Showing 129001 words to 132000 words out of 241571 words

Chapter 44 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14719

Hadiye yawu nayi kafin na juya naga iya Mufidah ce a gefena. "Ina!" "Yana bayan Hajiya tazo tana kitchen!" Ajiyar zuciya na sauke, kafin na lumshe idanu. "Don Allah ka mai da ni gida!" "Na ji amma sai kin warke." "Amma na warke ai!" "Da saura!" Sai da ruwan ya kare ya cire min da kanshi sannan ya haɗa min ruwa nayi wanka, kafin na fito ya cire min kayan da zan saka, sannan na fito na shirya. "Ya jikin naki?" "Da sauki kan!" Haka na koma na kwanta, ya gayawa Sagir shi ya gaya mishi yadda xan mai da min wani ruwan. Kwana biyu ina kwance Hajiya ke min kome domin ta dawo kusa da ni, Yaran ma a wurinta suke. Haka yasa nima kome yazo min da sauri. Ana jibi sallah na matsa ya kai ni Biu, haka muka tafi Hajiya ta koma gida, an karbe da farin ciki. Haka na kwanta a kafadar Babana, yayi ta tambayata ko akwai wani abu ne? Na ce mishi babu. A daren ranar muka dawo gida. Washi gari Jajiberan sallah, muka tashi aikin sallah, wuni nayi ina aiki domin ba wani abu ba ne a wurina don ma yana ta min faɗa, na share shi kafin karfe biyu na rana na gama cin-cin da cake da nayi, sai soyayya da dambun nama da nayi kadan. Sai dai kuma a duk lokacin da na tuna da sakon Mahmoud ji nake kamar zan mutu, domin wani irin bugawa zuciyata take sau biyu ina kona cin-cin sai da Tafida yazo mun faɗa.
Dakinshi na shiga nayi alola, sannan na duba abin da Hajiya ta bamu, na zo na sha wunin ranar shi nayi ta sha ina karawa da abubuwan da zai gyara min jiki. Tunda ya ga ina sallah, sai ya zama kamar ɗan Maraya yayi ta narke min kamar man shanu. Murmushi nake mishi domin ya cancanci nayi mishi murmushi. A hankali muka gama kome, sannan na wuce bangarena nayi wanka ina zaune wayata tana saman gado naji tayi ƙara. Tashi nayi na dauki wayar Tinah ce a hankali na dauka ina faɗin. "Tuba nake!" "Yar dad'i miji kin manta abokiyar gwagwarmaya!" "Kiyi hakuri Tinah ina cikin damuwa ne!" "Jikina ya bani!" Zama nayi a bakin gadon na rasa yadda xan mata bayani. Sai na mata karya tare da gaya mata abin da ya faru Mama ta tafi Umara na biyo tafida muna cin amanarta. Dariya yayi tana cewa, "normal ne ai!" Jin ta kawai nayi amma ba shine asalin abin da nake son gaya mata ba, wani irin tsoro yasa na yi shiru. Sallama muka yi sannan na kashe wayar, shiryawa nayi sosai sannan na wuce wurinsa da Yaran da suke rarrafe. Zama nayi ina kallonshi.. ajiyar zuciya na sauke ina kallon wani Turkiyya drama ada aka saka a MBC 4, yadda yaga na zubawa tv idanun yayi dariya. "Me kika fahimta!" "Matar ta gano mijinta da Aminiyarta suna cin amanarta, haka yasa ta dauki matakin tura kawar ta window!" "Hmm! Ni idan na kama mata ta, da abokina ba zan kashe su ba amma xan tabbatar da na basu sakamakon da sune zasu bukaci mutuwa da kansu. Sannan ki lura ita kawar har hoton kawar ta samu a wayar mijinta da kuma ita kawar, haka yasa ta tabbatar da mijinta yana cin amanarta. Mace ma kenan ta dauki wannan kasadar ina kuma namiji ai ina ga sai garin nan yayi min kad'an da shi kwarton domin wallahi sai na yanke mishi azzakarinsa! Ita kuma na rabu da ita na barta da Allah da haduwarta da shi." Hawaye ne ya zubo min yau naji na kara tsanar Mahmoud, "idan kuma aka ce ni na aikata?" Kallona yayi yana hararata. "Ba zan yarda ba domin babu alamar kin aikata wani abu don ni ne mutum na farko da na fara sanin darajarki. Ke nemi wata rigimar ban da wannan." Girgixa kai yayi yana faɗin. "Ban da jaraba irin taki har da kuka wai meye matsalar da batun cin amana haka kawai kina kukan banza yau zaki gaya min dalilinki nayi min bori babu gaira babu dalili!" Tura baki nayi na wuce kitchen na fara fito da kayan abincin bude baki, ina gamawa ana kiran sallah , addu'a yayi sannan ya shafa na taya shi, bude baki yayi ina kallonshi labarin Fim din nan ya tsaya min a rai, haka yasa har muka gama ban kara nutsuwa. Wayata ma bakiɗaya na kashe ta. A daren dakyar Tafida ya kyale ni, na kasa barci tunda muka fito wanka. Parlour na dawo na zauna, tare da kunna wayata domin yau kamar jira yake mu fito wanka ya kama barci. Yayi gaba da shi, shine na samu na fito, shima yana bukatar hutu. Wayata ce ta kawo, na tsura mata idanu. Sakonnin Mahmoud na fara gani hawaye ne ya cika min idanun na dafe goshina. *Zuwa yanzu ya dace ki bar Tafida! Domin idan na sake wannan fefen videon kujeransa da mutuncinsa duk zasu tafi! Waye zai damu da Fyade ne? Hmm! Kiyi tunani Ummu ki kashe aurenki kawai ina jiranki tunda ba zaki iya shagali da aurenki ba!* A hankali na wuce kitchen na rufe kofar na fashe da wani irin kuka, ina goge sakon wayar, layin na cire na karya shi sannan na tattaune shi na sha ruwa akai, wayar kuwa bani da wani mafita da ya wuce na wurgata a ruwa. Na zauna na fashe da kuka ina jin kamar xan kashe kaina don bakinciki.
***
"Deen*
Yana kwance tunda Matarshi ta dawo ya samu nutsuwa, wayarshi ce take kara a hankali ya janyota. "Hello!" "Yallabai akwai wani sako na tura maka ta email! Ya da kyau ka gani don Allah!" "Ok!" Ya fada yana kashe wayar. Ya cigaba da barcinsa.


Da asuba da ya tashi sahur ya ga tuna, da sauri ya kunna wayar, sakon da aka turo mishi ya gani, a hankali ya fara dubawa. Jikinshi rawa ya dauka, yayi maza ya kira Number. "Kwaro me yasa baka gaya min ba?" "Yallabai ina cikin mutane ne, ba zai yiwu na gaya maka ba, yallabai His Excellency zaka fara covering ba sauran, nasan is not easy zakulo irin wannan abin, amma akwai matsala!" "Mahmoud!" Ya kira sunanshi. "Yes Sir nima abin nayi mamaki kenan, har sai yaushe zaka bayyana shi." "Bana son Ummu ta shiga tashin hankali ne, amma na jima da sanin yana bibiyarta na gode zan cigaba da tuntubarka." Ya kashe wayar, shiru yayi yana mamakin abokinsu yadda yake abin da ransa yaƙe so.


Tashi yayi ya leka masu jego, bayan ya gansu yayi shiru yana kallonsu, Uwar da jaririnta. Murmushi yayi sannan ya fito waje, haka ya koma daki ya kwanta ya kira Number dazun. "Duk rintsi kada ka bayyana kanka, sai ka ji wani abu ya faru mara dadi kayi ƙoƙarin haduwa da Malam Zailani! Ka fahimci." "In sha Allah!" "Kai fa yallabai!" "Ba kome! Zan samu Mahmoud kada kayi gaggawan fitowa nasan Mahmoud!"
***
*Tafida*
A hankali yake shirinsa, kamar ruwa ya cinye shi, yau ya tashi da wani irin yana duk da kasancewar gobe sallah, kunna wayarshi yayi a yana jin wani irin sanyi har cikin cikinsa. Kallona yayi da nake kwance yau shi ya shirya duk da bayan sallah asuba Deen ya kira shi akan zai zo shi da Mahmoud! Haka yasa ya shirya a hankali ya juya yana kallon yadda nake kwance. "Yau ba zaki tashi ba ne?" A hankali na bude idanuna na kalle shi. "Kaina na bala'in ciwo!" "Ko na kira Dr Sagir ne?" "A'a ba sai ka kira shi ba, zan kwanta." Na fada ina rufe idanuna. "Deen ya kira ni tun dazun zasu zo da Mahmoud wai akwai maganar da za ayi har dake!" Ban san lokacin da na tashi zaune ba ina dafe kirjina. "Ni?" "Eh!" "Innalillahi wainnalihir rajou! Tow me ya faru?" Yadda na rikice ya da shi matsowa ya zauna a gefena. "Ke ba wani abu aka ce min yi ba, kai Allah ya shirya ki ." Kwantar da kai nayi a pillow na share shi naki magana, yanayin da na shiga Allah kaɗai yasa ni tun da nayi sahur nake gayawa Allah abin da Mahmoud ya min Allah ya saka min. Wayar Tafida ne yayi kara, ya ɗauka yana sakawa a kunne. "Innalillahi wainnalihir rajou! Ke dauko Yaran nan da kayansu, Deen!" Ya fada da sauri, tashi nayi zan mike wani irin duhu na gani a idanuna a hankali na ji nima na zube a wurin. Ban kara sanin me ya faru ba, tashin hankalin da Tafida ya shiga babu iyaka, Ummu ya kai Mota ya dawo ya dauki Yaran, ya kai su sannan ya kira Sharif ya gaya mishi ya dauko Hajiya ya kawo ta Asibiti. Da yake Sharif yana wurin rabon sadaka, haka yasa bai zo da wuri ba har dan wani lokaci, Hajiya tayi matukar razana musamman ganin halin da Tafida ya shiga bakiɗaya likitocin da suke kan Deen sun fi ashirin, an yi juyin duniya ya fita amma yace babu inda zai je, idanunshi yana kan Deen, hawaye na zuba mishi. Idan ya rasa Deen, har abada ba zai samu me cike mishi gurbin Deen ba, yana tsaye har aka fito da Deen wanda kanshi da da jikinshi aka yi masa sara kamar ba dan adam ba, an mishi dinki kamar wani kwarya. Fitowa yayi ya wuce waje, matar Deen da Ammah ya gani suna ta kuka, gidan Malam Zailani ya nufa. Duk da yau shi da kanshi yake tuki ga jami'an tsaro na binshi. A zauren karatu ya same shi zubewa yayi akan gwiwarshi. "Ka gaya min me yasa Deen?" "Me yasa Deen?" Malam ya tambaye shi, sai yayi murmushi ya ce mishi."wallahi ban tab'a istahara, na ji babban al'amari akan wasu ba sai akan ku ukun nan!" Murmushi yayi yana ƙara faɗin. "Istahara ba a ganin kome, amma daga ranar da na ganka da shi, na fahimci ba iya aboki yake maka ba, akwai Babban al'amari a tare da shi. Aliyu yanzu ya dace ka nutsu wanda yake tayaka yaki yana kwance ko? Duk wanda yayi wannan abin ba kai yake bibiya ba, abu me daraja yake bi a tare da kai. Mulkinka baya gaban wanda yayi haka!" "Taya ka sani?" "Saboda abin ya faru ne a akan idanun mutane dayawa, kenan ka ga babu bukatar sai na sani tunda ko ban je ba za a gaya min. " "Me ya dace nayi?" "Da farko ka dauki aikin da wasa ne? Kai banda Mahaifiyarka tana hana idanunta barci ai nimanka da ake sai ka kusan barin duniya zasu kyaleka. "
Rufe fuskarsa yayi yana faɗin, "duk wnada yayiwa Deen haka sai na tabbatar da hukuma sun rataye shi." "Allah zaka roka ya tona asirinsa ba hukuma ba domin za a shekara ana nimansa ba a ganshi ba, ka ajiye a ranka yanzu ake lamarin kuma ba za a daina ba sai ko idan zaku mutu kai da Deen domin kuwa ka saka idanun akanshi don lamarin bai kare ba."


Tashi yayi ya juya zai fita, "Ka godewa Allah, an zubar da jini yau, da kuma addu'a da ake kai, daga yau har ranar da zaka sauka akan kujeran ka tabbatar an yi sadaka ana rabawa mutane idan ta kama har da abinci ka bada ayi, Kasan inda kake kuwa? Wasu da jinin mutane suke bukatar zuwa wurin basu samu ba kai kuwa Allah ya d'aga darajarka, kana wasa." Fita yayi ya kira Sharif. "Zan tura maka kudi a sayi kayan abinci a raba sadaka!" Ya fada yana shiga motarshi, kifa kai yayi ya fashe da wani irin kuka. Domin bai tab'a ɗauka lamarin haka yake ba, Ummu da Deen suka cikin wani hali, hawaye ne yake zuba mishi, yau daya yaji ashe yana da rauni sosai haka. Wayarshi ya dauka ya kira Matori! "Matori a saka idanun akan Deen don Allah!" "An gama" duk sai ya kasa aikin, a hankali aka buga kofar ya d'ago kai Malam Zailani ya gani yana murmushi, sauke glass din motar yayi. "ungo wannan sannan ka fita a wurin tukin su ja ka." Amsa yayi, murmushi Malam yayi yana kara faɗin. "ka fita zasu kai ka, sannan ka godewa Allah da lamarin zo a haka."
Fita yayi daga cikin security din ya shiga gabatar motar, sannan ya ja suka bar kofar gidan.
*Malam Zailani*
"In sha Allah Deen zaka tashi, nufinka na alkhairi da alkhairi da yake zuciyarka zaka tashi in sha Allah,...
```All spicess
Jollof mix
BBQ mix
Thyme plus
Garam masala
Curry powder```






```Special zobo
Special yaji
Spice kuli kuli
Miyar kuka
Miyar kubewa
Special daddawa```




```Garin masa/sinasir
Garin alale da kosai
Garin kunun tsamiya
Garin kunun aya```
*Shin ko kun san kayan kamshin da kayan zobo tare da duk wani dangin kayan abincin gargajiya da Ummu take amfani yana samuwa ne ta wurin Shaharariyar me kayan kamshi na AIDA spicess! Ina mata yan yayi ina masu abinci na online kayanku ya tsinke a gindin kaba, ga Hajiya Aida special spicess tazo mana da kayan girki na gargajiya da na zama kai Jama'a wata miyar sai a makota! Na gwada sauran ku gwada ina jiranku! Za a iya samun Aida spices ta wanann number:+234 806 968 1068 Whatsp siyan na gari mai da kudi gida! Hajiya ki zama yar gayu me sauki ne amma girkin yan gayu dai da Aida spicess*🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


*Ummu*
Karfe shida na yamma na farka, Uwani na gani a dakin tana ta shirya abin bude baki. "Aunty Baby kin farka?" Lumshe idanu nayi na bude, "yanzu Babansu Mufidah ya shigo." Kokarin tashi nayi ta ajiye abin hannunta, ta d'aga ni "na gode!" Karin ruwan dake hannun nawa na kalla kafin na kalli bakin kofar da ake kokarin shigowa. Hijab na janyo domin na saka Uwani ta taimaka min, shigowa yayi yaga muna saka hijab. "Mahmoud zai gaishe ki!" Kura masa ido nayi kafin na sunkuyar da kai, umarni ya basu suka shigo. Ban sake na d'ago kai ba, "Man ko dai Maman twins ta sake karban wasu twins ne?" Ban kalli fuskar Tafida amma yadda naji ya amsa ciki-ciki na fahimci maganar bata mishi ba, haka yasa na kara sunkuyar da kaina ƙasa. "Tow Allah ya baku lafiya!" "Amin Ya Allah!" Uwani ta fada tana mika min ruwan dumi, shima Tafida fita yayi. Ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar na tsira daga Mahmoud.


Ana bude baki Doctor Sagir ya shigo yana kallona, "Kashe kanki zaki yi ko? Wani irin damuwa ne da har jininki yana shirin tab'a zuciya. Idanuna ya cika da kwalla girgixa kai nayi, ina me hadiye yawun bakina, "kawai ciwon kai ne fa!" "Wai me ke damunki?" "Ba kome!" "Akwai mana Ummu waye zai ganki yace babu wani abu." Haka ya gama duba ni, sannan ya fita abinci aka kawo mana daga gidan Abba, a hankali na samu nayi sallah, sannan kwanta duk sai naji babu dad'i, washi gari aka tashi da bikin sallah, sai bayan sallah idi Abba da Baba suka zo, dama Deen mahaifinsu ya jima da rasuwa, Ammah ke faman fadi tashi. Yadda nayi azabar lalacewa yasa Abba da Babana suka yi ta min faɗa min ko ina da matsala ne nace musu babu kome, haka yasa Abba yace a kyale ni. Binsu nayi na ga Deen, sai da na kasa tsayuwa na fashe da kuka, haka kawai nake jin kamar akwai wani abu a wannan yanayin da muke ciki. Ga Matarshi da danyen jego, jarumar uwa irin Ammah tana tsaye akanshi idan ka cire jiya da tayi ta share kwalla.


Komawa dakina nayi, na kwanta ina wani irin kuka, Deen ya bani tausayi. Haka lamarin ya kasance, a daren anan naji labarin za a tura shi abuja, domin zuciyar Tafida ya kasa nutsuwa da asibitin, a can asibitin da za akai shi akwai tsaro da kulawa, haka kuwa aka yi da shi a tafiyar suka wuce Abuja.
*Mahmoud*
Kifawa mutumin gabanshi mari yayi, kamar zai kashe lalata mishi fuska. Sai hakuri yake bashi kafin ya kyale shi. "Me yasa ka sare shi na tare da ka kashe shi ba? Kasan waye Tafida kuwa? Kasan waye shi kuwa? Yaron da kaf arewa babu mara kunyar da ya tsaya a ƙwaryan majalisa yayiwa yan majalisu rashin mutunci! Bari na gaya maka ka tabbatar da ka goge duk wani shaidar da za a gano ka, idan hali ka hada kayan Yaranka ku bar Maiduguri idan ka kara jin motsinka sai na kashe ka!" "Kayi hakuri! Amma akwai da yasan zaku hadu da Deen! Mun bibiye wayarshi bai dauka ba, asalima kiran baya shiga." "Ina wayar yaƙe?" Mika mishi yayi tare da kallon wayar duba wayar yayi ya ga babu duk wani abu me muhimmanci layin daya ne da aka rubuta Begger! Jinjina kai Mahmoud yayi yana faɗin. "an duba waye shi?" "Mun bibiye layin baya shiga, sannan da nace Cuna ya duba mana kome akan layin wallahi babu kome sai dai a wayar naji yana faɗin. Haka" ya kunna wayar sai ga Muryan Deen faɗin. "ka tabbatar da yi nisa da Maiduguri, sannan kada ka kara amfani da wayarka saboda nasan zasu bibiye IP codenka, idan ka ji labarin bana raye kada ka bayyana kanka, ka nutsu zata ji da kome. Ka bata kome tare da wasikar da na baka zasu nime Tafida ka kula da rayuwarka ka yi tunani idan kanwarka ce Ummu Hadiyya waye zai tsaya maka, sannan ka ji a ranka idan Aliyu ne Abokinka me zaka yi zaka kyale rayuwarshi ta lalace ne saboda kawai Mahmoud ya maka barazana, ka tabbatar ka yi record nima ina yi." Cikin fusata ya buga wayar a kasa, yana huci yana faɗin. "Ku nimo min Yaron a duk inda yake sai na kashe shi!" "Ai babu lamar shi a garin nan, domin mun yi kome don yaron ya fada tarkon mu amma babu alamarshi, idan na fahimci wani abu Deen tarko ya maka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login