Showing 135001 words to 138000 words out of 241571 words

Chapter 46 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14733

da bani Ummu a karo na biyu, na gode sosai na gode zan baki mamaki in sha Allah." Ya saka kai ya fita, "Idan kika kuskura wani abu ya samu cikinki da gayya Allah yana ganinki!" A hankali na fita daga cikin gidan. Ban san lokacin da kuka ya zo min ba, bai saurare ni ba ya bar gidan a mota na same shi, ya gyara kwanciyar Mufeedah ya amshi Mufid. "Na san tausayi yasa kika fada, zan kaisu gidan Hajiyata Doctor Falmata zata duba su." Kifa kaina nayi ina kuka har muka isa gidan Hajiya, ina jin shi yana waya da ita Doctor Falmata. A parlourn Hajiya na zube ina shashekar kuka. "Innalillahi wainnalihir rajou! Tafida mai ka mata kuma?" "Hajiya ban mata ba, Mama ce ta koro mu!" "Da tayi me?" "Da ta.." yadda na d'ago kai na kafe shi da idanun yasa shi cewa. "Kai Hajiya maganar nan da nauyi yake, amma za a yayesu Mufidah!" "Alhamdulillahi! Ubangiji ya raya su tafarkin addinin Muslunci, ita kuma ya sauke ta lafiya. Ya bata lafiyar shayarwa." Daukar yaran tayi tana sumbatar kansu. Haka nayi ta kuka tana rarrsshina tare da min nasiha, sannan ta ce min. "Gobe za a kawo su Nana kin ji, Asma'u zata zo ta zauna a wurinki! Ta rage miki aiki!" "Yar shekara bakwai ce zata taya ta aiki? Hmm idan zaku koma kawai wata sati ki dawo gidan, domin ummu ba zata zauna a government house ba!"
"Allah ya nufa!" "Amin Hajiya! Amma zan tafi da Ummu Yaran yanzu za a zo a duba su!" Kaina ne ya fara ciwo na kwanta a kujerar, Hajiya ta nufi kitchen tana faɗin. "da kin shiga daki kuka kwanta ki huta!" Girgixa kai nayi, tana shiga ya dauke ni. "Ka sauke ni!" "Idan na ki fa!" Ya wuce da ni dakin Hajiya ya kwantar da ni. "Ya kike son nayi? So kike a zubar da cikin nan kenan?" Da sauri na bude idanun ina gyad'a kai. Girgixa min kai yayi yana faɗin. "Ban san yadda zan miki bayani ba, amma ina cikin farin ciki kamar na goyaki nayi ta yawo dake a garin nan! Kina dauke da cikina a karo na biyu! Lallai ni dan gata ne Allah yasa Deen zaki haifa min!" Sai a lokacin na ware idanuna akanshi, "Ni fa kawai a cire shi yaran nan abin a tausaya musu ne, basu kai shekara ba balle mu ce sun sha na shekara daya, wata bakwai fa gaskiya sai dai a cire cikin nan ba zan iya tashi biyu ba!!" Duk yadda zai fahimtar dani nima so nake na fahimtar da shi amma yaki nima, zuciya nayi na juya mishi baya. A wannan lokacin na fuskanci kawaici irin nashi bai yarda ya biye min ba, ina jin bayanin da likita tayi masu, tare da musu allura na tsawon kwanaki arba'in, sannan nima za a bani maganin da xan na sha na cigaba da basu nono.
***
*Asiya*
``All spicess
Jollof mix
BBQ mix
Thyme plus
Garam masala
Curry powder```






```Special zobo
Special yaji
Spice kuli kuli
Miyar kuka
Miyar kubewa
Special daddawa```




```Garin masa/sinasir
Garin alale da kosai
Garin kunun tsamiya
Garin kunun aya```
*Shin ko kun san kayan kamshin da kayan zobo tare da duk wani dangin kayan abincin gargajiya da Ummu take amfani yana samuwa ne ta wurin Shaharariyar me kayan kamshi na AIDA spicess! Ina mata yan yayi ina masu abinci na online kayanku ya tsinke a gindin kaba, ga Hajiya Aida special spicess tazo mana da kayan girki na gargajiya da na zama kai Jama'a wata miyar sai a makota! Na gwada sauran ku gwada ina jiranku! Za a iya samun Aida spices ta wanann number:+234 806 968 1068 Whatsp siyan na gari mai da kudi gida! Hajiya ki zama yar gayu me sauki ne amma girkin yan gayu dai da Aida spicess*41


*Kafin na fara zan soma da tayaki murna zagayowar shekarar haihuwarki Mom Sayyad da Noor! Allah ya albarkaci rayuwarki ya kawo yan uku in sha Allah a raba cake a kawo min nawa🎉🍧🍨🍦🍰🍮🎂🧁🍭🍬*


*Asiyah*
Kallonta bokon yayi yana nunata da yatsa, "Zaki auri Tafida! Ba makawa da amincewar matarshi, amma ki sani Tafida ba sauki cikin lamarinsa domin Allah yana kare shi, abu daya na sani babu abinda zai tab'a samunshi domin matarshi kadai zamu iya samun Matarshi saboda laluran juna biyun da take da shi." Murmushi yayi yana faɗin. " Itama ba dole ba ne, domin tun ranar da kika tafi nake aiki akanta, iyayenta da iyayenshi suna tsaye akansu! Akwai wani munafikin malamin da yake tsaye kan lamarinsu, nayi kokarin na razana malamin aljananuna talatin da biyar ya kona minsu da Yasin! Idan kika samu damar shiga gidansa ki tabbatar an had'aku gida! Sannan ita me uwa wawuya ce ki ja yaranta a jiki yadda zata sake da ita!" Buga kasa yayi yana faɗin. "Ba zaki tab'a nasara ba sai kin shiga jikinta domin suna son juna ita kuma yanzu cikin jikinta zai ta juya mata lissafi! Karbi wannan ki tabbatar ya shiga hannunta daga haka zata, amince!" Turai ta kalle shi da kyau tana faɗin. "Mai zamani kana nufin sai mun tafi har Maidugurin kenan?" "Da yare nawa zan gaya miki? Ke tashi ki asko min gashin gabanki maza!" Jikin asiya na rawa ta mike. Mika mata sabon reza a takardan ta ya yayi yana kallonta. "Maza cire dan kanfen ki asko sannan ki yanka jikinki da shi yadda zaki jini zai tab'a gashin!" Haka tayi yadda yace, sannan ya amshi gashin gabanta ya haɗa abinda zai hada ya kalleta. "Ki zuba a turarenki, ki tabbatarwa kin hadu da Tafida! Yadda kome zai tafi mana! Tashi maza gobe Laraba tabawa ranar samu ki bar garin nan da sassafe kada ki dake rana tafi zafi baki bar garin nan ba domin sa'arki tana gobe ne." Gyada kai take tana jin kamar ta auri Tafida ta gama. Kudi suka zuba mishi sannan suka juya zasu bar dajin. "Ke mace ce kuma karuwa kiyi amfani da karuwancinki wurin jan hankalinsa!" Gyada kai tayi ya kara sake murmushi ya ce mata. "Yana amincewa ki dawo nan akwai sauran aiki." Gyada kai tayi, suka bar dajin, Ajiyar zuciya Hajiya Turai ta sauke tana faɗin. "Matukar aka yi nasara to ba makawa, sai mun samo hanyar da zamu mallake Tafida bakiɗaya yadda wani ma ba zai more shi ba."
"Mu fara samun kan Matarshi, Mama Matarshi ba da wasa ta kama shi ba, sannan duk shige-shigen Hajiya Hindu haka Tafida ya fi ƙarfinta kin ga kenan babu hanyar da zamu kanta." Haka suka fito sai da suka huta kafin suka bar garin, koda suka isa gida dare yayi drive suka sake sakawa a gaba, ya dauki Hanyar Maiduguri, bayan sun loda kayanta a motar. Wurin karfe tara suka bar Yola. Dake driven ya san hanya, sannan babu wasu ababen hawa a hanya. Ba karamin tafiya suka yi ba amma kuma cikin ikon Allah basu hadu da kome ba.
***
*Ummu!*
Daga ni har yaran magani da abubuwan gina jiki aka bamu, a wannan lokacin babu laulayi sosai dai tsirfa, bana cikin kowani abinci sai wanda na zab'a, gashi ko sati ban yi da dawowa ba Tafida suka Tafida Abuja, naso zuwa domin mun yi waya da Tinah take gaya min jikin Deen sai addu'a, kamar zan yi kuka domin a Tafida ne ya bar wayar a dakina ni kuma na dauka ina waya da shi. A tsaye yake jikin kofar ya harde hannunshi a kirjinsa. Yana murmushi ya ce min. "Zan sauya password, na ga ta yadda zaki takurawa wayar me girma Gwamna!" Ba wani abu ya fada ba, amma naji raina ya b'aci na ajiye mishi wayarshi na fashe da kuka. "Sannu shagwab'a, wato ga yar kwai da ba a mata magana. Hajiya xan gayawa ta daina riritaki!" "Ni ka rike wayarka ba xan kara ɗauka ba, don ka ga bani da amfani shine kake min wulakanci!" Dariya yayi yana faɗin. "Gaskiya ban ga wani amfanin da kike min ba!" Wayar ce tayi ƙara, na mika mishi zan fita rungume yayi ta baya yana daukar wayar ya saka a kunne. "Barka da dare Mama!" "Yawwa Barka da dare dai, ina Ummun take?" "Gata nan!" Ya saka min wayar a kunnena. Cikin kuka na ce mata. "Mama don Allah ya dawo da ni, sai saka ni kuka yake!" "Tow sannu Yar yaye da bata rena kuka, ki kira Ummu Kulsum ki gaida ta yarta ta kone, Ayya zan kirata amma
Mama ba nida number ta ki ce Uwanina ta turo min zan kirata da layin hajiya." "Shi layin Mijinki fa? Ke bana son munafuncin, ina da uwani kuka munafunce ni!" Kashe wayar tayi na fara matsar kwalla sumbatar dokin wuyata yayi yana faɗin. "Idan ba rigima irin naki ba kiyi hakuri mana!" Haka yayi ta lallabani har na share na hakura, an turo min number da layin mama na kirata na mata ya me jiki, ta ce da sauki da gayya nayi ta hira da katinshi. Murmushi yake yana kallona don ya lura ba karamin aikina bane na fashe mishi da kuka, nima na rasa dalilin wannan shagwab'ar. Koda yake Hajiya ta daure min kugu, nayi yadda nake so, satinmu daya da dawowa itama ta dawo, da jikokinta, ni kuwa na kama su na rike abuna, haka ya ƙara min daraja a idanunta. Domin ta kwashe Yaranmu ta riƙe. Sharif tafida ya kira ya kai Nana Asma'u makaranta Humairah kan tayi karama da makarantar. Su Mufidah tsakanina dasu nono.


Tunda suka tafi Abuja, na tare a bangaren Hajiya. Tow ta hanani aiki sannan ta dauko wata yar dan uwanta daga kauye tana aiki girki kuwa da kanta take mana. Ina kwance Nana Asma'u ta kawo min dan wake da mai da yaji, tashi nayi da sauri nace. "Hajiya na gode!" "Allah ya miki albarka!" Ta fada daga kitchen, Fanna ta ce mata. "Inna kina shagwab'a Ummu kamar yadda Tafida yake faɗa." "Eh nayi din!" Ta fada tana murmushi, hmm matar nan tayi domin goye take da Mufid da yake rigima ta ce mishi. "Ba fa zan sauke ka ba, na gaya maka sai taci ta koshi!" Ta fito min da gulli da ta yanyanka da tumatur da albasa ta matsa lemon tsami a ciki, ta ajiye min. "Allah Ubangiji ya tabbatar dake a cikin gidan Aljanna!" Na fada ina cin abincin bayan na juye gullin a cikin dan waken. Mufidah kan tana wasanta. "Hajiya !" "Na'am!" Ya bani hankalinta kaina. "Kiyi hakuri!" Haɗe rai tayi tana faɗin. "Ba Falmata ta ce ki rage yawan damuwa ba? Ko so kike na kira Babangida na gaya mishi kin sake tadda maganar!" Murmushi nayi nace mata. "Hajiya ba zaki iya gaya mishi ba, Hajiya kiyi hakuri su shigo ko sau daya ne, Ya Abubakar ya roki haka kiyi hakuri don Allah!" Na fada ina loda abincin a bakina. "Ke baki damu da kanki ba ne." "Hajiya ina dake ina da Allah!" Na fada ina kara loda abincin. Wayata ce tayi ƙara. Domin kafin ya tafi ya saya min amma don jaraba nace mishi. Don kada na dame shi da karban waya ya saya min ko? Tow wallahi ba zan yarda ba ni wayarshi nake so. Tow ya ce min ya tafi, *Sweetpie* na gani dauka nayi ina hade rai. "Sai yanzu ka gadaman kiranmu Daadi?" "Hmm baki tambayi Deen ba?" "Allah sarki ya jikin nashi?" "Alhamdulillahi yanzu haka zamu wuce da shi india ne, kuma kin san akwai wani hadin gwiwa da zamu yi tsakanin gwamnatin kasar da borno, ina son idan na je na samu ganawa da Ministan harkokin waje kasar, Ummu i need pray!" "Kana da Allah da Hajiya in sha Allah mun gama maka! Amma Daadi meye matsalar Yayana?" "Akwai aikin da zasu mishi a kwakwalwarshi ne zuwa dokin wuyarshi kin san ya auna arziki, sare kanshi suka so yi! Ummu ki taya mu da addu'a idan ayi aikin a dace!" "In sha Allah za a dace " mikawa Hajiya nayi suka gaisa tayi ta musu addu'a ina cewa Amin, bayan sun gama na amsa nayi mishi sallama kafin na ce mishi. "Yallabai Daadi, su zaso ganin Hajiya don Allah kayi hakuri!" "Ina wasa dake ne na saka doka ki karya min? Kada su shigo min gidana!" Murmushi Hajiya tayi ta bamu waje, kwalkwal nayi da idanuna, ai kuwa na fashe da kukan da yada shi dole ya janye mitarshi. "Ni gidan Mama xan wuce!" "In sha Allah kafarki sai ta makale a gidana!" "Kayi hakuri su zo su ganta mahaifiyarsu ce! "Hmm! Idan suka miki wani abu babu ruwana." "Na yarda!" "Allah ya miki albarka, ki shafa min babynDaadi!.dasu Babana da Mamana sannan sun gaya miki zasu zo dayawa kada ki sake ki shiga kitchen saboda wasu yan iska."
"Zasu ji in sha Allah!" Haka muka yi sallama, ashe zuwan ba iya su Maryam ba ne, sun shiryawa zuwan. Kallon agogon parlour nayi, na kalli Mufidah tashi nayi na shiga kitchen Falmata tana faɗin. "Kai Maman Mufidah me zaki yi?" "Kayan cake nake bukata." "Daren nan?" Na ji muryan Hajiya. Gyad'a kai nayi ina faɗin. "Eh Hajiya!" "Ummu" "don Allah Hajiya!" Na fada kamar zan yi kuka, "shi kenan sai ki fada mana Me zamu taya ki?" Murmushi nayi na ce mata. "Hajiya Sakwara zamu yi gobe idan Allah ya kai mu!" "Sakwara da lafiyarki!" "Akwai abin dakawa na zamani!" Na fada ina mata dariya. Haka muka daura aikin cake da miyar egusi, kafin karfe sha daya mun rage aikin, Yarann duk sun yi barci Hajiya ta musu wanka ta kwanta dasu bayan tayi musu addu'a. Hankalina kwance muka gama rabin aikin, cake din sai sha biyu na gama, a lokacin muna waya da Tafida ban gaya mishi cake nake ba, sai da na gama na gaya mishi shiru yayi kafin ya ce min. "Bana ce banda aiki ba?" "Eh bakina yake jin kwadayi Malam!" "Allah ya shirya mara jin magana!" "Amin Malamina! Ina kewarka amma!" "Kiyi hakuri idan na dawo zan sake zuwa duba shi tare zamu zo!" "Hmm na gode" na fada ina murmushi. Haka muka cigaba da hira har barci yayi gaba da ni, Hajiya ta dauke wayar ta saka a charger, ta gyara min kwanciyata. Sannan ta fara sallah,


Gudu nake sosai a cikin wani bakin daji, wata mace tana bina da wuka, zata caka haka yasa nayi ta gudu kamar xan tashi sama, sai tayi kamar zata caka min sai nayi mata nisa, garin gudu Na fada wani rami me cike da kwayoyi, Maryam da Saadiya da rukayya ke min dariya, suna zuba min kasa a kaina, ban san ya ka yi haske ya bayyana ta ramin me karfi da yasa dukkanmu , muka fasa ihu. Farkawa nayi Hajiya tana gefena tana tofa min addu'a. Haki nake kamar wacce taci Uban gudu. Mika min goran zam-zam da Malam Zailani ya bada a bani yayi na sha. "Ummu kin kwanta babu addu'a!" Hawaye ne ya cika min idanun nace mata. "Hajiya na manta ne ina waya da Daadi!" "Allah ya mana tsari da mugun ji da mugun gani, tashi kiyi alola ki zo kiyi sallah.." "tow Hajiya na!" Haka na sauko na wuce ban daki nayi alola sannan na dawo na samu ta ajiye min wani abin sallah, tare da kayana, ta wuce can tana nata haka nayi sallah na dake da addu'a gabana sai faduwa yaƙe.


*Asiyah*
Karfe biyar na asuba suka shigo gidan Abba, kowa yayi mamakin ganinta, domin a dakin Inna ta sauka, a bakin Inna ta ji labarin zuwansu Maryam gidan Tafida. Don haka yi kasa da Murya tana faɗin. "Inna don Allah na je dani, ina son ganin Yan biyun nan!" "Idan nabila zai tafi sai ka bishi, don na ji yana cewa har da Yaron gurin shuwa zai je samha da sadiya!" "Allah sarki zan je don Allah!" "Tow sai ka shirya!"
Haka ta hada kome, nata tayi wanka bayan ya fito ya je ta gaida Hajiya Kaltuma ta gaya mata zata itama Gidan Ummu, tace shi kenan su shirya ai.
Koda lokacin Tafiya yayi kwalliya ta cab'a kamar me shirin zuwa gasa.
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7642
*Ummu*
Haka na wayi gari jikina ba karfi, Hajiya ta bani addu'a na sha, ta saka ni a gaba na ci abinci kaɗan. Hajiya duk ta damu, haka na daure na fara aiki fanna ta gyara min doya ta daura na shiga aiki akan lokaci, kafin karfe daya mun gama, ina wanka na ji hayaniyarsu, ban fito ba sai da na shirya cikin shigar alfarma, na kira Mama muka gaisa na gaya mata yadda nake ji a jikina. "Allah ya kawo miki mafita duk laulayin ne" haka muka ta hira sama sama, jin kira yasa na duba wayar Tafida da number kasar waje, murna na yi na ce mata. "Mama Daadi yana kirana. Kashe zan kiraki!" Murmushi tayi tana faɗin. "Ko kin kira ba zan dauka ba!" Ta kashe wayar, tana kashe wayar na dauki nashi da ya kira a karo na biyu. "Koda na bi Allah na ki Annabi idan ban bi ka ba, Allah sai ya nisanta ni da gidan Aljanna, Allah ya albarkaci nimanka da samunka, Ina kwana hasken rayuwata!" "Lafiya lau, mace mutum kin tashi lafiya, ya jiki jikin?" Shafa cikina nayi ina faɗin. "Alhamdulillahi Daadi!" Turo kofar dakin Hajiya aka yi, na d'ago kai ina kallon ta, ban santa ba amma kuma sai da naji gabana ya fadi tana rungume da Mufidah, tana murmushi. "Makullim aljannata yau gidan da baki." "Eh na sani shi yasa na kira kada wani ya tab'a min ke." Murmushi nayi nace mishi. "Na gode makullin aljannata, ina kewarka." "Ina kewarki wallahi!" "Nima haka Uban Yarana! Ina kewarka ba iya ni daya ba hatta Hajiya Yaranmu." "Yaushe zasu tafi?" "Hmm! Ai kwana zasu yi da wuni kaga ba batun tafiya!" "Ummu ! Bana son irin wannan wasar ki gaya musu nace kowa ya tattara ya bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login