Showing 108001 words to 111000 words out of 241571 words

Chapter 37 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14720

xai yi yawa kuma ya dauki lokaci haka ba, sai da muka kusan makara ya kyale ni, kasa tafiya nayi domin kafaffuna kamar ba zasu dauke ni ba, haka ya riko ni zuwa banɗaki nayi wanka asalima zama nayi cikin ruwan dumin, a gurguje na fito na samu ya hada min tea mika min yayi da zafi-zafi na sha sannan ya ce min! "Sannu kin ji!" Dake ina bakin gadon daure da towel, kasa kallonshi nayi ina gama sha ya mika min farfesun jiya, kafin ya wuce yayi wanka sannan ya fito shima yayi sahur. Ganin ina bawa Yaran nono ya dawo bayana ya zauna tare da saka hannunshi dukka biyu a kasan cikina. "Ina tumbin?" Murmushi nayi nace mishi. "Ya koma!" Shiru yayi kafin ya sumbaci dokin wuyata. Muna zaune a wurin aka sake kiran sallah, amsa Mufid yayi ya kwantar da shi sannan ya amshi Mufidah ma, kafin ya ciro min doguwar rigana, muka yi raka'atul fijr. Muna idarwa ana shiga sallah asuba, a tare muka yi sallah, bayan mun idar mun jima muna addu'a, da azkar sai da rana ya fara fitowa na rarrafa domin sai yanzu na ji kafar ya min tsami. Gadon na hau na kwanta don wallahi jikina ciwo yake, musamman yadda ya makale yaki kome don rashin kirki, na juya xan harare shi. Ware idanun yayi yana faɗin. "me nayi kuma ake hararana da alamu ana zagina a rai kenan, tow na yafe miki, yar aljannata!" Kwanciya nayi ya dawo bakin gadon ya zauna tare da rike hannuna yana murzawa, murmushi muke sakarwa juna, a hankali barci yayi gaba da ni, shima gadon ya hau ya kwanta a bayana, tare da janyo ni jikinshi. Ban da azumi babu abin da zai hana shi komawa ruwa shi ya san abin da ya ji ya kuma tab'a ya ji. A hankali shima barci yayi gaba da shi, wato ranar Tafida tun kafin yau ya mikawa Deputy koma ya ce mishi sai Monday.


***
A bangaren Mama tunda ta sauka ta kira uwani suka gaisa ta ce mata. "Ina Ummu!" "Yaronta bai da lafiya, sun kai shi asibiti ita da Deen wayarta kuma kin san tun tafiyarta ta saba barin shi a gida!" "Tow Masha Allah idan na samu lokaci zan na kiranku, yanzu lokaci ne na ibada a kwanakin karshe xan mika lamarin Ummu da naku ga Ubangiji, in sha Allah kafin na dawo zan yi addu'a sosai Ubangiji ya kawo miki miji na gari mijin marainiya kin ji Uwanina!" "Tow Uwata sai kin dawo Allah ya baki ikon mana addu'a!" Suka yi sallama. Mama tana son Uwani sosai irin so na gaskiya nan takewa Uwani yarinyar ma tana son Mama. Haka Mama da ta kira Baba Bulama shima ya gaya mata ai Ummu danta bai da lafiya ne, ganin duk bakinsu daya yasa Mama ta yarda, bata san cin amanarta suka yi ba.
***
Karfe daya da rabi na farka, na samu yaran an musu wanka sai wasa suke da junansu, idan ba mafarki ba ina ga har nono Tafida ya ciro ya basu amma dake barci ya ci karfina ban iya bude idanun ba. "sleep beauty!" Make hannunshi nayi ina faɗin. "Kai da Yaranka sai da kuka shanye min nono ko?" Na fada ina gyara zaman rigar jikina. "Ayya sun tashi na rasa yadda xan yi shi ne na gyara ki na basu kowanne ya kama, suna gama sha na dama masu madara suka sha, kin ga har wanka nayi musu!" "Yaushe ka dawo Nanny!" "Taso na hada miki ruwan wanka kin ji!" Tashi nayi na ga yaran aka wani abin wasan Yara. Yana tsaye yana kad'awa Mufidah da take bangala mishi baki, na zo na rungume shi ta baya, karatu Tinah. "Good afternoon My Yallabai!" Wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Qurratul-Ayn! Kin tashi lafiya?" Juya mishi idanun nayi na wuce banɗaki, na leko yana tsaye inda na barshi. "Baby bani jakata akwai brush da toothpaste!" "Akwai sabi na bude mana!" Murmushi nayi na ce mishi. "Ban gani ba!" "Don Allah ki rike wannan muryan taki, wallahi ban shirya yin sittuna ba!" Ya shigo ban dakin ya dauka tare da matsa min. "fita kafin ka karya mana azumi!" Na fada a sanyaye. "Idan aka ga na suma kece wallahi!" Murmushi nayi na rufe ban dakin nayi wanka sosai, sannan na fito, shi da Yaranshi suna can parlour, na gyara jikina kafin na fito, muryanshi da naji da Deen yasa na koma dakin, sai kuma na saka Babban hijab na fito na gaishe da Deen, sai Hararata yake yana faɗin. "Ke bana ce kada ki fito ba!" "Ka ji guntun dan iska, ita Kanwata ce yayar Jalila ce, ka saka Ammah ce ta haife ta dan iska kawai! Ummu ina fatan bai miki kome ba ko?" Ya tambaye shi yana nad'e hannun rigarshi. Dariya suka bani na girgiza kai ina faɗin. "Bai min kome ba! Ya Sadika tana lafiya ta kusan sauka kan yanzu ko!" "Eh wallahi ina kyautata zaton karshen watan ko farkon sabon wata!"
"Allah ya raba lafiya! Yallabai kitchen nake son shiga na maka aikin kafin na tafi!" "Ba fa zaki tafi yau ba, sai wata sati!" Rufe bakina nayi da hannayena, wani irin tsoron Mama ya dirka min kamar an wurgo dutse daga sama. "Ka rufa min asiri!" Murmushi yayi ya ce min. "Allah da gaske wayar mana na saka an sace shi a can Saudiya amma fa za a dawo mata da shi, kiyi hakuri Alhaji Bulama da Babanki sun sani, hankalin Mama ya kasu gida biyu tana ibada kuma kafin faruwar haka tayi waya da Mijinta da kuma Uwani, ki fahimci wani abu ina son mu kasance tare shi yasa na zabi haka amma kiyi hakuri da abin da nayi, wallahi bani da zabi ne ina son na zauna da ke na wasu kwanaki kafin ta dawo Please!" Hawaye ne ya zubo min. "Yanzu kawai don ka zauna da ni sai ka sakata a zullumi bata yi magana da kowa ba." "Mama ba irin sauran iyaye ba ne, Mama tayi magana da kowa kafin na saka.aka dauke wayar amma bari Deen ja ce yarinyar ta maida mata wayarta." Juyawa nayi zan koma dakin ya ce min. "Ki shirya zan mai dake gidan!" Yadda yayi maganar sai naji hankalina ya tashi, haka na wuce dakin na zauna ina jin kuka yana zuwa min.
"Kana burge ni Tafida, kai tsaye kake lamarinka. Na ji dadi da kake fadar gaskiya ba ƙaramin aiki bane fadarta." "Deen tafiya zata yi fa!" "Ba zata tafi ba, yanzu ka je kace ta shirya zaka fita. Sallah juma'a zaka ajiye ta a gidansu!" Ya kuwa mike, ya nufi dakin Deen sai dariya yake mishi yana wasa da Yaran kaunar da yakewa Iyayen Yaran ya shafi yaran sosai, don yana jinsu kamar na shi.


A bakin gadon na zauna ina shashekar kuka, domin nasan ba wani sauyawan da yayi, yayi min laifi kamata yayi yazo ya rarrashe ni amma yace wai na shirya zai ajiye ni a gida, wato yaci moriyar ganga, duk sai naji na tsani kaina da ban biyo shi ba da ba zai min haka ba, haka na cigaba da kuka, ban kawo a raina zai zo din ba sai gashi ya turo kofar, wani irin sanyi naji ya tsirga min, na d'ago kai ina kallonshi shima kallona yaƙe. "Allah ya huci zuciyarki, nayi laifi a yafe min dama can ni tsohon mai laifi ne, kuma na kara aikata bayan laifi ayi hakuri ba zan kuma ba." Ban kalle shi ba, na cigaba da share kwalla da yake zuba min, "Tow tunda ba zaki min magana ba, bari na hada kayanki na kai ki gida!" "Dama ka kawo ni ne ka min koran kare!" *Yes i hit the point!" Narke min yayi cikin rarrashi ya ce min. "a'a tashi na kai ki gida don Allah, wannan abin da nayi ina jin kunyar kallon idanunki!" Ya fada yana me durkusawa a gabana ya zuba hannunshi akan cinyoyina. "Ni dai kada garin son zama dani kayi ta aikata kuskure bayan kuskure, ka rufa min asiri kada kayi wani abin da zai tab'a rayuwarmu bakiɗaya." Na fada ina kuka, "ita mahaifiyata ce, dole naji wani abu na ga kamar ba sona kake ba, dama can na san Babu so kawai muradi ne ta zuciya...." hannunshi ya saka ya rufe min bakina. "Don Allah ki daina fadar haka wallahi bana jin dadi, nima Uwata ce, yanzu haka na saka za a maida mata wayarta ba zan kara wasa da rayuwar wani saboda ke ba, amma kiyi hakuri ba zan kara ba kin ji!" Gyada kai nayi ina share hawayen da yake zuba min. "Kiyi hakuri xan tafi sallah kada na makara!" "Allah ya tsare muje na tayaka shirya." Gaban closed din shi muka nufa na cire mishi wani babban kaya shadda ce fara sal, sai hular da zai haka da kayan, sai takalmi da links zamana da shi a abuja, baya saka babban kaya dai ranar Juma'a. Amma kusa na haddace shigarshi. Yadda yaga ina taya shi saka kayanshi ba tare da na damu ba, ya ce min."Ina tunanin ko idan kika dawo na barki a nan ne ba sai kin je government house!" Shafa kumatunshi nayi ina faɗin. "Duk yadda kace yallabai na!" Jan hancina yayi yana faɗin. "An gama yarinyar nan hancinki Mufid ya dauka. Mufidah nawa!" Ya fada yana haɗe rai. Dariya nayi ina faɗin. "Kuma laifi ne don haka ya faru?" "Kawai dai kishi nake da kika raba shi Abba ya dauki hancinki Ita Uwata kika barta da irin nawa hancin!" "Ba ka ga yadda yaran suka zamo kalanka ba!" "Hmm kuma haka ne kin fini gaskiya!" Ya fada yana rike hannuna, "ki so ni koda dan ne, ni dai nasan ina miki mahaukacin so ne! Ummu Hadiyya ina sonki sosai, irin son da nake jin ban yiwa kowa irinsa ba." Girgiza kai nayi ina faɗin. "'Lokaci yana tafi kace fada zaka je sallah!" "Eh anan nake zuwa tunda na zama gwamnanku!" Jan kumatunshi nayi ina faɗin. "Ka kyauta!" "Gobe asabar zamu shiga Biu ki shirya da wuri fa." Kallenshi nayi kafin na ce mishi. "Gobe kace amma kana ce min na shirya da wuri!" Na fada ina yaƙe. Mika mishi hular da yake hannuna nayi ya kansa ya kafa, wurin turaren shi na nufa na ciro na fara fesa mishi yana murmushi. "Na gode zan tafi mai xan sayo miki!" "Duk abin da ka gani ya maka kyau ina so nima zan min kyau!"
"Hmm ji nake kamar kada na tafi!" "Muje maza Yayana yana jiranka, ka wani bar mishi renon Yaranka!" Muka fito ina gefenshi, "Nanny sannu da kokari ka ji!" "Kam uban can ni ne Nanny?" Deen ya fada da karfi yana nuna kanshi. "Lallai tafiya daga dan iska sai kai, a rashin mutunci ni zaka kalli tsabar idanuna kace min Nanny ka ɗauke ni dan daudu ne!" Yadda Deen yake tijara sai naga sam haka bai damu Tafida ba, asalima sumbatar goshin yaran yayi yana faɗin. "Kuyi hakuri Abbanku yana ta ihu, sai na dawo Yarann Daadi da Abba! Idan ka gama basu dariya muje don Allah!" Wayarshi ce tai ƙara ya kalla yana sake tsaki yayi ya ce. "Deen ya zan yi da Asiya ne?" "Ina ruwan sly Queen!"
Juyowa yayi ya kalle ni, "wata cousin dina ce!" " ka gaya mata me kama fatalwa kin san an bashi mace dan iska ya ce baya so!" "Deen kada ka ja min bala'i don Allah!" "Yaya Deen kace dama can amanata kuke ci?" "A'a ban dani dan iska dai yake cin amanarki!" Ya nuna tafida da hannu, "Ka aurota!" Na fada zan juya, "Ni fa ba dan iska ba ne, kuma abu daya gare ni kin ga ya wuce daya ne? Da zaki ce na aurota!" "Yallabai ko bance ka aurota ba, wajibi ne auren mata sama da daya, Allah ya baka budi da rufin asiri in dai ba son zuciya ba, ai kana da damar rike mu mata hudu!" "Ummu Hadiyya ki fita idanuna na rufe. Auren ce miki aka yi da sauki ne da shi da zan rike mace sama da daya Hadiyya ki fito Ki gaya min bakya bukatar zama da ni mana!" Murmushi nayi na wuce shi don nasan ya cika haka suka fita, a waje ya amsa wayar yana me bude mata tsohon littafinsa na tijara, jin tana kuka yasa shi sasauatawa ya tambaye ta me ya faru, bai karasa ji ba ya kashe wayar ya nufi massalaci yana zargin Deen da hada mishi husuma me Deen zai yi ban da dariya.


Bayan fitarsu nayi alola na zo nayi sallah, sannan na kunna wayata na kira Uwani na gaya mata ba zan dawo ba, ta ce min ai Baba ya gaya mata. Murmushi nayi sannan na kashe wayar na ja Yarana muka shiga kitchen, mamakin yadda aka zuba kome na zamani nayi, ina cikin aiki wurin karfe biyu da arba'in da biyar, ya kira ni. "Ummu Hadiyya! Akwai matsala!" "Ina tare da kai babu wata matsala gaya min me nene?" Daga can na ji Deen yana faɗin. "wallahi billahi azim ba zata zauna a inda Ummu take ba, ka kaita gidan Abba ko ko gidan Hajiya ba zata zauna ba, Ummu tana buƙatar ka kana bukatar Ummu, meye amfanin kebewan da kayi ba don ku huta ba ne, Yaran nan wallahi ban da suna shn mama da na rabaku dasu, ko ka kaita gidan Maryam amma ban da Ummu."


"Wai me ke faruwa ne?" Kashe wayar yayi.
Mamaki ya kara kamani na kira Tafida, "zan kira ki!" Kashe wayar yayi..
**
A can kuwa Abin da ya faru, Asiyah ta sab'a lamba, domin ta tabo Saadiya a daidai lokacin da take cike da Tafida, abun da ya faru kuwa, tun da Tafida ya bar gidan bai gaya mata zai tafi bude sabon titi a wani kauye ba, take cika take batsewa domin a bakin yan gulmanta take jin labarin, har dare aka sha ruwa babu Tafida, ta kira Deen lokacin yana waya da ya gama ya kashe wayar domin shi dai bai da amsar da zai bata, wurin karfe hudu na asuba kamar ance ta fito ta hango Asiyah ta fito kamar daga ɓangaren Tafida, haka yasa ta kara kallon sosai ganin ta ga sun sake rungumar juna, kafin ta wuce inda take zama, tana ganin ya shiga Mota ya bar gidan. Jikinta yana tsuma kawai ta fito da gudu lokacin Asiya ta shiga bangaren da take ta rufe kofarta, komawa tayi ta shirya har karfe daya na rana Asiya bata fito ba, sai wurin karfe biyu ta fito. Ai kuwa Sa'adiyya tayi wuf da ita tayi ta bugata da kasa, tana bata kashi. Sannan ya yakushe mata fuska tana ihu karuwa kwartuwa me bin mijin wasu. Yadda kuka san mahaukaciya haka aka dauke Sa'adi baby akan Asiyah, duk abin ba dadin gani. Da ta samu ta shige dakinta ta kira Tafida tana kuka, shiri tayi amma bata zata wannan me kalar samudawan zata mata mugun duka haka ba, sai gashi ta yakushe mata fuska, sai da tayi kukan bakin ciki, bayan sallah juma'a Tafida yazo gidan ganin har lokacin Sa'adiyya tana ihun sai ta kashe Asiyah yasa Tafida kallon Deen. "Ku sake ta ku je!" Suna barin wurin ya nufeta. Aikuwa farar shaddan jikinshi ta damke wuyar rigarsa da ta yaga har kasa. "gaya min me nayi maka zaka ci amanata, ashe karuwa ka ajiye a gidanka, shine ka hanani hakkina, wallahi ba zan yarda ba muje ka bani hakkina nima na haihu kamar Ummu." "Kin ga nan ba kamar da can baya bane, ko ina akwai jami'an tsaro Please mu shiga daga cikin gidan!" Dake tana ganin girman Deen haka suka shiga rarrashinta da tambayar me ya faru bakincikin ya hanata fadar abin da ya faru sai kuka da rantsuwar matukar bai d'aga Asiyah a gidan ba zai samu gawarta, dakyar Deen ya kwantar da rigimarta, sannan yazo ya ga Asiyah sai da yaji babu dad'i. Yarinyar fuskarta ya kumbura. Shine yake tunanin ya kawo ta wurin Ummu ta yi jinya, Deen yace karya kenan. Ba zai yiwu lokacin da ya samu zai kula da kanshi da iyalinsa yace zai karawa kanshi yan sa'ido ba, don haka yasan yadda zai yi da ita......
#Tafida
#Deen
#Ummu
#Sa'adiya
#Asiyah
#Mahmoud🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Kada ki ce zaki dauki burgewa akan nawa rayuwar ni da Yarana muna bukatar Uwa a cikin gidan nan, don Allah ki mana alfarman ki zauna a gida, ina matukar kishinki!" Ya fada yana kamo hannuna, ji nayi kamar zan yi kuka wani ya fada min abin da yake ranshi wanin ma Tafida da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Kasa magana nayi ya kai ni wani daki yana faɗin. "Wannan shine dakina, yayi kyau ko na sauya domin dakuna uku ne a nan bangaren, naki dakuna hudu saboda baki da wasu laluran. Bangaren dayan kuma akwai dakuna uku shima kamar nawa." "Duk yaushe ka yi gidan nan?" Hannunshi ya kai gefen fuskata. Yana murmushi ya ce talla aka kawo min lokacin muna abuja, shine na gayawa Deen ya shi kuma ya gayawa Abba. Kafin na turo kudin ma Abba ya biya sai na maidawa Abba kudinsa, amma kin san me? Ko da aka zo saka sunan mamallakin gidan Abba sunanki ya saka." Murmushi nayi sai na kasa magana, ya fito dani zuwa daya dakin yana cewa. "Duk wani abu na gidan Deen ya zuba min su." "Saboda baka da lokaci ne?" Gyada min kai yayi yana jan hancina. "Bani da lokacin da xan zauna nayi ta wannan aikin, shi da Matarshi da kanwarshi Jalilah suka min wannan aikin." Murmushi yayi yana faɗin. "Ina tsoron kada wata rana na juyawa Deen baya." "Idan haka ya faru zai maka uzuri! Domin shi ma'abocin uzuri ne!" Murmushi yayi wanda tunda muka fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login