Showing 54001 words to 57000 words out of 241571 words
Chapter 19 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
and More! Kayan kitchen ne na gani na fada ina iyayen Yan mata ina iyayen Kwailayen ga dama ta same ku, Uwargida da Amarya, Budurwa da bazawara maza ku fito ga kaya nan sayan na gari mai da kudi gida. Kayan mu daban da na shago!*
Paid book
18
Ashe ana can suna ta tattaunawa yadda idan nazo bikin zasu min tozarci, ni anan ban sani ba sai da Nabila ta kira ni take gaya min abin da yake faruwa, ban ce mata kome ba nayi dariya kawai domin nasan ina da gaskiya kuma Allah yana tare da mai gaskiya na babu abinda zai tsorata ni. A bangaren shi kuwa babu abinda ya sauya domin ya rantse sai ya mai da ni yar iska, haka yasa na ki yarda, sai gashi ya dawo da rashin mutuncina, haka na zuba mishi idanun tunda babu Allah cikin sha'aninsa. Ina ga idan na bashi damar ya samu yadda yake so iskanci sai wanda ya ci Uban na da, haka yasa nayi bala'i kama kaina, abin sai ya zama kamar renin hankali daga gareshi, amma na zuba mishi idanu don na fahimci waye Tafida me taka, don haka tun kafin ya fara min horon yunwa na saka kaina sayan kayan abinci, na ajiye. Kamar na san haka zai faru abinci yana karewa na gaya mishi, murmushi yayi yana faɗin. "Ba zan iya cigaba da ciyar da mummunar halitta irinki ba, gara dai a kira gida a roke su kamar yadda aka saba wai ma tsaya!" Ya fada yana mikewa. Bayan nayi kadan ya rike kugunsa yana faɗin. "ina kudin da kike samu?" Hadiye yawu nayi ban iya bashi amsa ba. "Ba tambayarki nake ba ne?" Zubewa nayi akan gwiwata na fashe da kuka, tunda nake a rayuwata Mama sau daya tayi min tsawa amma Tafida bai da aiki sai min fada da cin mutuncina. "Ko kina turawa wancan Matar ne tana tuwo-tuwo..." a yadda na d'ago kai a fusace ya sa shi ma bai karasa abin da yake bakin shi ba, murmushi yayi yana faɗin. "Kin san zafin Iyaye ashe!" "Saboda ni ba jahila ba ce, kuma ba dabba ba ce. Saboda sanin zafin Iyaye yasa nake zaune da kai ai baka isa ka..." Shake wuyata yayi tare da hada ni da bango, saboda azabar zafi ko kuka na kasa sai lumshe idanu, ja na yayi har cikin dakin, yana faɗin. "yau zan koya miki hankali, wallahi baki isa na ciyar dake sannan ki na min rashin mutunci ba!" Ya fada yana kokarin yi abinda ya saka kanshi. Sai dai me yana kai ga cimma buƙatarsa ya samu ina bakonmu na mata, kamar ya rufe ni da duka. Haka ya bar ni a wurin hawaye na cigaba da zubarwa, na sha kukana sosai sannan na tashi a hankali na shige ban daki nayi gyara jikina. Kitchen na shiga na hada tea na juye zan fito na ganshi a bakin kofar. Baya nayi ya shigo ya amshi tea din yana faɗin. "Idan kika sake na gano inda kike kai kudinki sai na lalata miki in da bakyso na shiga.." na rab'a gefenshi na wuce, ni yanxu bana mamakin abin da zai min domin duk abinda zai aikatawa baya danasani. Haka nayi ta maneji da irin halin Tafida gara ka zauna babu aure, domin haka kawai zai kwaso min abokan aikinsa su kwana na ciyar da su, su tafi ko kuma ya zo da yan mata hadaddun irin yan iska-yan iskan su kwana nayi musu hidima, su tafi akwai wata yarinya da tazo ta kwana, sai dai hatta bakin dakina sai da nayi mishi wankan tsarki domin karni da wani irin wari yake, ko sati ba ayi na ta sake zuwa min, tsakani da Allah nace tayi amfani da ban dakin parlour, abin ya bata haushi, ni ko a jikina domin nasan ba wani abu bane cuta nake gudun dauka. Ashe ta gaya mishi, cikin hayagagga yazo zai min tijara na dauki wayata na kira Abba. "Barka dai Abba, ya gida." Juyawa yayi ya kalli Yarinyar ya riko hannunta ya ce ta tafi kawai. Dawowa yayi ya samu har lokacin muna magana ne, bayan na gama na kalle shi. "Da ace abin da kake min zan gaya mishi, ni nasan hatta inda kake gadaran kana aiki sai an sallame ka, Tafida mu zauna mu fahimci juna shine muradin iyayenmu!" Wani shegen dariyar ya saka yana nuna ni. "Ke ni ne zan zauna mu fahimci juna? Ni ne zan zauna dake muyi sulhu don kawai na kyautatawa wancan mutumin!" "Abin da kake aikatawa idan Allah ya baka nisan kwana sai Yaranka sun maka, ka kyautatawa iyaye ma ya aka kare, balle kuma ka saka su bakinciki. Babban damuwa kada ka gurbata min zuriar da zan samu da kai da mugun dabi'unka, domin idan haka ya faru ni ne zan wahala tun haduwana da kai ban huta ba, zuwa yanzu ma ban huta ba na girma lokacin da ya dace na huta fitinarka ya sani na kasa barci. Kai ba yaro ba ne, saboda irin wannan kazamar rayuwar naka laifinka yaso ya shafe ni, in sha Allah na kusan gama contract din da nake na abinci, daga nan ba zan kuma dawowa rayuwarka ba, amma ka sani Allah ba azzalumin sarki bane sai wanda ya zalunci kasan har yau ina gayawa Allah idan zama na da kai alkhairi ne Ubangiji ya daidaita mu idan babu alkhairi Ubangiji ya kawo sanadin da zamu rabu ba tare da mun cutar da juna ba, sannan abu na gaba da zan kara tunatar da kai shine duk abinda na maka don Allah kada ka zagi Mahaifana domin bayin Allah nan sun yi matukar kokari akan tarbiyya da suka bani, bai dace yadda nake ganin darajar ahalinka kai ka gaza ganin darajar nawa ba, sai abu na karshe ina son na tuna maka ni ba yarka ba ce, da zaka na mangare ni son ranka, kana da Yayu mata da kanne idan ka cigaba da haka zan gayawa Abba da iyayena su shiga wannan lamarin tunda na fahimci baka gane karatun, gida naka ne duk wanda ka kawo daya ne, shi zina kamar bashi ce." Na fada ina kuka domin zuwa yanzu idan na tuna abinda ya faru sai naji kamar zuciyata zata buga,, idan na tuna saboda Tafida Mahmoud yaso keta min haddi sai naji na tsani zama da shi, haka yasa na kara raba kaina da Tafida. Ana haka sai ga Ammah abin ya bamu mamaki, koda yake Uwa ce ta gari, bata yarda tazo hannu haka ba sai da tayi min kayan abinci, tunda tazo na gyara mata dakina, ni kuma a daren ranar na koma dakin Tafida da kwana, ina kasa yana sama. Daga shi har ni kowa harkan gabanshi yake, sannan shi ya lura da yadda nake kyamar gadonshi. Abin mamaki yake bashi don ya rasa gane me yasa bana son na kwanta a gadon, sannan yana kara tinzura idan ina baya baya da abin da zai saka na tab'a ba, kwanan Ammah uku ta bar gidan, a daren na koma dakina. Sai dai albarkacin Ammah ya saya mana kayan abinci, kai Tafida mugun dan wasan kwaikwayo ne, domin har da cewa. "Ummu Hadiyya maza rubuto min kayan abincinmu nan da ya ƙare." "Ai kayan abinci da saurin karewa yake, don ma baku samun baki akai-akai ba ne." "Eh sai dai ranar juma'a tana yin abincin sadaka, nace tana yi." "Masha Allah Tafida girma yazo Ubangiji ya dafa maka!" Dariya abin ya bani yadda bai ji kunyar gatta karya ba. Nima ban yi musu ba domin na fahimci mutuncinsa yake kankarowa. Bayan tafiyar Ammah ba laifi abinci dai gashi nan sai yadda aka yi da shi, Ni haka bai dame ni ba domin nasan yana karewa iskancinsa zai dawo sabo dal. Bikin Sharif da ya karato ana ta shiri, na kira Hajiya Kaltuma na tambaye ta meye shirin da ake murmushi tayi tana faɗin. "Ki ware duk abinda Allah ya baki, ki basu idan kuma zaki mana su cake da kayan ciye-ciye ne muna murna." "Tow shi kenan!" Na fada mata ina murna, a inda muke hidimar girki akwai wani dan Senegal yana kawo kayan maza da mata, haka na sayi Senegal lace, me kyau sannan na gayawa Tinah batun bikin ai kuwa tayi tsalle ta dire har da ita zamu zo. Don haka na kira Hajiya na ce mata ina son ankon da za ayi a turo min Abuja har guda biyu. "Ke Ummu kayan nan kala shida ne Abbanku ya saya miki dukka don yace Mijinki matsolo ne bai zama dole ya saya miki ba." Dariya muka saka na gaya mata wacce take so, na.tura kudi aka saya mata sannan aka turo min dasu har da nawa Tinah ta kai ɗinki bakiɗaya. A nan Abuja na sayi kayan aikin da xan yi sannan ana saura sati muka bar Abuja, Tinah zata zo saura kwanaki hudu. Mun sauka lafiya akai ta murna, dake iskar dare muka yi washi gari na hada tsaraba na kai cikin gida, na bawa Hajiya nata sannan na wuce wurin Inna tana gani na ta ce. "Yaron kirki kun iso lafiya? Ina tafida take?" Murmushi nayi nace mata. "yana barci amma nasan zai shigo." Na ajiye mata tsarabarta na fita, sannan na wuce wurin Hajiya Kaltuma na gaidata sannan na ajiye mata nata, dakin Hajiya Salamatu na shiga duk yaran na zaune, suna cin abinci na gaida ta. "Mutanen Abuja, har an iso kenan!" "Eh Hajiya, ga wannan tsaraba ce. Wannan kuma gudunmawa ta ce ayi hakuri babu yawa." Amsa tayi tana faɗin. "Ikon Allah me yawan kenan, Ummu ashe kina koyar da girki ne a can?" Cikin girmamawa na ce mata. "eh amma na kusan kammala dake na wa'adi ne idan na gama shi kenan." "Allah ya dafa miki, ya kuma baki sa'a." "Amin Hajiya bari na gaida Abba!" Na dauki na shi kayan na fitar da shi, "Gaye nan ya samu mace fa, amma yake biyewa duniya yana mata iskanci." Inji Alfah Kanin Sharif. "Eh ya samu mace ga Allah, kuma irin matan nan ne na rufin asiri, Allah ya sa nima tawa tana da wannan halin!" "Amin Ya Allah. Ai naso lokacin da Alhaji ya kawo batun wa kai ya nimawa yarinyar domin tana da tarbiyya da hankali, ku kalli bata dauke ni a matsayin da suka dauke ni ba, yadda take mutuntatta ni yafi min kome dad'i, Allah ya mata albarka!" Ta fada tana murmushi. Da naje parlour Abba nan aka zuba min abin karyawa, ina ci ina bashi labarin wurin aikina. "Ai na gaya miki, nan gaba sai wata jami'an ta dauke ki aikin girki kafin nan ki nimo min takardunki!" Zare idanun na fara ina sosa kai nace mishi"Abba ni fa na tsani karatun boko ne!" Ware idanu yayi yana rike baki ya ce min. "Yau naga wacce bata kaunar boko, idan Mijinki ya zama.wani fa?" "Sai ya auri yar boko, tunda ni gaskiya bani gane kome na bokon nan!" Dariya abin ya bashi bayan na tab'a abincin na dauki tsarabarshi na bashi ina cewa. "Ba yawa wannan kuma gudummawata ce!" Na mika mishi, kamar da wasa Sai gashi Abba yayi ta min addu'a, kwanakin da suka biyo baya, ana ta shiri ne sosai. Ranar da aka fara biki a gkdansu amarya nima na fara nawa shirin aikin, a daren ranar Tinah ta iso na kaita har parlour Alhaji da su Hajiya, sun ji dadi sosai. Washi gari na kaita gidanmu muka wuni, sannan muka dawo ita da Sa'adiyya wani gani-gani sukewa Juna, abokinta ta biyo, amma sai zuwan ya koma nawa. Ana gobe daurin aure Abba ya kira ni. A gabansu Hajiya ya ce musu. "Ku ji da naku aikin ku bawa Ummu nawa aikin!" Mutane masu matukar kirki da mutunci suka ce. "yawwa gara da ka hada Ummu da aiki mu.ma mu ji da namu!" Haka ya aka bani aikin na shiga kitchen na amso kome na wuce bangarena, sannan aka turo min Nabila da Na'ima da kawayensu. Da Tinah muka daura aikin pepper chick. Muka kuma hada miyar jollop, washi gari muka tashi aiki kamar ba gobe yan matan nan da su muka ci Uban aiki, abinci ya kusan sauka kawai sai ga Aunty Rukayya da flat. Zata bude tukunyar Tinah da bagwaren hausarta ta ce mata. "Look me kake so?" "Abinci zan diba!" "Ba zaka saka ba, ina kake lokacin da muke aiki sai kazo kai me cin abinci!" Jin maganar Tinah yasa ni fitowa a daki ganin rukayya yasa na fahimci inda zancen ya nufa na ce mata. "Ki je ki tambayi Abba kosu Hajiya abincin nan na Abba ne."
"Eh nasan na shine na zo diba, ko ban isa ba ne?" "Gaskiya kin isa amma.ba zaki diba ba." Na fada ina gyara wutar. Fita tayi fuuu, sai ga ta tare da Maryam da Safiya Matar Ya Umar. "Ke yar uban waye da zaki hana abincin? Na kira Tafida ma yazo ya diba mana. Dama ina cike da ke yar iska mara kunya!" Inji Maryam, ban tanka musu ba, Tinah zata shiga na rike hannunta ina girgiza mata kai. Shigowar Tafida da Deen yasa na dauke kai ina cigaba da gyara murhun. Nan suka gaya mishi abinda yake faruwa. Ba don Allah yasa yazo da Deen ba ban san me Tafida zai min ba. Domin shi da Tinah kamar zasu bugu yana gaya mata ita bakuwa ce kada tayi wani abu da zai saka mutuncinta ya zube nan ta.kara harzuka. "Zuba musu abincin!" Ya fada yana takowa gabana. "Ba zata zuba ba, abinci na Alhaji ne su je su same shi ko matanshi, ai gaskiya ta fada dake su masu dangi ne shine akazo cin mutuncinta! Ba zata zuba ba!" Inji Deen, "Kai ya ishe ku Ummu Matata ce! Babu Dan iskan da ya isa shiga tsakanin mu." "Ni kuma Ummu kanwata ce babu shegen da zai ci zarafinta na kyale dan kutumar." Ai ba sai ga Tafida da Deen zasu bawa hammata isa. Da gudu nabila da Na'ima suka kai labari cikin gidan, Alhaji da zai wuce wurin daurin aure ya shigo har cikin gidan yana kallon yadda na shiga tsakaninsu. "Wai ni don Allah ya kuke so nayi ne? Abotarku na.tsawon shekaru zaku lalata saboda ni? Idan abinci ne gashi can su diba yadda suke so abu daya na sani Allah zai kamani da hakkin cin amana, ba yau na fara hidimar abinci ba, amma ba zaku yi fada saboda ni ba don Allah!" "Allah ya maka albarka Safiyyudeen! Allah ya tsare bayanka da gabanka. Abinci ni nan na bawa Ummu tayi min domin gudun fitinarku na bata, Aniyarku zata bi ku abin da kuke mata Allah sai ya bi mata hakkinta. Inda ake zuga ku ." "Abba don Allah kayi hakuri!" Murmushi yayi ya kalli Tinah ya bata hakuri cikin harshen Ingilishi, daga nan ya fita ya ce a kwashe mishi abincinsa a kai mishi cikin gidan. Haka kuwa aka yi na dauki sabin kullolina na alfarma na zuba pepper chick din, sannan na koma daki muka shirya shiga aikin cake, muna gama kwabi na bar musu na buga donut, kafin wani lokaci har na gama na kai shi rana.
A can bangaren Shuwa kuwa daura su tayi akan keken bera, tai ta zuga su tana gaya musu abin da ba shi ba ne. Karfe hudu na yamma muka gama sannan muka shiga cikin gidan bayan mun yi wanka . Dakin Inna muka shiga naga dasu Rukayya ko minti goma bamu yi ba muka fita na cewa Tina. "Mu koma bangarenmu!" "Ok!" Muka dawo, ko minti ɗaya bamu yi ba sai ga mata yuiuuuu. Hayaniyarsu ta fito da ni daga cikin kitchen na je diban abinci. "Lafiya?" Wucewa dakina Rukayya tayi tana faɗin. "bincike zamu yi bari na fara da dakinta!" "Ban gane ba?" "Shigar ku dakin nan, aka nime kudi aka rasa kuma.a inda kika zauna kudin yake!" Dariya nayi nace musu. "Bismillah!" Na koma kitchen din ina diban. "Innalillahi na gaya muku ita ce haka zuwana Abuja ta hada ni da dan uwana wai ina mishi sata, bayan ita ce take shiga dakinsa. " ba tare da na fahimci me suke nufi ba, matan nan suka rufe ni da duka, wanda ihun Tinah ya janyo hankalin mutane cikin gidan har da Tafida da suke kofar gidan, suka shigo ni kan ai na suma. Abba babh takalmi a kafarshi ya shigo parlour lokacin kowaccensu ta gudu sun bar gidan bakiɗaya. Tinah sai kuka take tana rungume. "Abba ka saka Tafida ya sake Ummu, Abba don Allah ka ce ya sake Ummu ba matar shi ba ce kashe ta zasu yi shi da Yan uwansa. Abba Tafida bayan son Ummu don Allah ka ce ya sake ta ni xan aureta!" Inji Alfah da ya shigo hankalinsa a tashe, ruwa akayi ta watsa min, kafin na sauke ajiyar zuciya. "Wallahi ban dauka ba, wallahi ban tab'a sata ba, ban iya daukar abin wani ba." Na shiga fada ina ihu, durkusawa yayi a gabana, ya janyo Ni jikinshi. "Allah sai ya saka miki, Allah sai ya bi miki hakkinki, nayi kuskuren barwa dabba ke bayan ke ce kika dace da samun mutum na gari na bawa Dabba rikonki!" "Tina rikota zuwa bangaren Kaltuma!" Ya tashi yana me kallon Tafida. "Ina son takardanta nan da awa daya!" Mai da hannunshi baya yayi yana me sunkuyar da kanshi. "kayi hakuri amma ba xan iya sake ta ba, ina son Matata!" "Tass!" Ya kifa mishi mari, duk da bana cikin hayacina sai da na juya ina kallon shi yadda ya zube akan gwiwarshi. A farkon rayuwata da naji wani irin mahaukacin matsayinsa me hade da kaunarshi da ban san yaushe ya min bazata ba. Abba sai kara marinshi nace mishi. "Don soyayyarka da Annabi Muhammad, kayi hakuri." Na isa gabanshi ina me durkusawa. "Don Allah kayi hakuri, laifina ne da ban je dakin ba, haka ba zai faru ba." "Ya sake ki tow!" Daga ni har Tafida muka kalli Abban. "Abba ina son mijina!" A fusace ya fita daga