Showing 87001 words to 90000 words out of 241571 words

Chapter 30 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14710

ce. "Don Allah Baba kada ka tambaye ni kome. Ina Ummu take, kayi min rai ina bukatarta ne." "Aliyu na gaya maka gaskiya Ummu bata tare damu, ka je duk inda zaka, kayi bincike iya yadda ya dace, amma maganar gaskiya Ummu ta b'ata. Bamu san inda take ba." "Innalillahi wainnalihir rajoun, Na shiga uku!" Ya furta yana kashe wayar, a daren ya kira Kwamishin Yan sanda da duk wani me ruwa da tsaki, tare da Deen aka fara bin tasha amma babu labarin Ummu kai a takaice har ƙarfe uku na dare, ana niman Ummu. Wannan barci barawo bai dace Tafida ba. Lokacin da Abba yaji labarin Tafida ya hautsina garin Maiduguri ana niman Ummu, sujada yayi tare da d'ago hannu sama yana zabga kirariwa Ubangiji.




Hajiya ma lokacin da labarin ya iso kunnanta, hawayen Farin ciki da bakin ciki take. Domin tasan kaf duniya ban da Ummu babu wacce zata jure halin Tafida ba tare da Mutane sun shiga tsakaninsu. Ai kuwa tana son yin Azumi amma ta gagara dole ta dafa abinci na sadaka ana ta rabawa mabukata. Haka lamarin ya kasance, lokacin da Shuwa ta ji labarin b'atar Ummu da Yaranta, kiran Malaminta tayi tana faɗin. "malam aiki kayi mana me zafi haka? Domin Yarinyar nan an nime ta an rasa." Murmushi yayi yana faɗin. "Ifiritu kaezuzu ne ya ɗauke ta da cika Umarnina, ya tsallaka da ita bangon duniya Ummu ta tafi kenan har abada, ba zata kara waiwayar gida ba har abada." Nan ya cigaba da cika shuwa da karya da kuma gaya mata wannan aikin da ya mata sai da ya kashe sama da dubu dari uku, domin ifiritu kaezuzu harijin ifiritu ne baya aiki sai ya kwanta da matan aljanu guda tari cak, saboda kada ya ji sha'awaar mace ya fasa aiki don rauninsa kenan, don haka Shuwa ta tura mishi dubu dari hudu.


Wasa wasa Tafida yana tsaye ne, amma ya zabge kamar bishiyar da aka wanke mata rasanta. Kallon Abba yake da yasaka shi a gaba yana mishi fada. "Ayi haka akan Ummu ka daina zuwa office sai dai kawai kayi ta yawo a gari, Al'umma suka zabe ka ba Ummu ba, ka tsayar da hankalinka akan Mutane ." Bai ce kome ba har Abba ya gama sannan a hankali ya mike yana faɗin. "Na ji Abba!" Ya bar parlourn, yana fita ya fada Motarshi. "Ghali wuce da ni Biu!" "A daren nan?" "Muje babu abinda zai faru!" Haka suka dauki hanyar biu. Basu isa ba sai karfe biyu na dare, a kofar gidan Baban Ummu suka tsaya, a tsohuwar daren nan ya buga gidan Baban Ummu. Sai da suka buga sau uku Baban Ummu ya fito yana faɗin. "waye ne a wannan daren?" "Aliyu Tafida ne!" "A wannan daren?" "Eh Baba!" Bude musu kofar aka yi ya shiga parlour da a can baya yake renawa da kallon talauci ne yasa aka ki gyara parlour, yau sai yaji bakiɗaya babu inda yafi mishi dadin zama kamar parlourn. "Barka da dare Baba!" "Yawwa Aliyu kai ne ashe!" "Eh Baba!" Gyara zaman shi a kasa Baba ya ce mishi. "Ka koma kujeran yafi kasan nan!" "A'a nan ya ishe ma Baba!" "Meke tafe da kai?" "Ummu nazo dauka?" "An gaya maka Ummu tana nan ne?" D'ago kai yayi yana kallon Baba. "Bata so nan ba, idan baka yarda ba ka shiga cikin gidan ka duba!" Dafe kai yayi yana faɗin Innalillahi wainnalihir rajou, abin da yake nanatawa kenan, kafin ya mike yana faɗin."zan tafi nimanta." Kaman hadin baki Baban Ummu ma fada ya mishi, idanunshi ya kad'a jajjur, sai huci yake yana kara jin tsanar duk wanda ya taya shi wulakanta Ummu, yaji ya tsani kowa. Haka a daren ya dawo Maiduguri ana shiga gida ana shiga sallah asuba, haka ya tafi masallaci ana ta jajjanta mishi domin ana ganin, abin kamar saka hannu ne.
Da gari ya waye ya tafi office, da wuri ya dawo ya rufe kanshi a daki, bai taɓa jin b'acin rai irin wannan ba Ummu ta b'ata ita da Yaranshi ina suke ne.....🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


Dama da take cewa zata tafi idan bai kyaleta ba da gaske ne dama? Shi ya dauka tana mishi barazana ne don ya kyale ta ashe har cikin ranta da gaske take, tunda Sa'adiyya taji labarin Tafiyar Ummu, ta saka Tafida a gaba da rashin mutunci kala kala, wanda ya ja dole ya zuba mata idanu, a lokacin da Mahmoud yaji labarin zama yayi yana nazarin yadda zai shiga tsakaninsu. Ya jima yana nazarin abin, duk da lamarin duniya kome ya faru idanun jama'a da yan jarida yana kan kowa haka Yan jarida suka fara rubutu akan b'atar Ummu yayinda su suke cewa. *Me yasa Ummu Hadiyya Matar Gwamna Aliyu Muhammad Jadda ta gudu? Ko dama can tana da wani saurayin ne ta bishi?" Wannan al'amarin ya saka Tafida tashin hankali inda ya saka aka kawo dan jaridar cikin fushi yayi kanshi Deen ya rike shi yana faɗin. "Me yasa zaka fusata? Su je su ta fadar abin da ya musu! Calm down my Friend fada ba naka ba ne, idan kayi da shi akwai gidajen Jaridun da nayi Imani da Allah biyansu aka yi su tunziraka, by now Ummu ba ita bace rauninka balle har ka yi hukuncin don an fadi maganar banza, koma ka zauna." Deen ya kalli gayen Matashi ne wanda bai wuce shekaru ashirin da biyar ba, ya ja kujera ya zauna gayen yana tsaye. "Ga kujera ka zauna!" "a'a nan ma ya ishe ni!" Murmushi Deen yayi ya ce mishi. "Jarida tana fitowa aka turo min, ina gani na ce a bincika min waye kai da inda kake waye mahaifinka, sai naga ashe dan bautar ƙasa ne daga Kaduna, na kuma saka an bibiye har garinku da ungimuwarku, ka fito tudun Wada layin yan kosai, kusa da masallacin Izala!" Zubewa Yaron yayi tare da sunkuyar da kai jikinshi yana rawa. Deen ya sake murmushi. "Mahaifinka tsohon drive ne, kafin yayi hatsari Mahaifiyarka tana sayar da kamun kunu da itacce,kana da kanwa tana sayar da awara da koko da la'asar. Da da dare tana abinci kamar taliya ko?" Ya tambaye shi yana nuna shi da yatsa. Kuka gayen ya fashe da shi. "Look ban san Tafida zai kawo ka ba,domin ni na gama nawa abin da zan gaya maka shine ka sake nuna Tafida da Yatsa." Murmushi yayi yana faɗin. "Ba bincike zan yi ba hukunci zan yi kada ka yi tunanin nafi Tafida sauki! Ni nan jekariyarshi, na kara jin kayi rubutu ka kuka da abinda zai faru tashi ka tafi" kuka gayen yake yana bashi hakuri ya ce mishi. "Lukman muna da halin tab'a kowa amma kafin muyi magana, mu fara duba waye wanda zamu tab'a waye yake tare da shi. Nasan akan kudin da zai kare aka baka, kayi a hankali da rayuwarka! Su waɗanda suka saka ka wannan aikin su fuskanci Tafida ido da ido shine zasu cika maza, ban da muna lissafi da na shafe labarinka daga Kaduna! Tunda ka iya rubutu baka iya nazari ba ka kira Mamanka, ka ji ya jikin Babanka yake out of my sign!" Mikewa yayi da sauri yana ta buga godiya yana kuka, wannan masifar da me yayi kama, "Me yasa ka kyale shi?" "Kana da hauka ne? Niman hanya ta kowani fuska a lalata maka suna, matukar ina raye zan zama Inuwarka in sha Allah idan ka ga abu ya same ka haka Allah ya rubuta zai faru da kai, tun fil azal amma ina tare da kai babu abin da zan taba bari ya same ka. Ka ajiye Ummu a gefe duk inda take tana kallonka, ka fuskanci al'ummar da suka zab'e ka!" Deen ya mike yana faɗin. "Kasan Allah ka rame wallahi!" Ya fada yana bude wani basket da yazo da shi zuba mishi abinci yayi yana faɗin. "Maza ci!" "Deen na koshi!" "Sha kunun!" Amsa yayi ya fara sha a hankalin, yana sauke ajiyar zuciya. "Deen bana barci!" "Ba zaka iya barci ba domin zuciyarka tana ga Ummu!" "Ba fa wasa nake ba!" "Saboda girman kai yasa ba zaka iya fitar da shaukinka ba kada a rena mai girma Gwamna!" Banza yayi da Deen yana faɗin. "ka kyautawa kanka da kayi shiru!"
Bayan sun gama Deen ya kwashe kayanshi yana faɗin, "zan tafi wurin aikina! Idan an tashi ka kira ni zan zo daukarka mu fita wani wurin." "Tow na gode!" "Aliyu ka fuskanci al'ummarka kada ka kara tasa zancen b'atar Ummu ko da kuwa da ni ne, na gaya maka " "na ji Deen!" "Mai kan kwakwa!" Ya fada yana barin office din. Yana zuba kayan abincin a motarshi ya kira wani abokinsa wanda lauya ne da ya daukawa Deen, mutumin Bayarabe ne, ya gaya mishi ya jira shi gashi nan zuwa, yana zuwa ya samu lauyar da wasu lauyoyi uku. "Mr Safiyyudeen ka iso!?" "Eh na iso ka biyo ni!" Ba tare da sanin Tafida ba,Deen ya tafi har gidan Alhaji Mansur Goza, da yake wajen garin Maiduguri. Da lauyoyi, lokacin da suka tafi ganin Lukman ya kara tabbatar mishi aikin Alhaji Mansur ne, "Kai me ya kawo ka nan? Kana son ka mutu ne?" Ciro madubin idanunshi yayi yana hure Madubin yana faɗin. "Waye ya gaya maka mun zo nan ne mu daya kalli sama!" Wata karamar jirgin sama ce irin ta yara amma shi wannan da tambarin sojoji. " sannan wannan madubin akwai abin ɗauka. Kasan me? Kayi rigimarka kamar yadda kaso ya zame maka kamar Jela shi kuma yaki. Ni masanin kimiya ne ba iya kimiyya ba hatta yadda ake haɗa mugayen sinadarai irin abin shan da yake hannunka na san kansu. Na fahimci lissafinka baya ja, ka turo yaro ba gaya masa waye mu, na kuma kara bashi shawara ya tsaya a gefe. Yaron nan da Tafida suna bayan kulawa ne, musamman mutuncin Tafida da iyalinsa. Idan ka sake wani abu ya kuma faruwa Lauya ajiye takardan yarjejeniyar sulhu idan wani abu ya kara faruwa ku zama shaidana allon kalla zan saka akfta min katon hotonka a manna a gari kowa yana gani na rantse da Allah, ka kara gwadawa ka gani!" Haka lauyoyi suka bashi takardan saka hannun yaki sakawa. Mika mishi wayar aka yi ta bayanshi ya dauka. "ga wasu jami'an tsaro a kofar gida zasu shigo! Wai zasu yi bincike ka san da su?" Kallon Deen yayi ya d'aga mishi gira daya yana faɗin. "Zaka saka hannu ko sai sun shiga cikin gidan sun binciko abin da kake boyewa? Tun muna Yara na gayaws Tafida ya girma ya zama babban Mutum ni zan zame masa jekariya duk abin da nake zan saka idanuna akanshi, kasan me yasa ban damu da sauran abin da yake ba, iya zama a tare a shi wani arziki ne na musamman. Ka zama mutumin kirki yadda kowa zai yi koyi da halinka, saka hannu ko su shiga wannan dakin da kake boye shi!" Saka hannun yayi jikinshi yana wani irin rawa, domin wallahi bai tab'a sanin akwai wanda yafi Tafida rashin mutunci ba, hadiye yawu yayi ya saka hannu. "ka kyautawa kanka!" Ya amshi takardan yana faɗin. "daga yau babu ruwanka da Tafida!" "Idan ni ka raba dani da shi sauran da suke kokarin ganin ya gaza fa!" Murmushi Deen yayi yana faɗin. "Kada ka damu yadda na iya tsamo ka sauran zan iya tsamo su kamar yadda ake tsamo nama a cikin miya!" "Kada tsoron rayuwarka ne? Ko baka da wani fata ne?" "Tsoron me zanji? Ko mutuwa nayi akwai Mahmoud, sannan fata na daya na tashi da Tafida a karkashin alrshin Ubangiji ka fahimta, ni ba kare ba ne da kudi zai sauya min rayuwa!" Daga haka ya kalli Lukman. "Zaka zo mu tafi ne ko zaka zauna da shi?" Mikewa yayi yana kallon Alhaji Mansur Goza. Shima tashi matsalar tafi ƙarfin ya kula shi, "Ya batun jami'an da suke kofar gidana!" "Ai tuni sun kara gaba!" Deen da mutanenshi suka bar gidan Gonan.


Deen da Deputy suka tsaya sosai akan Tafida, domin aikin jaha guda a halin da Tafida yake ciki ba karamin al'amari ba ne, bakiɗaya ya tsinke ya fita hayyacinsa, gani yake kamar wayewar gari za a ce an ga gawar Ummu da Yaranshi, amma babu labarin, ranar da Ummu ta cika sati uku da kanshi ya tafi gidan Malam Zailani ta taimakawan Deen. Tunda ya isa gidan ya zauna yana me sunkuyar da kanshi. Murmushi Malam Zailani yayi yana faɗin. "matarka da Yaranka Lafiyarsu lau!" D'ago kai yayi yana kallon Malam Zailani idanunshi jajjar har kana ganin kwalla yana taruwa. Murmushi yayi a karo na uku. "Da kyau jekariya ba gari, ka kasance da shi zuciyarshi take sarrafa shi da kwakwalwarshi. Yarinyar lafiyarta lau ita da Yaranka, matsalarka girman kai ka amshi laifinka zata iya sassauta maka!" D'ago kai yayi yana faɗin. "Akan me zan amshi laifin da ban san nayi ba?" "Akan me kake barin zuciyarka take ciwo? Gaba kaɗan zaka fara kuka kana rike kirjinka!"
Ya fada yana murmushi, ya cigaba da cewa."koda yake akwai dole Kanwar naki zata saka ka fadi laifinka da bakinka, yanzu aikin al'ummar borno ya dace ka fuskanta, domin kada Ummu ta zama rauninka yadda zaka kasa tabuka kome!" Yadda Malam Zailani yake mishi magana yana rubutu ya ce mishi. "Kai yanxu idan ka bari Ummu ta dawo ba kyautawa mutane dayawa ba, ka nuna baka damu da tafiyarta ba ta haka ne zaka fahimci meke faruwa." Haka yayi shiru har zuwa wani lokaci kafin ya wanke rubutun ya mika mishi. "Kai ce maka aka yi rashin barcin nan da baka yi kawai tunanin Ummu ne? Ko daya don ma Mahaifiyarka tana tsaye kanka daga nan ka wuce ka duba ta." Gyada kai yayi yana kallon kasa, haka Malam yayi ta mishi nasiha tare da nuna mishi kuskuren shi na rashin kyautatawa Iyaye. Sannan suka baro gidan wurin Hajiya, suka wuce anan suka zauna har dare haka kawai Tafida ya ji baya son barin gidan. "Deen jeka zan kwana anan!" "Alhamdulillahi shi kenan, Hajiya zan tafi sai da safe." Har waje ya rako shi, "Deen unguwarsu basu da wuta sannan akwai wuraren da ba su da kyau ina gaya maka ranar na je na fad'a kwata kada ka ji wari da nake don Allah gobe a tuna min ." "In sha Allah!" Suna tsaye Deen ya tura sako wa security. Kafin su yi sallama unguwar ya samu bakoncin hukumar tsaro, "zan tafi Tafida! Ka gaida Madam!" "Yawwa zasu ji ita kuma Sa'adi baby fa!" Danna mishi ashar Tafida yayi ya juya cikin gidan. Dariya Deen yake yana karawa.


A parlourn Hajiya ya kwanta ta ce mishi. "Zo ka shiga daki ka kwanta!" "Hajiya nan ya ishe ni!" "Shi kenan!" Ya fada yadda tayi maganar sai yaji bai ji dadin haka ba, mikewa ya nufi cikin dakin ya kwanta a gadonta, ita kuma ta zauna a kujeran dakin rike da casbi, mikewa tai ta kashe wutar dakin ta koma ta zauna, tun yana iya hangota a dan hasken da yake ratsa dakin, har barci yayi gaba da shi. Tana zaune a wurin jin saukar ajiyar zuciya yasa ta haska shi da torching ta. Hawaye yake zubarwa yana barci. Tashi tayi ta koma gefenshi tayi tana tofa mishi addu'a, a hankali hawayen ya daina zuba. Mikewa tayi ta nufi banɗakin da yake cikin dakin tai alola tazo ta shimfida abin sallah. Matar nan raba dare tayi tana gayawa Allah kukan da danta yaƙe, tun karfe sha biyu take ganawa da Ubangiji bata tsaya ba dai karfe hudu cif, ta cigaba da addu'a bayan tayi sallah. Ita kanta bata san iya adadin raka'o'in da tayi ba. Allah ya daidaita Tafida da Ummu wannan shine fatanta, tuj wurin karfe daya aka buga bindiga haka ma hudu na asuba da rabi aka kara bugawa. Kallonshi tayi tana me shafa fuskarshi. "Babana tashi ka tafi sallah!" "Ummu!" Ya furta a hankali. Murmushi tayi tana kara jin tausayinshi ta shafa kanshi. "Babana tashi ka tafi sallah asuba!" Bude idanun yayi yana kallon Hajiya idanunshi sun kad'a jajjur. A hankali ya tashi, ya nufi banɗaki alola yayi ya nufi waje, da jagorancin jami'an tsaro ya isa masallacin, abin sai ya bawa yan unguwar Mamaki Tafida a unguwarsu. Matsa mishi aka yi akan ya shiga sahun bayan liman, cikin sassanyar murya yace musu. "Bismillah." Ya tsaya a sawun baya tare da mutane da yawa, ana idar da sallah, kowa yayi tsammanin zai fita ne, abin mamaki sai aka ga yana zaune yana azkar, kusa a shi Abubakar ya dawo ya zauna yana murmushi. Mika mishi hannu yayi suka yi musabaha, wani abin mamaki bakiɗaya masu sallah aka kasa fita. Can Limamin ya fara addu'a da bayani da kuma rokon alfarman abubuwan bukatar da suke so kasancewar Unguwar sabuwa ce. Bayan sun gama ya kalli Liman ya ce mishi. "Ku hada kwamiti na yan unguwa ka bawa Yayana sakonku, idan ma baku same shi ba, ku kai sakon wurin Hajiyata zata iso muku da shi har wurina, tafiya ce ta ratso ni nan, na gode sosai da mutumtawa ku taya mu aiki gwamnati ba zata manta da ku ba, na gode sosai da bani damar sallah a cikinku!" Suma godiya suke suna kara jin dadin ciki ashe haka suke basu da girman kai. Sannan ya musu sallama ya koma gidan hajiya, ya samu ta hada mishi abin karyawa tea ne, a gurguje ya sha yana me faɗin. "Deen zai zo amsa min abincin rana!" "Kai ba zaka zo ba ne?" Yake yayi Abubakar ya ce mata. "uzuri yake da shi, Hajiya nima a saka min tea din!" Ya shigo parlourn yana kallon Tafida da yake kurban tea. Bai shanye ba zai mike ta rike hannunshi. "sunnar Annabi ne cin kome a nutse, zauna kada ka kware." Zama yayi yana hura tea din amsar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login