Showing 231001 words to 234000 words out of 241571 words

Chapter 78 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14725

Ummu tana da mugun nufi da yau ban kawo haka ba!" Ita bata yarda ba, amma tunaninta kawai asiri akawa yarta. Koda muka kai abincin nan matar nan kiri-kiri ta so nunawa Tafida bata son abincina, shi kuma ya ce ai Asiyah ce tace tana so, duk yadda taso hanawa bai samu ba, haka ya bawa Asiyah taci ta sha magani. Tun daga ranar sai ta tsiro da wani abu kafin nayi abinci na kawo ta gama, ta bata dole ta ci, a hankali lafiya na samuwa, Mahaifiyar Asiyah na kara neman hanyar raba zaman lafiyarmu. Kwana biyu sai ga baki daga Yola sun zo yayun Asiyah mata ne, Amrah da Safna. Sai wata dattijuwa, me kama da yan bori . Kana ganinsu kaga marasa mutunci, tunda Fanna ta gaya min yadda suka mata, da ta kai abinci sannan suka dawo min da shi, na saka Fannah ta mikawa su Matori. Allah ya sani tunda ta fara wannan abin na rufawa kaina asiri na mike da addu'a, ba dare ba rana. Haka yasa bakiɗaya na tattara shirginsu na watsa a gefe, a idan yamma yayi lokacin dawowar Tafida za a bunka wani hayaki, wanda kowa ya shaka sai ya ji wani irin abu, Tafida da yake bai da kirki ranar da ya shafa sai da ya rufe idanunshi yayi ta fada shi baya son irin wannan hayakin bai da dad'i. Ina ruwana ni kan su suka ji wurin. Sai aka bar shi sai bayan ya dawo ake sakawa. Sun zata Tafida haka kawai yake zaune, basu san cewa a shirye yake ba. Ai kuwa aiki suke kamar ba kama hannun yaro, satin matar nan daya da zuwa da safe muna barci naji hayaniyar mutane ana ta salati, tashi nayi na d'aga labulen parlourna, hango dattijuwar nan nayi dauke da wani bakin abu kamar leda, ta fito tana nunawa. Tafida da ya fito daga ɓangaren shi ya tsaya yana kallon abun. Kallon windowna yayi ya ga ina tsaye nima, ba zan iya karantar abin da yake kan fuskarshi ba amma tabbas akwai wani abun da na kasa ganowa b'acin rai ne ko takaici. Oho Ni dai kitchen na shiga na yi abin karyawa na ci tunda sun mishi magana cewa yana raba mana kwanakin mu don ana shiga hakkin Yarta, wato da sune abin da yayi min hala mutuwa zasu yi, a bangaren Asiyah kuwa bata jin dadin abin da suke yi. Domin tayi ta fada kenan tana kuka ita bata son tashin hankali su bar mata aurenta kada suyi abin da zai janyo ta rasa mijinta da aurenta.
**
Kallonshi Deen yayi a tsannake, kafin ya cigaba da cewa. "Ka gaya musu gaskiya domin Ummu itama ba jin dadinka take ba, asirin da suke fada tayiwa yarsu basu san cewa yarsu ce ta yiwa kanta ba ko me suke bukata? Ni wallahi shi yasa bana son Tara iyali,kai kanka kasan cewa babu adalci a cikin gidanka." "Yes i know Deen amma ya zan yi? Wallahi kamar nayi hauka, itama Ummu ta zuba min idanu." "Ba dole ba, tunda ita Asiya ce y'a ita kuma baiwarku!" "A'a Safiyyudeen!" "Da gaske mana, yaushe Ummu zata huta a gidanka?" "Na sani tsorona daya kada su min sanadin b'allewar sauran aurena, domin zasu cuce ni ne!" Tsaki Deen yayi zai bar office din. "Ina zaka muna magana!" "Idan Ubanka zan tafi !" Ya fada a hasale, "Allah ya baka hakuri!" Dawowa yayi ya zauna yana kallon Tafida, "ka zauna da iyayenta da kai kanka, da itama kuyi maganar gaskiya, idan da hali ka sako Ummu a cikin lamarin nasan ta ba mai yawan magana ba ce,." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mishi. "A'a Ummu ba sai ta shiga ba. A haka ma suna cewa ta gama da ni!" Shiru Deen yayi kafin ya ce mishi. "Kayi duk yadda kake so!" Sannan ya bar office din, kanshi ya kulle kamar yayi ta ihu, haka ya taso office din ya dawo gida. A hankali ya wuce bangaren Asiyah ya same su, tana parlour a wheelchair. "Barka da dawowa." Ya fada tana sauke ajiyar zuciya. "Asie ya jikin naki?" " Da sauki!" Ta fada a hankali, "Kin ci abinci?" "Eh!" "Me kike so?" "Zan tafi wurin Aunty Baby ne kwana biyu ta ki kawo min Junior na ganshi!" Shafa kanta yayi ya koma bayan keken ya turata suka fita akan idanun Yan uwanta babu yadda suka iya, asalima sun tare a gidan kamar gidan Ubansu. Shi ma Tafida a bangaren shi ai yaso haka domin kashe musu kudi yake kamar hauka, don saka Asiyah suke ta kira shi tana son abu haka za a kawo mata, idan kudi ne haka zai tura mata account dinta kafin kwana biyu sun kwashe tas. Wannan abin yana damunta, ko tayi magana basu kulata haka yasa yayi shiru tana kallon, asirin da aka tono kuwa wai nice na binne kada Asiyah ta haihu da Tafida basu san ni tsabar tsoron haihuwar har FP nayiwa kaina ba, ina zan iya jarabar Tafida.


A wurina ta zauna sai dare muka mai da ta ɓangarenta, bayan tayi ta bani hakuri da irin zaman da muke, da zata tafi ta rike hannuna. "Aunty Baby kiyi hakuri don Allah kiyi hakuri." "Ba kome wallahi." Na turata har parlournta, anan na ga Yayarta tana min wani irin kallo. "Ke dai bakya jin magana, uban me kika fita yi a wajenta? Bayan kowa yasan yadda ta miki asirin hana haihuwa!" Murmushi nayi mata sannan nace mata. "Asie Allah ya baki lafiya, sai da safe." Ina fita suka rufeta da fada, ba ruwana su suka sani yar Uwarsu ce. Bangarena na wuce na je na gyara yarana muka kwanta. Can wurin sha daya Tafida yazo. Na fara barci ya tashe ni. " Wai me ke faruwa ne a gidan nan?" "Ban gane ba?" Na mai da mishi tambayarshi. "Kin bawa Asiyah wani abu ta ci ne?" "Babu abinda na bata ban gane ba, wani abu ta ce an bata anan?" "No kawai dai yanayin ne sai a hankali, tana can cikinta yana ciwo!" "Tow ba dai nan ba!" Na gyara kwanciyata, ni ban san wani irin yanayi muke ciki ba, haka ya gama zaman shi ya fita a daren suka kaita asibiti, wurin asuba aka dawo da ita. Aka ce food poisoning ne, shi kenan aka saka ni a gaba na bata guba ta ci, waye ya mutu waye ya dawo duk ka zuba musu idanun bayan na kai ƙarar su wurin Allah, domin abin ya min ciwo shima Tafida bai nuna min ya ji haushi ba.77
Amma kuma idan na bashi abinci ina ganin yadda yake tsince tsince don ma ba Ni ce nake girkawa ba, da wannan abin na barshi da Allah amma da ciwo matuƙa, kai karshe dai lamarin sai da aka kai da Abbanshi ya shiga lamarin domin ya daina shiga harka ne, nima da na ga haka na tattara kowa na watsa a gefe, ko Mama ban gaya mata ba, balle Tina, na hadiye a raina, na cigaba da harkana, abin da suke bukata kenan, ita kan Asiyah tana jin su kamar an rufe mata baki, sai dai tayi ta binsu da ido, amma abinda yake faruwa yana mata ciwo. Ni kuwa zuba musu idanun nayi domin nasan Allah ne zai wanke ni, kuma shi zai bi min hakkina, domin ban yafe musu ba, kullum da haka nake kwana. Abin da ya kai kuwa Abba yazo cikin maganar yadda Tafida ya mai dani ban san ciwon kaina ba, na farko baya cin abincin duk da bani ce nake girkawa ba, amma sai ya kauracewa abincin idan aka kawo aka jera, dalilin da yasa na kara yarda zargina yaƙe ranar na tafi bangarenshi yana girki ya shiga dakinshi kafin ya fito naji kauri a kitchen din, shine na leka kitchen din na kashe gas din, abin mamaki yana fitowa ya fara tambayata da cewa. "Me kika zuba min a cikin abincina? Ummu me kika saka min a cikin abincin yanzu na saka na tashi fa!" Wani abu na ji ya tsaya min a raina, na ce mishi. "Yanzu na kara yarda da zargina kake Tafida tun tuni ban ciyar da kai guba ba, sai yanxu Anya kayiwa kanka adalci? Ba kome!" Na juya na bar bangaren shi ashe wasa farin girki, domin ya zubar da abincin, ya sha tea. Washi gari na shirya yarana na barsu a wurin Fannah. Na nufi gidan Abba da rakiyar jami'an tsaro, koda muka je Abba baya gida a wurin Inna na zauna naki gaya mata kome, ina zaune sai ga shi ya dawo, bayan mun gaisa nayi shiru kafin nace mishi. "Abba nazo niman alfarma ne!" "Na me fa!" Ummu, murmushi nayi me ciwo kafin na ce mishi. "Ina son ka saka Tafida ya sake ni!" Sake goran swan din hannunshi yayi ya kalle ni, "akan me?" Gyara zama nayi, domin yanzu nayi alƙawarin ba zan kara barin a cutar dani da bakina ba. "Abba zama da zargi kasan haramun ne?" Jinjina kai yayi, "tow Tafida ta kai ni madakanta da ba zan iya zama da shi ba, Abba Tafida ba shi ɗaya ba ne, amma namijin da zan tsaya kullum ina kuka akanshi ba, Abba idan na cigaba da kallon Tafida yana zargina raina zai ta b'aci, ina da gata ina da kome akan me zan kashe rayuwata akan Tafida, Allah ya gani ina son aurena amma ba zan iya zama.da Tafida ba kome muka hada da shi na yafe." Na gayawa Abba gaskiya, hakuri yayi ta bani, na sake murmushi na ce mishi. "Abba idan don rigimarmu ce ba zan zo gare ka ba, amma tunda ka ga nazo tow kasan maganar ta wuce iyakarmu tafi karfina, Abba idan Mamana taji abin da Tafida yake min ba zata yarda na koma gidansa ba, gara muyi tsayayya magana." "Na sani amma kiyi hakuri!" Haka yayi ta bani hakuri dakyar na hakura na dawo gidan, ban san yadda suka kaya ba sai ga shi nan ya kwaso babban riga zai min iskanci na dakatar da shi ta hanyar bude mishi idanun nima. "Ce maka aka yi ina tsoron rabuwa da kai ne? Ko an gaya maka akan kawai xan kare? Ba gaji ka je kayi duk abin da zaka yi amma aurenka ka saka a ranka na gama! Auren da tun da nayi shi ban cika shekara daya cikin farin ciki ba."
"Haka kika ce?" "Eh na fada sai me? Me xaka yi ko an gaya maka ni wancan Ummu da ka sani ce , bari ka ji da kyau ka sake ka kai maganar nan gaban Uwata zaka fahimci Allah da girma yake na daina jin tsoron saki tun daga ranar da ka sake ni na gane i'm just useless a tare da kai, bukatarka kake biya ni kuma oho!" Jin haka yasa shi kwasar kafarshi ya bar bangarena, ai don bala'i har part dinsa na bishi don ba zan cigaba da kallonshi yana cutar da ni ba, haka muka yi ta rigima ganin bai da gaskiya fita yayi ya bar gidan, na dawo part dina, kada ku dauka ihu da jaraba nake a yadda muryata yake da sanyi a haka nake ta faɗa da masifa. Bai shigo gidan ba sai dare, lokacin munyi barci, washi gari Juma'a, na tashi bana son yin kome ashe ya gayawa me yin abinci za ayi baki, ina kwance ya ta kirana ina ganin kiran naki dauka sai da na ga number Deen na dauka muka gaisa ya ce min. "Gashi nan yana son magana dake!" Kashe wayar nayi, ya sake kira naki dauka. Wajen karfe uku na yamma sai ga Abba, Baba Bulama,da Babana. Suka zo sai Tafida da Deen, anan aka zauna suka bude taro da Addu'a, kafin suka tambaye shi, kame-kame ya fara yana zare idanu. "Ummu ta gaya min kome ban san abin bai wuce ba." "Au dama kasan da rigimarsu?" Baba Bulama ya tambaye shi. "eh na sani Alhaji !" Nan Abba ya gaya musu abinda yake faruwa, take jikinsu yayi sanyi. Kaina a kife a kasa ina kuka. "Ni dai don Allah ya janye igiyar aurenshi na huta da abinda nake gani wallahi zan iya mutuwa don Allah ku roke shi " "A gaskiya ba zan boye muku ba na gaji da maganar auren Ummu da Tafida!" Baba Bulama ya fada kai tsaye, duk suka bishi da idanu. "Alhaji Bulama!" "Da gaske nake gaya muku, Tafida ba yaro bane, duk wani abin da Yarinyar nan zata yi tayi domin ta zauna lafiya a gidan aurenta, Ummu tun tana yarinya ba me fada ba ce bata da abokin faɗa, har mamakin yadda ake kawo min karar kowa amma ban da Ummu. Kai kanka kasan Ummu bata da matsala, zargi ya shigo da batun guba don Allah ya sawwake mata ta huta, yana da damar aure yake bukata yaje yayi, amma ya saka Ummu a gaba gaskiya akwai matsala, idan baka son Ummu ka sauqaqe mata, kayan nama bashi kashe dan kura!" Wannan maganar da Baba yayi ya sani jin tabbas ina da gata, kuma yadda ya tsaya min yasa Ni jin kuka ya zo min, haka aka yi ta bashi hakuri ya ce tow. "yana zaune da ita bata kashe mishi kowa ba sai yanzu zata kashe mishi Matarshi? Har ya kauracewa kome nata, kawai ya sawwake mata, ai tun sakin farko naso kowa ya kama gabanshi amma ganin ita Ummu tana son Mijinta Ni da mahaifiyarta muka dawo da ita me yake da shi da zai na wulakantatta. Kawai ya sake ta ya huta itama ta huta, irin wannan bakin cikin ne za a wayi gari mutum ya mutu?" Sai na kasa cigaba da kuka domin jin dadi da farin ciki, na ce mishi. "Baba wallahi na gaji ne, na gaji ne na gaji ne na gaji kullum na rasa yadda zan yi ita Matarshi bani da matsala da ita, amma shi ya kasa ganewa na gaji!" Ai kamar na kara zuba mishi ruwan zafi haka Baba Bulama ya kara hawa, dakyar Babana ya bashi hakuri ya kuma shiga maganar Abba kan ya kasa magana. Haka aka dawo ana bani hakuri, dakyar dai kome ya wuce aka bamu hakuri suka tafi, ni kuwa naki ko gaida Asiyah na daina,abincin gidan na daina ci nawa nake girkawa.


A bangaren Abba kuwa shiganshi wurinsu Asiyah, ya ce Turai ta tattara ta bar gidan Idan ya kara jin labarin tana nan zai saka a sake Asiyah ta je can su zauna, ai dole ma Ummu ta rabu da Tafida an hada makirai a gidan, bayan tafiyarshi aka fara jefa min habaici da zagi da cin mutuncin, abinka da yan Yola ga fulatanci ga shuwa, ni dai ban bi ta kansu, idan ma na damu tow tabbas naji zafi kenan. Kwana biyu a tsakanin suka bar gidan bayan sun yi alƙawarin zaa kawo mata wata me kula da ita, ana murnan an rabu da Bukar ashe za a haifi Habu, yo me kuwa ya kawo haka, ba kome ba ne sai yadda Tafida ya mai da ni hoto, domin bakiɗaya tausayi Asiyah yasa yana min gashin kumma, babu wanda yasan da haka sai ni da shi, ban sani ba amma tabbas na gaji bana son a ga kamar bani da hakuri ne. Ita dai a bangarenta bani da matsala da ita amma a bangarenshi bani da banbanci da da namiji, idan ma mu'amalar aure ce a take zai fara mita ya gaji yayi me,.sai yanxu na kara gano dalilin da yasa matan gwamnonin wasu suka lalace kenan, daga nan ban kara sarewa ba, sai da muka samu wani matsala ya saka Matarshi a gaba suka tafi inda, nayi kuka nayi bakinciki nayi danasanin dawowa ga Tafida, bayan tafiyar shi na fahimci zaman me nake a gidanshi? Haka na danne zuciyata. Nayi kuma hakuri har suka dawo, nayi musu tarba me kyau, sai dai basu wani farin ciki ba, haka na cigaba da dauke kai, har muka samu shekara ɗaya,lokacin Junior yana yawon shi ko ina, na fita hayacina ban san me nake ciki ba, wata rana ina zaune a parlourna, nayiwa Yarana kwalliya ta shigo min. Ina kallonshi kamar wanda aka wurgo shi, ya kalle ni kafin ya ce min. "Ummu!" "Na'am!" "Ko zaki tafi gida ne sai na nime ki!" Bai idda rufe baki ba, na mike zubur, na wuce daki na shirya kayana iya nawa, na juya na fito duk da raina a b'ace yake amma sai naji kamar an yanke min wani azabar da ake gana min, ina fitowa ya kalle ni. "Yaran fa ya zanyi da su?" Ya tambaye ni ban san lokacin da dariya ta kwace min ba. "Bura uba! Ni zan kwasar maka yara? Tow bari kaji ai bada su na zo ba, ka manta ni ne wato? Bye." Na saka kai xan fita ya dibo jiki yana faɗin. "Ummu kizo ki kwashe Yaranki!" "Baka da dangi ne? Ko baka da wanda zai rike maka su ne? Nima gidan Ubana zan tafi malam bani hanya na wuce" na bangaje shi abuna, na bar gidan Matori suka ka ɗauke ni a mota muka wuce biu, tunda na shiga gidanmu. Tunda na shiga parlourn Babana nake kuka nima sai yanzu nake jin kamar an yanta ni da kunci nake ji kamar ma fito daga azaba, nayi sallah nayi addu'a bana barci amma ina Tafida ba mijin aure ba ne..
Bai gayawa kowa halin da ake ciki ba, ya kwashi Yaran ya bawa Asiyah da Fanna, ita kan ba lafiya ce da ita ba, sai Fanna ce take fama da yaran, musamman Junior da yake rikici, A lokacin da ya dawo Asiyah ta mishi magana, "me yasa ka raba su da Uwarsu? Fisabiilillahi Ya Aliyu baka da adalci, Aunty Baby tana kokari tana adalci amma ka rabata da Yaranta, idan har wani abu ake maka wallahi ka tashi tsaye domin rabuwa da Aunty Baby kamar rusaka ake son yi." Daga nan tayi kwanciyarta, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login