Showing 213001 words to 216000 words out of 241571 words
Chapter 72 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
yana me shiga gaban motar, asibiti bar asibitin, titi mutumin ya ɗauka a guje, ta riko hannuna tana murmushin da ya ke karawa fuskarta kyau, Ni sai naga ta kara kyau zuciyata ce ta tsinke kamar zata buga. "Ummu kwanta Babangida ya gaya min cikin ki yana nan!" "A'a Hajiya ke zaki kwanta dai!" "A'a kwanta Ummu ina son koda xan kwanta a kan kafarki ya zama na karshe haka kema nake son ki kwanta, shi wannan rayuwar da kika gani abin da kake so ba shi kake samu ba!" Ta fada tana kokarin kwantar da ni, nace mata. "A'a Hajiya bar ni na zauna ki kwanta ke!" "Hajiya ki kwanta kawai tunda ta ce hakan!" Bata so ba, haka ta kwantar da kanta tana min nasiha, da bani shawarar kada na kara yadda nayi irin kuskuren da tayi, kafin tayi shiru, a hankali muka cigaba da tafiya kafin wani lokaci ta ce min. "kun zo min da ruwa ne?" "Eh gashi!" Ya mika min, na bude mata, na d'ago kenan ina bata ruwan sai na ga kamar ruwan yana dawowa jikina ne ya fara rawa nace mata. "Hajiya ruwan baya. Wucewa ne, Daadi ruwan yana dawowa !" Juyowa yayi yana kallon yadda nake rike ta, murmushi yayi ya fara biya mata kalmar shahada daga nan na fahimci Hajiya nesa tazo kusa, "A'a Hajiya don Allah kada ki min haka A'a Hajiya don Allah Tafida yana buƙatar ki!" Tana karanta kalmar shahada tana murmushi, damke hannuna tayi da karfi da har sai da naji karar ........(Allah ka jikan Iyayenmu bakiɗaya!)
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+234813026964169
Ban tab'a ganin mutuwa a idanuna ba, ban tab'a zama inda wani Allah ya dauki rayuwarshi ba, yau akan idanuna a gefena Allah ya amshi rayuwar Hajiya akan kafadata a Hajiya ta cika, yadda yatsuna suka yi ƙara na kafin a hankali ta sassauta riƙewa, na ji kome na duniyar nan ya tsaya min cak, wani tsoron Allah . "Daadi mu koma asibiti Daadi!" Driven ne ya tambaye shi, ya juya Jidda ko ya? "Muje tace ko ta rasu tana bukatar ayi mata jana'iza a Makka wannan shine wasiyyarta." Ha fada da Larabci, gefen hanya ya saka driven ya sauka, ya fito tare da bude min, yana bude min na fara kwara amai, domin cikina a hautsinewa yayi. "sannu!" Ya ce min, ina ajiyar zuciya ya shiga bayan motar ya gyara mata kwanciyar, sannan ya ce min." Ki daura kanta a cinyarki kada ki takura!" Gyada kai nayi, ya juya zai shiga motar, ban san ya akayi ba, sai ji nayi ya rungume shi. "Ba lokaci Ummu!" "Kayi hakuri!" "Mutuwa yana kan kowa nima kema, dukkanmu lokaci muke jira!" Ya fada yana me nuna min yadda xan zauna, akwai abin kuka ma yaci kaniyarshi domin mutuwar Hajiya bakiɗaya na nemi kuka na rasa kuka ya ƙare sai ciwon da nake ji, kiran Abba yayi da yake Madina ya gaya mishi, sannan ya kira Asiyah. "Ku kwashe kayan Hajiya a kai masauki sannan ki ce Tinah ta nima miki sallama, ku zo Makka Hajiya ta rasu." "Wasa kake ko? Yaushe Hajiyar ta bar nan ko awa daya baku yi ba!" "Na gaya miki kuyi abinda nace ku tawo Hajiya ta rasu ki gayawa Fanna!" Ya kashe wayar, ina kallon juyowa yayi yana kallona kafin ya amsawa Balaraben "Dan koma gefen hanya!" "Zaka dawo da ita gaba ko?" "Eh!" Haka kuwa aka yi na koma gaba ya dawo baya, yana mata addu'a, ni kamar ban tab'a zaman aji ba, bakiɗaya ilimina ya dauke karatuna babu kodaya, haka yasa naji kamar bani ba ce. Tafiyar da muka yi ko digon barci babu a idanuna, bana minti ɗaya ban juya na kalli Hajiya da take bayan motar kwance ba, tare da shi kanshi Tafidan har muka isa garin Makka, duk wani doka da ake cikawa yayi, karfe hudu da wani abu aka yiwa Hajiya jana'iza a babban masallacin harami, tare da dubbanin mutane da suka halarci sallah la'asar, sai a lokacin na samu damar yin kuka, sai nake ganin kamar nice na rasa Hajiya ba Tafida da Yan uwansa ba, Hajiya ta tafida burin Yaranta su hada kai, Hajiya taso Yaranta su had'e kai koda ba zasu kasance a wuri guda ba, Hajiya ta tafi da matukar son zumuncin Yaranta, daga cikin kalaman hajiya da ta fada min ta ce min. "Ummu zumuncin daga mahaifa Allah yake sakata, idan mace ta tsarkake kanta da darajarta Allah zai sanyawa Yaranta su zama masu matukar zumunci, Ummu Hadiyya ban tab'a zina ba, ban tab'a raba kowa da dan uwansa ba, Ummu gaya min hadin kan Yarana yana da nasaba da laifina na tafi na barsu, na dawo na fifita soyayyar Aliyu akan na kowa na manta da cewa dukkansu Yayana ne, Ummu Hadiyya ki taimaka min kada kan Yarana ya rabe, naso kaina na nuna son zuciya don Allah ki taimaka min!" Wani irin tsoron Allah ne ya shige ni, har aka yi sallah Magariba da isha a lokacin su Fanna suka iso, Tafida yana bakin kofar mashigan mata, yana musu bayani, yayi sanyi kamar ba shi ba na hangosu. A hankali nake takawa har na iso inda suke. Da kuka Fanna ta rungume ni, na dan rungumeta ina kallonshi duk sai ya bani tausayi kamar zan yi magana sai nayi shiru. "Fannah saketa!" Inji Asiyah, "Hajiya ta huta, domin ciwo azaba ne;" kallona yayi ya karaso yana kallon yatsun hannuna. "Sorry da zafi ko?" Ya riko hannun yana hura min. "Ka ci wani abu?" When Ummu ta tambaye shi ya ci wani abu? Yadda nake kallonshi murmushi yayi, ya ce min. "Muje akwai clinic a duba hannun!" "Ka ci wani abu?" Na kara tambayarshi, ina kallonshi a sanyayye ya ce min. "Na koshi!" "Muje ki tea ka sha!" Riko tsinsiyar hannuna yayi yana faɗin. "tow!" Muryan shi tayi bala'in sanyi, haka muka wuce masaukin, yayi mana oda a wani parlour muka zauna muna shigowa Abba yana shigowa, gaisuwa muka yi sannan muka zauna shiru. Na rasa yadda zan fadi yanayin da Tafida yake ciki, a wannan yanayin na tabbatar da shi din babban mutum ne, ban san me yasa nake jin kamar bana iya sarrafa kaina ba, domin hatta abinci kusan yadda na saka shi a gaba yasa shi ci ba wai yana jin dadinsa ba. Yadda nake ta kallonshi yasa suka yi ta watsewa, ya rage daga shi sai ni ganin Babu kowa ya d'ago ya kalle ni. "Tsawon rayuwata nayi ba tare da ita ba, nayi ta jin haushinta ina ganin kamar tayi min wani abu, na manta Uwa tana haifar d'a bata ganshi ba bai ganta ba ta mutu." Ya ja hancinsa yana d'ago kai yayi yana kallon sama. "Ummu! Na zata duk yadda na yi mata zata yi fushi ne, na zata idan nayi ta nuna mata bana buƙatarta zata yi fushi ne, sai na ga ashe zata iya karban haka. Nayi ta b'ata mata rai, don ta ji haushi sai na ga duk abin da nayi mata, sai naga kamar farin ciki take." Numfashi yake saukewa me nauyi yana kallona. "Bayan na hadu da ke ce na fahimci girma da soyayyar Uwa, ba a tarin dukiya ba ne, ba a tarin daukaka ba ne soyayyar Uwa daban take bata da na biyunta, kamar yadda ba zan iya kwatantta zafin haihuwa da zafin mutuwa ba, haka ba zan iya kwatantta yadda soyayyar Uwa yake ba, Hajiya tayi me wuyar saura mu, mu mu rakata da addu'a. Ummu kin san me?" Girgiza mishi kai nayi, ya rike hannuna yana faɗin. "Ina son nayi kuka kamar yadda naga Abba yayi da muka iso da gawarta, sai dai I try all my best na kasa ko zubar da hawaye, Ummu ina son nayi kuka ko zan huta da abinda da nake ji sauki abin da nake ji, ban sani ba ko zuciyata ba irin naku bane, bana jin tsoro ko faduwar gaba, bana jin kome anya da zuciya a kirjina?" Ya ƙarshe maganar da tambayata, sai naji kamar bani da amfani a rayuwata idan na barshi shi daya don kanshi, "Kana da Allah kana da Abba, suna tare da kai ga As..." "Ummu ina da Allah ina da Abba ga Asiyah!" Abin da zan fada kenan ya ƙarshe min, tabbas yana da Asiyah, sai da yadda ya dauki goran ruwa ya sha, yasa ni karan jin tausayinsa sama da koda yaushe. "Ina da Asiyah, amma ki sani zan koyawa kaina zama cikin kaɗaici kafin lokacin ya zo, domin itama kokuwa take da rayuwa zata rayu ko zata mutu ! Ba mu sani ba, domin kaso me yawan gaske na kwal-kwalwarta ya lalace cutar kansa ya lalata mata su, tana nimawa kanta farin ciki ne domin bata son ta kasance cikin kad'aici, ba soyayya a cikin al'amarinmu amma kuma yarinyar bata da kowa a tare da ita sai ni, sannan nayi kokarin janye ta daga mahaifiyarta yadda zata samu nutsuwa. Ummu Mama tayi kokari ganin ta gina miki tarbiyyar da ya da ce, amma ki sani kafin na samu mace irin Mama sai an tona, from beginning Asiyah bata samu soyayyar Uwa ba, a yadda naji a bakin Saadiyyah Mahaifiyarta kwaso cikinta tayi a wurin yawon bin malamai da bokaye, bayan nan ta rasa tarbiyya da rashin kare kai, Ummu na gaya miki ne saboda na gaji da nauyin al'umma." Taysayin Tafida ya gama raunana min zuciya, ban san ina kuka ba, sai da ya rike hannuna yana faɗin. "Ni bance ki tara min jama'a ba, ni dama can haka Allah ya halicce ni, a lokacin da zan samu soyayyar gaskiya a lokacin nake rasa wanda zai so ni, na farko na rasa ki yanzu na rasa Hajiya. Bani da kowa a gefena. Na san Allah yana sane da ni kuma yana sane da rayuwata." Rungume shi nayi ina kuka, ban san yadda aka yi ba, na tsinci kaina da faɗin. "Ina tare da kai, ba zan nisance ba, ina tare da kai Tafida ba zan kuma nisa da kai ba." Murmushi yayi ya kwantar da kanshi a kirjina ina shafa bayanshi. "Ummu ina jin kadaici babu kowa a tare da ni!" "Na sani!" Na fada cikin kuka. "Ummu kin ji dad'i, kina kuka ni kuma bani da ikon yin kukan, Ummu ina son nayi kuka ya zanyi ina son naji yadda ake jin maraici, ina son nima a kalle ni a ce min maraya! Ummu ina son ganin Hajiyata, Ummu ina kewar Hajiyata!" Ya zan gaya mishi ne ya bar gaya min haka yana sani kuka? Ya zan gaya mishi maganarshi yana saka ni kuka, taya zan fahimtar da shi nima zuciyata tana tabuwa!" Taya xan gyara abinda yake tsakaninmu. "Ya isa haka!" Na fada ina cigaba da kukan. "shiiii! Nayi shiru na daina maganar. Ummu ki kira Deen kirjina zafi yaƙe min, ciwo kirjina yake min, Ummu " yadda ya birkice min a wannan yanayin yasa ni kiran Abba da ƙarfi, haka ya fito ya same ni rungume da Tafida ya rikice min kamar yaro karami irin yaron da aka yaye shin nan, ba kuka yake ba sai wani irin rikici da yake ji, kiran likitan masaukin aka yi, shi yazo aka kaishi daki, aka mishi allura. Damuwa ce tayi mishi yawa, haka yasa yake min wannan rikicin. "Maman Mufidah ko zaki tafi ki kwanta ne?" Inji Asiyah, kallo daya nayi mata fuskata babu wanda yasa ta juya a hankali ta kama hanyar waje, na kwanta a gefenshi ina kallonshi. Ina kallonshi tare da tuno zamanmu da shi da duk abinda ya faru. Zuwa yau da ya rasa Hajiya s rayuwarsa sai nake jin kamar an wanke min zuciyata bana jin fushi a kanshi bana jin zan cigaba da hukuntashi da laifin da ya dace na yafe mishi, na san yau da Hajiya tana nan ba zan dawo rayuwar Tafida ba, akwai asiyah ga Abba amma bana jin sun wadatar, shafa kanshi nayi a hankali barci yayi gaba dani.
Asiyah
Tun da suka bar parlourn nan, hankalinta yaƙe tashe domin idan ta ga Ummu sai ta dinga jin kamar ta ji haushinta amma idan ta tuna, cewa idan kana son ganin haukar Tafida ka tab'a Ummu yanxu zai haukace maka sai taji wani mugun tsoro, tunda suka dawo dakin take juyi, yawan tunani yasa kanta ya fara ciwo, wanda ya haifar mata da habbo,ban daki ta shiga ta sake ruwan sanyi akanta har wani lokaci kafin ta fito ta kwanta, sai dai ta kasa barci ta mike tare da nufar waje, a dan koridon din da zai kai la parlourn ta makale, tana jin abinda suke fada bata san lokacin da tayi ta kuka. Tana rike da hannunta wannan ita ce ƙaddaransu bakiɗaya. Yanzu idan Ummu bata dawo rayuwarsa ba, haka zata tafi ta bar Tafida alone wani irin kuka take mara sauti, sai take jin kamar wani abu suka yi haka ya faru su ne? Tayi kokarin rike kukanta har lokacin da Ummu ta kira Abba kafin su iso ta riga kowa zuwa, durkusawa tayi a gabanshi, tana kuka hannunshi cikin nata tana faɗin. "A'a Yaya ka farka Yaya dube ni don Allah. Ka nutsu." Ta fada tana kuka, lokacin da Abba ya fito ma tana durkushe har aka kai shi dakin. Ganin babu wanda ya ce ko Ummu zata bashi wuri don tafi kusanci da shi, sai dai yadda Ummu ta kalleta sai take jin kamar kallon nan ne na mai wuri yazo, cikin sanyin jiki ta bar dakin. Tasan za ayi haka sai dai wani irin girman Ummu take gani da kwarjinin haka yasa kome tayi take bala'in shakkar ta ko tsoronta.
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7670
Ummu
Da asuba na riga shi tashi, yana kwance da alamu barcin yayi mishi nauyi ko nace hala sun saka mishi alluran barci ne, ban iya tafiya masallaci ba domin gani nake kada na tafi wani abu ya same shi, sai naga kamar zan dawo naji labarin ya rasu shima. Bakiɗaya bani da nutsuwa. Haka yasa na zauna a dakin har nayi sallah asuba, karfe shida da wani abu ya bude idanunshi, tashi zaune yayi yana kallon inda nake. Tashi nayi na je inda yake, a hankali ya rungume ni ya daura kanshi akan cikina. Sai a lokacin naji ya sake wani irin shashekar kuka, bubuga bayanshi nake yana sai a lokacin yayi kukan da dakyar yayi shiru, janye jikina nayi na shiga ban daki na hada ruwan dumi na zo na saka shi yayi wanka da alola yana fitowa ya gabatar da sallah, sannan na fito amsar abin karya, a bakin kofar na ga Asiyah da alamu bata yi barci ba. "shiga yana ciki!" Kamar zata kifa ta shige dakin, samunshi tayi yana zaune, har lokacin hawaye bai daina fita a idanunshi ba. Zuwa tayi gabanshi ta zauna tana me rike hannunshi. "Kana son Hajiya sosai ko?" Ta tambaye shi itama idanunta cike da kwalla. "Kayi hakuri kada kayi kukan dayawa, ka manta ina da sauran lokaci ne har zuwa shekara daya! Kada kayi kuka don Allah ka yi hakuri." Rike hannunta yayi yana kallonta. "Kin sha maganinki?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Eh na sha!" Hannunta ta kai tana share mishi kwallar da yake zuba mishi. "Kayi hakuri kaji!" Ta fada tana kukan itama. Murmushi yayi yana me kallon kofar da nake tsaye. "Shigo Ummu!" "Tow!" Na ce a hankali, ina me shiga dakin na ajiye mishi tire din, dauka tayi ta mika mishi kofin tayi tana. "Da zafi ma!" Mika mishi tayi tana cigaba da cewa. "Ko zaka surka ne?" Murmushi yayi yana kallona ya ce mata. "A'a!" Aliyu Muhammad Jadda, da na sani a baya bashi bane wannan a gabana. A hankali na juya zan fita ya ce min. "Jirgin yamma zamu bi, ki shirya kafin na gama!" "Tow!" Na fada ina me fita, kallonshi tayi ta ga har lokacin idanunshi yana kan kofar, "sha Ya Aliyu!" Kurba yayi yana kallon yadda take ta mishi surutu yana jinta har ya gama, sannan ya mike ya shirya tana ta mishi magana. Tunda na fito nake kallon wayata domin na kasa cin kome, har muka shirya sannan muka bar masaukin, zan iya cewa tunda na kifa kaina a kan cinyata. Sai dai lokaci zuwa lokaci Abba yana tambayata lafiya nace mishi ba kome, wurin karfe biyar muka iso airport na jidda, dakyar na sauko saboda jirin da nake ji. Kallona yayi yana tambayata, "yunwa nake ji!" Na fada a sanyaye. "Yunwa?" Suka kara tambayata, ya karaso inda nake yana riko hannuna. Ya tallafe ni har cikin airport din, abinci aka fara nimomin amma na kasa ci, ruwan zafi aka kara kawo min na sha sosai, sannan naji zufa na karyo min. Sallah suka tafi aka bar ni da Tinah. "Yarinyar nan tana da sanyi Sosai!" Da idanuna bita da shi, "Matar Tafida nake nufi!" Murmushi nayi da zan kira shi murmushin dole. "Eh!" Murmushi itama tayi tana faɗin. "Amma naji tana da matsalar ƙwaƙwalwa ko?" "Eh yace Cancer ne!" "OMG!" Gyada mata kai nayi, ita kanta sai jikinta yayi sanyi domin kuwa bana son ta ji haushi Asiya idan tayi wani abu, koda suka dawo na gaji don har na fara barci. "Maman Mufidah idan tana barci tafi kyau inji Asiyah tana gaya mishi. " "Nima nasan da haka!" "Amma me yasa bata cika magana ba!" "Nature dinta ce bata da yawan magana kamar ke!" Ya fada yana kallonta, yar dariya tayi tana faɗin. "Hmm! Haka dai ka ce." Ta fada tana zuwa inda nake kwance. "Ma.." "me zaki yi? Ba kyau tashin mutum idan yana barci!" "Ayya ban sani ba ne!" Ta fada kamar tayi kuka domin yadda Tinah ta mata magana. Koda Lokacin tafiyarmu yayi, shi ya tashe ni na tashi ina faɗin. "Banyi sallah ba fa!" "Ki shiga idan mun isa gida kinyi ai ke sai da Uzuri!" Ya fada yana dauke kai, yadda yake magana da kome