Showing 63001 words to 66000 words out of 241571 words

Chapter 22 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14713

Ummu Hadiyya a kawo!" "Tow Dr Sagir!" Ta fita. "Ummu bari a kawo miki madara da dafafe ne daga Yola aka kawo min." Mamaki ne ya kama Tafida. "Wannan kulawar fa?" "Kanwata ce!" Gyada kai yayi, ina zaune aka kawo madaran a wani bowl, na fara sha a hankalin ina gyada kai. "Ya Sagir! Wata sati xan kawo maka sako a kaiwa Baba da Mamawo!" "Allah ya kai mu!" Ina sha aka kawo result dinsu, yana gama dubawa ya kalle shi. "Babu wani abu sai dai ciwon sanyi, Ita take dashi zan dauraku akan Magani ita kan Ummu ba zan bata magani ba saboda bata da kome, idan kana son a haifa maka Yara da lafiya sai kun yi treatment din ciwon sanyinku!" "Idan kuma aka samu matsala fa!" "Yaran zasu iya mutuwa, ko a haife su da ciwon idanun ko suma da ciwon mafi akasari ana haifan Yara da ciwon ." "A'a rubuta mana maganin da zamu sha." Ni kuma ya haɗa min chocolate da wani kwali ya mika min. "Nauyinki yayi kasa, ki sha kafin ki dawo ban da skiping abinci, duk abinda kike so ki ci saboda idan babu nauyi tow yaran zasu samu matsalar domin yunwa zai kama su!" Wayyo Allah na, tuni Tafida ya rikice mana, tun a asibitin yake min sannu har muka iso gida ta wuce bangarensu. Ni kam Kayan ya kai kitchen ya zuba ai a firji.
Ni kan kayan Dr Sagir ya haɗa min nake ci da abinci.
Washi gari Abba ya aiko da cefene, Tafida ya shigo ya same ni ina shan ice cream, "ko zaki zo ki raba kayan nan ne?" Girgixa kai nayi ina faɗin. "Ta raba kawai!" "Tashi nace!" Yadda yayi maganar a dake na tashi a hankali, na nufi tsakar gidan na raba, kome na nuna mishi ya dauki nawa ya kai min. "Kaji nan ka cire guda hudu da danyen nama nayi maka dambu!" Zare idanun yayi yana faɗin. "Amma baki da lafiya fa!" Murmushi nayi ban ce mishi kome ba, na saka ya kira min Harira muka fara aikin kafin karfe shida na yamma na gama,na bawa Harira nata tayi ta godiya da wani abu tayi wanka. Sai ga yarinyar nan ta dawo tana min wanke-wanke da shara da gyaran gida, ni kuma ina girki a daddafe Tafida yayi kwana biyar ya dirko dakina da sunan ya gama kwanakin kenan. Tunda na ga haka na rufawa kaina asiri da nuna mishi ina fama da kaina, na zata zai yi hakuri ne sai naga ashe ba haka bane, jarababshi ta kawo shi kamar bai da mace a gidan. Kwana biyu bai waiwaye ni ba amma yau da ya waiwaya sai da naji kamar abin cikin zai fito bakiɗaya. Washi gari tun asuba naji ana ta buge buge da fada. Sallah nayi na koma na kwanta, ashe fada aka yi ya maketa, karshe aka kai sharia gaban Abba, ya ce ai babu ruwanshi. Sai gashi an fara ganin laifina dama nasan kome ya faru Ni ce, ina fama da kaina aka ce na sace mata girki a kwanakinta . Ban damu ba na zuba musu idanu. Cikina yana wata takwas Kanwarshi Sabirah ta rasu wurin haihuwa. Dama hanya nake nima rasuwar ya bani na tafi na bi yan gaisuwa. Na bar masa Matarshi a lokacin sun tafi yawon campaign, tunda na isa a matuƙar wahale, haka ta tsaya a kaina duk da itama bata da lafiya, ba karamin tausayi ta bani ba Allah yasa nazo da kudi, Yaranta mata kamar ba Uwarsu ba. Tafida baya gari lokacin da ya dawo yaji labarin na tafi ranshi ya b'aci . Yana kirana na ce mishi. "Kazo ka ɗauke ni kawai idan kayi niyya!" Kamar wanda na bashi umarni ranar addu'ar bakwai ya shigo cikin gidan. Ina zaune a wurin suyar masa, ya shigo ya zabga min harara. "Wannan uban nisan kika kwaso katon cikinki salon ki haifa min Yara a gefen titi ko? Ummu baki gane condition dinki bane? Fisabiilillahi idan wani abu ya same ku fa? Kin san yadda aka yi na dauki kwanaki ina zulumi? Idan wani abu ya same ki ba zan yafewa kaina ba, kuma wallahi ki daina min shishigi!" Kuma kada kuyi tsammanin a kebe yake maganar nan. Deen yana bayanshi yana murmushi. "Ummu don Allah a me kika bashi ya zama bita-zaizai haka?" Yana dariya. Ni kan kunya ya kama ni, na tashi da kyar ina faɗin. "ku shiga Hajiya tana ciki, zan kawo muku abincin karyawa." Riko hannuna yayi yana faɗin. "a'a muje ki zauna ki huta waye ya sani ko tun zuwanki kike musu aiki!" Ya fada yana hararata. Har cikin dakin na kai su suka zauna suna gaida Hajiya na fita na fara hada abincin yan uwansu da suke abokan wasa Sai tsiya suke min. "Ummu gaya mana gaskiya me kika bashi ya sha!" Dariya nayi na zuba musu kunu da masar. Na kai dakin, sannan na fito na dauki miyar da haka kawai nayi tun jiya ina fatan kada ya bani kunya Tafida yaki zuwa. Cikin hukuncin Allah sai gasu da safe sun shigo ashe tun daren jiya suka shigo. Sai nafi Hajiya Murna, kallonshi take cike da so da kauna. Bai tab'a zuwa ba ko wancan zuwa da yan uwansa suka zo bai zo ba. Yana cin abinci Rukayya ta shiga. "Tafida bamu da kudin mota. Ko zaka taimaka mana ne?" "Rukky ina zaki kai kudi ne? Ina baki kudi amma kamar ina baki kasa? Fisabiilillahi."
"Shi kenan kada ka bani ka kunyata Ni a gaban makiyana!" Murmushi nai tare da barin dakin ta ja tsaki. "Bana son haka, kada ki d'aga min hankalin matatta jininta ya hau." "Sannu yaushe ta samu zama a ranka!" "Aunty Rukayya kefa babba ce! Yarinyar nan tana mutuntatta ki sai zubda mutuncinki kike akan idanunta!" Inji Deen.
"Hmm!" Dake tana son Abu a hannun Tafida kuma tasan matukar yana tare da Deen baya barinshi haka sai ya saka yayi mata. Shigowa nayi da kofin tea har biyu na ajiye musu. "Gashi babu dambu nasan kana so da bread!" Murmushi yayi yana faɗin. "akwai sauran na ai na zo da shi!" Mika min key motar yayi ya ce. "Je ki dauko min!" Make kafadarshi Deen yayi yana faɗin. "Sannu uban yan son zuciya, tunda muka shigo take shiga da fita, dan banza zata kuma fita har waje tayi wani aikin!" Karban key din yai ya fita. "Ayya Yayana da ka bari na tafi na dauko!" Haka ya share ni, ya dauko bokitin, yana kawowa na zuba mishi na raba biyu na bawa Hajiya tayi ta godiya. Bayan la'asar aka yi addu'a, tun da yazo muka kebe na mishi magana akan Hajiya itama bata da lafiya. Ya share ni. Jan hancina nayi ya d'ago kai yana kallona. "Yaran Dady kun ga zata fara ko? Ni dai ban mata kome ba kawai ita ce dai da rikicinta." Ai kuwa na fashe da kuka, "ya isa me kike so?" "Abinci da kulawa kaga mijinta yanzu baya raye sannan Yarann sabira zata rike su a rage mata dawainiyya!" Sosai goshinsa yayi yana faɗin. "hmm! Naji!" Ya fada yana mikewa. Ya dawo gabana ya durkusa yana kallon cikina. "Yarana kuna kewata ko?" Ya fada yana shafa cikin. "Zan kawo Nanny har biyu su taya ki reno, domin naga ke baki da lokacin kula dasu. Sannan ba zasu sha nono ba saboda!" "Saboda ni yar karamar gajeruwar mace ko?" "No ba haka ba ne!" Hmm Tafida ba zai tab'a canjawa ba. Haka na gayawa raina ba zai canja ba.


Haka muka kwana da zan fita ya mika min kuɗi yace min. "Wannan ki bawa Hajiya, wannan kuma ki bawa Rukky!" "Allah ya saka da alkhairi!" Na fita na nufi cikin gidan, na samu suna ta mita. Mika musu kudin nayi na nufi Hajiya na mika mata nata, na ciro wanda na riko mata na mika mata. "Hajiya xan bisu ya ce, Allah ya ƙara miki hakuri!" Godiya take min kamar ta durkusa min. Muna haka ya shigo ta kalle shi a raunanane ta ce mishi. "Allah ya saka da alkhairi! Na gode Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi ya baka sa'a da nasara akan abinda kake nima, ka rike Ummu mace ce ta gari tana da mutunci kuma ta fito daga gidan da ya dace kayi hakuri Baba Ali kayi hakuri da yan uwanka kai ne karami kai ne babba Allah ya baka matsayin ne don ya jaraba imaninka!"


"Amin Amin Amin!" Deen yake faɗa yana kara fada "Tafida ni gaskiya ku xan bi ke bashi kudinsa" inji Aunty Maryam, itama Rukayya, haka ta hakura amma ta ki bada kudin, ya ce musu. "Kada ku takura mata domin ni gaskiya muje tasha nayi shatar mota ku tafi ni kwanciya nake son tayi saboda Yarana." Ai kuwa tashar ya kai su tare da ɗaukar musu mota nasu iya su, haka muka bar garin cike da kewar Hajiya. Maryam bata so ba don haka ta gayawa drive yayi ta bibiyar su Tafida. Haka kuwa aka yi duk inda aka tsaya sai sun tsaya domin ayi musu abinda ake min. Haka muka shigo Maiduguri ya kai su gidajensu.


Lokacin da muka dawo Abba da kanshi ya zo gaida ni, nayi ta dariya ina faɗin. "Abba na dawo babu tsaraba!" "A'a da kika dawo lafiya ma ai arziki ne!" Haka ya gama gaida ni ya fita. Bayan na dawo na zata zan huta ashe ba haka ba domin kuwa Sa'adiyya da Uwarta suka saka ni a gaba, na farko cikin ya hanani barci, haka yasa cikin dare zan ga Sa'adiyya ta shigo dakina tsirara musamman idan baya gari, ganin haka na fara daina barci nima sai na maida hankali wurin raya daren, amma a haka nake jin kamar na bar gidan. A hankali na je na gayawa Mama ranar a naje awo nace Sagir ya kai ni gida, lokacin da muka isa Mama ranta ya b'aci don bata son alaka.da nake da yan uwan Babana. Da na kwanta ina nishi. "Mama bana son tashin hankali, amma ina ganin ya dace ki tsaya min na samu yancina, Mama gidan Tafida jin shi nake kamar wuta ake hura min wura min." "Nayi miki alkawarin tsaya miki gabanki da bayanki, amma dole kiyi hakuri." Wannan shine karo na uku da take min alƙawarin. Sai yamma da suka dawo campaign yazo ya dauke ni, yana ta Godiya. "Wai Ummu meye matsalarki ne?" Ya kalle ni yadda na lalace!" "Zaman gidan ne bana so." Shafa kaina yayi yana shiru kafin muna isa ya raka ni cikin gidan, sannan ya wuce wurin Abba, ban san me ye matsalar ba sai dai tun ranar ya fara kawo min ruwa a goran swan yana kawo min, ashe rubutu ake da Farin zuma ana wankewa da ruwan zam-zam. Tunda na fara sha barci ya fara zuwa min, ina hutawa shima ya rage yawan tafiyarshi, sannan cikin dare zai dawo ya kwana a gida domin lafiyar cikina.


Ana haka zabe yazo aka yi cikin kwanciyar hankali aka fara na shugaban kasa, sati biyu a tsakani aka.yi na gwamnonin. A nan Borno Tafida da wani Yaron Alhaji Mansur Goza aka yi takarar kuma Allah ya ba Tafida sa'a. Koda yake Sa'adi ta fita campaign amma ni ko waje ban fita ba, wani labari me dad'i shine yadda yan ƙaramar hukumar biu suka zaɓi Tafida saboda yana aurena. Tun daga nan Tafida ya kara ganina da kima. Tun da aka fitar da sakamakon nake nakuda a tsaye, mun yi sintirin asibiti har na gaji. Haka muka hakura jiran ciwon.
Wani abin mamaki kiri-kiri yan uwanshi da wanda suke uba daya suka koma gindin Sa'adiyya, musamman yadda ta fita campaign sai suke ganin ai ita tafi dacewa da zama First Lady, ni dama bai dame Ni ba ina dalili. Tinah ta kirani tana taya ni murna, a wannan lokacin Abba hakuri yake bani domin tunda aka ce shi yasa ci ya dan rage bani lokacinsa. A haka Shuwa tana ganin kamar sun shiga tsakaninmu ne.


A hankali kome ya zo karshe zuwa daren da za a kawo ni asibiti, yaso ya gayawa yan gidan nace a'a muje kawai. A lokacin da muka je Dr Sagir baya nan. Nabila ne a daren har wurin asuba kafin Allah ya sauke ni lafiya..
****
Dawo labari
Ajiyar zuciya na sauke ina jan kukan da y zo min, "Wai Ummu saboda nace ki koma dakinki kike wannan kukan? Ummu idan don haka ne Ummu ki zauna muna goga kafada da kugu wuri guda, kowa yana dakinsa yana rufawa kanshi asiri ke zaki tona min asiri a saka ni a gaba da habaici da gori?" A hankali na bude idanu na kalleta, kafin nayi magana ta dasa da cewa. "Ba zan takura miki ba, amma ki sani har abada ba zan tab'a farin ciki ba idan kika kashe aurenki!" Tashi nayi zaune idanuna sun yi fulu-fulu, don kumburi gashi babu barcin da nayi, hasken da nake gani ya fara daukewa a hankali na dunguro daga gadon ai kuwa ta sake salati.......


*Wash hannuna! Anan na kawo karshen free Page na labarin Ummu da Tafida! Hmmm Ga Ummu Hadiyya ga Tafida mai girma Gwamna! Wannan ba labarin soyayya ba ne kamar yadda kuke gani labarin gidan aure ne da yadda ake gwagwarmayar gidan aure. Yes ba labarin da zan cika ku da soyayya kiss! Sex scene da sauransu wani bangare ne na wata rayu idan har soyayya zata biyo baya tow ba mamaki farin ciki zata wanzu a zukatan masu hakuri da Imani! Ina labarin Mahmoud? Shin ya hakura da kudirinsa ko har yau yana bibiyar motsin Ummu! Shin Ummu zata hakura ta koma dakinta ko zata rabu da Tafida kamar yadda ta ce! Shin Tafida zai sake ta kuwa ko zai cigaba da riketa kamar yadda ya fada, Mahmoud zai samu biyan bukatarshi akan Ummu kuwa! Ya Tafiyar Sa'adiyya da Yan uwan Mijinta? Shin zasu dawo jikin Ummu? Ya Mahaifiyar Tafida Ummu zata iya dawowa Hajiya dan ta kuwa? SHIN AKWAI SOYAYYA? INDAI AKWAI SHIN WAYE ZAI iya amayar da nashi don.a koma sabuwar duniya! Tafida zai iya rike Borno kuwa a matsayinsa na gwamna! Sa'adi ta saka smarty ya lalata fake soyayyar Ummu da Tafida shin wai me zai faru? Hmmm wannan labarin ko? Ban yi kome ba domin idan tafiya yayi tafiya gumurzu zai fito rikici da soyayya zai jagoranci Yar Mace, wacece Yar macen nan ne?......*


TAFIDA
UMMU
DEEN
MAHMOUD
SA'ADIYYA ...... ALL IN YAR MACE kowa da kuka gani zai taka nashi matsayin don haka ku biyo alkalamin Uwar Muwaddah Ammyn Anum! Mai rikon Walid 😂🐐🤣


500
NE MALAMA IDAN KIKA GA LABARIN NAN A WAJE TOW SATOWA AKA YI Yawwa na gaya muku na kudi ne..



Zan tafi hutu sai Friday zan cigaba in sha Allah....




500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Innalillahi wainnalihir rajouna! Ummu!" Ta kira sunana da karfi tare da nufo kaina, tana salati wannan salatin ya tashi Uwani daga barcin da suke ita da Zakiya, suka shigo dakin da gudu. Ganin yadda Mama take kokarin d'ago ni amma jikinta ya mutu, ita kanta zaune take akan gwiwarta. Da gudu Uwani ta fita tare da nufar waje tayi ya buga kofar Baba, ai kuwa suka tawo tare ganin halin da nake ciki ya fita yana salati ya taso kawu gwani. Aka fita da ni zuwa asibitin Dr Sagir. Har gari ya waye Dr Sagir yana kaina. Sai da garin ya fara haske ya nufi waje yana kallon Baba. "Don Allah kada a shiga da kanta zata farka!" "In sha Allah!" Sai lokacin suka nufi massalaci, bayan sun yi sallah Baba da Kawu Gwani suka dawo gida, Uwani ta hada abin karyawa aka saka a basket aka kawo asibiti. Ban farka ba sai karfe biyu na rana, Tafida na gani zaune a gabana yana ta jijjiga Mufidah da take rigima. Ajiyar zuciya na sannan na fara yunkurin tashi ya ce min. "Da dai kin jira a zo a duba ki!" Ya fita da Yarinyar a kafadarshi, can kuwa sai gashi tare da Dr Sagir, yana tsaye a kanmu ana duba ni. "Ummu!" "Hmm!" "Yanzu ya kike ji?" "Kan dai yana ciwo!" "Sannu bari a kara miki alluran kiyi barci ko zai daina!" "Sallah zan yi!" "Ok?" Ya fada yana kallon Fadila. "Ko zaki cire mata ruwan!" Haka ta cire min ruwan. Na tashi zaune ajiye Mufidah yayi ya ce. "Kawo hannunki!" "Bar shi kawai!" Na fada ina dauke kaina, zungure min kai yayi yana faɗin. "Oya tashi kada ki saka a ji labarin Tafida ya ajiye mukaminsa ya tare asibiti." Dago fararen idanuna nayi ina kallonshi. "Kasan me?" Girgiza kai yayi yana faɗin."kasan me?" Yayi wani iri da bakinshi, "ka fita bana son ganinka!" Na fada ina kokarin mikewa,na fada ina kauda kaina. "Akan me?" A hankali na sauke kafana kasa, na saka takalmin da na gani a dakin. A hankali jiri ya nime kada ni, yayi maza ya rike ni. "Ki kula!" Ture shi nayi tare da bin jikin gadon zuwa bangon dakin. "Ki bari na rike ki mana!" "Ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login