Showing 78001 words to 81000 words out of 241571 words
Chapter 27 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
Tafida zai dawo ta zo su yi abinci, dake bata da lissafi Allah ya zuba mata kwadiya, don ko Maryam bata gayawa gudun kada maryam ta mata faɗa, haka ta ki faɗa. Aikuwa Ana gobe zasu dawo Shuwa da kanta ta shiga bangaren Saadiyyah ta gyara mata, sannan ta koma bangaren Ummu da tasan dole ta nan sai fara shigowa, haka yasa ya turara bangaren tas. Da kyakkyawar shirinta, haka kuwa ya faru tun a jidda ta fara mishi tijara, bai kulata ba domin burinsa kawai ya isa ya nufi wurin Ummu da Yaransa. Don haka yaki yarda ya amsa mata domin kada ta yarda ta fusata shi lokaci zuwa lokaci yana murmushi, don na karamin dad'i yake ji ba, koda suka bar Saudiya a jirgi ma magana take gaya mishi. Har su iso garin Maiduguri Allah yasa sun iso da dare, don haka ba tare da ya damu ba ya kalli Mahmoud ya ce mishi. "Ka wuce da ita gida! Ni zan tafi ganin Ummu!" Ya kan wasu akwatina guda biyu. "Tow na zata gida zaka wuce!" Wani shu'umin murmushi dariya Sa'adiyya tayi, tana faɗin. "Allah yasa rawan kan da ake yi akan Ummu ya koma upside down" banza yayi mata bai yarda ya kula ta ba zai shiga motar Deen ta ce mishi. "Da alamu dai gudu abin kunyar da aka aikata yasa ana ƙoƙarin rufa-rufa, waye ya sani ko yaran ba jininka ba ne!" Cak ya tsaya kamar an dasa shi a wurin ya kasa gaba ya kasa baya. "Waye ya sani ko bayan kai akwai mata yi tunda ai kafin kai akwai wani a gidansu da yake sonta!" Ta shige motar da gudu, wani irin tafasa ranshi yake tunda ya shiga motar, jikinshi yake kyarma, asalin yarinyar ta san spot din da ya dace ta buga ta koma buga yadda ya dace, "wuce da ni gida na ci Uban Yarinyar nan." "Kayi hakuri ka fara kai musu kayan!" "Wuce da ni gidan kawai!" Yasan yadda ya fusata nan, ba zai saurare shi ba, don haka bai yarda ya kai shi gidan ba, ya wuce da shi gidan Malam Zailani. Ai kuwa yayi ta fada kamar zai daki Deen yaki kuma fitowa, Malam da kanshi ya tawo har wurin motar. "Aliyu!" "Sannu Malam!" "Allah ya tayaka riko tunda ba zaka samu shigowa ba, ina jiranka Allah ya tsare hanya." Bai ce kome ba shi dai burinsa ya isa gidan, Deen bai ji dadi ba haka ya ja motar ya bar gidan Malam. Har ga Allah Malam Zailani tausayin Tafida yake ji, domin zuciyarshi ita ce matsalarshi. Lokacin da suka isa ko parking Deen bai gama ba, ya fita daga motar ya nufi bangaren Shuwa don yasan Sa'adiyya tana can, yana shiga cikin fusata ya shiga kwallo da Sa'adiyya, yadda yake dukanta zaka ɗauka Allah ne ya aiko shi yana faɗin. "Ke din banza karuwan banza kin isa ki kama kafar Ummu yarinyar da ta kare rayuwarta da mutuncinta zaki zaga. Ke karuwa da maza suka gama hawa da sauka akanki zaki zagar min.mata da tafiki daraja." Bai damu ihun da Shuwa take ba ya mata duka har yana ture shuwa. Sannan ya bar bangaren jikinshi yana wani irin rawa domin bai tab'a jin fushi irin na yau ba, riko hannunshi Abba yayi kamar zai yi kuka ya kai shi parlourn shi ya ajiye shi tare da bashi ruwa, yana.sha yana haki domin babu abin da ya mishi kamar sheganta mishi Yaranshi a duniya bai da sama da su. Gumsar ruwan sanyi Inna tai ta fesa mishi, ya sauke wata ajiyar zuciya me karfi a kai akai. "Tafida!" D'ago kai yayi yana kallon Abba kafin ya ce mishi. "Yaushe Ummu zata dawo?" "Sai lokacin da kayi hankali ka koyi sanin darajar iyaye da Macen aurenka, ku zama shaida na raba Aliyu Tafida da Ummu sai ranar da yayi hankali!" Ya juya ya koma dakinshi, ya rufe kofar ya zauna a bakin gadon shi. Baya son yayiwa Tafida kuka amma tabbas deeply inside dinsa yana jin rauni a ranshi dama haka Ummu tayi hakuri da shi. Waye ya sani ko har dukanta yayi Allah Sarki Yar Mutane. Kiran Malam Zailani yayi ya gaya mishi a hankali yake kuka kamar karamin Yaro ya ce mishi. "Malam Tafida yana son fin karfina ji nake kamar na mutu da takaici,na rasa yadda zan yi da shi." "Alhaji Muhammad kenan, ka daina kukan nan kada ya tab'a shi!" "Ba shi nakewa kuka ba." "Kada ka damu, ka godewa Allah yadda ya tsaya a haka bai zama wanda zai na janyo maka magana daga waje ba, zan zamu cigaba da addu'a." Rarrashin abba Malam Zailani yayi, sannan suka yi sallama. Dakyar Deen ya saka shi a gaba har bangaren Ummu ya kwanta yana jin kamar zuciyarshi zata buga musamman yadda Abba ya haramta mishi maganar Ummu! A daren bayan tafiyar Deen ya kira Ummu Hadiyya, "ki kira Abba ki ce zaki dawo gidana!" Dariya tayi tana faɗin. "Allah Sarki Malam Tafida, da fatan ka dawo gida lafiya! Ai kai yanxu yayana ne don haka babu maganar dawowa!" "Ummu me yasa ba zaki dawo dakinki?" "Saboda bana son aurenka bana sonka bana kaunar na bude idanunka, Tafida bana sonka bana son aurenka ka rabu da ni na samu Lafiya!" "Naji amma ki gaya min me yasa kika tsane ni?" "Kai baka san dalilin tsanarka ba, ba kasan dalilin da yar baka mummunar me siffar goron bobo ta tsane ka ba, ka manta dalilin da yar Mace yar matsiyata. Yar mace me sayar da tuwo a kofar gidansu ba.." kamar zai fasa ihu ya ce mata. "Dama kina rike da wadannan kalaman na zata ya wuce tunda between ni dake ba wani abu ba ne don an samu ire-iren waɗannan stuffs din shine kike ta threating din kike wani d'aga min kai, Ummu ki cigaba da zama da aurena tunda ba zaki dawo ba, kina nufin ni Aliyu Muhammad Jadda Tafida na kira ki ina baki hakuri tow baki isa ba, har yau baki kai macen da zan bude bakina na baki hakuri, ki zauna a gidanku ." "Ba zaka tab'a sauyawa ba, ina bakincikin rashin samawa Yarana Uba na gari, na fada rayuwarka Idan ka gadama ka cigaba da rike auren har ranar da zaka ji labarin na mutu sai kayi murna, ba zaka sauya ba ba zaka tab'a sauyawa ba!" Ta fada tana jan hancinta. Kashe wayar tayi ya bi wayar da idanun, bai san lokacin da ya maka wayar da kasa ba ya mike tare da nufar dakinsa.
*Ummu Hadiyya!*
Ni a tunina da lissafina Tafida zai sauya ashe ba haka ba ne, domin bai sauya ba kuma babu al'amar zai sauya. Kowa damuwarshi na koma dakina amma basu san Tafida ba, hawaye ne ya zuba min, na share da bayan hannuna shigowa Mama tayi da ta kawo min namar da Baba ya kawo. Ganin yadda nake kuka yasa ta zama tana faɗin. "Kuka kuma?" A yadda tayi maganar a tausashe yasa ni na sake fashewa da kuka na kalleta cikin kuka na ce mata. "Don Allah ki bar ni na koma wurin Babana!" Kallona tayi bata iya magana ba, "wani abu ne ya faru?" "Kawai zan tafi nesa da nan ne!" "Kun yi fada da shi ne?" Cikin sheshakar kuka na ce mata. "Don Allah kada ki ce min na koma ki ni na koma can wurin Babana!" Yadda nake rokonta yasa ta kasa magana, bakiɗaya. "Me ya faru?" "Kawai na gaji ne na gaji na gaji wallahi gawata zaki gani na gaji na kai matakin da bana son kome sai nutsuwa!" Murmushi tayi tana faɗin. "Dakinki ne wurin da zaki huta, ki koma dakinki ki kara sa yakin da kika fara!" "Me yasa ba zaki gane halin da nake ciki ba, me yasa kike ƙoƙarin ganin ko zan cutu sai na koma ga Tafida? Mama Tafida ba mutum ba ne, ni ba zan iya gyara shi ba, don Allah ki bar ni na tafi!" Yadda nake kuka har da jan zuciya. Bakiɗaya ji nayi zuciyata tana zafi, tashi tayi ta bar ni a dakin. Bayan fitarta ko minti talatin bata yi ba sai ga sakonshi.
_Idan kina burin na sake ki ne ki auri Mutumin gidanku, kin yi kuskure ba zan tab'a sake ki ba har abada gara na ga mutuwata da naga aurenki da wani mara kunya don ina bin ki shine zaki rena ni! Don haka ki zauna har ki rube!_
Hawaye ne ya zubo min kamar an bude pampo, a daren na kira Mudan. "Aunty Baby lafiya?" "Ana kiran sallah farko ka zo don Allah zamu yi tafiya ne!" "Aunty Baby lafiya kuwa!" "Kayi min alƙawarin haka!" Ina cikin wayar Baba Bulama ya shigo shi da Mama, kashe wayar nayi suka rufe ni da fada kafin suka daura da nasiha, kafin suka kira Babana, shima ya nuna min b'acin ranshi. Ashe bayan ya turo min sakon shine Tafida ya kira Babana ya gaya mishi ni da Abbanshi mun hade mishi kai, shi kuma Babana ya kira Baba Bulama ya ce maza na koma dakina. Daren ranar ban iya barci ba, domin ji nake kamar zan mutu kafin gari ya waye. A daren na hada kayanmu ni da Yarana, na saka Babban jaka sannan tun cikin daren na kira shi na bashi kayanmu, asubar fari muka bar Maiduguri, bayan na ajiye musu wayata, Bauchi na saka ya kai ni, ya juya duk yadda yaso ya fahimci halin da nake ci naki, domin sai karfe sha biyu muka shiga Bauchi. Kai tsaye na wuce inda motar da yake zuwa Lagos, don na fahimci Mudan ba zai tafi ba, haka na je na samu ana kiran motar Lagos da ya fito daga Yola,ina zaune har ya iso na biya kudin Abuja, Mudan yana nan ina sane don yaki tafiya. Haka motarmu ya tashi, ya fito yayi ta bin mu kafin ya juya ya koma Maiduguri. Number Tinah da na dauka a takarda na duba, Ban tab'a sanin Yan biyuna suna da farin jini ba, sai da mutanen motar suka yi ta daukarsu wannan ya dauka wannan ya mikawa wannan, har muka isa jos, Yaran suna hannun mutane, ni dai addu'a nake tofa musu. Bayan mun huta karfe shida na dare bayan nayi sallah muka bar Jos, karfe sha biyu muka isa Abuja, dare yayi don haka a tashan na zauna aka bani wani daki da aka tara kaya, sai a lokacin nake jin me yasa na bar gida, dakyar yarana suka yi barci. Kiran sallah farko nayi sallah asuba, sannan na fito na amshi aron wayar wani mutum na kira Tinah. Har wayar ta yanke bata dauka ba, na sake kiranta a karo na uku ta dauka tana faɗin. "Waye ne? A daren nan!" "Gari ya waye yan mata, ki saka a zo a dauke ni don Allah kada ki fadawa kowa daga Maiduguri!" "Ummu kece!"
"Eh nice!" "A'a gani nan zuwa a wani tasha kike?" Na tambayi mutum na gaya mata. "Gani nan ki jirani Please!" Kashe wayar tayi, wurin karfe shida da rabi sai gata da kiran waya ta iso,amsar Yaran tayi tana me rungumar Mufidah tayi tana faɗin. "Ummu!" Sai hawaye sharrr, cikin kuka nace mata. "Babu wnada ya damu da ni, n bar Tafida na huta amma ban huta ba, Tinah ya zan yi." "Shiga Mota muje!" Ta saka yaran a baya, sannan ta dawo ta saka kayanmu, muka bar tashan bayan ta bawa mutumin da ya bani aron waya dubu biyar, yayi ta godiya. Ganin yadda nake kuka sosai, taka motar take da mugun gudu, ranta yana sosuwa. "Gaskiya har yanzu Northeast basu fahimci Muslunci kamar yadda Annabinsu kawo da hukunce-hukuncen addini akan aure da kuma pillar da zasu rike auren! Ana." Shiru tayi tana jin zafi tasan wannan da kasar turawa ne da tuni an bindige auren, tsaki tayi yafi sau uku. "Yaranki masu kyau da haduwa!" Ni dai kuka na cigaba da yi ban kuma amsa mata ba, koda muka isa gidansu ruwan wanka ta hada min, nayi wanka tayiwa Yaran, ta shirya su tana faɗin. "gaskiya yaran nan sun girman fa!".....
#Mai_Dambuhttps://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
"Hakki?" Ya tambaye ta, kafin ya fara duba aljuhun rigarshi da wandon shi yana niman hakkinta. Inda ya ajiye amma bai gani ya d'ago kai fuskarshi babu annuri ya ce mata. "Matsa ki bani hanya na wuce!" Ciki ciki ta ce mishi. "babu inda zan matsa ka bani hakkina kawai!" "Ba zan bayar ba, ke din wani hakkin ne dake, bakiɗaya mace babu dandano kina tsaye mace amma a zahirin cikinki gara a baka dafaffen kaza mara hadi, domin zaka ci shi haka da akan ke." "Wannan matsalarka ce, ita matarka da ka iya ci meye banbancinta da ni?" Kallon renin hankali yayi mata daga sama har kasa ya ce mata. "Ita ni na fara yanka kazar na fige sannan na dafa da hannuna babu wnada ya taya ni daga gefe. Kin ga ba tare da ajinamota da gishiri ba. Na cinye kazata, kuma har yau marmarin kazata nake!" Ya wuce ta abinshi yana jin ranshi fess. "Allah zai saka min!" D'aga kafada yayi yana faɗin. "Can miki!" Idan tana jin asalin zaman doya da manja tow kuwa shi suke da Tafida, domin bawan Allah nan baya kunya ya gaya mata magana anyhow. Ranar da suka cika sati biyu suka fara shirin dawowa gida, sannan ya shiga manyan store yayi ta sayayya kamar hauka Yaranshi da Ummu kawai su yakewa sayayya, yana gamawa ya wuce gida. A bakin kofarshi ya hango Sa'adi. Murmushi yayi mata yana faɗin. "Matar Governor!" Banza tayi mishi tana faɗin, "Aliyu ka bani hakkina mana, tun ranar da ka kai ni asibiti baka kuma bani hakkina ba ana maganar wata kusan uku." Gyara tsayuwarshi yayi da kyau sai kuma ya shiga cikin dakinshi yana faɗin. "Ke hala Aljanu ne dake masu jaraba?" "A"a Ifriqai nake dasu ba Aljanu ba!" Banke kofar yayi yana faɗin. "Ki je can ni bani da lafiya, basir yana damuna!" Shiru tayi kamar zata yi kuka tayi ta buga kofar Amma yaki.
***
*Ummu Hadiyya*
Tun lokacin da muka dawo daga gidan Malam Zailani, maganar da muka yi ya tsaya min a rai. Amma na tattara ba ajiye a gefe Tafida ba kamar sauran mutane ba ne, da zan sake waiwayarshi cikin sauki, dole ina bukatar sanin halin rayuwa da kuma yadda mata irina suke tafiyar da mutum irin Tafida, ba wai ban san halin Tafida ba ne, sai dai bana fatan na koma mishi har ga Allah domin yan uwanshi ba kaunata suke ba, gara na rufawa kaina asiri. Nayi zurfi cikin tunani wayata tayi ƙara, Hajiya na gani cikin farin ciki na dauka ina faɗin. "Hajiyata!" "Na'am yata, bayan ƙoƙarin da kika yi amma kin kasa zuwa duba Mamanki? Kodai baki son na miki maganar Baba Ali ne?" "A'a Hajiya ban samu fita ba ne, amma idan na samu fita zan zo in sha Allah." "Allah ya nufa na gode sosai, Allah ya miki albarka, yasa kema Yaranki su miki abinda kike mana, Ummu Hadiyya Ubangiji ya shirya bayanki da gabanki na gode sosai!" Idanuna ne suka cika da kwalla tabbas Hajiya ta gama min kome irin wannan addu'ar. "Amin Ya Allah, Amin Ya Allah, Allah ya baki lafiya Hajiya." Na fada kamar xan yi kuka don bana son yadda suke min godiya. Kashe wayar nayi ina sauke ajiyar zuciya. Na kalli Yarana sai naji sanyi a raina tabbas Allah ya min ni'ima da ba kowa yake da shi ba. Alhamdulillahi da wannan damar da Allah ya bani.
*Shuwa*
A gaban Malamin take kamar zata yi kuka ya ce mata. "Ita yarinyar a tsaye ake kansu, na gaya miki sai an tashi tsaye domin ko muna aiki zamu samu masu warwaresu." Idanunta sun kad'a jajjur ta ce mishi. "Malam babban tashin hankalina shine uwarshi ta dawo taya zan samu biyan bukatana!" Zane yayi kafin ya d'ago kai yana kallonta kafin ya ce mata. "Yarinyar ta dawo da ita, sannan babu wata hanyar da zamu iya kulla wani abu, sai mun samu hanya." Ya cigaba da zane kafin ya d'ago da mamaki ya kalleta ya cigaba da cewa. "Akwai hanya amma ba nan kusa ba, abu daya zan gaya miki shine ga wannan hayakin ki tabbatar an saka ya sha shima dan banza yana da taurin kai, wannan kuma a jefa a rijiya mu ga me zai faru nan gaba! Tabbas hanya biyu ne na farko ki tabbatar ranar da ya dawo ranshi a bace yake na biyu kuma gaskiya za a iya rasa rayuwar wani ko.wata akan aikin idan kuma kina ganin haka zai zama mafita to!" "A'a ban da kisa Malam, a barshi xan san yadda zan yi da shi." Zufa ne ya karyo mata, kafin ta ce mishi. "Allah yasa a dace domin yaron nan na sha fama akanshi yanzu da zan huta amma kowa yana niman hanani! Yan uwansa da nake amfani dasu ma sun fara ja da baya." Murmushi ya yi ya ce mata. "Ga wanann ki tabbatar kin saka musu, ba zasu tab'a miki gardama ba, sannan zasu zama masu miki biyayya!" Kudi ta zuba mishi, tana godiya ta fito.
---
Tunda tasan abin da ta kulla, ta nufi bangaren Abba da ta dawo tana