Showing 48001 words to 51000 words out of 241571 words
Chapter 17 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
gidanka haramun ne domin idan yayi yunkurin rape Ummu fa?" Hadiye yawu yayi makwat. "Kina hauka ne? Taya Mahmoud zai aikata haka, abokina ne. Kuma bai da inda zai yi jinya sai gidana!" "Bana hauka amma idan ya tab'a Ummu zan tabbatar da daga kai har shi kun yi danasani na rantse maka da Allah!" Ta mike tare da fita tana me buga kofar office din. Tsaki yayi ya kira Number Mahmoud a kashe..
**
Dama jiya nayi azumi Alhamis, wanda yasa na shigo da wuka dakina da su lemo da safe naje dauka ina sauri zan yi abin karyawa, wukar ta fadi ban tsaya dauka ba na nufi kitchen na fara daura abin karyawa, domin Tafida, ina gamawa na wuce daki na bar musu ina jin suna karyawa har Mahmoud din yana fada mishi. "Yau xan tafi fa!" "A'a ka bari ka warware bakiɗaya." "A'a zaka iya dawowa ka samu na tafi don na warke!" Y fada daga nan ban kuma sanin ya suka kare ba, ina gama karyawa na kwanta abuna, sai wurin karfe goma na farka na shiga ban daki nayi wanka, ina fitowa na daure da Babban towel. Na nufi wurin kayana da yake kan gado, turo kofar aka yi na juya da sauri Mahmoud tsirara haihuwar Uwarshi da ubanshi da sauri na juya tare da ɗaukar hijab dina na fara kokarin sakawa, ji nayi an cira ni sama tare da watsa ni kan gado. Na fasa wata irin ƙara. Nan ya shiga kokarin cire min hijab dina, muka shiga kokuwa da shi har Allah ya bani sa'a na ture shi tare da tashi da sauri xan fita ya riko kafana, ya ja ni na fadi towel din jikina ya so ya fadi. Na rike da karfi idanuna.ya kai kan wukar nan cikin sauri na ja wukar na yanki gefen hannunshi da ita da sauri ya sake ni yana faɗin. "Kika yanke ni?" "Idan ka iso gare ni sai na kashe ka!" Na fada ina kauda kaina daga gare shi, hijab Dina yana can ƙasa. "Ummu ki yarda mu yi wanann al'amarin cikin sauki hada jikina da ke yasa ina ta xubar da ruwan sha'awar na gaya miki ba zan cutar dake ba, zan rage miki aikin da wancan lusarin ya kasa ne shine kika yanke ni!" Ya nufo ni da sauri kara rike wukar nayi ina nuna mishi, abinka da namiji yana zaune ya buge wukar da karfi wanda yayi sanadin faduwata, jan towel din yayi da karfi ya zame kasa. "ashe ba gizo nake gani ba,.sune a tsaye waw!" Ya kai hannu zai tab'a min na daddage na gwara mishi goshina a fuskarshi abin da yayi sanadin faduwarshi da gudu na shiga ban daki, towel din ya fadi can na rufe kofar da key. Na zube a ban dakin ina wani irin kuka, shi kuwa sai buga kofar ban dakin yake amma naki budewa. Haushi yau ya samu dama amma Ummu ta hana shi yasa shi dukar kofar toilet din da kafarshi, sannan ya fita yana faɗin. "Duk ranar da na kama ki sai na cika kudirina a kanki!" Ban tab'a shiga tashin hankali a rayuwata irin wannan lokacin ba, na ji garin Abuja ya min zafi, naji bakiɗaya kome ya min zafi na tsani kaina na tsani Aliyu da ya kawo ni. Nayi kuka kamar raina zai bar gangan jikina. Sai da nayi awa uku a ban daki kafin na fito na gyara banyi tare da hada kayana bakiɗaya, karfe uku saura ne, na fito parlour ya b'aci da jini haka na goge tare da saka turaren wuta, sannan na sauke salolin kaina, na kwanta a dakin saboda tashin hankali ko ruwa ban kai bakina ba wunin ranar, koda Tafida ya dawo bai bi kaina ba, tunda ya leka kitchen ya ga babu alamar abinci ya yi wanka ya fita a gidan bai kara dawowa ba sai goman dare. Washi gari tun karfe biyar na asuba na bar gidan, yana can ko ya tashi ko bai tashi ba, abin da na sani na bar gidanshi kome zai faru sai dai ya faru, karfe shida muka bar Abuja, na kashe wayata.
Tun lokacin ban kuma samun nutsuwa ba, sai karfe sha biyu da muka iso Bauchi, daga nan muka nufi fataskun, wurin karfe hudu muka yi sallah azahar da la'asar, sannan muka dauki hanyar Maiduguri, wanda shima koda muka isa bakin get an rufe, domin karfe bakwai muka isa, anan muka kwana.
**
Abuja
Tunda yayi sallah asuba sama-sama yake jin motsi daga baya barci yayi gaba da shi, bai farka ba sai karfe takwas, ya duba agogo wayar shi, da sauri ya nufi ban daki yayi wanka sannan ya fito ya shirya tsaf, haka kawai yake jin gidan kamar babu kowa don haka ya fito parlour ya daidai ne babu abin ya sauya, bai nemi abin karyawa ba ya fita, a office ya tura aka kawo mishi abin karyawa duk da haka ya ci ne amma dan sabo da yayi da abincin ta yasa shi fahimtar ita gwana ce a wurin girki. Yau yayi alƙawarin sai ya ci abincin dare. Lokacin da ya dawo gida bai ga alamar tayi abinci ba anan ne ya fahimci ba ta gidan ne fa, ya kira Tinah ya tambaye ta Ummu tana tare da ita ne? Ta ce a'a bata zo ba, zufa ne ya karyo mishi, ya kara kiran Tinah ko wasa take mishi nan ta rantse idan bai yarda ba yazo gidansu. Sannan itama ta gwada kiran Ummu wayar a kashe. Ta gaya mishi Deen ya kira ya gaya mishi Ummu ta b'ata. "Wacce irin magana ce haka? Ummu ta b'ata kamar wata yar kaza?"
"Wallahi na gaya maka da gaske Ummu bata nan!" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Ka tambayi Tinah?" "Eh basu tare!" "In sha Allah tana hanyar gida, domin nasan wacce irin mutum ce ba zata tsaya a wani wurin ba gida zata tawo, sannan nima zan tafi gate na jira zuwanta." "Don Allah kada ka gayawa Alhajinmu idan ka same ta ka gaya min " "Ok!" Haka suka yi sallama amma hankalinsa yayi dubu ta tashi, domin wannan shine karon farko da yaji tashin hankali da rikicewa, ba tare da ya fahimci haka ba, ya kira Deen yana tambayar shi ko an dace. Amma shiru Deen kuwa haka yayi ta bin tasha yana niman Ummu , daga karshe ya samu labarin akwai wasu motoccin da aka tare ba zasu shigo ba sai gobe, tafiya yayi can ya zauna, har tsakiyar dare Tafida bai kyale shi ba, karshe sai da suka yi fada ya cewa Tafida. "Dan iska kasan ka damu da ita kayi ta shuka mata rashin mutunci, banza dan iska!" "Ni fa bana gida na barta da Mahmoud ne zai bar gari bayan nan shima na nime shi ban same shi ba wallahi ban mata kome ba tow dama me nake mata idan ba sharri zaka min ba." Kusan kwana zaune suka yi shi da Deen, asuban fari aka bude kofar, Deen ya shiga bin motoccin da suke parke.
Ina sallah naji ana tambayar wacce Ummu Hadiyya, sai buga jikina nayi alamar nice, wata matar kusa dani ta ce musu. "Kamar gata tana sallah tayi alama!" "Mai gida gata nan an same ta." Sai da nayi sallama gabana ya fadi ba dai Tafida ba ne, a hankali na d'ago kaina ina kallon Deen a cikin dan duhu-duhu. "Ummu Hadiyya!" "Na'am!" Na amsa ina mikewa, "Malam sauke min kayanta zamu wuce!" Haka suka taso ni a gaba na nuna musu kayana, Deen ya dauka ya saka min a motar shi, baya ya bude min na shiga na zauna. Sai lokacin kuka yazo min. "Ina zan kai ki?" "Wurin Ammah!" Kallona yayi ta glass din motar, sannan ya cigaba da tuki. Gidansu ya kai ni, wurin Mamanshi. Tunda na shiga dakinta nake kuka, "ya isa haka mana Ummu kanki zai yi ciwo!" "Kyaleta tayi idan tayi zata ji sauki, zata kuma manta da kome, idan bta yi ba zai zame mata ciwo a ranta har zuwa mutuwarta barta tayi kukanta shi kuka ba ragwanta ba ne, jarumtace da juriya ke kawo shi duk wanda zai yi kuka zai manta abun da aka mishi, barta ta rage nauyin da yake ranta haka kadai zai bata damar fuskantar wacece ita wacce duniyar take raye!" Nayi kukan da ko a gaban Mama ba zan iya shi ba,haka yasa Deen ya zuba min idanun yana me tambayata. "Tafida ne ko Mahmoud?" Da sauri na kalle shi ina tsannanta kukana tare da girgiza kai. "Gaya min waye ne a cikinsu?" Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Na barsu da Allah!" Jin haka ya kira sunana kamar zai yi kuka. "Kika ce kin bar wa Allah?" Gyada kai nayi, bayan na zauna tare da dunkulewa wuri guda, na cusa kaina a tsakanin cinyoyina. "Ummu me kike so?" "Kace tafida ya sake ni, kafin wata rana na wayi gari a wulakance." "In sha Allah ba zaki wulakanta ba." Inji Ammah, bayan Deen babu wanda yasan ina Maiduguri, kai washi gari sai ga Tafida, a wannan abin na hango sanyi a tare da shi, nan yayi ta bawa Ammah hakuri yana fada mata bai san me ya faru ba, don Allah ta rufa mishi asiri kada Abbanshi yasan yazo. Abu daya Ammah tace mishi. "Zan yi hakuri amma ka sani dole zan na turo wani zuwa Abuja ya ga irin zaman da kuke ko na gaya Alhaji Muhammad Jadda!" A kade ya ce mata. "Ban gane ba Ammah?" "Nufina tunda kana tara yan iska a gidanka zan gayawa Alhaji Muhammad Jadda, cewa ka mai da gidanka hotel wurin saukar yan iska, sannan ya je ya ga irin zaman tozarci da kake da Ummu Hadiyya!" Kamar zai kwanta a kasa ya ce. "Wallahi daga yau zan zauna lafiya da Ummu lafiya!" "Ban yarda ba, nasan waye kai da taurin kai!" "Na rantse da Allah." Ba wasa Ammah ta fara wanke shi kamar yadda Deen ya gaya mata, a ranar sai da yaji kunya ya kama shi. Haka ta ce mishi ya tafi ya bata wuri ta ma fasa na koma wurinshi, kawai zata kai ni wurin Abbanshi ne. Kamar yayi hauka domin san Abbanshi ya mishi alkawarin. Duk ranar da Ummu tazo da kukan ya zalince ta har abada bashi ba kara aure ko na wacce mace ce, balle Sa'adiyya shi yasa yake shakkar Abbansu yaji labarin nan, sannan yasan kome na shi zai koma baya ne.
**
Tun daga Maiduguri har jibiya na garin Katsina suka isa. Can wani kauyen jibiyar suka shiga ciki. Shafa kasar yayi da yake katon tire yana shafa farin gemunsa. "Yaron nan tun fil azal babu aikinku da yake kama shi, har abada ba zai kama shi ba domin Uwarshi tana tsaye akanshi, yana biye muku ne saboda kece kika tsaya mishi da abinci lokacin da yake jin yunwa. Sannan na kara gaya miki kaf duniya babu wanda ya isa mishi wani abu domin Uwarshi tana sauke numfashinta ne da bugun zuciyarta. Hindu ko?" Ya kuma tambayarta sannan ya gyara zama yana kallon Sa'adiyya. "Bari naga muku gaskiya, ƙaddaran yarki yana kusa da shine, amma shi ƙaddaranshi yarinyar ce, kuma kin san me? Shi din babban mutum ne nan gaban, zata iya aurenshi taci arzikin shi amma... lokaci ne zai gaya muku haka bokaye malamai irina, ba zasu iya muku kome ba domin Tafida kainuwa ne dashen Allah, zaki iya zama da shi domin ki ci arzikin shi amma ba wai yadda kike tsammani, idan zaki yi nasara sai dai akan Yan uwan shi da yan gidan amma akan Tafida. " wannan abin ya d'aga mata hankali. Don haka ta sauke ajiyar zuciya, tana faɗin. "Tow yanzu zamu tafi daga baya mu dawo." "Zaki tafi Nijar ne, a can za a hadaki da wani boka wanda kafin ya miki aiki sai ya kwanta da yarki," dariya yayi ya fada mata siffar matar da ta gaya mata bokan da kome sannan ya shafa kan tirenshi yana faɗin. "Kaf duniya babu wanda zai miki aiki ya kama Tafida na rantse da Allah, sannan idan kika sake yarki ta kwanta da shi, daga ranar ko auren Tafida sai ya mata wahala, gara ta samu kan yan uwanshi su saka shi a gaba yadda zai kula da lamarinta amma kika bari wani ya kwanta da ita kusa da Tafida ma ba zata samu tsayawa ba."
Kai karewa sai da ya gaya mata kome hatta fadar Ummu da Tafida, ya ce mata yanzu haka Tafida yana Maiduguri, sannan Ummu tana gidan abokin Tafida idan karya ne ta kira Tafida zai gaya mata. Ai kuwa kamar yankar wuka.haka ta kira shi ta gaya mata yana Maiduguri sun samu matsala ne da Ummu, bayan ta mishi fatan Allah ya daidaita su. Ta kashe wayar tana kallon malamin ya gyara zama.ya ce mata."abin da yasa Tafida ya biyo ta saboda Ubanshi yace masa matukar Ummu ta kawo karan shi har abada ba zai auri yarki ba, ƙaddaran yarki tana kusa shi ban san me zai faru ba amma ki koma lokaci na zuba da zai auri yarki kada ki sake ki rasa damarki na moran arzikin da kika tsaya ya ginu ta sanadin ki....
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
17
Ammah tayiwa Tafida wulakncin da bai tab'a zata ba, domin ta kuma rantse matuƙar bai gyara ba Abba zai ji, kwananmu biyar muka juya Abuja, Ammah tai min nasiha tare da nuna min na rungumi Aurena nayi hakuri kada na dogara da shi, Ammah bata san tuni na wuce wannan matakin ba, sannan ta ce tsakaninsu da su Deen su hadu a wurin aiki, wai a haka ban gaya mata kome ba, sannan ta ce mana tana nan zuwa kada muyi tsammanin zata gaya mana ranar zuwa zamu ganta ne kamar diran yesu, sannan ko kallon banza ya min nayi mata magana zata tambaye shi Hujja, haka muka isa Abuja lafiya lau. Sai dai muna isa madadin ya gyara halinsa sai ya karo rashin mutunci sama da baya ma, iskanci da tozarci sai naji me yasa ma na tafi Maiduguri, kullum ina cikin kuka da tashin hankali, domin na fahimci Tafida indai ba Abba ba ne zai zauna a gidanmu babu dalilin da zai saka ya kyale ni. Yadda yake zabura idan yana fada sai na koma da baya domin kamar zai buge ni haka yake ji, dalilin da yasa na kama kaina na kara nutsuwa, dayawan mutane suna faɗin idan aure yana sauya mutum wani ikon Allah sai gashi gidan na cire class da nake aiki a wurin koyar da girki na yi wani irin sanyi wanda ko magana kai yi min zan iya samun kaina da jin tsoronka. Dama can halina ne rashin son hayaniya da kwaranniyya, haka ya ƙara samar min da wata irin nutsuwa, wasa wasa kamfanin da suka dauke ni aiki suka tab'a gayyatatta nayi zuwa Lagos, akan wani festival na girke-girken Africa. Yana kwance a parlour na shigo gidan a gajiye ya amsa Sallama da nayi bai amsa ba, ni dai ban sani ba na ajiye jakata na shiga kitchen, a gurguje nayi na gama taliya da miya amma yau nayi mamakin yadda na same shi a gidan. haka na shiga dakina nayi wanka kakarinsa na ji, na fito yana ta amai yana rike cikinsa. "Subhanalillahi Ya Tafida naka da lafiya ne?" Gyada kai yayi yana amai, haka na dauko abin mofin da parka na kwashe sannan na gyara mishi inda ya bata. Hadiye yawu nayi tare da zazzare idanu. "Ko zaka tashi ka cire kayanka, na wanke maka su ka b'ata su." "Ummu ba zan iya tashi ba!" Ware idanu nayi cikin tashin hankali. "Ba zaka.." matsawa nayi na dafe goshinsa rau yana kuna da zazzaɓi. "Bari na cire maka!" Na fara ƙoƙarin cire mishi amma na kasa, abun da na sani tafida dogo ne me kauri da fadi, sannan duk wannan kokarin da nake kallona kawai yake ganin yadda nake kokarin cire mishi rigar na kasa sai shawagi nake a gabanshi, ya sa shi cewa. "Tsaya na gwada" a hankali ya cire rigar sau daya na kalli kirjinsa wanda yake cire da wasu irin gargasa, sai ji nayi jikina yana rawa, na tattara rigar na bar wurin dakina na wuce na zuba a banɗakin na shiga wankewa. Bayan na gama na fito na samu yana rawan sanyi. "Muje na taimaka maka " haka na isa gabanshi Dakyar ya mike muka tafi dakinshi amma ji nake kamar na dauke shi yadda ya sake min ragamar jikinshi. Haka ya zube a saman gadonshi, na gyara mishi kwanciya. "Me zaka ci?" Na tambaye shi, "Babu!" "A'a ba zaka zauna da ciwo haka ba!" A wannan lokacin na tsaya sosai akan shi domin nice dai a kusa da shi. Sai da ya kwashe kwana shida, har Tinah tazo tana tambayata ya maganar tafiya wata sati kuma an ji ni shiru. "Kin ga Ya Tafida bai da lafiya, ba dad'i na tafi na barshi idan lokacin tafiyar yayi bai warke ba su yi hakuri ciwo na gaba da kome, kuma ban gaya mishi ba kin ga kenan dole na hakura." "Amma" saurin dakatar da ita nayi ta hanyar cewa. "Ki bar maganar bani da ra'ayi a tafiyar ne shi yasa na tsaya jinyarshi." Duk tozarci da yake min ta sani amma tayi mamakin yadda na hakura da nawa damar da na samu saboda jinyarshi. "Matan aure kenan kuna da kirki da sadaukar da kome domin mazajenku" murmushi nayi na ina faɗin. "Aure ba abin wasa ba ne, idan kayi wasa da aure Allah ba zai Barka ba, kada ka cutar da aure domin shi ne mafi girman kuskuren da ake aikatawa, sannan shi auren Ibada ce bakiɗayansa." Ashe duk hiranmu yana ji, domin ya fita wajen wurin Motarshi, ta window kitchen yake jin mu. "Amma Ummu kina son mijinki ko?" Kallonta nayi a rayuwata bana jin akwai tambayar da take matukar bani