Showing 147001 words to 150000 words out of 241571 words
Chapter 50 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
daura auren don Allah ya gani tsoron fitinar Uwar Yarinyar suke ji.
***
*Ummu*
Bayan sati guda.
Naji sauki sosai kamar ba ni ba, tun ranar da na cika kwana uku da fara jin sauki Tafida ya saka lallai aka sallame ni shi kawai Doctor Sagir ya cigaba da zuwa gida ana duba ni. Murmushi nayi ina jin yadda yake jan gashina, shi nan yana gyara min gashi na ya cukurkude. Bayan ya gama ya saka ban ya kama min su. Yana faɗin "kin san su Mama zasu zo ko?" Gyada kai nayi ina kwantar da kaina a kirjinshi. "Sadauki!";na fada ina kallonshi. "Na'am jaruma!" "Aikin gidan yayi sauri sosai!" "Eh haka kowa yake faɗa!" Ya fada yana basar da zancen. "Amma na ga kamar part biyu ne a haɗe?" Banza yayi min bai kula ni ba, haka yasa ban kara magana ba, kaya ya ciro min, na saka skirt din hannunshi ya kai ya shafi cikina yana faɗin. "Yarinyar nan yaushe zaki taimakawa bawan Allah? Ya shiga fadar zuma!" Ya fada can cikin kunnena. Ture shi nayi ina faɗin. "kai ja can ni yanzu murna nake Mamana zata zo ka kira min abin da zaka sake jika ni!" Langwabar da kai yayi yana faɗin. "A dai duba lamarin bawan Allah!" Share shi nayi na wuce abina na saka yar bra. Ina gamawa ina kallonshi ta madubi ya balle su haushi ya saka na ce mishi. "Allah ya shirya min kai..." hannunshi dukka biyu naji akan boons din, nayi kewarshi sosai ba zan iya juyawa bukatarsa baya ba, haka yasa na mai da kaina kirjinshi ina sauke ajiyar zuciya,don nayi kewarshi kamar hauka. Na azabtu kewarshi juyar da ni yayi tare da cewa. "Nayi Ummuna!" Gyada kai nayi ina jin wani abu na yawo a jikina. Haka ya shagaltar dani wannan lokacin, Aliyu namiji ne da yasan meye so, Aliyu ya iya jiyar da mace so, Aliyu ya shayar dani zumar da ba zan iya cewa ga yawan dadinsa ba. Amma dai daga ni shi har sai gamu muna wani irin kuka na farinciki da kuma kaunar juna. Ina kwance a jikinshi na ji wayata tana kara, dauka nayi a hankali. " Ummu Hadiyya!" "Na'am Mama kun iso ne?" "A'a ba zan samu zuwa na zan tafi Biu ne anyi mana rasuwa!" Da sauri na mike ina tambayarta. "Waye ya rasu?" "Munirah kanwar Rakiya!" "Allah ya mata rahama, Allah sarki jinya ya kare ki yiwa Zakiya ta'aziya, kafin na zo."
"In sha Allah zata ji, idan mun dawo zamu saka lokaci mu zo mu ganki!" Gyad'a kai nayi ina jin kamar na bisu. "Allah ya dawo da ke lafiya sai kin dawo!" "Ki gaida Hajiya da Yaran ta kwace min mijina!" Murmushi nayi mata sannan na kashe wayar. "yau baka da aiki ne?" "Eh jibi layya!" " Hmm karfi da yaji ka hanani azumi;" shafa fuskana tayi yana faɗin. "kiyi hakuri wata shekara zaki yi!" "Hmm!" Wanka muka yi ya kalle ni. "Kina saka ci da addu'a sosai, da nasan kina da yawan Ibada, yanzu kuwa kin watsar, daga ni har ke muna raye ne cikin makiya, yana da kyau ki kara yawan ibada idan ma ba zaki iya sallah dare ba, yana da kyau, ko walaha ki rike, sannna ki kara mai da hankali akan sadaka domin ita maganin masifa ce." Shiru nayi kafin na ce mishi. "In sha Allah zan yi!" Daga haka na koma gadon na kwanta. "Kin yi alola ai?" "Eh nayi!" "Taso muyi sallah!" Ban mishi musu ba, na biye shi muka yi sallah, sannan ya jima yana mana addu'a kafin ya shafa, juyawa yayi ya kalle ni da na jingina kaina da gadon, barci nake. "Lazy girl!" Ya fada yana mikewa, daukata yayi ya gyara min kwanciyata, sannan ya zauna a gefena yana shafa hannuna da ya riƙe, yana zaune a wurin, ajiyar zuciya ya sauke. A hankali yayi ta jiyo hayaniyar masu aiki. Gyara kwanciyarshi yayi kusa dani, a hankali barci yayi gaba da ni.
*Deen*
Ance duk tsanani yana tare da sauki, anyi nasara aikinsa, sai dai tunda ya farka ya ga me kula da shi ya ce mishi. "Ina son barin kasar nan taya zan fita ba tare da matsala ba? Sannan ka gayawa wanda ya kawo ni baka san inda nake ba. Ina son na bar kasar nan yau zan karasa jinya a wani wurin." "Tow ina zaka sir!" Murmushi yayi ya ce mishi. "wata ƙasar!" Ya fada, yana kwance. "Amma ba zaka iya tafiya ba?" "Kada ka damu zan iya!" Deen ya sauka akan gadon. Jikinshi babu kwari, ya cigaba da cewa. "Yau nake son barin garin nan!" "Ok!" Haka mutumin ya fita Deen ya duba kayanshi, ya ga kome a cikinsa kafin mutumin ya dawo ya cire musu kayan majinyatar ya fita, yasan tunda ya rayu tabbas za a iya bibiyarshi. Kuma idan suka kama shi kashe shi zasu yi, duk wannan abin ana yi ne domin Tafida ba don Ummu ba ne, akwai abin da ya manta akan Tafida, ko lokacin da Tafida ya zama ɗan majalisa bai samu masu bibiyarshi ba, amma lokacin da mutanen suke sararshi yaji daya yana faɗin. _idan muka kashe wannan samun gurbin shiga rayuwar Tafida mai sauki ne, wannan shine kofar Tafida_
Shiru yayi lokacin da yayi nisa da asibitin, yasan zasu iya bibiyarshi don haka yayi wasa da hankali mutane kafin ya wuce inda ya hau jirgin Kashmir, akwai wani malaminsu wanda koyarwa ya kai shi Sudan, idan har yadda ya ji labarin ya bar sudan tow yana Kashmir ba makawa, don haka ya bi address din malamin, tafiya ce da suka kwana, da safe suka isa, ba tare da ya sha wuya ba, ya gano gidan kasancewar Malamin gidansu manyan mutane ne, yana fadar sunanshi aka kai shi har gidan Malami, cikin farin ciki Malamin ya karbe shi, nan suka gaisa kafin Deen ya bashi labarin abinda yake faruwa. "Gaskiya abin da zan gaya maka, shine ka koma ga Aliyu, idan ka cigaba da gudu zasu cimmaka, idan har kana son Aliyu ya samu nutsuwa ka boya a bayanshi yadda zaka kara zakulo mutanen da suke bibiyarshi!" "Naso haka amma ina tsoron kada haka ya zame min matsala ne!" "Ba zai zame maka matsala, abin da zaka yi zan nima maka ticker din gida, amma zan fara gayawa Aliyu" asalin layin da iya Deen yasan Tafida yake da shi babu number kowa Deen ya bawa Malam Anwar.
*
A can asibiti kuwa, wasu kartine majiya karfi, lafiyayyu kosasu suka isa asibitin tare da shaidawa shugaban asibitin sun zo sauyawa Deen asibiti daga gwamnatin jahar Borno. Ba musu aka kai su dakkn. Abin ya basu mamaki lokacin da aka samu babu Deen babu alamarshi, abin da ya d'aga musu hankali kenan suka fita niman shi kamar karanuka.
***
*Ummu*
Kallon Tafida nayi da yake ta barci, hankalinshi kwance. Ban daki na shiga nayi tsarki sannan na yi alola na fita, saboda sallah azhar da yayi, shima shafa mishi kai nayi ina faɗin. "Barka da rana yallabai!" Bude idanun yayi na sakar mishi murmushi. "Ummu!" "Na'am wayata a kashe take ko?" "Eh ka kashe hala!" Da sauri ya tashi zaune, ya bude drower din gadon ina kallonshi ya dauko wata Nokia, kunnata yana jin wani iri a jikinshi. Kurawa wayar idanun yayi, "wani abu ne?" "A'a kawai ji nayi kamar Deen yana cikin matsala!" "Lokacin sallah yayi kayi alola ka zo."
Ihun Sa'adiyya ya sashi dafe kanshi, a hankali ya wuce ban daki tana ihu da nimanshi. Ina sallah naji ihunta kamar zata fasa gidan, ina idarwa nayi addu'a sannan na mike ina me barin dakin bayan na gyara inda muka kwanta. Bude kofar nayi kamar zata shige da ni, da sauri na bata hanya. "Ina yake? Akan me zaka min kishiya da yarinyar da ka gama isksmci da ita? Akan me zaka ci mutumcina?" Waje nayi ma barsu, sai dai ban yi nisa ba naji ya buga mata tsawa, sai da na diririce. Jikina yana rawa na wuce bangarena, na zube a parlour. Saadiya fitina ce bata kaunar zaman lafiya, ihunta da ke ki yasa na ji a raina dukanta Tafida yake, yadda jikina yake rawa na fito, ganinta nayi ta cukume mishi rigarshi a gaban Mutane, mamaki ne ya kashe ni don ga Hajiya a gefenta. "Sake shi ki tafi kafin a gama miki gyaranki!" Kamar arziki ta sake shi tana huci. "Ummu Hadiyya! Kina tsammanin kin samu wuri har da wani cikin ko? Tow nima zan dawo kuma sai nayi cikin nan na nuna miki babu abinda zaki yi min!" Murmushi nayi girgiza kai nayi ina faɗin. "Ina fatan ki dawo dakinki lafiya, ki zo ki ta haifa mishi yara masu kyau irin shi!" Na fada ina barin wurin, ban san me yasa naji a raina gara ta dawo, babu rana da ba zan ga takaici a fuskar Tafida ba. Gyalenta ta sab'a a kafadarta, yadda kasan yar tasha haka take ita bata da nutsuwa ne kawai amma mace ce sai dai rashin mutunci kawai. Ina kallonta ta window ta shiga cikin gidan tana dubawa, tana gamawa ta fito ta bangarena, tana kallon kofata sake labulen nayi, ina zaune naji ta bude kofar parlour. "Kuma Tafida ne ya zuba miki kayan gida haka?" "Eh!" "Kambu idan bai zuba min ba wallahi zai ga rashin mutunci!" Tashi nayi na shiga kitchen na kawo mata ruwa da juice. Na koma na zuba mata cin-cin da cake, wanda Fanna da Hajiya suka yi saboda bikin sallah, aka kawo min nawa. Ci ta fara tana zare idanu, "kuma don munafunci me yasa kika ce sai ya auro Asiyah? Ke yarinyar nan ban yarda da ita ba, kuma ban zo nan don mu hada kai ba na zo na miki kashedi ne idan kika sake ta kara shigowa da iskanci sai na hada dake da ita naci.."
"Zo ki fita min a gida!" Ya daka mata tsawa, kusan Allah sai dariya take bani ina dannewa. Ta cika bakinta da cake ta ce mishi. "Kasan Allah babu inda zanje yawwa sai ka gaya min dalilin da yasa ka amince zaka auri wancan yar iskar yarinyar, ni ban isheka zama gaban mota ba? Ko an gaya maka i don't know what is going on? Look Tafida dole a fasa auren nan ko nayi muku rashin mutunci kuma a kammala min aikin gidana a zuba min irin kayan Ummu, sannan nima wurinka zan tare" dole na fashe da dariya don na fahimci babu amfanin tashin hankali akan irin saadi baby.....
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opayar
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH
*Gidan zafafan kayan Mata masu kyau da inganci na yar mutan sokoto maman Yusuf likitar Mata,*
*Bayan kayan Mata muna tura abubuwan da zasu amfanemu game da Zaman auren da wasu magungunan da zaku iya hadawa da kanku da sauransu*
47
Idan na ce muku yarinyar nan mahaukaciya ce, kada kuyi mamaki domin karfi da yaji bata da hankali. "Yawwa kayiwa Ummu ciki ni sai yaushe zaka min cikin nima?" Wulakantaccen kallo yayi mata yana nuna mata hanya, ta ce mishi. "Ba fa inda xan tafi na gaya maka!" Wucewa wurin kayan kallo yayi ta ga haikan wayar wuta zai dauka, da sauri ya fice a parlourn na kwashe da dariya, ina nuna shi da yatsa. "Ango ango!" Zuba min idanunshi da suka ji jajjur yayi, ganin yadda yake kallona na rike kunnena. "Kayi hakuri!" Na fada a hankali, takowa yayi ya gabana ya durkusa. "Ummu!" "Wannan lamarin ba na wasa ba ne" "na sani Daadi!" "Baki sani ba, don bake kike jin zafin ba ko?" Saka hannunshi nayi a kumatuna nace mishi. "Kayi hakuri!" " ba fushi nayi ba amma ya mata ki fahimci wani abu yarinyar nan bata da amfani a rayuwata!" Kallonshi nake wani dakika kafin nayi murmushi. "Idan akwai wanda zai ba da labarinka, daga Deen sai ni" na fada ina cizon bakina na kara kallonshi da kyau. "Har yau kina tuna abinda nayi miki ko?" Murmushi nayi ina girgixa kai. "Ai na manta da shi,domin nasan dole wata rana za'a iya tuna maka, amma Ni bana son a tuna maka don har abada ya wuce." Zama yayi yana kallon yadda nake wasa da wani zaren mayafin kayana. "Me yasa kike boye abin da yake damunki?" "Ni!" Na nuna mishi kaina kafin na girgiza kai ina faɗin. "Ni ba zan ajiye kome na tuna ba!" "Kina kullace da ni kenan har yau? Ummu shi yasa kika yi draging dina na auri Asiyah?" "Me kake fada ne? Ka ga ni ba haka nake nufi ba amma yana da kyau ka yarda da ƙaddara me kyau ko mara kyau sannan ni ban saka ka dole auren Asiya ba, abin da nake ji a raina ya wuce wasa, idan ba zaka auri Asiyah ba shi kenan amma ka daina zargina da turaka auren Asiyah!" Yadda ga na koma ina magana sanyi -sanyi ya sashi rike hannuna yana faɗin. "Ok shi kenan ya wuce, amma!" Shafa fuskarshi nayi nace mishi. "Fatana kayi mana adalci!" "Ki tafi dakina ki dauko min kayana ba zan iya fita da wannan kayan ba!" Murmushi nayi ina kallonshi. "Shi kenan." Zan tashi ya mai da ni yana cewa. "Koma ki zauna na fasa. Ni gobe arfa ko yau ne? Ciwonki ne yasa ni na daina azumin nan fa!" "Muje sauya kayanka!" Na fada ina me riko hannunshi. Muka fita tare, Sadiya na tsaye a ginin da yake yi, ware idanun yayi akanta bai tab'a ganin mutum mara jin magana irin sadiya ba. Bai kulata ba muka wuce ashe tana binmu. "Ke Ummu wai ke bakya gajiya da namiji ne? Abu daya ba zai tab'a gunduranki ba ne!" Ban kulata ba domin kamar bani da abin yi ne, har parlourn ta biyo mu. "Aliyu wai meye matsalarka da matsayina na first lady ne?" Duk da bai son kulata amma sai dai wannan karon zuba mata idanu yayi ya wuce dakinshi, tana tsaye a parlour ni ina kitchen, sai tijara take mishi. Ina cikin aikina naji, gudun kamar za a tashi gidan, dariya abin ya bani. Na fito na hango shi daga shi dai farin singlet da dogon wando. "Yanzu don Allah meye ribar haka?" "Ummu idan ba zaki iya saka baki Sadiya ta fita a rayuwata ba, ki daina nuna min baki damu da ni ba. Taya yarinyar nan zata na Abu kina dariya?" Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa. "Tow kayi hakuri na zan kara mata dariya ba." Sai kuma na tsinci kaina da yin dariyar saboda yadda yake haki da masifa. "Wato ga mahaukaci nan?" Girgiza kai nayi xan yi magana muka ji kar'ar waya zubar da abin hannunshi yayi ya wuce dakin domin ni dai ban tab'a jin karar ba sai yau, yana shiga ya dauki wayar yana kallon number da yake kan kiran, kafin ya saka a kunnenshi. "Hello!" "Aliyu Muhammad Jadda!" "Malam!" Ya fada da dan karfi. "Aliyu kana nan ashe?" Nan suka shiga gaisawa, kafin ya gaya mishi abin da ya faru. "Ina Deen din?" "Gashi nan!" "Ya jikinka?" "Da sauki! Tunda abin ya zama haka, kokarin barin India, mu hadu a sudan wata sati!" "Shi kenan!" "Tafida ya za'a iyalina, akwai matsala akanka da iyalinka, babban damuwata na dawo koda ace ba xan iya muku kome ba!" "Deen ka bar India yau, ka wuce Sudan!" "In sha Allah!" Kashe wayar yayi ya juyo yana kallona. "Deen ne!" "Alhamdulillahi! Ya yake?" Zaunar da ni yayi yana faɗin. "Rayuwarshi tana cikin hatsari ne, saboda haka nace mishi ya nufi Sudan zaki raka Ni?" Gyada kai nayi ina faɗin. "ina ne ba xan bika ba!" Shafa kaina yayi, yana faɗin. "Ina cikin farinciki sosai amma bana son na nuna haka a waya gara na nuna mishi a zahiri!"
"Allah sarki!" Na fada a hankali ina kallonshi yadda yake zama a gefena.
-- Tuni aka saka lokacin auren Tafida da Asiyah, sai dai yadda Tafida yake hidimarshi a raina cewa nake gulma ce, domin maza dayawa irin wannan lamarin ya taso zaka rantse da Allah basu son auren daga baya ka ga yadda suke rawan jiki. Sannan ma ai ba wani abu ba ne, amma Tafida kamar an hada shi da mutuwarsa, haka aka yi bikin sallah layya wanda shine karo na farko da muka yi a matsayin Manyan ni matar gwamna da shi kanshi muka tafi massalaci, inda aka ware min gwanin ban sha'awa ni da Yarana har da Hajiya d Fanna bakiɗayanmu gidan Nana Asma'u da Humairah. Kwana biyu a tsakanin bayan sallah, yana wurin aiki su Maryam suka zo, ina bangaren Hajiya, dake ban san me ya sa ba ni dai na tattara kaso hamsin na zamana a cikin gidan wurin Hajiya nake zama, Hajiya bata da matsalar kome. Ina jin sallamarsu na mike daga kwance ta ce min. "Kwanta abinki ai ba baki ba ne a gidan!" "A'a Hajiya na tuna ya bani aiki nazo na kwanta." "Tow shi kenan!" Ta fada tana kallonsu, zama suka yi kamar wasu na kwarai. "Lafiya!" "Lafiya lau Hajiya, dama mun zo gaishe ki ne!" Suka yi shiru tasan dai ruwa baya tsami banza. "Na gode!" Ta mike zata dauki dan karamin dish da tabawa su Mufida abinci. "Hajiya dama akan maganar auren Autanki ne, shine muka ce ko zai bamu hada kayan amarya da sauran matanshi." "Ai tuni ya bawa Ummu Hadiyya da Kawarta! Baku da labari ne?" Ware idanu suka yi suna faɗin. "Hakika Hajiya ba a kyauta mana ba, muna yan uwan Tafida, taya za a bawa wasu hada kayanshi, musamman Ummu Hadiyya da kowa yasan ba zata hada abin arziki ba, idan ma bata hada abin da zai saka kowa b'acin rai." "Allah ko? Tunda haka ne gara na ga b'acin ran. Kaf duniya Tafida bai da sama da ku amma kuka kware mishi baya, don haka kowa ya tashi ya bani wuri." Kasa da Murya Rukayya tayi tana faɗin. "Hajiya ki kara hakuri, wannan karon zamu baki mamaki zamu jira shi ya dawo sai mu roke shi ya taimaka