Showing 159001 words to 162000 words out of 241571 words
Chapter 54 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
a gidan a parlourn Hajiya suke kawo kayan da suka hada na Asiyah da Sa'adiyya. Bai dame ni ba kayana da Hajiya Kaltuma take hada min tana kirana ta gaya min abin da ta saka da kuma yadda kome yake tafiya a hankali, babu amfanin gaggawa. Bayan mun gama waya da ita naji ana buga kofar gidan. "Idan gari ya waye ki je ki gaida ita, idan kika gama abinci ki kai mata, kada wani shege ya buga miki kofa ki bude domin na saka matori yayi gadin kofar, kada ki bude matukar ba Hajiya ba ce." Maganarshi ya dawo min, "waye?" Na fada a hankali. "Ummu Hadiyya!" Jin muryan Mamana yasa na fasa ihu na bude kofar ina murna. "sannunku da zuwa!" Na ga Hajiya a bayanta. Shigowa suka yi ba shiga kawo musu abincin, dake bangarena nake. "Sannunku Mama! D'annaku Hajiya Uwani zaki kwana min biyu?" "Allah ya rufa min asiri,bar ni na koma gidan Mamana!" Ta fada tana kallon Mama. Kitchen na koma na dauko musu kullum jollop din shinkafa da wake da nayi wnada yaji kifi sosai, na kaiwa Hajiya Hajiya koda yake ban shiga ba Humairah na bawa na juya abuna don naga parlourn da mata har da Maman Ilham, yanzu itama ta sauya min. Ban shiga ba na juya abuna. "Ummu!" Na'am Mama!" "Ina Yaran suke?" "Suna barci!" "Me yasa kika daina kaiwa Hajiya Aisha su?" "Mama ba laifina ba ne, shi yace idan na kai mata Yaranshi zai min ba daidai ba " "kin manta ita mahaifiyarshi ce?" "Mama a cire maganar Mahaifiyarsa ce ayi maganar gaskiya me yasa Tafida ya ce kada ta bari a kai Yaran can? Na farko a lissafina akwai abin da suka yiwa Yaran kuma basu dauki laifinsu ba, na biyu ana amfani da Yaran a cusawa Aunty Baby b'acin rai domin kowa yasan yadda zuciyar Uwa yake akan Yaranta, na uku ita Hajiya me yasa bata samu shi Tafida tayi magana da shi ba ta kira ki, kiyiwa Aunty Baby magana, kada ki manta a Musulunce Aunty Baby ta hada gaskiya, ba xai yiwu ta lalata aurenta don gyara kuskuren da wani ya aikata ba, ni fa ba zan yarda da wannan abin ba domin kuwa Allah kadai yasan meke faruwa." Inji Uwani, shiru Hajiya tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta fara kame-kame. "Wato Hajiya dan yau ka haife shi baka haifi halinsa ba ne, ni bana son naga ana cutar da Ummu, kuma nasan tana kokari akan hadin kan iyalina, tow ya xan yi? Sun ce na fifita Tafida da Matarshi don ya zama gwamna, sun ce na fi son Yayanshi don Ubansu gwamna ne, wallahi." Sake baki Mama tayi ni kan abincin na diba na koma gefe na fara ci a hankali. "Hajiya Aisha!" "Na'am Maman Ummu!" "Ina ga Ummu tayi kuskure shigowa rayuwar Tafida ko? Tunda yan uwansa basu bukatarta da Yaranta idan Aliyu ya dawo ki ce mishi don Allah ya sako min ita kada ya sake na zo da sunan na zo amsar Ummu!" "Maman Ummu mai yayi zafi suna son juna fa!" " Da bata hadu da shi ba ai tayi hakuri yanzu idan babu shi ma zata yi hakuri Ummu ta koma gida sai ta haihu zan san abin yi tashi Ummu!" Ta daka min tsawa. "Mama ki kira Tafida tukun;" wani irin kallo tayi min, "kina tsammanin kiran waya daya zai saka na sauya ne? Idan har akan idanun Mahaifiyarsa aka cutar mishi da Yaranshi gaya min waye zai baki kariya babu Tafida babu ni sai Allah!" "Mama!" Nuna min yatsa tayi, tare da bani umarnin na hada kayana, kiran Mudan tayi ta ce ya dawo. "Maman Ummu ke da na zata zaki gyara kome, kuma shine zaki lalata kome! A matsayinki na Uwa bai dace kiyi haka ba!"
"Hajiya Aisha, bani bace da matsala kece me matsala, Yaranki sun zama sune a gaba kina bin bayansu, duk cikin Yarana babu wnada bana so, amma ki sani ba zan iya gani Yaranki su illata min yarinya ba, lokacin da aka yiwa Yaranshi kin nuna rashin jin dadin abin da suka yi? Amma kina cewa wai ba a kyauta ba." Kayana Uwani ta taya ni muka hada, sannan muka bar gidan, ashe burinsu Rukayya idan Mama ta tafi su kamani su min shegen duka sai aka yi dace Ubangiji ya sakawa Mama shakku akan abin da Hajiya tayi ta dauke ni, a ranar ta cewa Mudan. "Ka wuce da ita gidan Ubanta, idan har Aliyu ya shirya zama da Ummu zai saita gidansu, idan bai shirya ba a bar min y'ata ina sonta a haka! Wayarki ban ce ki kashe ba!"
"Mama na fita ba da izininsa ba fa!" Na fada kamar xan yi kuka. "Jikina ne ya bani wani abu zai faru, ki tafi idan yana sonki zai zo zai kuma nime ki!" Haka na bar garin Maiduguri na tafi biu, lokacin da za ayi ta'addancinsu, sun aiki Matori, sai Malam Habu me yiwa flowers din gidan ban ruwa, ya hango su dauke da bulala zasu shiga part dina, ita Hajiya ta can dakinta abin duniya ya dame ta(wasu zasu mamaki kada kuyi mamaki abun ko sai godiya yadda wasu suke rasin mutunci kamar ba za a mutu ba!) Shi ya kira Matori da sauri a waya yana zuwa ya ga suna ta dukan kofar, sannan shi kanshi matori bai san Ummu bata gidan ba, don har cikin gidan Mudan ya shigo ya dauke su, haka yasa shi kiran Number Tafida da yake tambayarshi lafiyan Ummu da su Hajiya, kira daya yayi, Tafida ya kashe sannan ya kira. "Oga gasu yan uwanka can, da abun duka zasu daki Hajiya Karama!" Wani irin ashar ya lailayo ya maka mishi uban waye ya ce ya bar wurin , kashe wayar yayi ya kira Abba. Yana tsaka da cin abinci Aliyu ya dauke mishi dadin abincinsa. "Abba ka ga Yaranka zasu kashe min matata da cikin wata uku! Abba wallahi idan na dawo sai na kame yan iska na zuba su a gidan Yari! Abba Matata da Yarana suna cikin hatsari idan wani abu ya same su wallahi ba zan yarda ba!" Kashe wayar Abba yayi ya dafe goshinsa. *Aliyun dai Aliyu ne! Ba zai tab'a bari a tab'a mishi matarsa ba! Alhaji na maka misali da zaki a dawa! Ka tab'a ji namun dawa sun tab'a iyalin zaki? Idan har haka ne shi yake farauta ya kawowa iyalinsa ya koya musu kare kansu, ko mutuwa anyi zaka tuna da kalmaina duk inda yake zai tsaka akan iyalinsa! Wannan wata kyautace da Allah ya bashi, lokacin da bai zaci haka daga Allah ba, ba zai tab'a barin a nuna ta da yatsa ba.* bai gama tunani ba Tafida ya kara kiranshi. "Aliyu! Ka kwantar da hankalinka, bari na kira Alfah muje mu daukota!" Shine ya kashe wayarshi, ya fita yana kiran Hajiya Salamatu ina Yaranta, "Sharif ne yana ciki!" "Ce mishi ya fito ya kai ni gidan Tafida, su Maryam dauke da makamai zasu daki Matarshi!" "Ina Hajiya Aisha take da wannan abin zai faru?" Inji Hajiya Kaltuma, "ina na sani!" Sharif da yaji haka bai tsaya wani abu ba, ya fito suka tafi a hanya ya kira Alfah yana gaya mishi ya same shi a can gidan Tafida. Kusan a tare suka isa. Sun samu Rukayya tana buga kofar gidan, sun fasa glass din window. Waya Abba yayi ya kira Kwamishinan yan sanda. Suna zuwa ya ce masu. "Yan ta'adda ne sun zo zasu kashe Matar gidan......
πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎ
*_GYARA SHINE MACE_*
*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎπ»πΎ
*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327
*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,
Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,π
Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu ajiπ
Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin kiπ
Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mataππ
Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin saukiπππ
Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babukuπππππ
Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima
KADAN DAGA CIKI WASU KALOLINππ»ππ»
Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi
Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu
Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra
Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa
Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka
*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbersππ»ππ»ππ»
07069711327 Whatsapp ,Ina maraba daku customersπππππ
Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mataπππππππππ
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH
*Gidan zafafan kayan Mata masu kyau da inganci na yar mutan sokoto maman Yusuf likitar Mata,*
*Bayan kayan Mata muna tura abubuwan da zasu amfanemu game da Zaman auren da wasu magungunan da zaku iya hadawa da kanku da sauransu*
50
Abin mamaki Abba yasa aka kama su bakiΙaya, har da surakanshi biyu da Yaranshi mata biyu su hudu kenan, kawai saboda kishi da hassada lallai sai sun ga bayan Matar danshi da ciki. Laifi na farko laifi na biyu wasu yan ta'adda mata biyu sun yi ΖoΖarin kashe matar gwamna da Yaranta, laifi na uku shine shigowa gidan gwamnar jahar Borno ba bisa ka'ida ba dauke da makamai tsirara. Wannan abin ya girgiza kowa sannan shi da kanshi Abba yayi ta karanto shashin dokokin kasar nan akan abin da suka aikata. Da hukuncinsu, Hajiya da take tsaye ta kasa magana sai share kwalla take ta rasa yadda zata yi da yaran nan nata mata, sam babu tausayi da imani a ranta.
Batun gaskiya ta kira Maman Ummu ne domin ta bawa Ummu Hadiyya hakuri, tana barinta ganin Yan jikokinta don Allah ya daura mata kaunar Yaran sai take ganin soyayyar da bata yiwa Aliyu ba ne takewa Yaran, sati daya da ya wuce Maryam tayi ta kiranta akan lallai ta saka baki Aliyu ya basu hada kayan auren amma ta gaya musu ya bawa Ummu don lokacin Allah ya gani bata kawo a ranta zai bawa Ummun ba, sannan koda ya bawa Ummu har Fanna tayi magana taji a ranta haka ma ba laifi, sai dai yadda ta ji Ummu ta bawa Hajiya Kaltuma hada kayan ya sosa mata rai, duk da Ummu tana bakin kokarinta wurin hada kan Yaranta sai gashi taji b'acin rai ita Yaranta basu mori tafida ba, ta dauka ta bawa Hajiya Kaltuma, shi yasa taki magana ko da Tafida ya ce su je su amsa, wannan abin ya kara b'ata musu rai amma suka share, gashi nan an basu kudin amma burinsu shine su san nawa aka bawa Ummu sannan me ake haΙawa Ummu. Ranar Samha kanwar Sa'adiyya ta je amsar abu a wurin Nabilah, take jin Hajiya Kaltuma tana waya da Ummu da irin abin da ta saya, gasu nan a daki, dake yarinyar ta kware a gulma ta nufi wurin Hajiya Shuwa ta gaya mata ita kuma ta kira Saadiyyah ta tambaye ta, Saadiya babu lissafi tayi ta dokawa Tafida kira amma yaki Ιauka ta tura mishi rashin kunyar da ta saba mishi, bai kulata ba haka yasa ta kira Rukayya ta wanke ta tas ta kuma ce mata tasan adadin kudin da ya tura wallahi suka makale mata kudinta sai sun gamu da ita, haka yasa duk suka sha jinin jikinsu. Jin labarin kayan Ummu suka yanke hukuncin a gidan Hajiya za a hada kayan, tunda sun mata alkawarin ba zasu kara batawa Aliyu rai ba, zasu kaunace shi kamar kullum, shine zuwansu na farko yar gidan Rukayya ta janyo Mufidah ta fado a kujeran Hajiya tana sallah, Fanna ta zo ta dauke tana Amir dan Rukayya yana faΙin. "Afnan ce ta janyo ta fadi!" Haka bai gama rufe baki ba Mufid da yake wasan shi ta gantsara mishi cizo, lokacin Maryam ta shigo parlour kenan daga kitchen, ta ga Fanna tana buge ma Afnan, "Fanna ya haka da zafi?" "Cizon Mufid tai bayan ta janyo Mufidah daga kujera!" Daidai Hajiya ta fito daga dakin kenan, "Mu gani!" Inji Maryam tana gani ta kyalkyale da dariya tana faΙin, ana koya mata jarunta ne, shi kuma an nuna mishi shi namiji ne ai Yara ne!" Ai kuwa Fanna ta hau bala'i tana masifa ta ce. "Wannan shine karo na biyu da kuka yi haka, duk lokacin da kika zo sai wani abu ya sami Yaran!" Tana fada tana jijiga Mufid, "To ai yara ne ni ban ga abin tashin hankali ba, da ake ta wani cece kuce." Shi kuma Tafida yazo ne domin maganar tafiyar shi da Ummu tow ya bawa Hajiya ajiyar wasu takardun Deen, yana zuwa bakin kofar yaji abin da suke fada karshe ma suka maida Fanna mahaukaciya Har Rukayya tana zungure goshin Mufidah da c. "Uwarsu ta maida mana Uwa Nanny, Yan banza masu idanu irin na zuriar da suka hada iri da arna, bar kallona don Uwarka!" "Wai me yasa kike haka ne, a madadin ku rarrashi yaran sai ku zauna kuna irin haka." "Hajiya ke kika mana alΖawarin babu bambanci tsakaninmu da Tafida, mu kuma zamu zauna da shi lafiya don Allah kada ki ce kome, idan kika yi magana zamu dauka goyan bayan Tafida kike, yara kuma sun yi laifi dole a hukunt..." turo kofar yayi a tunaninsu Ummu ce har rukayya tana faΙin. "Ku ji yar iska ta ji kukan Yaranta ita me yara wato zata nuna mana ita uwa.." maganar ce ta makale ganin Tafida ne a tsaye da sauri Hajiya ta nufi Fanna zata dauki Mufidah. "A'a Hajiya! Kada ki tab'a min Yarana, ba sai kin nuna min kin fi son su da ni ba. Idan na kintatta daidai tow kina tare da ni ne don daukakar da na samu amma bayan nan babu ruwanki da rayuwata, kaf duniya mutane uku suke sona a yadda nake bayansu babu kaso daya na soyayya ta a idanunki, amma Abba, Ummu, Deen, sune kaΙai mutanen da nasan suna kaunata ba tare da abin da nake tare da shi ba, kina tare da ni ne Hajiya domin darajarki amma Yaranki sune a gabanki, amma ni bana gabanki domin kuwa na gani a idanuna na kuma.." "Tafida baka san wasa ba ne? Yaran nan wasa suke da junansu " yadda ya zabura yasa Hajiya ta shiga tsakaninsu. "Da kin sake na tako inda kike sai na zubar miki da haΖora bar ganin kin girme ni sai na zane ki wallahi." Yadda yake shiga banan yake fita ba, sannan ya ce su fita mishi a gida ko ya basu mamaki. Duk da haka Hajiya bata wani nuna damuwarta ba, sai da ta ga ya tafi kuma ya hana Ummu kawo mata Yaran, ga Maryam da suka yi rigima da mijinta da kannen mijin, Uwar mijin ta goya musu baya da cewa bata isa ta raba mata kayan Yara ba, idan ita Uwarta ta kasa hada kansu taci karya bata isa ba, don suna hakuri da ita da mugun halinta waye zai iya zama da ita da wannan halinta, wannan abin ya bawa Maryam haushi ai kuwa tayi tsalle ita Yayar gwamna Tafida za a ci mutuncina, ta bar mata danta idan ta haifi dan halak ya aiko