Showing 132001 words to 135000 words out of 241571 words

Chapter 45 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14721

ka duba wannan." Ya mika mishi wata takarda ya cigaba da cewa. "A lokacin da muke saran shi ya ce na baka." Amsa yayi yana kallon takardan kafin ya warware. _Kai mahaukaci! Ka sani yadda kake yiwa Ummu barazana! Na saka ka ka fada tarkona! Shi yasa na fito maka a mutum kai kuma dake jaki baka gane kome daga mata dai mata, baka iya lissafi irin na maza! Daga lokacin da kayi wani motsi! Mutane na suna kallonka! Kana motsi ban san wani irin yanayi zaka tsinci kanka ba! Mahmoud kana tab'a Ummu kai ma za a tab'a ka, domin na bada sako a bawa Ammyn na yadda kake lalata yar mutane! Kasan me? Duk motsin kowa yana sane musamman shashsha irinka. Ka hada hannu da mutane dayawa kowa ya juya baya saboda shakkar abin da zai faru, amma ka tab'a hijabin da ba naka ba! Ka duba Email dinka ka huta lafiya ko mutuwa nayi Ummu ta tsira idan kuma kana son Mahaifiyarka ta gano cewa kai din na musamman ne maza maza ka duba zaka ga abin mamaki kai jama'a duba_


_Flashing back!_


Ranar da Deen ya ware manyan masana akan cyber security ya dauko duk wani number da Tafida yake amfani da shi ya tafi har kamfanin Mtn ya karba, sannan ya kira Jabir Adam da dare. Bayan sun ci abinci ya mika mishi file yana faɗin. "Bana son kowa ya gane kai na musamman ne a gare ni! Wadannan numbers din, ka fahimci me nake nufi?" "Na fahimta amma maganar gaskiya sai dai ka ware laptop din da zan yi wannan aikin kasan muma ana bibiyarmu!" "Shi kenan gobe kazo ka amsa!" Haka Deen yayi bai tab'a yin abu bai gayawa Malam Zailani da Abba, su kuma suka mara mishi baya, haka yasa kome suna sane da shi, wasa gaske Deen ya saka idanu akan aikin a kaf numbers din babu matsala, sai number Sa'adiyya da Mahmoud da aka samu yawan kira a tsakaninsu da musayan sakonnin, tare da wasu bidiyo kazamai, a binciken ne ya suka hango videon da ya boye don razana Ummu, sannan shima Deen ya kara da wani irin bincike, a cikin gidan ya haɗa da masu yin aikin gidansu Mahmoud da drive da kome ya basu kudi me yawan gaske, tare da ce musu kawai su dauko mishi duk wani abu na tsiyar da Mahmoud yake, sannan kuma Deen ya kara bugan cikin Alguburo ya gaya mishi Mahmoud yana lalata yarinyar da take aiki a gidansu, haka yasa Deen yasa aka bibiyeta, da haka da hikima aka samu video daga ɓangarenta da kome, Deen ya shiga rayuwar Mahmoud ya zakulo kome, dama tun can yasan yana halinsa da son mata, a hankali ya cigaba da bibiyarshi, a lokacin da ya kara kama Mahmoud ya bar abin sai ya tab'a Ummu, kuma abin da ya faru kenan. Har zuwa shirin Deen da abin da cigaba da bibiyarshi da yake da abin da yake turawa Ummu,duk yana gani.


Barazanar da yayiwa Ummu yasa shi fitar da kome, sannan ya kira Tafida wayewar garin jiya ya gaya mishi gasu nan zuwa tare da Mahmoud akan wani magana, sai gashi Mahmoud yasaka an bi motarshi an far mishi, wannan tashin hankalin yasa ya gayawa Jabir Adam ya gudu wurin Tinah, da ya gaya mata kome, amma ta saka idanun akan Mahmoud da Tafida, yanzu haka Jabir Adam yana garin Ibadan cikin tsaro, ita kuma Tinah tana Abuja tare da Tafida da Deen.


---
A hankali Mahmoud ya duba wayarshi sako ne rututu, ta email dinsa a hankali videon ya bude na kan sunan Deen shine tsirara haihuwar Uwarshi da ubanshi, a kan Khairat, fita yayi yana jin zuciyarshi kamar zata buga. A kasar video ya ce mishi, _Akwai irinsa an tura kwafe dinsa kan wayar Ammyn hmm! Ban sani ba ko zata iya jure haka, kana kara motsi akan Ummu har gidan Tv za a turo kowa ya gani Mahmoud ko mutuwa nayi nasan baka isa taka Ummu da wannan abin ba, sai na saka ka biya abin da kayi don haka ni da kai Allah ya bawa me rabo sa'a ka sani ko mutuwa nayi ba zaka tab'a tsira ba sai an.kamaka don haka shawara ya rage naka kamar yadda kake da hannu haka nike da hannu akwai masu tsaya mana haka.ma Allah ya tsaya mana_


Shiru yayi kafin ya kalli yaranshi. "Ku bar garin nan, idan na matsa dayawa za a samu matsala kuje ta sha." Ya faɗa yana barin gidan, tabbas tunda Deen ya fada mishi ba makawa haka ne duk inda ya sake akwai matsala. Wani kira ne ya shigo mishi ya ɗauka. "Akwai nasara!" "Babu domin Safiyyudeen ba zai tab'a barin mu tab'a Tafida da iyalinsa ba, sai dai mu jira dama daya tal! Idan kuwa muka samu xan baka damar cimma matsaya ni na dauki nawa!" Daga can ajiyar zuciya aka sauke kafin ya ce mishi. "Kai da Hamza Safiyyudeen ya hana ku sakat ko? Idan ya mutu fa?" "Ba iya ni ba, kai da kake gefe sai mutuwarshi ya shafe ka, ka ajiye maganar tab'a Safiyyudeen domin Tafida mahaukaci ne daga kai har ni idan ya kamo mu, Borno yayi mana kaɗan." Ya kashe wayar yana tsaki.


Tun daga ranar da aka sallame ni, ban kara kwana ɗaya ba sai gida. Kamar ban je ko ina ba, muna waya da Tafida lokaci zuwa lokaci da wayar Uwani don nawa wayar ta lalace. Sannan na gaya mishi na koma gida, don gidan ya min girma shima bai da nutsuwa yasa bai min magana ba, sati daya yayi ya dawo ya kama aiki, a can kuwa an canzawa Deen asibiti kafin Tafida ya bar garin, iya Tinah kadai take zuwa shima ba kasafai ba akwai masu kula da shi. Domin an b'adda kafa yadda ba za a bibiye shi ba.
Tunda ya dawo bamu hadu ba, domin ya dawo da kwana ɗaya Mama ta dawo, kai murna kamar me amma zuciyata a razane nake, don kada a samu matsala wani ya labartawa Mama abinda nayi. Tsakanina da Tafida haduwa yayi wahala, aiki yake tsakaninsa da Allah, sai da aka yi sati uku cif kafin wata Juma'a yazo, cikin sanyin murya ya ce min.."ki roki Mama ki koma dakinki don Allah!" Tsoro yasa na kasa amsa mishi. "Tow ni zan mata magana tunda kina jin tsoro." "Gara kai ka mata magana!" A daren kafin ya tafi a zauren nan sai da ya lallabani yayi yadda yake so, amma ranshi a b'ace yake. Bai koma gida ba sai da ya kira Abba ya roke shi yayiwa Mama magana, shi kuma ya mishi alƙawarin zai yiwa Baba Bulama magana koda aka yiwa Mama magana bata ce kome ba, haka wata sati ya kuma shiga. An gama azumin sitta shawal, a lokacin na fara wani irin tsirfa, da zaben abinci. Bana son kamshin manja ko man gyad'a. Sam ban fahimci haka ba, abinci kuwa ina son mai yaji, duk zuciyata bata bani wani abu ba. Mufid ya fara wasu kananun rashin lafiya, wanda yasa dole na gayawa Tafida ya ce na tafi asibiti a duba shi, Mama ce ta mashi Yaron tana kallonshi tana sauraron wayar da muke da Tafida. "Tow shi kenan zan kai shi " na fada ina gyara daurin dan kwalina. "Kai Uwani manja nan nata bai da dad'i." Na wuce ban daki ina jin aman da ya taso min. Ka sake Mama tayi tana kallon yaron da yake fesa. Bakinta a sake tana kallona na amshi Yaron na fita ina mita a tsakar gida, itama fitowa tayi bakinta dauke da mamaki. Tsirta da yawun bakina nayi da ya yanko min kamar xan yi amai.... (Burinku ya cika kun kashe mama da mamaki ko?)
```All spicess
Jollof mix
BBQ mix
Thyme plus
Garam masala
Curry powder```






```Special zobo
Special yaji
Spice kuli kuli
Miyar kuka
Miyar kubewa
Special daddawa```




```Garin masa/sinasir
Garin alale da kosai
Garin kunun tsamiya
Garin kunun aya```
*Shin ko kun san kayan kamshin da kayan zobo tare da duk wani dangin kayan abincin gargajiya da Ummu take amfani yana samuwa ne ta wurin Shaharariyar me kayan kamshi na AIDA spicess! Ina mata yan yayi ina masu abinci na online kayanku ya tsinke a gindin kaba, ga Hajiya Aida special spicess tazo mana da kayan girki na gargajiya da na zama kai Jama'a wata miyar sai a makota! Na gwada sauran ku gwada ina jiranku! Za a iya samun Aida spices ta wanann number:+234 806 968 1068 Whatsp siyan na gari mai da kudi gida! Hajiya ki zama yar gayu me sauki ne amma girkin yan gayu dai da Aida spicess*🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Gaskiya Uwani Allah zai kamaki da hakkina wannan wacce irin rayuwa ce, sam Manja nan bai da dad'i." "Kuma haka zaki dawo ki ci abincin da nayi da manja ban da gulma haka kawai ki hana ni kasuwancina!" Mama sai ta koma kakar wata mutummutumi, ni ban lura da halin ta ke ciki ba, nayi mata sallama saboda ya turo a dauke mu.
*Mama*
Idan hankalin Mama yayi dubu ya tashi, sannan wani abun da ta lura yadda Ummu take zumudi idan Tafida ya kira wayar Uwani, idan ma idanunta bai mata karya ba, har hiran dare suke, sau biyu tana kamata suna wayan dare, gyada kai take kawai tana tafa hannunta. "Uwani!" Ta kira ta, tana juye abincin sayarwa a babban kula, ta d'ago kai tana amsawa. "Na'am Mama" "Bayan tafiyata Umara tafida yana zuwa daukar Ummu ne?" A matuƙar razane ta zare idanu zuciyarta da Mama zata gani sai ta fahimci a razane take, amma ta boye tsoron tayi shiru kafin ta ce mata. " A'a, baya zuwa gaskiya ban ganshi ba." "Ba cewa nayi yana zuwa ba, baya turowa a dauke ta?" Uwani a matuƙar rude ta ce mata. "Gaskiya idan ba rashin lafiyar Deen ba gaskiya bai tab'a turowa a dauke ta ba, shima saboda Baba Sarkin noma ya zo ne!" Ajiyar zuciya ta sauke, bata kara magana ba, ita kan uwani tayi maza ta bar gidan, har wurin azhar tana baza idanun Ummu jiran Ummu, ai kuwa biyu da rabi sai gasu nan.
*UMMU!*
A matuƙar gajiye na dawo domin ina goye da Mufid, Mufidah tana hannuna na shiga gidan amsar Mufidah Mahira tayi tana min sannu. "yawwa!" Muka shige bangarenmu, har dakin Mama ta kai min ita, na zauna ina gaida Mama da take kan abin sallah. Sauke yaron nayi na wuce ban daki nayi alola, amma amai ya saka ni a gaba. Kura kofar idanun yayi ita ɗaya tasan yadda take ji. "A hankali na fito muka hada idanu. "Aman me kike yi haka Ummu?" Kallonta nayi shiru, mikewa tayi daga abin sallah ta bani wuri na dauki abin sallah. "Yaushe rabonki da bakonki!" Har na tadda kabbara, tambayar nan ya sani na wani juya a gigice. Murmushin takaici tayi tana kara kallona. "Yaranka wataninsu bakwai da wani abu, kai bana jin sun cika bakwai ma." Zubewa nayi a gabanta cikin tashin hankali da. "Mama ba abin da kike tsammani ba ne, ba ciki ba ne" na fada ina hadiye yawun bakina nayi, ai kuwa ya taso min da amai da sauri na koma ban daki na fara kwara amai, ba ma kome a cikina. "Don Ubanki zaki gaya min yaushe kika bashi kanki da kananun Yaranki?" Ya fada rike da muciya don na bata haushi, a gajiye da aman da nake, zare idanuna cikin tsoro na ce mata. "Don Allah kiyi hakuri!" "Zaki gaya min gaskiya ko sai naci Ubanki!" Ta daka min tsawar da yasa na fashe mata da kuka, domin yadda ta ja dagga zata maka min muciyar na ce mata. "Tun tafiyarki Umara ne, ya dauke ni wallahi ban san haka zai faru ba don Allah ki yi hakuri!" "Eyee binshi ma kika yi wato na hanaki farincikin rayuwa shine kika biye mishi yayi miki ciki Ummu Hadiyya? Ni kika watsawa kasa a idanun maza kira shi ya kwashe mu ba zaki zubar min da mutuncina ba, munafukar banza mara kunya!" Ta mika min wayarta cikin tsawa hannuna yana rawa na amsa, na fara saka number shi da na haddace. "Ni Ummu zaki mai da sakarai, har kin haddace number Mijinki! Maza kira shi!" Ina dial number shi sai gashi ya shiga, kashe kiran yayi na kara zare idanu hawaye na zuba min, na kara kira amma ina bai dauka ba, yadda Mama ta hayayakomin na manne da jikin bangon ban dakin, kamar yasan ina cikin wani tashin hankali ya kira ni. "Ummu ya jikin Babana?" Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Don Allah kazo ka cece ni." "Kut da ban buga miki muciyar ba Ummu? Shine zai zo ya kwace shi yazo shima mara kunya ya gaya min dama dalilin biya min Umara kenan ban bashi ke ba ya dauke min ke ya dirka miki ciki!" Ta fada da karfi, "Wayyo Allah Mama don Allah kiyi hakuri gani nan zuwa!" Ai kuwa Mama ta cigaba da kurari tana fada kamar zata buge ni, kai na ga tashin hankalin da ban tab'a gani ba, ni sai ban damu da halin da nake ciki ba, yadda yake ta bata hakuri tana balbale shi da fada ya sani kuka, don wallahi tausayi yake bani. Juya tayi ta ce min m "wuce kiyi sallah ki shirya Yaranki, sai ki tafi Allah ya baku sa'a." Ta fita tana mita kamar zata aro baki ta kara, dakyar nayi sallah. *Ciki!* na furta a zuciyata, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, me yasa Tafida zai min haka, ban tab'a jin tausayin Yarana irin yau ba, a yanayin yadda mama takr magana Mufid ya sha nonon ciki ne, yasa ya fara kashi, ai kuwa ina idar da sallah yana shigowa unguwarmu daga karan saren dinsa.
Ina zaune Mama ta shigo ta zabga min harara, tana faɗin " maza tattara kayanki gashi nan yazo ba xan iya abin kunya ba!" Shigowa gidan yayi gaisa da yan gidan da suke waje, da sallama ya shigo. Yadda yake tafiya a sanyayye yasa duk zafin ranta, sai taji tayi sanyi. Har cikin dakin suka shigo da shi, ta zauna a bakin gadon shi kuma ya zauna a bakin kofar dakin. "Aliyu ka kyauta min kenan?" Kasa d'ago kai yayi yana buga key din hannunshi a kasa, Mufidah da idanunta biyu ta ganshi tayi ta mika mishi hannu. "Wato ka tura ni Umara!" Kunya ce ta kama shi wanda bai tab'a jin irinta ba, "Sai ka ɗauke ku tafi Allah ya kyauta! Babanku ya gaya min kome!" D'agowa yayi da sauri yana faɗin. "a'a Mama ta zauna idan kika ji a ranki tayi mu tafi xan zo ɗaukarta!" Harara ta watsa mishi. "Eh ga tsohuwar banza ka cigaba da zuwa kuna rashin kunya a gabana ko? Ba dani ba wallahi oya maza ɗauketa ba zan iya ganin rashin kunyarku ba." "mama kiyi hakuri ba zan bishi ba, wallahi cewa suka yi ni ce na zubar mata da cikinta na rantse da Allah, zasu kashe ni ya zan yi da raina?" "Idan ya so ki mutu maza bani wuri "
Abin da ya faru.
Fitar Maman Ummu a dakin ta kira Alhaji Bulama tana fada Tafida yazo ta dirkawa Ummu ciki, ba tare da wani damuwa ba ya ce mata. "Alhamdulillahi kin ga ai dole ki bashi Matarshi idan dai ba ado zaki yi da ita ba, tun tafiyarki Umara ya dauke ta kuma ban hana shi ba, ban ga dalilin hana shi matarsa ba" "Alhaji da kai aka ci amanata?" "To don Allah wani amana aka ci? " Shiru tayi saboda yadda ya mai da abin wasa, daga karshe ya bata hakuri tare da mata bayani ta barsu kawai su tafi kafin mutanen gida su fahimci wani abu yana faruwa idan ma rana zata saka shi kenan, dake tana jin haushi tace su shirya kawai su tafi ba bata son ganinsu. Haka ta kashe wayar, tana gama haɗa kayanmu. Ganin yadda Tafida yake ta kallona a dame, yasa ta cewa. "Kai bana son munafunci ɗauketa ku bar min gida, lokacin da kika bi dadin kalamanshi ai kin manta da zan dawo ko zaki samu ciki sai da na gaya miki kanku rawa yake daga ke har shi, ki jira nasan abin da zan miki, jikinki yana rawa kika bashi ya dirka miki ciki ko tausayin wadannan bayin Allah da babu ruwansu baku ji ba, daga kai har ita kuka yi son ranku, maza ku bar min gida kafin a fara min gori tai kunika!" Daukar kayan yayi a bakin kofar gidan Matori ya amshi kayanmu, wasu mutane biyar suka shiga aka kwashe kayan da ya saura. Ina zaune a dakin ban fita ba ina kuka. "Zaki fita ko sai na karya kafarki munafukar banza!" "Amma don Allah a zubar da ci...." "Kauuuu!" Naji ta dauke ni da wani irin marin da ya fasa min hancina. "Da ana zubda ciki da naki zan fara zubarwa saboda bana son Ubanki amma haka na rungume ki har na haife ki ban tab'a tsanarki ba! Sakarya samodara! Fita min a gida kafin na tattaka ki!" Cikin kuka na fito a bakin kofar na same shi, yana kallona. Na rasa fahimtar haushi yake ji ko kuma bakin ciki yake ji, wani irin murmushi ya sakar min ya juya abinshi. "Aliyu!" "Na'am Mama!" Ya juyo yana kallonta kasa. "Na Barka da Allah idan ka cutar da ita, sannan ka saka idanun akanta kada ta zubar maka da ciki don sakarya ce bata da hankali! Duk wanda zai juyawa kyautar Allah baya sakarai ne Alhamdulillahi Ubangiji ya rabata da shi lafiya amma ka saka idanun kada ta zuvda maka ciki! Allah ya muku albarka!" "Allahummah Amin, Mungode sosai Mama Allah ya huci zuciyarki, kiyi hakuri da laifinmu ba zamu kara ba, na gode sosai Mama da gatan da kika min, na gode

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login