yasa zaki tafi ba zaki min yadda xan gane ba?" Kuka nake itama tana share kwalla. Deen ya mana sallama ya tafi aka bar nida su Mama, can Mam Amina tazo bata san me ke faruwa ba, saboda bata gari tayi tafiya tsawon wata biyu. Tana jin haka ta shigo ya cewa Mama. "Tunda Allah ya nufa an dawo da ita, tow maganar kome babu shi, ta fahimci kanta da rayuwarta garin gudun b'acin suna ki rasa yarki!" "In sha Allah!" Basu rufe baki ba, Rukayya da Sa'adiyya suka shigo. "Maman Ummu Hadiyya ko?" Mama ta gyara tsayuwarta da kyau. "Tow ki gayawa yarki da ta tafi yawon karuwanci kada ta sake ta dawo rayuwar mijina idan ba haka ba sai na wulakanta rayuwarta kare sai yafi ta daraja!" Fitowa nayi na kalleta kafin na ce mata. "Karuwanci ba tambarin gidanmu ba ne, tunda ban bi na miji har gidan aurenshi ba. Kuma ki tambayi Tafida da kyau ba yar iska ya aura ba domin a bai kai ni asibiti gwajin a duba lafiyata ba, idan don Tafida ne ki je na bar miki shi ki kwad'a shi ki ci." "Kika fadi haka Ummu har kina da bakin fadar haka!" Inji rukayya. "Ina ganin girmanki saboda dan uwanki, ki fita mana a gida kafin na saka a muku a tule!" Ummun da suka sani ba ni ba ce rashin mutunci nayi musu suka fita da kunya, sannan na zauna na cigaba da kukana, "Ita yar uwanshi ce, ba zan taba samun nutsuwa a cikin gidan ba domin basu kaunata." "Bama zaki koma ba su je can su ci kansu!" Ɓangaren Mama na wuce na karya sannan aka yiwa Yara wanka, na kwanta sai barci. Can wurin karfe daya naji tana faɗin. "Mun gode, amma Hajiya kiyi hakuri ba zan bada yarinyata ga Tafida ba domin dazun Rukayya da Matarsa sun zo nan suka ci Mutuncinmu, nima ina son abata na bar halas don kunya ne amma yanzu ko shekara dubu zata yi babu miji zai fi min kwanciyar hankali na ganta haka da ace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login