Showing 201001 words to 204000 words out of 241571 words

Chapter 68 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14717

a hankali, dakinshi ya shiga ya kunna wayar shi. Sakwaani suka yi ta shiga kafin ya kira number ta, a can wani ya ɗauka. "Hello ina me wayar?" "Yawwa kace mata ta dawo min da kudaddena da ta kwasa ko na biyota har gida na wulakantatta ita karamar karuwa ce da take sata ashe bata isa international karuwa ba!" "Kai Malam kasan da waye kake magana?" "Da mijinta ai naga alamar haka, kai jakin ina ne da baka san matarka tana bin maza ba? Kai ka gaya mata nan da kwana uku ta dawo min da kudina ko nazo har gadon barcinka da Yarana su bi kanta daya bayan daya, kai kasan waye Ni? Wallahi kwana uku ku dawo min domin sai na baka mamaki!" Ihu Mahmoud ya fara mishi yana faɗin. "Kayi kaɗan ka tab'a min matata wallahi karya kake! Matata ba karuwa ba ce." Yayi mishi ya cigaba da musu ihu, yana musu zagin wulakanci. Tare da musu alƙawarin kashe su idan wani ya kuskura ya zo gabanshi, yadda ya haukace kamar zai mutu, domin yana jin bala'in kishin Matarshi. Dariya Mutumin yayi ya ce mishi. "Nayi maka alƙawarin duk ranar da na kama ka, sai na dasa maka ciwon da ba xaka iya maganinsa ba, ku dawo min da kudina, idan ka sake muka hadu babu kudina hatta uwarka matukar tana raye sai na fanshi kudina akanta baka san waye kake tab'awa ba, zan yi hakuri akan kome, zan share akan zagina da kayi amma kada ka tab'a min kudina domin shi kamar fitar numfashina yake. Dukiyata bana wasa da su."


Mahmoud a tunaninsa sharri aka yiwa matarsa aka yi yasa shi, aunawa Mutumin da kana jin muryanshi kasan irin marasa mutuncin nan...
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


(Kuyi hakuri nasan page din yana kaɗan, amma zuwa Friday kome zai zawo dai-dai yanzu ina wani uzuri ne in sha Allah Friday zan gyara bana son na ɗauki hutun jaki da kaya ne nake muku kaɗan)64
Dariyar da Mutumin yayi ya kara fusata Mahmoud sosai wanda ya janyo yayiwa Mutumin alwashin matukar suka haɗu sai ya kashe shi. "Ni duk wannan bai dame ni ba, kudina kawai na sani kuma ya dawo min da shi xan kyale ta xan maka afuwa idan kuma kuka sake muka hadu haka ba zai mana kyau ba domin zan ɗauki duk matakin da yayi min. Sannan zan rama cin mutuncin da ka yi min akanka da kuma duk wanda ya shafe ka." Ihu Mahmoud da yake mishi yasa Mutumin kashe wayarshi. Kamar mahaukacin kare haka yayi ta ihu da faɗa shi ɗaya kafin ya iya calming kanshi kamar ba shi ba, sannan yayi wanka ya shige dakinsa ya kwanta. Sai yau yake matuƙar jin haushin cikin da Khairat ta dauka, da yanzu yana tare da ita yana moran arzikin da Allah ya mata, sai dai har yau bai cire ranshi da Ummu ba, Saadiya kuwa yana hauka ne zai aure ta bayan yasan da auren Tafida ta iya bashi kanta, kut ai karen hauka bai cije shi ba da har zai iya zama da ita, Ummu da ko wadancan abin da ya haɗa su zamanta da Tafida babu jin dadi bata yarda dashi ba, amma ita saadiya da jin dadin da kome ta bashi hadin kai, gaskiya ba zai iya wannan gangancin ba, gara dai Ummu ita ce daidai da lissafinsa, don yasan matukar Ya aureta, zai samu yara na gari masu tarbiyya da sanin ya ka mata, duk abinda zai fito daga Ummu to me daraja ne, shi yasa da yaga ba zata rabu da Tafida, idan taki ya lalata mata rayuwa amma shima ta tsira, "Mace ta gari kenan!" Ya furta yana murmushi lokacin da ya tuna da Saubai bata nan take ya ji hankalinshi yayi azabar tashi. Don gani yake ba zata tab'a cin amanarshi ba.
***
*Ummu*
Ina ga tunda aka gayawa Tafida, cikin nan bawan Allah nan bai barni ba, kai ni mamaki ma nake da cikin bai zube ba, yake kuma duk abin da aka yi, kallona Tinah tayi da tazo jiya, "Malama lafiya?" Na fada ina hararanta." "Kau kawai yadda kika yi kiba ne abin ya dame ni." "Tow sannu aiki yana gabanki!" Na fada ina cikin dan wake. "Allah da gaske kin yi kiba!" Ta ajiye min duk abubuwan da tazo shi. "wanann karon za ayi shi ne Egpty, ga shi nan ki fita ki nunawa duniya baiwarki." Shiru nayi na wani lokaci kafin na cire hannuna a cikin dan waken na ce mata. "Wani lokaci bamu cancanci kyautar da muke samu ba, imma ya zame mana alkhairi imma ya zame mana sharri. Tinah nasan waye Tafida shi ya ce miki ina bukatar haka?" "Ko daya ni na ga dacewar haka!" Gyara zama nayi, na ce mata. "Zan je amma ki gaya mishi kada ya sake ya shiga rayuwata. Irin waɗannan abubuwan da yake faruwa ya dakatar da shi. Bana son haka"
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallona, yadda na hade rai ina kokarin mikewa. "Babu hannun Tafida, idan ba zaki ba ba laifi amma ki daina jingina da na miki da Tafida saboda bana tare da abin da ya miki" ban kara magana ba, har Mama ta shigo, tinah ta gaya mata abinda yake faruwa. Tayi murna sosai kafin ta ce mata. "Zata je ko Ummu!" Ta fada tana murmushi, nima murmushi nayi ina kallon yadda take farin ciki. "Eh Mama!" A ranar Kulsum ta zo, ta wuni domin kuwa tunda yazo Uban mijinta ya hanata fita, sai yau kuma itama ta rantse ba zata koma gidan ba sai ana jibi zata koma gidanta. Da la'asar aka zo daukar Tinah, ina tsaye a gefenta da hijab yellow ta ce min. "Sai mun haɗu a lagos!" "Allah ya kai mu!" Na fada ina kallon har ta isa wurin motar security ya bude mata. "Ina saka idanunki akwai kome sannan zasu turo miki duk abinda kike bukata!" Murmushi nayi mata sannan na cigaba da d'aga mata hannu.
Zan iya cewa wasu nasarar basu samuwa sai da kalubale, haka yasa na samu Mama a gefena, domin ta taka rawa sosai a rayuwata. Ina shiga dakin Mama na zauna, Mufidah ta zo ta hau cinyata. Hayaniyar da na fara ji yasa na leka, ta window Mama, Baba Bulama ne ya saka Safina a gaba yana zane ta, dakyar Mama ta shiga tsakiyar yana huci ya ce mata. "Ni zaki kunyata? Har kasuwa Abdulhadi ya same ni da cewa nayi hakuri kada na ga ya sake, ba laifin shi bane yayi kokarin zama dake amma abin ya ci tura duk abinda ya faru na tambaye. Na tambaye ki kin ce Baba na Tambaye mahaifiyarki ta ce babu, ashe abin da kike aikatawa kenan mai nayi miki na cancanci wannan kyautar? Hatta bukata na ce idan kuna da shi ku gaya min, hassada da yake damun mahaifiyarku shine kuka dauka? Nan ko wata biyu ba ayi ba take gaya min Tafida ya sake Ummu don taci amanarshi, lallai na kori Ummu tunda tana da gidan Ubanta bayan karya ce, sharri ce na kwabeta Karima kin ga sakayyar Allah tun a duniya kenan ba a je lahira na, wallahi kuka sake Allah ya kama ku da abin da kuke aikatawa kun shiga uku. Ba zan miki baki ba amma Allah zai saka min" ya fada yana me barin wurin, Mama sai hakuri take bashi amma ranshi ya b'aci, Ummi kan babu ruwanta. Don ta ga Ishara akan abin da ya faru da. Ajiyar zuciya na sauke ina jin ba dad'i, zama nayi ba kalli Mufid da shima ya shigo, dake suna samun kulawa yadda ya dace tafiya suke. Shigowa Mama tayi ta ga nayi zuru -zuru. " Kina buƙatar wani abu ne?" Ta tambaye ni, murmushi nayi na ce mata. "Kawai ban ji dadin yadda kome, yake tafiya haka ba, gani nake kamar wata rana za a samu matsala." "In sha Allah babu matsala!" Ta fada tana zama. "Allah yana sonki da rahama ne yasa kome yake bayyana, sannan ban nufi kowa da sharri ba taya ni wasu zasu nufe ni bayan na yarda da akwai Allah, shine wannan rayuwar kamar aika ce, idan aka yi dace aka samu a tafi lafiya idan aka rasa kome ya cab'e. Bana fatan ki saka wasu a gabanki, ki cire kome ki rungume kaddaranki Allah baya barci kuma baya gyangyadi, kafin yau nasan ai kin san me yake tafiya, bayan yau kuma kome ya tafi yadda ake bukata, nayi imani da Allah babu abinda ba zai wuce ba sai ikon Allah kuma muna nan muna gani idan muna raye mai rai baya fidda tsammani da nasara ko faduwa. Ki rike Allah ki kuma rike mutuncinki." Gyada kai nayi kawai ina jinta. Janyo kular dan waken tayi ta fara ci tana faɗin. "Kai Alhaji Muhammad zo muci!" Rarrafawa yayi wurinta, ya zauna ta fara ci yana mata wasa. "kin koshi?" Gyada mata kai nayi, wayata ta fara kara. Ganin number Tafida yasa ban dauka ba, d'ago kai tayi ta kalle ni. "me yasa ba zaki dauka ba." "Bani da matsala da shi ne!" "Haka ne!" Ta fada tana cigaba da cin dan waken, ganin ya kara kira ban dauka ba sai ta dauki Yaron suka fita, a fusace na dauka. "Wai kai meye matsalarka da ni ne?" "Baki gane ba ne har yanzu? Tow dama na gaya miki Hajiya tana son magana dake ne, idan don ni ne ba zan kira ki ba!" Shiru nayi "kina jina? Zata kira ki duk da Fanna ce Please ki saurare ta, Hajiya bata da lafiya." Duk da hankalina ya tashi amma na danne kafin na ce mishi. "Tow me zan yi?" "Ummu mahaifiyata ce, kada ki fadi abin da zan ji ba dad'i kin ji."
Kashe wayar nayi, ya turo min sakon. *Don Allah kada ki kullace ta har yau tana sonki sosai* shiru nayi ina nazarin maganarshi. Duk halin da nake ciki na rasa waye zan daurawa laifi, Hajiya son Tafida yasa ta kasa boye shi a ranta, su kuma yan uwansa kyashin da hassadar Allah ya d'aga shi cikinsu yasa suke jin haushinsa. Su Matan gani suke kamar tunda ya ajiye yarinyar da bata musu ba, zata mallake shi sai yadda tayi da shi. Sannan babban tashin hankalinsu yadda ta haifa mishi yara har biyu har da namiji, ina laifin tayi ta haihuwar Yara mata, yadda basu kwashe duk wani abu da ya tara ba, amma ta haɗa da namiji. Wannan shine a zuciyar Maryam ita matukar tana raye Tafida ba zai ajiye iyalinsa ba da tana da halin kashe yaran ma da tayi domin ta haka ne duk abinda tafida ya tara zai zama su. Maryam da Abubakar lissafinsu ɗaya. Don haka ita Maryam yakinta ta samu Tafida yadda zata yiwa mijinta da Iyayensa rashin mutunci, idan ta gama da shi ta kwace Yaranta. Sai dai kuma inda labarin ya sha bambam tunda Tafida ya sake Ummu basu kara gane kanshi ba, domin ya sauya musu sosai dama kuma tunda Ummu ta dawo bayan rigimar farko ta gane tafiya ya fada soyayyar Ummu yadda ba zai iya sauraron kowa ba, tasan yana mugun son Ummu ta kuma yi imanin da haka, sai dai inda matsalar take, Ummu Hadiyya ita ce rayuwar dan uwansu.....
Hajiya ta kira ni, mun yi waya da ita sai dai bana jin abin da take fada, sai da Fanna ta amsa ya ce min. "Aunty Baby don Allah ki zo! Duk da muna da nisa kizo Hajiya tana son ganinki!" "Shi kenan In sha Allah zan zo!" Tayi shiru sannan ta ce min. "Aunty Baby!" "Na'am!" "Don Allah ki zo ki ga Hajiya muna asibitin jidda." Ajiyar zuciya na sauke na ce mata. "Fanna ba haka bane, yadda xan zo ne yana matuƙar wuya, sannan kuma ban san da wani yare zan gaya Mamana zan zo wuri gaskiya ba zan iya." "Shi kenan!" Ta fada a raunane, kashe wayar tayi, nima na bi wayar ina kallonshi kamar ina ganinsu a cikin wayar, "Waye ba lafiya?" Mama ta tambaye ni, "Hajiya ce kakarsu Mufid!" "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah!" Daga nan ta cigaba da harkan gabanta, tana faɗin. "Wani abu suke bukata?" "A'a cewa suka yi wai Hajiya tana son magana da ni, kuma da na mata magana ban san me take fada ba, alamar tana cikin ciwo sosai!" Murmushi tayi tana faɗin. "Kina son ganin ta ne?" Nan kan shiru nayi mata domin ban san yadda zata fassara abin ba, kawai sai na zabi nayi shiru da nayi magana. "Ba zan rabaki da dangin mijinki ba, sai dai har ga Allah yan uwansa suna da matukar hatsari domin sun maciji hatsari, Ummu ban hana ki komawa Tafida ba, sai dai kisan aure da zargi." Wannan kalaman da Mama tayi amfani da shi yasa na kasa motsi, "har abada ba zaku tab'a nutsuwa da juna ba, domin ya riga da ya zarge ki, koda kuwa a ce kun haifi Maiduguri ne." Sai na rasa bakin magana na sunkuyar da kaina ina jin hawaye na zuba min. "Ki taimakawa kanki kada kiyi kuka domin zuwa nan gaba zaki hnago abin da nake nufi, tun daga farko nayi kuskure yanzu kuwa." Shiru tayi bata kara magana ba, haka yasa na fahimci Mama sosai, murmushi tayi ta ce min. "Bana jin dadin mutuwar aurenki, amma akan zargi gara ki nime wani mijin, domin har tsufa da jikoki Aliyu zai na tuna abokinsa ya ganki tsirara sai yaji abin ya dame shi. Sannan zai najin ba iya lamarin ya tsaya ba an biye mishi wani abu! Mutane masu kishi irin na Tafida, suna da matuƙar wuyar sha'ani, domin koda sun yi nadama gani suke kamar zaka aikata wani abu.".yadda Mama take bayanin nan sai nake ganin kamar da na gaya mata cewa Tafida sun kwana daki guda da saadiya tabbas da yau sai ta ce abin da ya shiga yake girba, ko ni yau sai naji kamar Tafida ya boye min wani abu don ko da ban fada ba Tafida yadda suke ta malakewa juna shi da Saadiya duk me hankalin yasa akwai magana a kasa, haka yasa naji hankalina ya tashi.
**
Mahmoud
Yau kwana shida kenan, a yau Saubai'a ta dawo, da la'asar a matuƙar gajiye. Duk yadda ya so dauke kai domin a tsakanin kwanakin nan babu inda bai je nimanta ba, amma maganar daya ce ba a san inda take ba, a wurin aikinsu suka ce an bata excuse ne domin ta tafi wani aiki. Shigowa dakin yayi ya same tana zaune gaban Mirror tana gyara kanta. "Daga ina kike?" "Na tafi aiki mana ba gashi na dawo ba." "Karya kike, ina kika je waye kika sacewa kudi ya kira Ni?"
"Wani irin magana ce haka? Zargina kake? Nace zargina kake? Ka gaya min me nayi da zafi kake zargina bayan kuwa kai ne ka fara sanina y'a mace shine zaka min mummunar zato" "ba haka ba ne baby, yadda Mutumin ya kira ne, yasa." Wayarshi ce tayi ƙara, da sauri ya dauka yana nuna mata. "Me yasa ba zaka dai na kira na ba? Matata gata nan aiki ta je kuma ni na yarda da Matata dari bisa dari!" "Ka ce mata ta ajiye min kudina a waje damuwta kudina idan ka sake na zo akan kudina wallahi ba zan kyale ku ba na rantse da Allah!" Ihu da rashin mutuncin da Mahmoud yake kamar zai shiga wayar ya daki mutumin, haka duk bai mishi ba yayiwa Mutumin barazana. Tare da cewa matukar suka haɗu sai ya mishi abin da ba zai tab'a mantawa ba. Ita kam sauba'a tsoro ne ya kamata, ta san waye Oga Hakim, kazungurmin dan fashi da makami, kusan kansu a hade da ogansu na banki, domin bibiyar masu ajiya a bankin suke suna bin su gida suna musu fashi da makami, tasan Oga Hakim ba zai kyale ta ba, gara ta kai mishi kudinsa, ta shi tayi ta nufi waje ta kiran James tayi ta gaya masa ya bawa Oga Hakim. Muryanta yana rawa ta ce mishi. "Oga Hakim kayi hakuri ga shi nan zan dawo maka da abin da na dauka don Allah kayi hakuri!" Dariya yayi ya ce mata. "Nayi kokarin koyawa kaina hakuri amma Mijinki ya zage ni ta sanadinki, kina tsammanin zan yafe mishi ne? Idan kina tsammanin haka tow ki daina domin ni baya yafiya, kudi kuma ki ajiye shi zan zo daukar abina, amma kiyi barci da ido daya domin bana bada notings sai dai a ganni kawai." Hakuri take bashi tana kara gaya mishi ba zata kara ba, dariya ya saka ya kashe wayar bayan ya mata gargadin kada ta kara kiransu. Wani irin tsoro ne ya kamata domin ya gaya mata duk inda zata ta sani ana bibiyar sawunta don haka ba ta isa gudu ba.....
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7665
Da gasken gaske ta tsorata da lamarin, yasa ko barcin kirki bata yi ba tayi ta kiran Ogansu na wurin Aiki tana bashi hakuri, shima ya ce babu ruwanshi ya ga yadda take da hankali ne ya hada ta da Hakim bai san haka take ba, babu ruwanshi ta je can yasan halin Hakim idan yayi mishi magana yanzu sai ya ce ya hada baki ne da ita ta mishi sata, kuma dama ya kira shi ya mishi bala'i da masifa kenan ta kira itama, har gari ya waye Saubai'a bata nutsu ba, ta shirya ta nufi bank, koda ta isa ta rasa yadda zata yi domin kuwa tana son zuwa wurin MD amma tsoron kada ta samu wani tashin hankalin yasa ta zama har wurin karfe daya na rana sannan ta nufi office din, MD din tana zuwa ta shiga a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login