Showing 72001 words to 75000 words out of 241571 words

Chapter 25 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14701

yayi yana faɗin. "Abba ni danka ne har abada ba zan tab'a juyawa bukatarka baya ba!" "Ka zauna da Tafida koda bana raye ka zama dan uwa, Uba, Uwa, kamar shakikinsa!" "Abba kana raye in sha Allah zan zauna da shi!" "Na gode da ban yanke hukuncin kai tsaye ba, na kiraka na san zaka fini sanin wani abu na gode sosai Deen!" "Ba kome Abba!" Sun yi hira sama sama sannan yayiwa Abba sai da safe ya nufi bangaren Tafida, ya buga kofa. "Ka shigo!" Shiga yayi ya same shi ya zauna rashe-rashe, yana kallon abincin da Sa'adiyya ta girka. "Zauna kaci!" "Allah ya rufa min asiri, abincin Ummu ne nake iya ci zuciya daya salon a saka min wani abu!" "Bana son tashin hankali!" Inji Tafida yana kallon abincin. "Wai me yasa na zaka koma bangarenku ba,.nan bangaren Ummu ne fa!" "Me zai hana ka ɗauke ni ka mai dani bangarenmu tunda na kanwarka ne nan din!" "Allah ya baka hakuri!" "Mtseew!" Ya ja tsaki yana hararan abincin. "Muje ka raka ni asibiti!" "Waye ba lafiya?" Sake baki Tafida yayi yana kallon Deen da yayi tambayar hankalinsa kwance. "Ni ne ban da lafiya!" "Allah ya baka lafiya ka tafi Sa'adiyya ta baka magani!" "Idan zaka tashi muje naji me yarinyar can ta dauke ni muje idan ba zaka ba naje da kaina!" "Allah ya huci zuciyarka, gaskiya ba inda zani!" Ya mike zai fita, "Ok zan je da kaina!" "Better!" Inji Deen yana kunshe dariyarshi, haka suka rabu, Tafida ya nufi asibitin, Deen yana biye da shi don yadda yake tukin hauka kada ya ja musu magana kuma ya hana kowa binsa. A hargitse yayi parking motar ya shiga asibitin, ana ta gaishe shi bai kula kowa ba.
*UMMU*
Ina shan magani na ji an banko kofar dakin, ba ni ba hatta Mama sai da ta firgita. Rintsa idanuna nayi na bude shi akan Tafida. "Mama!" "Na'am Aliyu!" "Kin tambaye ta yaushe zata dawo dakinta!" Shan ruwa nayi abina domin nasan ita kanta bata da amsar tambayar da ya ce ta min. "Ummu!" "Akan me yasa ka dame ni ne? Kai kace ina haihuwa zaka bani damar nayi rayuwata ni ɗaya dauke Yaranka idan don sune zaka dame ni!" Na fada ina hade rai, tashi Mama tayi zata fita ya ce mata. "Don Allah ki tsaya ta saurare ni!" "Bari na baku wuri!" Fita tayi ya ja kujera yana faɗin. "Nayi kokarin koyawa kaina dauke kai akanki, amma na lura zaki mai dani dan iska ne!" "Wannan matsalarka ce ba nawa ba, na gaya maka ba yau ba ni idan na tsaya akan kalamai na ba zan tab'a sauka ba kace karya nake!" "Ummu ki dawo dakinki!" "Baka mummuna gajeruwar mace, yar Mace, yar talakawa ko ba haka ba? Ni bani da gata sai Allah amma ba xan tab'a komawa gidanka ba kaje na yafe maka amma gidanka ku kare kalau da danginka." Sake baki yayi yana faɗin. "Ummu Hadiyya!" "Na'am!" "Ki koma dakinki umarni na ne!" "Ba zan koma ba, idan ka dage kuwa na koma zan tafi inda ba zaka kara jina ba!" Na fada ina sauka a gadon. "Kina nufin zaki bar ni kenan?" "Ai dama tuni na barwa masu kaya kayansu, su yi sama sama da shi!" "Ummu ni Mijinki ne nake baki umarni!" "Kai ma baka ji umarnin Allah da na iyayenka ba, sai me don ban ji naka ba, Mallam idan ka tafi gida ka aiko min Deen da sakina. Na fara zawarci!" Mikewa yayi cikin wani irin zafin nama ya fisgo ni. "Idan na sake ki Allah ya tsine min ke babu shegen da zai shiga min gonata ko waye sai na kashe shi!" "Hmmm! Na gaya maka gaskiya kenan na gama zama da kai!" Kafin ya bar dakin muyi fada kaca-kaca, abin har mamaki yake bashi yaushe bakina ya bude da har na iya fada haka, bai yarda nice nayi fadar ba koda ya fita tsayawa yayi jim kafin ya bar asibitin. Domin na gaya mishi na bashi nan da kwana hudu ya sallame ni ko ya ga tijara. Fadar da muka yi sai naji kamar an sauke min wani irin nauyi da yake kaina da zuciyata, Mama kuwa bata min magana ba, domin tana jin yadda muka yi fadar tana jin yana faɗin yaushe bakina ya bude haka har na ke maida mishi maganarshi. Na kuwa gaya mishi tun lokacin da na fahimci bani da mai tsaya min sai Allah, bakina ya buɗe. Wannan maganar ya bashi haushi, inda yace ina nunawa Allah yana tare da shi wato shi shaidanune a tare da shi ba Allah ba! Ni kuwa nace mishi abin da ya min a zamanmu na yafe mishi idan kuma na cuce shi Allah ya saka mishi, shine ya bar dakin a fusace.
Washi gari
Doctor Sagir ya sallame ni da magani masu yawa, sannan ya bani shawarar yadda zan kula da lafiyata, Mudan ya kawo mu har gida, sannan muka shiga makota da abokan arziki na ta zuwa min gaisuwa, haka ko a cikin gidan Matar kawu gwani ma ta shigo suka gaishe ni.


Tuwon alkama Ummi ta kawo min, miyar yauki, naci na koshi nayi wanka na kwanta bayan na sha magani. Tuni barci yayi gaba da ni ban farka ba sai azhar, Allah ya zo yaran ana basu madara kuma ana hada musu da nono,sun sha sun koshi sai wasa suke, bayan nayi sallah ma ka basu nono suka sha. Wurin karfe biyar na Yamma Abba ya kirani ya min ya jiki sannan ya gaya min abin da yake tafiya nayi godiya sosai. Hajiya an kawo ta kuka kai tsaye asibitin Doctor Sagir aka kaita, sosai suka tsaya akanta da kulawa ashe ciwon sugar ne, nan da nan aka daurata akan Magani.


Sosai nake samun kulawa daga ɓangaren Mama da Ummi. Sai Mama Amina kafin mu yada wanka tuni nayi wani kiba har da kumatu, cikina kuwa Mama ta sani nayi ta matse shi saboda kada tumbi ya zauna min, tunda muka bar asibiti ban kara jin labarin Tafida ba gashi har muna niman sati biyu da dawowa gida, amma babu labarinsa.


***
*TAFIDA*
Tafiyarshi Umara daga shi sai Sa'adiyya, duk da sun zo Umaran amma kuma bawan Allah nan niman shi tayi ta rasa kuma ai dama ba daki daya suka sauka ba, haka yasa ta fara zargin ko ya zo da mace ne Umrah kamar yadda yayiwa Ummu ai kuwa shaidan ya kawata mata kome Tafida da mace yazo Umaran bayan ita.....
*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML*


*Ina mata yan yayi shin ko kun san kayan da Ummu take amfani da shi, yana fitowa ne daga shahararren Shagon nan na R&U Exclusive Kitchen and More! Kayan kitchen ne na gani na fada ina iyayen Yan mata ina iyayen Kwailayen ga dama ta same ku, Uwargida da Amarya, Budurwa da bazawara maza ku fito ga kaya nan sayan na gari mai da kudi gida. Kayan mu daban da na shago!*
#Mai_Dambuhttps://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


*Sa'adiyya*


Bata taɓa sanin cewa tana da zafin kishi ba sai yau, babu Tafida babu me kama da shi yana can hotel da karuwan da ya kawo, wani irin kuka ta saka tana me daura hannu akanta, wiwi take kuka kamar ranta zai fita, tayi kuka har ta godewa Allah ta kuma yi rantsuwa matukar ta ga Tafida da mace sai ta kashe ta, haka yasa ta fita daga masaukin ta nufi waje, tafiya take tana bin mutane da idanun ko zata yi sa'an haduwa da Tafida amma bata same shi ba, babu me kama da shi. Banda asara bata da wani amfani zuwanta Umaran don ba ibada take ba. Shi kuwa Tafida dawowa yayi harami da zama yana jin kamar duk inda zai zauna babu inda ya kai wurin dad'i, abu na farko da yake zuwa mishi a rai Ummu ba zai taba mantawa ba zuwan da Ummu anan ta tab'a ganinsu da SA'ADIYYA amma ta dauke kai kamar bata gansu ba. Wata balarabiya ce ta ajiye jakarta tana mishi larabci, a hankali ya amsa mata kasancewar a sudan da yayi karatu kuma sai ka nazarci harshen larabci kafin ka fara karatu infact yana jin luggatul Arabia. Ai kuwa kamar ta ga dan uwanta suka shiga larabci tana tambayar shi shima Balarabe ne ya ce mata a'a daga Afrika yake. "Allah ya tona maka asiri karuwa ma dauko!" Ta yi maganar da karfi, tana nufar balarabiya, mikewa yayi yana fadawa balarabiyar zai tafi dama yana jiran Matarshi ce. Ya finciko Sa'adi da take ihu tana tutture shi tana ihu. Bai san lokacin da ya kifa mata mari ba, ai kuwa tayi tsit. "Ki wuce muje jaka!" Ya fada a matuƙar fusace, sannan yayi gaba mutane sai kallonsu suke musamman tsirarun hausan can, tun tana daurewa har ta kasa tana bin shi tana kuka. Masaukinsa ya wuce ta shige dakinta. Ta kira Uwarta tana kuka wiwi da kyar ta iya gaya mata marin da yayi mata. Kashe wayar tayi ta kira Tafida, da yake wanka bai san tana kiran ba har ya gama ya fito yana zaune ya ga kiran. Dauka yayi yana faɗin. "Lafiya?" "Me tayi maka ka mare ta?" "Da alamu baku mata tarbiyya yadda ya dace ba ne, sannan bata san girma da daraja irin na mijin aure ba." "Kai din tarbiyyar ce da kai!" "Koma dai me zaki ce ni nan renonki ne, ai kin san bani da tarbiyyar kika bani aurenta marasa tarbiyya ne suka hadu kin ga ai ba wani abu bane tayi min na mata!" "Aliyu!" "Me zan miki?" "Idan ka sake taɓa min Y'a sai na maka ka kotu!" "Allah ko? Ashe kuwa yanzu zan fara dukanta idan kin so ba kotu ba kuliya zaki hada ni da shi. Babu ruwanki da gidana ita yarki ce ni surukinki ne!" Daga haka ya kashe wayar yana tsaki, shi fa babu wanda ya isa mishi ganganci ya kyale. Yana gama jin haushin shuwa da Yarta ya kira Ummu. "Hello waye wrong number!" "Ke!" "Waye kai Malam?" Ta tambaye shi, yadda tayi tambayar a wani sanyayye da shagwab'a, yanayin maganarta amma shi gani yake kamar da gayyya tayi mishi wannan maganar. "Ummu Hadiyya!" " Ai kai ne?" "Eh!!" Ya bata amsa yana shafa kanshi. "Idan na dawo ki bani lokaci na zo mu tattauna kin ji!" "Akan sakina ne?" "Ummu Hadiyya!" "Ni ba sake ki zan yi ba, ki dawo dakinki!" "Ba zan dawo ba fa." "Me yasa baki jin magana Ummu?" "Ayya ai kuwa koya nayi!" "Daga waye?" "Oho!" "Tow yayi tunda oho ya koya miki mugun abu!" "Hmm zan kwanta kaina yana ciwo;" "Ummu!" "Don Allah ka kyale ni!" Ta kashe wayar. Bin wayar yayi da idanun kamar yana son hango Ummu ta wayar. Kiran sallah ya katse mishi kallon wayar ya shirya ya fita, a bakin kofar dakinshi ya ganta. Wani matsiyacin kallo ya watsa mata. "Ina zaka wallahi sai na bika?" Magana yaƙe son yayi amma kamar an rufe mishi baki ya dauke kai kamar bai san tana wurin ba, ya wuce haka ta biyo shi yana tafiya tana bin bayanshi. Sai kallonsu ake. Har massalaci ya wuce bangaren maza ita kuma ta wuce bangaren mata, tunda ya shiga Masallacin bai fito ba sai da aka yi sallah isha sannan ya fito a bakin kofar ta ganta tsaye. Kamar bai san tana wurin ba ya wuce abinshi haka ta bi bayanshi. Haka suka iso hotel din ya wuce restaurant ya zabi abinci, bai kulata ba ya amsa mata suka juya, ita nan tana bin shi ne don ta ga wacce ta biyo shi, girgiza kai yayi yana tafiya, har ya wuce dakinsa ya ajiye mata abinci. A bakin kofar dakinta, yana shiga dakinsa ya ajiye abincin ya zauna yana me hade hannunsa biyu wuri guda. Wayarshi da ya bari a parlour ya ɗauka a hankali ya shiga niman number Abba don har ga Allah yasan Abba kadai Ummu zata saurara. "Assalamualaikum Abba!" "Tafida dare yayi!" "Eh na sani amma zan tuna maka maganar Ummu ne!" "Ikon Allah Aliyu dama nayi maka alkawarin zan shiga maganarku ne?" "Amma Abba!" "Kasan bani da lafiya kuwa?!" "Innalillahi sannu Allah ya baka lafiya, yaushe xaka samu Ummun?" "Kai sai da safe!" Abba ya kashe wayar, bin wayar yayi da sauri yana kallonta. Nan ma ya kara kiran Ummu. Sai da ya kusan tsinkewa ta dauka. "Wai don Allah waye kai ne ka dame ni?" "Allah ya baki hakuri Ummu ya Yaranmu?" "Yaranka dai ni kuma na isa na haifi kyawawan Yara irinsu ne jiki duk baki kamar bayan tunku..."
"Kin ga ban kira ki muyi rigima ba, na kira ki na tambaye ki yaushe zaki koma dakinki!" "Ni dai ba zan koma ba!" "Me yasa kike min haka ne?" "Me yasa ba xan maka haka ba? Tafida ka fita idanuna na rufe ko na maka rashin mutunci!" Ai kuwa ya hau shima ganin zai fara mata hayagagga yasa ta kashe wayar bakiɗaya. Takaici kamar ya ciji kanshi, yana cikin wannan takaicin Sa'adiyya tayi ta buga mishi kofa. "Uban me zan miki?" "Na ji kana magana da mace ne shi yasa na ke buga kofar kada a dauko karuwa!" Kuri yayiwa kofar tabbas yarinyar nan ta ga gadon barcinsa. "Idan na dauko ƙaruwar ai ba sabon abu bane. Tunda kema kin tab'a harkan kenan!" Wayyo Allah na, ji tayi kamar zata hadiye ranta. "Zargina kake?" "A'a ni bana zargi a rayuwata sai dai na gaya maka abin da kake aikatawa, sannan ba xan yi zargi na lalata aurenmu ba, wai na tuna miki kin tab'a biyo ni muka kwana gado daya, kika ce nayi miki!" Wani irin dukar kofar tayi, ya sake murmushi yana kallon kofar tabbas shi a duniya babu wanda zai cinye shi da baki domin Allah ya bashi baiwar magana sannan bata isa ta gaya mishi magana ya kyale ta ba ko da kuwa kwaya yake sha. Washi gari tun karfe uku ya nufi harami yayi dawafi, ya tsaya gaban dakin Ka'aba yayi addu'a sosai. A karon farko da yaji yana son yayi iyayenshi da Yaranshi da zamansu da Ummu, sannan ya kuma mika lamarinsa da na mukamin da ya samu,sai dai duk da haka ji yake kamar yayi missing wani abu me muhimmanci a rayuwarsa, duk addu'ar da yayi amma yana jin kamar akwai wani wawakeken rami a zuciyarsa da bai cika, Sa'adiyya da yake ganin itace zata kawo sanadin farin cikinsa ashe ba haka ba ne. Gashi tun ba aje ko ina ba ya fara gajiya da halinta. Ita kuwa Ummu yar renin hankali ce fisabiilillahi akan me zata wani dauki zafi ai ya dace tayi hakuri ta dawo dakinta, don ta samu yana damuwa da ita, tsaki yayi can kuma ya tsaya kafin ya samu wuri ya zauna yana kallon dakin Ka'aba haka yana ganin lokacin yadda tayi ta dawafi yana ganin yadda take kuka sai ji yayi tsigar jikinshi ya mike yarrr "ko me ya sata kuka?" Ya tambayi kanshi, tsaki yayi a karo na biyu yana faɗin. "Ta cika sakalci haka kawai ma kuka take kamar cry baby!" Ya fada shi daya kafin ya ware manyan idanunshi yana murmushi ya ce . "Yanzu da ta zama Maama ya zata daina kuka ko zata cigaba?" "Barka da asuba!" Wani ya fada mishi yana murmushi, zama mutumin yayi Tafida ya mika mishi hannu suka yi musabaha. "Yawwa Barka dai!" Suka yiwa juna murmushi. "Ban gane ba?" "Eh nima na ganka ne kawai sai na ga kana murmushi kana magana kai ɗaya, nace Allah yasa ba Madam bace ta hada maka kafi Malam!" Shafa kai Tafida yayi yana kallon Mutumin ya ce mishi. "Eh wallahi tana can rigima take ji, na bita taki saukowa hala so take taji na rataye kaina."
"A'a baka bita ba dai, ita mace yar riritata ce da zamu yi hakuri da halinsu tabbas da tuni an manta da wuri, ni da ka gani mata na hudu kuma kowacce ina zaune da ita da halinta mutum daya ce take bani ciwon kai, kuma kaf dangina da duk wani na kusa dani sonta yake saboda halinta da kirkinta. Sai dai har yau sama da shekaru goma sha biyu Allah bai bata haihuwa itace Uwargidana, amma kasan me? Duk matan da nake aure a bayanta sun haihu. Ba don na tsaya akanta ni da Mahaifiyata ba wallahi da tuni bana tare da ita,saboda fitinar mutane kai sai da ta kai ta kowa na rantse da Allah duk wacce ta mata gorin haihuwa na gama zama da mace har abada, idan kuma kai dangina ne na datse alakarmu da shi, Alhamdulillahi Ubangiji ya ga nufina ya kuma bani ikon samun galaba akan kowa domin ina sonta ina kaunarta ban yarda wani ya tozarta min ita ba, ni nasan darajarta ni nasan amfaninta a rayuwata idan ba bari ya wani ya tozarta min ita ni nayi asara, Ina kuma girmama duk wani abin da zai fito daga gare ta. Yanzu haka Umaran da muka zo a tare da ita muka zo da Amaryata." Bakiɗaya Tafida kallon Mutumin yake gabanshi yana tsannanta bugawa, a hankali ya cewa Mutumin. "Gaskiya ka mata adalci ka kuma hana wani ya tozaratta, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba itama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login