Showing 60001 words to 63000 words out of 241571 words

Chapter 21 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14702

yan kananun magana yasa ni fahimtar maganin yayi kyau. Bayan ya gama ya sauka ya shiga yayi wanka a ban dakina, ya fito yana faɗin. "Ke anan zan kwana a hada min kayan abinci na!" "Tow!" Ina jan hancina, ban daki na shiga nayi wanka sannan na nufi kitchen na hado abincin zuwa dakin ya zauna ya ci sannan ya huta kafin ya shirya ya tafi sallah tarawe. Bayan ya dawo ya kuma fita da abinci waje. Suka ci bai dawo ba sai karfe goma sha ɗaya, har na fara barci ya shigo min, sai da gabana ya fadi. Fita yayi sai gashi da kayan barcinsa yazo ya kwanta a bayana, bai nemi wani abu ba don yaga yadda nake dan kerma a gabanshi. Bayana ya sumbata, yana faɗin. "Kwanta babu abinda zan miki, sai asuba zaki bani kafi shayi." Ban yi wani barcin kirki ba, tunda mutumin nan ya maida ni tuwon laushi. Ranar jajiberin sallah, yana gidan bai fita ba a tare muka yi ta fama, wurin karfe daya na dare, kashe kome yayi yana faɗin. "malama muje barci naje ji!" Haka na bar kome na kwanta, don gulma mutumin nan har da min tausa, ai shi ba zai yi aikin banza ba yana ganin na huta ya fanshe aikinsa, haka muka yi bikin sallah ni dai bana jin wani dadin zaman shi saboda jaraba. Sati daya ya koma, bayan na ji rigimar su da Sa'adi, ban yi farin ciki ba domin kuwa har parlourna Hajiya Shuwa ta biyo ni tayi min tijara wai bokana yayi nasara amma na shirya ko bai auri Sa'adiyya ba zai zo da wata ai, me ilimi gogayya wacce ta fiki wayewa. Ko inda take ban kalla ba na cigaba da harkan gabana. Lokaci ya tura sosai ba zato ba tsammani kawai sai matar Sharif ta haihu, a lokacin aka sakani a gabana da habaici da magana,ko ta kansu ban bi ba na bawa Maijego gudummawata na bar gidan, daga nan na zo nayi shawara na bude online business dina, yayinda muka yi da Mudan zai na min deliver. Wasa wasa Sai gashi gidajen abinci sun fara gayyatatta ina zuwa na musu dan karamin program, haka yasa na zama sananniya, ai kuwa na koma yar kasuwa kamar me ina cake ina abinci sannan ana oda sosai, abin dariya sai ga Rukayya ta fara abincin itama online, wasa wasa Sai gashi ana son abincina haka suka yi ta sake min habaici da sharri kala-kala, dake akwai kyakkyawar manufa a raina. Kawai ina zaune wani zuwan da Tafida yayi, yana kallon kwallo. "Ummu ki barwa Rukayya online business dinki nan!" "Ban gane ba?" "Eh ina nufin ki daina sayar da abincin nan da kike yi na Baby's Mama kitchen!" "Fisabiilillahi;" "ba zaki bari ba kenan?" "Gaskiya ba xan bari ba domin da shi na dogara idan." "Ba zaki iya ba kenan!" "Zan gayawa Abba ya ji abin da kike nufi da ni!" Ina saka Abba cikin maganar ya bar zancen, ashe sun same shi da zancen ne ko zai iya hana ni, ni kuwa naki. Ba karamin haushina suke ji ba, ana haka Aunty Maryam ta haihu, tana haihuwa da kwana biyu na je barka na kai mata dubu goma, ko zama ban yi ba na bar gidan, sai ana jibi suna ya kirani wai Maryam ta ce wai ni zan mata abincin suna naje, shafawa idanuna toka nayi nace su kawo idan tana bukata ni ba zanje suna nuna ni a matsayin barauniyar su ba. Na zata zuciya zasu yi sai naga ba haka ba, washi gari sai ga kayan girki, duk abinda aka kawo a bai kai ba,haka na kwashi kayan mu na musu abinci me kyau. Kawai nayi ne domin bana son ayi shi a babu isashe. Da aka zo dauka Rukayya ce, naga ta fito da babban kula ta diba, ya kai gidan shuwa. Ko kallo bata ishe ni ba ina ruwana, ana kai abincin Aunty Maryam ta kirani bayan na dauka nace mata. "An fita bakwai lafiya?" "Lafiya lau! Ya abincin haka? Ko Rukayya ta diba ba ne?" "Hmm wato dama kin kawo min ne da nufin na dafa ace na sace na boye ko?" "Ba haka ba ne, abincin ne kamar an diba!" "Ok ki tambayi yar uwarki!" Na kashe wayar, ina jan tsaki. A can kuwa zagina suka yi tayi wai nayi abincin na kwashe dake Allah ba azzalumin sarki bane sai ga Sa'adiyya ta fasa mata taya a gaban jama'a, ta ce mata. "Aunty Rukayya abincin ki yana bayan Motar Mama." Shiru tayi tana wani zare idanun.


A shekara na uku da auren mu ne ya samu goyan bayan manyan dattijan borno, masu political powerful na arewa bakiɗaya suka goya mishi baya, aka fara hidimar yawon zabe, ni bai gaya min na domin a lokacin abin ya zo ne da maganar shi da Sa'adiyya wanda ya saka ni a gaba da fitina da wulakanci wai yana zargin nice nake hana Abba amincewa, a lokacin yanayin ya sauya min da sabon ƙaddara, domin haka kawai na fara wani irin ciwon da ta sa na bar duk wani abin da nake, na nutsu wuri guda, tun karshen shekarar na fara haka kullum ina fama da magani har na shiga sabon shekara, da ya gaji da ganina kwance ya saka ni a gaba muka tafi asibiti, gwajin farko aka tabbatar da cikin wata uku ne daram a jikina, hmm! Sai ga Tafida ya tashi hankalinsa domin ana maganar aurenshi da Sa'adiyya ne, haka muka fito yayi, y kalle ni da kyau. "Yaushe cikin nan ya shiga? Ina kina ganin nake saka condom! Ba don ni na fara koya miki ba da wallahi sai na musanta cikin nan nawa ne!" Rintsa idanuna nayi, naji kamar xan mutu, bayan mun isa gida bawan Allah nan bai huta na, yayi ta shige da ficce lallai zai zubda cikin jikina, a wannan yanayin aka yi bikin Mahmoud da Deen kusan sati guda ne a tsakaninsu. Ban samu damar zuwa ba, domin duk inda Tafida yaji zai samu magani sai ya kawo min ya tsaya a kaina na sha, wani hukuncin Ubangiji magani dai shi ake kira Daram ko jiri bana ji, duk abinda ya kawo zan sha domin ni kaina na kawo aurena ya zo karshe da Tafida. Haka aka yi ta fama ganin cikin ko nasha magani bana kome sai ya kai Ni asibiti wai a cire cikin, likitan yana min scanning ya gano yan biyu ne kwance mahaifata, nasiha yayi mana ya ce mana. "Cikin nan yan biyu ne, kana da damar da zaka iya zubarwa baka san arzikinsu ba, sannan kai ne ake tsammanin zama gwamnan jihar Borno, don Allah kayi hakuri ka barsu! Daga kansu sai ka ajiye haihuwar ma domin cikin ya shiga wata hudu idan aka tab'a za a iya rasa uwar da yaran ma!" Jin haka ya sa shi hakura amma shi kansa yana ganin da zaran ya zaman gwamna zai rabu da ni. Haka muka dawo gida cikin sanyin jiki, daga nan ya fara fito min da abin da yake shiryawa, cikina yana wata bakwai aka yi bikinsu da Sa'adiyya, akwia wani abu da idan kace Allah zai amsa maka, rawan kai da na kafa da Tafida yayi lokacin sai da na taba farkawa da wani irin ciwon ciki kamar haihuwa, ana gobe daurin aure a asibiti na kwana, a wannan lokaci yan uwanshi suka yi ta fitar da abinda yake ransu na idan na haihu zai rabu da ni ya kwace yaranshi, Abba kuwa ya ce . "A duk lokacin da kika samu dama, zan rike miki kan maciji kiyi wasa da bindin yadda ranki yake so," haka ma Inna ta goya min ba, kwana ɗaya nayi aka sallame ni washi gari da ya dace ango ya fito da kaudi sai ga Mutumin ya fito daga bangarenshi kamar ruwa yayiwa zakara duka...........
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*


*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML*


*Ina mata yan yayi shin ko kun san kayan da Ummu take amfani da shi, yana fitowa ne daga shahararren Shagon nan na R&U Exclusive Kitchen and More! Kayan kitchen ne na gani na fada ina iyayen Yan mata ina iyayen Kwailayen ga dama ta same ku, Uwargida da Amarya, Budurwa da bazawara maza ku fito ga kaya nan sayan na gari mai da kudi gida. Kayan mu daban da na shago!*






Paid book


Last free Page




20


Da mamaki yazo ya zauna a gefena, ina rike da hisnulmuslim, ina karanta addu'o'i domin Inna ta ce min domin samun Yara na gari masu nutsuwa na rike azkar, kusan abinka da gajeruwar mace. Cikin ta fito sosai, haka yasa nake yawan saka hijab ba dare ba rana, yau ma ina zaune ya zo ya zauna a gefena. "Ummuna!" Abin mamaki batar nono a kirjin budurwa, da mamaki na kalle shi kafin nace mishi. "Wani abu ne?" "A'a kawai ina son magani me bani da lafiya!" "Ai ho, Allah ya sawwaka ka tafi wurin Sa'adiyya zata baka ni maganin da yake nan na masu ciki ne sai wanda da kake kawo min don cikin ya zu...." rufe min baki yayi yana girgiza kai. "Kada ki tuna min shirmen da nayi, Allah ya sauke ki lafiya ayi shagalin suna a government house!" Shiru nayi kafin nace mishi. "Ni can zan shiga gidan gwamnati? Ka manta ina haihuwa zaka dauke Yaranka kai da Sa'adiyya da masu renon da zaka kawo daga kasar waje ni kuma na tafi na samu yanci!" Mikewa yayi yana faɗin. "Wasa nake miki!" Murmushi nayi na cigaba da azkar dina. "Babyyyyyy!" Naji Muryan Amarya me maganar sugar. Kafin ya amsa ta diro dakin kamar daga sama. "Haba masoyi!" Wani irin kallon banza yayi mata daga sama har kasa. Ya daka mata wani shegen tsawan da ya razana ni, na dafe cikina. "Don Allah ku fita likita ya hanani jin hayaniya saboda lafiyata!" Juyowa yayi yana faɗin. "Sorry My uwar biyu, bari na ji da wannan mara kunyar." Ya saka kai ya fita ta bishi, da rarrafe na nufi kofar dakina, na rufe na daina jin hayaniyarsu kome ta haɗa su oho. Wasa wasa rikici ya balle a tsakanin Ango da Amarya, babban al'amari fa, yadda kowa ya dauki laifin ya daura min wani nayi musu asiri. Shi Tafida ya kafe babu asirin da nayi musu ita ce asirinta ya tonu. Yan uwansa da suke ciki daya Musamman matan suka juya bakiɗaya suka koma wurin Sa'adi, sai ya zama daga ni sai halina. Ana haka Naziha ta fara shigo min. Idan suka zo dake akwai sauran hidimar da ake yi ba a gama ba. Amma Tafida yayi tsalle yace an gama biki a gidanshi. Abin dariya ina kwance da cikina kowa yasan yadda masu ciki suke fama da yan kananun cututtuka. "Ke tashi!" Ya fada min, kallonshi nayi kafin na gyara kwanciyata. "Ni don Allah ka kyale ni naci abinci ne bai fada min ba!" "Tashi nace!" Ya buga min tsawa, haka na tashi ina nishi. "Saka hijab ɗinki!" Ba musu na dauka na saka, ya kalli kafana da suka kumbura. "Muje!" Ya fada min a harzuke, haka na fito a hankali ina tafiya har waje ya shiga bangaren Sa'adi, yadda suka fito kowa ranshi a dagule yasa ni kame kaina. "Ke Ummu fito daga baya nan!" "Ni dai don Allah ka kyale ni, wallahi gaban nan hana ni sakewa yake kuma hajijiya nake gani." Zare idanun yayi kamar zai fasa ihu. "Zauna zauna!" Ya fada yana hararan Saadi. Shiga motar yayi daidai lokacin da Shuwa ta fito da gudu. "Ina zaka kai min y'a wato rashin mutuncin da ake fada kana yiwa matarka da iyayenta shine zaka fara a kaina?" "Zan kaita a mata gwajin cutar kanjamau ne saboda na sayi rariya mai yoyo. Batun rashin mutunci kuwa tunda kuka bani sauran gardawa ai kin san abin da zai faru, idan har Mahaifina zai zaba min alewar da yake nad'e cikin ledarshi a killace cikin muhallinsa nayi shakukatin bangaro da shi gaya min me zai faru da zabina da ta zama kamar rijiya kowani guga ke fadawa cikins. Hajiya Hindu ke a tunaninki abin burgewa ne Uwa irinki ta sake kiwon akuyarta kowani bunsuru ya barbareta? Ok na ji rashin mutunci da nayiwa iyayen Ummu Hadiyya kece kika jagoranci haka kin dauka ni irin Kawu ne da ake bashi manta uwa?" Zai sake magana na bude motar na fara amai, dama nasan haka ne zai faru matuƙar ban huta ba, daga cikin abinci na fito tow abinda zai faru shine amai da mutuwar jiki. "Sannu-,sannu!!" Yayi min sannu ya fi sau goma, sannan ya bude bayan motar ya ciro ruwan gora ya bani, na wanke bakina. "sannu Maman Twins na dauko ki ko?" Shiga motar yayi ya bar Hajiya Hindu tsaye kamar gunki, tsaki yayi ya ja motar da sauri yana kallona ta madubi. "Sannun kin ji!" "Tafida amma kasan zaka tozarta ni me yasa ka aure ni?" "Ita da tasan zan tozartatta me yasa ta aure Ni? Ko kin manta sau nawa kika zo bangaren mu a lokacin tana amarya?" "Akan me yasa zaka dauko kishiya kana cin zarafina a gabanta." X
"Sau nawa naci zarafinta a gabanki? An gaya miki zan kyale ki ne don kawai ga ki yar gwal? Tambayeta yadda na sameta a daren farko da na.." "innalillahi wainnalihir rajouna! Na shiga uku na lalace, ni dai don Allah ku daina irin wannan maganar a kunnen Yarana!" "Ok okay! Suna jin mu ko?" Ya tambaye ni a dame, daga haka yayi shiru sai ita ce ta cigaba, kamar xan yi kuka sai da ya daka mata tsawa, tayi shiru asibitin da nake zuwa awo mutumin da yace kada mu cire cikin nan nake zuwa awo bakiɗaya staff na asibitin sun sanni. Koda ya isa sai da na kai minti goma kafin na fito a hankali, duk yadda nake tafiya a hankali Tafida bina yake a nutse, yana min sannu yafi baki dubu. Kallonshi nayi yadda yayi sanyi daga jiya zuwa yau. "Kai ma ka huta da sannun nan!" "A'a Ummuna!" Ya fada yana bina har muka shiga cikin asibitin office din Dr muka isa, dukkanmu uku muka shiga. "Maman unborn twins kece a tafe ai sai ranar juma'a zaki dawo,?mu ga yanayin kwanciyarsu!" "Dama akwai matsala ne Dr Sagir?" "Eh kasan dake biyu ne daya ya kwanta daya kuma yana zaune, idan tayi sa'a lokacin haihuwarsu daya yana fita daya zai juya, idan aka samu matsala kuma wanda xai juya ba sai anyi aikinsa!" "Zauna Ummu, ai dole lamarin nan a hada da addu'a!" "Ranka ya dade zabe na ta karatowa!" Tsaki yayi yana faɗin. "Duk kome ya fita kaina wallahi, na gaji bakiɗaya!" "Allah ya tabbatar da alkhairi! Lafiya dai?" Ya tambaye mu yana kallon Sa'adiyya. "Lafiyar kenan test din HIV zaka mana, bakiɗaya ." "Tow!" Ya ce yana kallonmu, "amma ita Maman unborn twins lafiyarta lau, domin tana da kyakkyawar record a files dinmu." Gyara zama yayi yana faɗin. "ka ga wanann amarya ta ce." Ya juya yana zabga mata harara, kafin ya juya yana kallon Dr Sagir, "Ka mana gwajin bakiɗaya saboda Yarana kada su ɗauki wani cuta!" Tashi yayi ya bude wani drower ya fara ciro files dinmu ya mika mishi yana faɗin. "wannan file dinta ne da Yaranta da suke cikinta. Lafiyarta lau idan muka cire jininta da yake hawa. Bata da matsalar kome!" Kallon Dr Sagir yayi ya ce mishi. "ita wannan a gwada ta domin ina son kada ta shafa mana!" Wayar office din ya dauka ya kira Nurse can sai gasu har su biyu. Suka gaishe ni sannan suka wuce suka dibi jininsa na Sa'adiyya ce zata musu taurin kai ya daka mata tsawa, sannan ta tsaya aka diba nata. "Fadila ki kawowa Maman unborn twins, fruits." "Ok Dr!" Suka fita, Dr Sagir ya ce min. "Ina samun barci kuwa?" "Eh tow gani nan dai!" "Wani abu ya same ya ne?" "Bata samun barci ne cikin dare, haka yasa jininta yake hawa! Amma zan bata wani magani tana sha zata samu barci!" "Dr Sagir! Ya zanyi na kula da su ita da Yaranmu!" Kallona Dr yayi zai magana Fadila ta kawo min wani bowl da fruit. "Aunty Ummu gashi nan!" Amsa nayi ina faɗin. "na gode Yaya Sagir!" Kallona Tafida yayi yana faɗin. "Kun san juna ne?" "Eh bata gaya maka ba ne?" Ya kalle ni, yana murmushi, "Babanta Yayan Babana ne, sannan a hannun Babanta na tashi wannan asibitin ma shi ya gina min, a can Biu ma akwai daya asibitin duk sati a can nake spent weekend dina!" Juyawa Tafida yayi yana kallona, kafin ya juya ga Dr Sagir yana faɗin. "Ai zurfin ciki ne da ita!" Ni ma dai ban san dan uwana ba ne, sai da na fara awo idan nazo matukar ya san na zo zai ce na shiga nurse su duba ni a gabanshi. Lokacin da ya gaya min dangatarkarmu, ban yarda ba sai da ya kira Babana ya gaya mishi ai wurinsu nake awo, ya bani wayar muka gaisa da Babana, bayan mun gama wayar na ce mishi. "Don Allah kada ka gaya mishi abin da ya faru kaji, ka ga idan." "Ni likita ne, kuma na rantse da boye sirrin kowa kamar nawa!" Ko baya asibitin nazo za a gaya mishi, haka zai tawo yazo ya duba ni.


"Sannu ko zaki kwanta ne?" Girgiza kai nayi ina faɗin. "A'a kawai xan mike kafana ne!" Tashi yayi ya dauko wani stool har biyu ya kawo gabana, ya saka min na gyara zamana, ina jingina. "Kina cin abinci kuwa?" Gyada kai nayi ina faɗin. "Eh!" Ina zaune a wurin Nurse Fadila ya shigo tana faɗin. "Dr an kawo maka sako daga jimeta!" "Ki zuba kankara a ciki a damawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login