Showing 18001 words to 21000 words out of 241571 words
Chapter 7 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
da dad'i. Tunda aka rantsar da shi bakiɗaya yan uwanshi da yan daki daya da waɗanda suke yan uba, suka kara shigewa Sa'adiyya wacce ita basu ne a gabanta ba, ga gidan nan dai Ummu ta bari sai me? Tafida ne kuma babu hadin kai yaƙi kulata ma, tana zaune a parlournta tana shan fruit Wanda ya sha kayan Mata, aka kirata a waya. Dauka tai tana yatsina fuska. "Tanko shi dade, Hajiya Larai ce shugaban Mata, na kira na tayaki murna sannan na tuna miki da alƙawarin da kika mana!" Wani haɗe rai tayi tana faɗin. "Tow ai bamu shiga gidan gwamnati ba ko?" Ta tambaye ta, sannan ta kara da cewa. "Idan muka shiga xan kira ki!" "Yawwa haka ne kan, Hajiya ko kin ga abin da yake faruwa Mai girma gwamna da wata mata da Yaranta hala kishiyarki ce ko?" Wani irin dauke wuta Sa'adiyya tayi kafin ta ce mata. "Ban gane ba?" Ta fada da sauri, "Eh tow ki duba zaki ga ana ta daura hoton a media! Sai an jima" matar ta kashe wayar, sororo tayi tana bin wayar da yake hannunta da idanun. Jikinta yana rawa ta buɗe data, abin da ta fara gani shine sakon da arewa fashion trending suka turo na *Mrs Tafida Mama's Kitchen! Long live Mr and Mrs Tafida!* Jikinta yana kerma ta shiga duba notifications hoton Tafida da Ummu ne, a yadda aka yi ta daura hoton zaka ɗauka soyayya ake zubawa a asibiti amma a zahirin gaskiya, rigimarsu da suka.fara ce take yawo a tsakaninsu yayinda media suka kafa hujja da cewa soyayya ce kawai.. a wani page da ta ga wata tana faɗin. *OMG maza kyawawa sun iya karewa a jikin Mata munana ba mamaki yayi breaking heart din kyawawan Mata Allah ya jarabce shi da auren wannan yar karamar yarinyar!* a kasar comments din aka rubuta. _Ke dalla ba yarinya ba ce, dakyar idan ya bata shekaru me yawa domin nasanta a dan gaba damu take Aunty Baby! Akwai mutunci da kirki* still yarinyar farko ta kara cewa *Amma ance su biyu ne ko?* *Eh su biyu ne akwai Amaryanta idan kika ganta wallahi sai ki dauka aunty Baby Yar aikinta ce saboda kyau da haduwa amma ki ga yadda ya kare* sai a lokacin Sa'adiyya ta sake murmushi, karamar wayarta ta dauka ta kira wani number. "Zan ajiye maka sako ta Whatsp! Kasan yadda zaka yi ka ruguza abin da ake daurawa a social media! Zan turo maka 20k!" "Ki nime wani yayi miki aikin ba zan yi ba" aka fada mata, tasan matsalarshi da maganar kuɗi. "Ok 50k!" "A'a bana bukata!" "Zan baka 150k yayi!" Ta fada a hankali, "tow ba damuwa bari mu tashi kura!" "Yawwa nasan zaka iya!" Ta kashe wayar tana me ɗaukar screen shot ta tura mishi ta Whatsp. _Kin san bana aikin banza ko? Don haka turo na miki aikin da zai zama trending!_
_Na sani! Sannan idan da hali ka karyata abin da ake fada na soyayya suke ! Ka gaya musu gaskiya Ummu ba zata dawo rayuwar Tafida ba aurensu mutuwa zai yi suna haka ne don hankalin mutane ya kau akansu! Zan kara maka idan har ka girgiza media!_ take ta tura mishi dubu dari da hamsin din. Tana jiran aiki domin tasan smarty matuƙar yace zai yi aiki tow babu me hana shi a duniya.
Bayan awa guda aka yi ta kiranta, ana tambayarta. "Sa'adiyya kin ga meke faruwa kuwa?" Dake tasan me ta kulla ko a jikinta. "Me ya faru?" "Hmm ke dai duba!" Bude data tai kamar da gaske ta ga abin da ya daura da cewa! *Labarin da ake ta damun kowa soyayya soyayya! Hmm soyayya for ma foot! To karya ce!* anan yayi ta rubutu akan wasu hotunan Ummu Hadiyya, da tafida. Yayi magana marasa dadi da kyau akan Ummu Hadiyya da Tafida. tare da kafa hujjar idan ana ganin karya ne a bincika Ummu bata tare da Tafida yanzu haka tana jiran takardan sakinta ne. Wannan abin ya saka mutane suka fara kokwanto akan maganrshi. Yayinda wasu suka yi ta zaginshi suna mishi mugun fata da Allah ya sakawa Ummu da Tafida.
Dariya tayi sannan ta karawa Smarty wasu kudadden, ta kashe wayar tana kad'a kafarta musamman inda Yaron ya rubuta. *Allah Sarki Uwar marayu gatan mai iyaye! Turmin tsakar gida shaluguden mahassada! Kin yi naki kin yi na me karamin karfi! Hajiya Sa'adiyya Aliyu Tafida! Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana! Madara mai kama da nono* wannan kalaman sun tsaya mata a rai! Sai kallon kanta take a wayarta. Tana murmushi ita yanzu idan da smarty ba zata kashe wa wani dan iska kudi ba, shi kadai zai yi draging kome out! Bayan la'asar aka yi sallama tana kwance bata tashi a wurin da take ba. Aunty Rukayya ce tare da yarta Naziha. Ita fa sun fara damunta daga ranar da aka tabbatar da Tafida ne ya ci zabe suka hanata sakat, amma dake makira ce mikewa tayi tana murmushi ta ce musu. "Aunty Ruky ke ce!" "Eh wallahi mun zo ganin Alhaji ne na ce bari na zo na gaishe ki!" "Ina wuni!" Naziha ta gaida ta sama sama, domin Allah bai had'a jininsu ba. "Mammy bari na shiga cikin gida!" "Au baku shiga ba ne?" Inji Sa'adiyya, "eh yanzu shigowarmu!" Aunty Rukayya take fada, "Ayya!" Ta fada fita yarinyar tayi, Aunty Rukayya kuwa tayi ta zuba tun da suka shigo bata kira an kawo mata ko ruwa ba, suna zaune aka kirata. Cikin dauki da murna ta ce mata. "Tow sai kun iso!" "Laraba!" Da sauri matar ta fito tana faɗin. "na'am hajiya!" "Yawwa maza a gyara parlour ki ce Rose ta hada kayan ciye-ciye ga matar mai taimakin gwamna nan zuwa da Yaranta!" "An gama Hajiya!" "Masha Allah yau gidan da baki kenan! Ai da sun fada da wuri ko abinci da anyi musu!" "Eh ba kome haka ma yayi" ta nufi dakinta tana hararan Aunty Rukayya, dake bata san meke faruwa ba. Ta tsaya aka gyara parlour sannan aka jera musu abin tabawa. Kafin karfe shida bakin sun iso, nata so Aunty Rukayya ta zauna ba, amma haka ta share suka yi ta ina zaka saka ina zaka ajiye da iyalin mataimakin Gwamna. Sai bayan Isha suka tafi shima lokacin Tafida ya shigo suka kara gaisawa, sannan suka rako su. Juyawa suka yi cikin gidan Aunty Rukayya ta shiga tattara abubuwan da aka sakawa baki tana zubawa a wani leda abin ya bawa Sa'adiyya haushi. A cikin gidan kuwa tunda Alhaji Muhammad Jadda ya ga Naziha ya tambaye ta. "Ina Mamanki?" "Tana can bangaren Uncle Tafida!" Jinjina kai yayi yana faɗin. "Ai haka yayi!" Yana sane da abin da suke ya zuba musu idanun ne kafin Allah ya hukunta su daidai da laifinsu. Ko da yayi magana za su ce yana bayan Ummu ne Gara ya zuba musu idanun tukun indai shuwa ce Allah zai kawo karshen abin da suke yi. Har aka yi sallah Magariba bata shigo ba sai bayan sallah ta shigo sama sama suka gaisa. "Naziha muje gida dare yayi!" "Tow!" Ta fada tana kallon Alhaji Muhammad Jadda, "Abba Allah ya baka lafiya, zamu tafi!" "Ku gaida yaran da mai gidan!" Suka fito da sauri tana faɗin. "Zai ji in sha Allah!" A kofar dakin Inna suka tsaya"tsohuwa zamu tafi ban samu shigowa ba!" "Ai kai kud'a me kwadayi ne ban yi mamaki dan baka shigo ba, a gaida Yaran!" Dariya ta yiwa mutanen gidan sallama suka bar gidan domin Tafida ya bada motar da za a kaita gida. Shiga dakinta tayi tare da kiran Uwarta. "Mommy na gaji! Wallahi na gaji haba don Allah akan shi aka fara zama gwamna ne? Ace kai da gidanka ya zama kamar gidan gandu, kowa zuwa yake bakin arziki ma sai anyi ta shige musu!"
"Kiyi hakuri lokaci ne zai tabbatar da haka, ina sane da kome. Sannan kiyi amfani da ruwan nan fa da hayakin da turaren" "Shi kenan!" Ta kashe wayar, ban daki ta shiga tayi wanka da ruwan rubutun tayi turaren da kome sannan ta wuce kitchen ta dafa mishi indomie aka barbad'a kayan aiki kafin ta wuce dakinshi, yana ta aiki a laptop. Karatun Sheikh abdurrahman sudais yake tashi a wayarshi. Ta kawo ta ajiye mishi, "sannu da hutawa!" "Yawwa!" Ya fada yana aikinshi. "Ga abinci!" "Me kika dafa?" "Indomie ne!" Ta fada tana kallonshi. "Barshi kawai xan sha tea!" Ya fada yana me cigaba da aikin. "Na hado maka?" "A'a ina aiki idan na gama zan sha!" Ya fada yana ta aikinsa kamar ta fashe da kuka tana zaune a wurin har barci ya fara daukarta, ya mike ya haɗa tea sannan ya bude drower dinsa, soyayyen nama ne da dambun nama, ya zuba a wani flat ya dauki bread guntu ne ma jiya Deen ya saya musu. A hankali yake ci yana jin dandanon kayan haɗin abincin Ummu, daukar tea din yayi da kayanshi ya kai parlour sannan ya dawo ya dauki wayarshi ya koma parlourn. Yana shan tea yana me kiran Ummu. Sai da ta kusan yankewa ta dauka da "hello! Waye?" "Kiyi tunani Ummu Hadiyya me kyau ga dambuna ya kare waye zai min irin naki?" Kashe wayar aka yi, ya kira yaji wayar a kashe bakiɗaya. A can dakin kuwa yana jin motsin fitarshi ta farka tare da bin shi ta makale tana me saka kunnenta. Jin sunan Ummu abin ya bata mamaki, wannan wacce irin masifa ce haka? Tana Barka an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kwafa tayi tana me barin jikin kofar ta kwanta karshe barcin da bata yi ba kenan har sai.da ya shigo a saninta shi din yana da bukatar mace a koda yaushe, amma sai ta ga tun barin Ummu Hadiyya gidan ya rage sosai asalima tana zuwa dakin zai dauki pillow ya shimfida bargo ya kwanta a kasa. Wannan abin ya mata ciwo ko yana mata ciwo kamar wacce tayi mishi wani abu bakiɗaya ya janye daga kulawar da yake bata. Dakyar barci yayi gaba da ita cikin takaici.
***
"Waye ya kiraki a wannan daren!" Kallon Mama nayi kafin nace mata. "Tafida!" Sannan na gyara kwanciyana. "Yaron nan yana ta kokarin ya ga kun daidaita amma kin ki ban san wani irin taurin kai yake damunki ba, amma ba xan daina gaya miki gaskiya ba domin kuwa shi ne gatan da zan miki." Kasa magana nayi ina kallon gefen da take kwance, a hankali naji alamar barci ya ɗauke ta.
Gyara kwanciya nayi ina son na tuna me yasa na rasa wanda zai tsaya min akan abinda Tafida yayi min? Me yasa Mama take niman juya min baya? Me nayi da zafi haka da kowa yake ganin kada na rabu da Tafida.
-
Sunana Ummu Hadiyya a sanina ni agola ce Mama ta auri Baba Alhaji Bulama bayan ta yaye ni. Alhaji Bulama yana da mata biyu da Mama uku Hajiya Balkisu ita ce uwar gida kuma me manyan Yara dakinta tana da yara biyar, Ahmad Bakura yana aiki a abuja yana da mata daya da Yara biyu, sai Muhammad sani Kawu Gwani sai Salman Bamai, sai Safina wacce ake kira Taima.....
N500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
*Assalamualaikum don Allah kada a tura payment ta GTBANK babu network zan saka Opay dina*
Paid book
08
Sai Saratu wacce ake kira Kwaise, ita ce autarsu. A gaban Hajiya Balkisu akwai Yar kaninta wanda ya rasu ya barta wato Mahira Hajiya Balkisu wato Ummi ita ta fito ƙabilar barebari ce wato kanuri kamar Hajiya Bulama Hajiya Balkisu tana da zafin kishi shi yasa kome nata ya banbanta da na kowa hatta Yaranta ba yarda su tafi . Sai Hajiya Karima wacce muke kiranta Umma, Yaranta uku duk mata ne , kuma kowacce tana gidan, Sadika, ita ce babba yaranta hudu, sai Asiyah tana da yara biyu sai Azizah ita ce har yau Allah bai bata haihuwa ba, dukkansu ukun nan suna aure cikin manyan ahali.
Mama ce matar Baba ta uku, lokacin da aurenta ya mutu ta bar garinsu tazo wurin Kanin Mahaifin ta zauna. Mama yar kabilar Baburawa ce. Anyiwa Mama auren dole ne da Babana wanda ya kasance malamin makarantan secondry school, Babana ya so Mama amma saboda kiyayar da take mishi taki zama, haka yasa dole aka raba auren lokacin ban wuce wata goma a duniya ba, shine ta dawo garin Maiduguri wurin Kanin Babanta da zama, matar kanin Babanta Mama Yahanasu gidanta cike yake da Jama'a kasancewarta tana sana'ar sayar da abinci a bakin kasuwar Monday market, wuni ake ana shiga da fita. Anan suka hadu da Alhaji Bulama, wanda ya nuna soyayyarshi a gareta kuma ba a wani sha wahala ba ta amince mishi.
Manya suka shiga cikin maganar, haka aka yi daurin auren ta tare, kasancewar ta san dadin niman kudi bata yarda ta aure shi ba sai da ta ce mishi zata fara sana'arta, shi kuma a bangaren Alhaji Bulama abin da ya kara bashi sha'awa da Mama ta gama secondry school, haka yasa shi kara bata kwarin gwiwa ta fida poly tayi diploma, wanda ta fara shi tana da cikin Ummu Kulsum, har aka haifeta ni a lokacin ina wurin Hajiya Yahanasu, duk da ban wani girma sosai ba, sai dai ina da matukar wayo a lokacin, bayan shekaru biyar a lokacin ina da shekara bakwai a duniya na koma gaban Mama, sakamakon rasuwar Hajiya Yahanasu, da Babana yaso amsata amma fir taki amincewa haka yasa saboda kaunar da yake mata ya hakura na zauna a hannunta, Mama uwa ce da ta tsaya min a ko ina, duk da kuwa ina shan gori a wurin yaran gidan amma haka bai hanata nuna musu ina da gata ba, ban san babana ba amma a yadda nake jin tana bada labarin Babana yana da rufin asiri. Har tana fadawa mutane yadda duk bayan wata shida yake min aike ita ce ta hana saboda bata son kome daga gare shi.
Duk yaran gidanmu suna da ilmi. Hatta kannena suna da kokari idan ka cire ni, duk yadda naso nayi karatu domin Mama dai ba tayan baya ba ce a ilimi, sannan tana aiki da local government. A lokacin Mama ta fara deciding fara yin abincin sayarwa saboda ta fara amma ta ajiye sakamakon aikinta, kuma tana sayan kayan abinci tana rabawa ma'aikata karshen wata su bata kudinta. Tunda muka fara abin karyawa na sayarwa idan muka tashi tun 4:30am muka fara aiki ba zamu koma.ba sai karfe sha daya na dare sakamakon yadda ake wuni sayar da abinci,ana sauke abinci karfe shida na safe, kafin karfe bakwai na safe ya kare an daura na rana. Ni zan tafi makaranta ita Mama aiki. Sannan akwai masu mana aikin wake-wake da daura abincin rana saboda zan dawo, ina da shekaru goma a duniya Mama ta sake min ragamar girkin abincin sayarwa tare da bani damar na cigaba da kula da kome tana lissafi, ba don kome ba sai yadda ta fahimci ƙwaƙwalwata bata iya gane kome sai sarrafa tukunya da kayan abinci, Mama tayi kokarin nayi karatu amma Allah ya gani bana ja bana iya kome ban san kome ba idan ba girki ba, tayi min nasiha har dukana sai da tayi amma ban fahimci kome ba. Alhaji Bulama da kanshi ya dakatar da ita ya ce ta yiwu bani da wani abin da zan amfana ne a can, sai ta saka ni a high Islam, na fara gara shi kan ba laifi na maida hankali sosai. Sannan a unguwar mu ina zuwa tahafiz kada ku sha mamaki yadda nake iya karatun Alqur'ani amma boko kamar zan mutu ko hala ban da rabo ne cikinshi. Mu hudu Mama ta haifa Ni ce babba sai Ummu Kulsum, sai Ummu Rumana, sai Ahmad domin Ahmad biyu ne a gidan mu, Baba Bulama yana da rufin asiri sosai, domin babu abin matanshi da yara suka nima suka rasa, Ummi wato Hajiya Balkisu turare take sayarwa shine sana'arta Umma kuwa yar zaman banza ce, sai gulma bata da aikin.
Akwai wani abu da nake kara jin dadi da tausayinsa a raina farkon dawowata gidan yadda Yaran gidan suka tsane ni, idan na cire Sadika wacce ta girme ni sosai, amma Asiya,Azizah, Taima, duk sa'o'i muje sai Yaran riko da Ummi da Kuma suke daukowa, saboda ni da Baba ya bar Mama ta dauko ni. Suna irin na cin mutuncin da cin fuska babu wanda ba a saka min a gidan ba, an saka min yar duna jikar masu daddawa, Mama ta tsaya kai da fata ita da Baba da Kawu Gwani wanda Allah ya haɗa jininmu, suka kashe sunan. Bayan nan aka sake saka min African queen, Kai har sai da sunan ya fita waje Baba ya samu me unguwarmu aka kashe sunan, sai da aka saka min suna yafi kala goma Mama da Baba suna kashewa domin akwia wani yaro me suna Farouk da ya saka min cinnaka baki san na gida ba, sunan har makarantarmu ya tafi, Mama ta wanke kafarta har gidan iyayen Yaron ta ce bata yarda ba. Shine aka dawo aka saka min Baby. Kun san dalilin, kasancewata yar karama domin bani da girma sannan ni baka ce ina da dan auki sakamakon yadda Mama take fada ai ni bakwaini ce shi yasa nake da karamin jiki.
A lokacin da na cika shekaru goma sha biyar, ina dab da gama high islam. A wannan lokacin Baba ya bude gadon sayar da Abinci ya ce min yaga ina da kokari na cigaba da sana'a. Haka na cigaba har muka yi sauka,.inda na kara kankaro mutunciwa