Showing 210001 words to 213000 words out of 241571 words

Chapter 71 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14694

Jidda, domin ya shiga Makka yayi Umara, anan suka hadu da Abba, yake gaya mishi abin da Ummu take a can. "Abba na ga gazawa a tare da ita, sannan rauni da gajiya na tattare da ita. Abba na shirya na zauna da Ummu Abba ka saka baki a karo na biyu Ummu ta dawo min!" "Ummu ko ta dawo taya zata yi handling matsalar danginka? Yaran da basu ji maganata ba, maganar waye zasu ji? Ummu ba kai take gudu ba danginka take gudu. Domin kuwa danginka sun fi kome tashin hankali ka kyaleta, ta huta bana son Kai Yarinyar nan tana fuskantar kalubale. Is too much ta cigaba da ganin bakinka sanadin yan uwanka!" "Abba nayi maka alkawarin zan gyara!" "Gyaranka zai lalata zumuncinku, idan har na fahimci Mahaifiyarta tsoro kada son da kake mata ya lalata zumuncinku ne!" "Abba ya zan yi?" "Ka kyale ta amma ka tsaya a gefenta, yadda zata ji ashe tana raye, matukar kayi haka tow zata iya tunawa da kai na musamman ne idan bata yi nazarin haka ba ka kyaleta tayi rayiwarta, wannan shine kaddaranku!" "A'a Abba kaddaranmu a hade take, ba zan iya rabuwa da ita ba, domin ita din rayuwata ce, ana iya sauyawa tuwo suna Ummu a rayuwata ƙaddara ta ce ita, don Allah kada ka ce min rabuwarmu ƙaddaran mu ce!" Murmushi yayi yana kallon Tafida da yake kallon dakin Ka'aba. "Yarona ka girma!" "Abba bashi nake son ji ba, ina son jin kace min go a head!" "Ni kuma?" "Eh Abba!" "Shi kenan Tafida idan kana ganin zaka sake dawo da ita duniyarka ina farin ciki, kuma na yarda ni na haife ka, idan kuma kayi fail ba zan ce kome ba zan kira shi da Fated!" "No need ka kira shi da ƙaddara! Ummu tana sona zata dawo gare ni na sani!" Dariya irin ta Manya yayi sannan ya wuce da zance zuwa ga faɗin. "Me ya samu Mahmoud da iyayensa?" "Yan fashi suka shiga gidan suka musu ta'addancin." "Wani mataki ka dauka a matsayin Abokinka?" Abba ya tambaye shi. "Abba babu abin da zan yi domin kuwa kamar fansa ce ba zalinci ba ne!" Shiru Abba yayi kafin ya ce mishi. "Yanzu waye a tare da shi?" "Deen!" "Wannan yaron dan halak ne, Allah ya mishi albarka domin duk ya fiku karfin imani!" Murmushi Tafida yayi ya ce mishi. "Abba ina kishin Deen fa!" "Sai kayi!" Dariya suka yi baki dayansu. "Abba har yanzu baka ce kome akan Hajiya Kaltuma ba."
Murmushi Abba yayi ya kalli Tafida da kyau kafin ya juya yana kallon dakin Ka'aba, ya ce mishi. "kana tsammanin lamarin zai tafi da sauki ne? " "Kamar ya Abba?" Murmushi yayi kafin ya ce mishi. "Kaltuma ita ta mai da kai Gwamna.........(What?) Jira jira jira..... Jama'a anya kun hango wani kwarya - ƙwaryar gurmi kuwa......🏃🏻‍♀️ Muje bingo .......
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7668
"Ban fahimce ka ba Abba!" Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana me hura iskar bakinshi ya ce a hankali. "nasan abin da Kaltuma take aikatawa tun daga kashe mazajenta har zuwa mahaifiyarta, amma kana da hujja? Idan baka da hujja ka kyaleta ka barta kawai!" "Abba me kake faɗa ne?" Murmushi Abba yayi kafin ya ce mishi. " A shekaru irin naka ba zaka iya hango abin da nake nufi ba, amma da zaka fahimci yadda rayuwa take tabbas zaka iya boye mai laifi domin wata kusurwan!" "Kenan Kaltuma ba zata fuskanci kome ba!" Lumshe idanun Abba yayi ya bude yana Murmushi. Tashi Tafida yayi hannunshi a cikin aljuhun wandonsa ya ce mishi. "Gobe xan wuce!" "Ubangiji ya tsare maka hanya ya kare ka da mugun ji da mugun gani!" "Amin Abba, amma me yasa ka ke kare Kaltuma?" "Na zata mun bar wannan maganar, akwai wani gidana a Dubai da na saya shekarun baya, yana wurin Deen zai tura baka, ko ya turo maka Dubai ka ɗauke matarka da Yaranka, ba laifi bane don kayi haka amma ka sani any single mistake zai iya janyo more regret har karshen rayuwarka." Kasa magana yayi yana kallon Abba, kafin ya bar haramin. "Ya Allah ka ga Aliyu ya Allah ka taya shi yaki da azzalumai na ci danna waje!" Ya fada yana zubda hawaye. Domin ya kai matakin da bai isa ya bari a cutar da iyalinsa ba, yasan idan ba haka yayi ba zai iya rasa Aliyu yasan wacece Kaltuma sau biyu yana tsallake rijiya da baya akan tuggun da ta haɗa mishi har yau yana taka tsantsan akan abinda zata bashi ya ci ko ya sha, yasan darajar rayuwa amma bai kawo zata iya saka Yaranshi a cikin lissafinta ba, yasan me take bukata yasan meye harinta. Na farko abin da ya faru akwai wani had'akar kamfanin hako zinari da Alhaji Bashir Ishaq suka saya a Zamfara wanda ake fitar da zinari zuwa kasashen waje, wannan kamfanin shi bai da wani kaso me yawa a cikinsa kashi ashirin da biyar ne na shi, saba'in da biyar na Alhaji Bashir Ishaq ne, wanda Alhaji Muhammad Jadda ya saka sannun Babban Yaron Alhaji Bashir din wato Ishaq Bashir Ishaq, wanda ya dauke yaron zuwa canada saboda yadda Kaltuma ta saka a kashe yaron da kanwarshi. Barista Sallau Jibia wanda yake zaune a Lagos shine lauyansu, sannan ya san kome domin da shawarar shi aka dauke Yaran zuwa can. Don har Kano ta saka aka bi yaran a kashe, Allah ya tsiratar d su, Kaltuma ba matsuyaciya ba ce tana da rufin asiri amma yadda kasan mayunwacci idan ta ji zancen kuɗi ko wata sabga na kudi, haka yasa, take farautar rayuwar Aliyu domin kashi ashirin da biyar na wancan kamfanin hako ma'adanan na Tafida ne, domin sun yi alƙawarin barwa Yaransu ne, tun a lokacin Haihuwar Tafida Allah ya budewa Alhaji Muhammad Jadda wani irin kofar samu da duk abinda ya tab'a sai yayi albarka, haka yasa yake gayawa Alhaji Bashir Ishaq, shi kuma ya ce su sayawa Yaransu wani abu da zasu amfana tunda sune silar samun damar haka, ance kowani Yaro da arzikinsa Amma zai iya cewa Tafida shi ake kira goshi daga haihuwarsa har zuwa yanzu bai tab'a fuskantar Babu ba, haka yasa yake matuƙar son Yaron, kuma ya lura rufin asiri da albarka a jininshi take, domin tun yana ƙaraminsa idan yayi baki suna mishi alkhairi, tow wannan kudin ya karba ya ajiye mishi yana tarawa idan ya sayi wani abu da shi sai yayi albarka, haka yasa shi gane cewa A Yaranshi Aliyu na daban ne kuma me albarka ne shi.


Abin ya faru a Saudi kenan.


Nayi barci kamar ba ni ba, koda na bude idanuna a gajiye kallonshi nake yana zaune akan abin sallah. Hannunshi dauke da hisnul Muslim. A hankali na fara kokarin tashi ya ce min.."Please ki kwanta za a zo duba ki!" Ya fada yana daukar wayar dakin ya danna number "ta farka!" Naji ya fada, ko minti goma ba ayi ba sai likita da nurse a gefenta, suka gama duba ni kafin suka bar dakin, likitan ya ce mishi.."akwai gajiya da damuwa a tattare da ita tana hutawa." "In sha Allah!" Ya fada yana me kallona, kafin ya shiga ban daki ya haɗa min ruwan dumi, ya fito . "Tashi ruwan na ciki, kiyi wanka zaki ji daɗin jikinki." A hankali na sauke kafana kasa, na nufi ban dakin na shiga ruwan nayi wanka, sannan na fito daga ban dakin, ya ajiye min doguwar riga da abin sallah, ina sakawa na gabatar da sallah, ina idarwa Tinah tana shigowa ta same ina addu'a, shafawa nayi ta ajiye min abincin. Sannan ta mika min newyork magazine! D'ago kai nayi ina kallonta, "me ya faru?" "Wai cewa aka yi a tarin girkin ba tab'a samun mai juna biyu da mijinta ya tsaya mata shi ya amshi kyautar da aka baki, sannan da aka tambaye shi me yasa yayi replace ɗinki ya ce kina buƙatar hutu saboda yanayin yadda kike aiki sannan kun yi da shi zai amshi kyautar." Kamar wawuya haka na sake baki ina kallonta, shigowa dakin yayi ya kafe shi da idanuna da ya cika da kwalla. "Me yasa?" Kasa magana yayi cikin fashewa da kuka nace . "Me yasa?" Na daka mishi tsawa, da yasa shi matsowa kusa da ni! D'aga mishi hannu nayi tare da cewa. "Ya isa kayi tafiyarka bana son ganin ko Inuwarka!" Hannuna ya kamo yana me sakawa a kirjinshi, wanda nake jin bugunsa kamar zai fito waje, wato zuciyarshi. "Ki saurari sakon nan don Allah!" Hawaye ne ya zubo min cikin shashekar kuka na rintsa idanuna nace mishi. "Kafin yau ni ka ajiye a inda kake, da kayi tunanin yadda zan fahimci Yaren zuciyarka, ba zaka tab'a juna min baya ba, amma sai ka juya tare da yanke min hukuncin nima mutum ce ka tab'a tunawa zuciya ce a kirjina! Kuskurena soyayyarka ka tafi ina son hutu daga kome har da kai, idan ka dame ni zan yi fatar na mutu." Hadiye yawu yayi yana kallon yadda nake kuka, tare da juyar da kai ina dan bubuga gefen zuciyata inda nake jin zafinta da kuna! "Please je ka!" Inji Tinah, fita yayi na kifa kaina a tsakanin cinyoyina duk da cikin da naji ya fara turo min.


"Ki ci abinci!" Ta ce min tana ajiye min abincin. "Kin san da zuwan shi ne?" "Eh tun daga farawa yake tambayata shin kina da lafiya kuwa? Ya ga kamar kin yi rauni, ban tab'a sanin cewa kin yi raunin sai da kika yi ta zuwa na biyu na fahimci raunin da kika yi, Ummu kina son Tafida soyayyar shi kike bukata kuma ya baki amma me yasa kike rejecting dinsa?" Hawaye ne ya zubo min, "Tafida bai san meye so ba, sai ya rasa wanda yake so a lokacin da yake tsakanin sonshi a nan zai fahimci ainihin kalmar so, yanzu yana wannan yanayin ne saboda abu biyu zuwa uku, na farko kanshi da bukatarshi na biyu saboda iyayenshi da gidansa na uku saboda kada Yaransa su taso babu uwa tare da su " sake baki tayi tana faɗin. "Ummu waye ya gaya miki haka?" "Nasan da haka ne, tun kafin mu samu matsala!" Ya fada ina shan tea me dumi tare da share kwalla da yake zuba.


Yana jikin kofar a jingine, sai ya rasa me mishi daɗi domin bai zata sonka shi na farko Ummu zata fahimta, gashi nan kome ya jagule shi, kamar ya saka hannu a kai yayi ta ihu, damuwa ta sako mishi kai daga ko wacce kusrwa ji yake kamar bashi ba, yana ji yana gani ya dasa kiyayar shi a idanun Ummu yana hango yadda take kin hada idanun da shi, bakiɗaya jin shi yake kamar fanko kamar bai da wani amfani, barin kofar yayi ya nufi waje.
Yadda nake kuka sai na kasa gane kukan abin da nayi mishi ne ko na farin cikin abin da yayi min ne, bana ce na ji zafin abin da yayi min ba, domin ban tab'a kawowa zai zo inda nake ba, "Me yasa?" Na tambayi kaina ina wani irin kuka wanda na rantse da Allah kukan abin da nayi mishi ne, ina jin zafin shi amma bana nufin nayi mishi abin da zai kara nisanta shi da ni ba, ban san me yasa naji zafin tsawar da mishi ba, haka yasa nayi kuka sosai.


Tsawon kwanaki uku, ina kwance duk wannan kwanakin ina samun kulawar da ya dace, sai dai har yanzu zuciyata bata huta da ciwon da nake ji ba, jin muryan Tinah nayi tana magana ƙasa - ƙasa, daga yadda na ji tana kallona yasa ni gano da Tafida take. "Ok bari mu shirya tunda jidda ne!" Bude idanun nayi ina kallonta. "Ina zamu?" "Surprise zamu miki!" Naji tace Jidda amma fir taki magana, haka yasa nima naki yarda na shirya ina kallonta. "Ki shirya muje duk inda zamu ai ba zan bari wani abu ya same ki ba,sannan tsakaninki da Allah koda Tafida yayi miki wani bai dace kina nuna mishi har yau abin na ranki, na zata Ummu da na sani ce me maganin kowa da ruwan sanyi ashe zuciyarta yayi rauni idan kika cigaba da fushin da Tafida zai ta nisa daga gare ki, kina son shi kina gudun tashin hankali ne, eh ba laifi ba ne." Tun daga nan na tashi na shirya na shiga ban daki nayi wanka na samu ta haɗa mana kayanmu, daga nan na shirya muka nufi airport, mun bar kasar Amurka da tarin kyauta me tarin yawa wanda na samu daga gare su saboda na zo na ɗaya, duk da haka farincikin da nake ji ba wani can ba ne, lokacin da muka bar kasar ina jikin window ina kallon kasar wanda ko a mafarki ban ta tsammanin zuwa ba.


Bayan wasu awowi muka sauka a jidda, naji na gaji, haka muka isa masaukin shi kuma ya wuce asibitin, sai da muka huta har washi gari sannan muka tafi asibitin, lokacin da muka isa asibitin, anan na gane Allah da girma yaƙe, dakin Hajiya muka fara sauka inda Hajiya ta kara ya mutsewa, sai gashi ina kuka fita yayi daga dakin yana me jan Tinah suka bar ni da Hajiya da ta mika min hannunta, da dan sauri na matsa kusa da ita. "Ummu!" "Na'am!" Na amsa ina kuka domin na rasa me yasa nake jin tsinkewar zuciya, rike hannun juna muka yi. "Ki ce su kai ni Makka nayi umaran bankwana!" Cikin wani irin tashin hankali na rike hannunta gam. "Hajiya ki daina fadar haka, Hajiya kece kwarin gwiwa Tafida, idan kina fadar haka ina muke son ya cusa ranshi?" Yau na gane ashe hauka nake, shigowa dakin yayi yana faɗin. "Hajiya kin ci abinci kuwa? Ina Fanna?" "Na ci ai." Kallona tayi tana son na mishi magana. "Daadi ko zamu shiga Makka Umara ne?" Kallona yayi bakinshi ya kasa furta kome, "Are You pity for me?" Dauke kai nayi na juya mishi baya, ina jin wani irin kuka na zuwa min. "Idan kika ganin zaki iya tafiya a mota Hajiya ai ba matsala!" Murmushi tayi mishi, tana me mika mishi hannunta, ya daura hannun a saman nata. Kallonshi tayi ta ce. "kayi min alƙawarin ba zaka sake barin tayi kuka ba idan ba na farin ciki ba!" Ta daura hannunshi akan nawa, kallon hannunmu nake hawaye na zuba na rasa gane soyayya ce ko tausayi ce. "Bari nayi muku booking!" Ya fada yana me zare hannun shi a saman nawa. "Ummu!" "Na'am Hajiya!" Yadda ya juya zai fita sai ya kasa fita. "Koda ba isa Makka ba Allah ya amshi rayuwata ayi min sallah a harami don Allah! Kada a maida gawata gida a binne ni a Makka wannan shine alfarman farkon da xan nima a wurinki, na biyu don Allah ki saka idanun akan Aliyu duk cikin Yarana shine ya rasa soyayya da jin kai na uwa amma ko daidai da rana daya ban fasa kai goshina kasa ina mishi addu'a ba, nasara da sa'a ban san iya adadin da na roka mishi ba, na kara roka mishi Allah ya bashi mace tagari Allah bai kunya tani ba, ya amsa min. Ummu ga amanar Tafida don Allah na baki amanarshi ban ce ki koma rayuwar shi iya haka kika min kin cika min burina, Ummu na gode sosai da zuwan da kika yi." Ban tab'a shiga wani irin yanayi kamar yau ba, fita yayi can sai gashi ya dawo ya ce mata. "Hajiya driven yazo bari na gyara kujeran!" Ya dauko ya gyara daga ni har shi jikinmu a mace, ya gama sannan ya nufe ta, ya dauke ta cak ya daura ta akan kujeran marasa lafiya. Yana me kallona, "muje ko!" Kayan dakin na kalla. "Kada ki damu zata dawo ai kwana sati daya zata yi a Saudiya sauran a zata yi a Madinah daga can jirgi zaku bi ku dawo nan sai ki wuce gida, kiyi hakuri na miki kutse." Ban iya bashi amsa ba haka nayi ta bin bayansu jikina wani sanyi yake kamar an lullube ni da danyen nama, sai da ya kai mu dakin Asiyah wacce suke ta hira da Tinah da Fanna. "Habibi! Kayi min addu'a Allah ya bani lafiya." Ta fada tana murmushi, idanunata yana kaina ta ce. "Hajiya Allah ya baki lafiya, yau ban zo miki hira ba da nazo har rawan larabawa zan miki!" Zuwa yayi ya make kafadarta yana me rungume. "Zan dawo ki jira ni kin ji!" Sunkuyar da kai nayi ina jin wani abu yana tokare min kirji idan wannan shine kishi tabbas zan jima da wahala. "Allah ya baki lafiya, yasa zakkar jiki ne ki kula da kanki kin ji ina son ki kula da mijinki dakyau!" "Hajiya gawa kike bawa sallawu?" Gabana ne ya fadi jan kumatunta, "waye yasan gawan fari yar nan? Ai kawai Allah yasa mu cika da imani, idan kika ji labarin mutuwata kizo min jana'iza kin ji!" "Hajiya ina hanata kina farawa me yasa suke son haukata ni ne? Ita bata da hiran sai nan da shekara daya zata mutu kema kina kara tayata!" Dariya suka saka Hajiya ta ce mata. "Kin ji ko? Yanzu zai fara faɗan nashi!" Tashi tsaye Asiyah tayi tana mata rawan larabawa tana faɗin. "Hajiya kyale shi dai nayi rawan nan!" Tura keken yayi yana faɗin. "Allah ya ganar dake!" Sai yanzu na kara jin hankalina yayi bala'in tashi, domin bayan waɗannan bayin Allah babu inda Tafida yake walwala, daurewa nake ina kallon yadda ya zabge amma yadda zaka hango juriya da hakuri zai tabbatar maka Aliyu ya sauya sosai, har muka isa wurin motar ya d'aga Hajiya ya saka ta a cikin motar, sannan ya rufe inda ta zauna zan bude yazo ya bude min, na shiga sannan ya rufe min kofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login