Showing 51001 words to 54000 words out of 241571 words

Chapter 18 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14697

wahala kamar kina son Mijinki, shiru nayi na ce mata. "Dama nace miki bana sonshi ne? Mijina ne kuma Yayana,sannan kuma dan uwa ne a musulunci." "Ba wanann tambayar na miki ba, domin na sansu shin kina sonshi na soyayya da rayuwa?" Shiru nayi ina kallon sama kafin na ce mata. "Wannan tambayar naki yayi tsauri dayawa bani wuri na wuce " dariya ta saka min tana faɗin. "silly girl!" Haka muka gama abincin rana alale da kunu muka dawo parlour, sai lokacin ya shigo yaga muna cin abincin. "Ya Tafida na kawo maka daki ne?" Na tambaye shi ina mikewa, "A a anan yayi kawo min nan!" Zan iya cewa a kwanakin da nayi ina jinyarshi, na sha azaba domin taimaka mishi ya saka kaya ma aiki ne. Wani abun da ya kara bani tsoro, shine yadda jikinshi yake tare da kai hannun shi cikina ko ya ya tab'a min kirji, ganin haka na fara baya baya, idan yace na rike shi nayi ta ɗan jan baya kenan ina dan nazarin taimaka mishi. Zama yayi yana faɗin. "Kada ki cigaba da tambayarta wasu abubuwan, Please." "Kana tsoron kada tace bata sonka ne? Ai na hango ka shi yasa nayi mata tambayar, yanzu ma ba haka ba maganar tafiyarta Lagos ka ware ka barta ta je!" "Zamuje tare!" "Ka fara sonta ne?" "Ina ga wannan ba matsalarki ba ne! Na sota ko na kita choice dina ne!" Haka na kawo mishi abinci na wuce dakinsa na dauko maganin anan na lura da dakin yayi datti na zauna na gama cin abincin sannan nace mata. ,"bari na duba dakinshi!" Na shiga duk da naga yadda ya kafe ni da idanun haka yasa na shiga da sauri na shiga gyarawa. "Tana da kirki da sanin ya kamata, matarka ce kana da damar gyara kome." "Jira ni mu fita tare zan tafi asibiti!" Ya fada mata yana me nufar dakin, na zage ina wanke ban dakin na ji shi a kaina yana gyaran murya, da sauri na d'ago kai. "Wanka xan yi ko zaki bani wuri!" Ya fada yana wani haɗe rai. "Ba damuwa na" na fada da sauri ina barin ban dakin, wanka yayi yana kara jin zazzaɓin yana dawo mishi. Sannan ya fito ya shirya muna tare da ita a parlour. Ya fito cikin farin material na maza, rigar kenan wandon Black kaftani ne me ɗaukar idanu, duk da ya rame amma kyan shi ya kara fitowa sosai. "Zan tafi amma maganar tafiyar tana nan?" "Ba zan samu zuwa ba!" Na fada mata ina murmushi, fita tayi yana bin bayanta, asibitin a unguwar yake ta kai shi ta wuce shi kuma ya wuce cikin asibitin. Yana shiga suka hadu da likitan dake sun san juna. Haka ya shiga ya zauna Abokin yana kallonshi ya ce mishi. "Ya jikin naka?" "Da sauki amma kuma!" Gyara zama yayi yana faɗin. "A yan kwanakin nan ina fama da matsanancin bukatar mace, abin da ban tab'a ji ba." "Ina Madam take!" Gyara zama yayi kafin ya shafa kanshi. "Matsalar daga ita ce, tunda ta fara kulawa da lafiyata nake jin kamar akwai wani abu a tare da ita, da tana kusanto ni zan ji kamar na tab'a kirjinta."
"Aliyu kasan matsalarka tun wancan jinyar da kai. Kana bukatar mace kuma itama mace ce." "Habib ba wai naki ba ne, a yadda nake ji kamar idan na same ta zan iya rabata gida biyu ne, ita kuma tayi kankantar da ina ga ko wucewa ba zan iya ba,.shi yasa idan na samu dama nake son na auri Sa'adiyya!" Kallonshi yayi kafin ya ce mishi. "Tafida kenan Ita matarka da kake ganin ba zata iya da kai ba, irinsu ne suke bada mamaki, sannan xan baka magani da zai rage maka zazzaɓin ita Sa'adiyya babbar mace yaushe zaka aurota!" Jingina yayi da kujeran yana murmushi ya ce mishi. "Abba yaki amincewa!" "Ya kyauta wallahi!" Ya cigaba da rubutu. "Kafin kayi magana akan mutum ka fara sanin waye shi, ita Yarinyar da ka rena ba zata iya daukarka ba, ka bincika ka ji tarihinta? Sannan ita wacce zata dauke ka kaji wacece ita? Aliyu kada ka so kanka dayawa, duk wata mace tana daukar bukatar namiji daidai da yadda yazo mata kai kuma ɗan kutumar abin da Malam ya hana fada kana gaya min ba zata dauke ka ba,kai din banza abinka da bai kai a matsayin wanda zai fito ta bakin mace ba." Ganin tozarcin Habib yasa shi ya kama dariya, yana kallon shi. "Ita mace matukar ba kai ne ka lalata ba, babu abin da zaka rasa a tare da ita balle kuma irin matarka ka kamar kayan hada abinci suke idan babu su babu dandanon ba zaka gane haka ba sai ranar da ka ajiye su zuwa biyu anan zaka fahimci haka."
"Ni rubuta min magani na fita kafin ka lalata min tarbiyyar da nake da shi!" Tsaki Dr Habib yayi ya rubuta mishi magani, sannan ya fito ya saya kana ya bar asibitin, a hankali yake tafiya har ya ya isa gidan.
Ina wanka na ji ana buga kofar da sauri na gama na fito, tare da saka Hijab kato, naxo na bude kofar yana tsaye. "Uban me kike nake ta buga kofar gidan?" "Kayi hakuri wanka nake?" "Wankan baki asarar ruwa kenan ko yayi ma kamar bai yi ba! Ke ki daina wannan wahalar domin ba wani burgewa zaki yi ba " kasa nayi da kaina na matsa ya shiga na wuce ban daki, sai kaji kamar gaskiya ya fada ko nayi wankar ai ba fatar xan sake ba. Hadiye yawu nayi domin dai ba zan yi bleaching saboda shi ba. Haka na dauraye jikina na fito zuwa dakina. Ina tsaye daure da Towel ina niman kayan da zan saka ya shigo dakin. " da sauri na juya abinda ya faru kwanakin baya ya dawo min da sauri na ja da baya, kallona yayi daga sama zuwa kasa idanun shi ya dauka kan kafaffuna, gyada kai yayi kafin ya tako har zuwa inda nake ni kuma ina komawa da baya. "Nazo ganin me yasa nake jin na tab'a kirjinki!" Baya nayi da sauri ina me k'amkame towel din kamar xan yi kuka. "Cire towel din na ganki da kyau!" Girgiza mishi kai nayi ina kokarin gudu zuwa banɗaki sai ji nayi ya saka min kafa na fadi can, takowa yayi yana kokarin mikewa ya damke towel din da karfi ya raba ni da kasa, kan gadon ya wurgani sai da gadon yayi wani irin ƙara, "don Allah kada ka min haka!" "Kada ki bata min lokaci kawai kallon abin zan yi na wuce!" Ya janye towel din da karfin tsiya rintsa idanuna nayi da ƙarfi, idanunshi a kan kirjina zuwa cikina. Hannunshi ya kai kan cinyata ya fara kokarin kallon gefen dama da hagu, kafin ya kai hannunshi tsakanin cinyoyina, da sauri na rike hannunshi ina jin kamar na fashe da kuka. "Don Allah kada ka min haka!" "Ke kamar takalmina ne, na saka shi lokacin da yayi min don haka na zo na yi gwajin takalmi ne naji ko zan shure shi duk lokacin da na shirya!" Mikewa nayi tare da ture shi ya janyo kafana tare da min rufa bayan ya danne hannayena da na shi. "Kada ki saka ni nayi abin da ban yi niyya ba nazo na gaya miki ne gobe zamu tafi Lagos don haka daki ɗaya zamu kwana. Daga yau kuma kin daina kwanan ke daya dai dakina wannan shine karshen abin da zan gaya miki."ya fada yana me kai hannunshi cikin wani irin yanayi da ban san shi ba, yana min tafiyar tsutsa akan cikina. "Don Allah ka bari, ka ji don Allah ka daina bana so." Hannunshi naji a wani wurin da nan zata ba, rintsa idanuna nayi ina ji kamar numfashina zai bar gangan jikina. A hankali jikina ya dauki rawa ban san lokacin da na fashe da kuka ba. "Don Allah nace ka daina!" Na fada da karfi wanda ya dawo da shi hayacinsa. Da sauri ya cire hannunshi da ya b'ata share min yayi a jikina na fashe da kuka, haka.ya mike ya bar dakin, tunda ya fita anan wurin ya bar ni cikin tashin hankali. Ban yarda na kuma haduwa da shi ba, washi gari ma haka ya saka ni a gaba muka bar Abuja zuwa Lagos sai dai har lokacin bani da nutsuwata, kuma shima ya gane haka. Sau dayawa Sa'adiyya tana son yayi mata, amma yake ki, idan bai yi ba kwana take tana juyi a gado, Sa'adiyya ita ce dalilin ciwonsa na farko na biyu nan ma haka domin akwai wani gidan cin abinci da suke yawan haduwa, duk da ya hanata zuwa gidanshi, haka bai haka shi kama mata daki anan garin Abujan ba, idan suka hadu tayi ta jarababshi da ya matseta shi kuma yana gudun abin da xai faru don yasan haramun ne. Haka zai jagwalgwalata, har sai yaga ta nutsu, ba zai ce ba amma tabbas akwai abin da ta bashi da jikinshi baya so wanda ya haifar mishi da rashin lafiya domin wani irin jaraba yake ji amma wani ikon Allah duk da haka baya nimanta, na wannan karon da yaji abin sau biyu yana ganin likitan shi yana bashi shawara, na karshen ne ya gaya mishi ya nime Ummu su daidaita amma karshe ya kare da hakan. Tafida ya ci alwashin sai ya biya bukatarshi kafin ya ji a ranshi yana da wata bukatar domin duk abinda Sa'adiyya take saka shi yu duk ya ajiye akan Ummu zai sauke. Koda muka isa lagos Tafida bai boye min ba, jikina yake so ya tab'a na shiga tashin hankali kamar zan gudu haka na daure, daki daya muke kwana ina kasa yana gado.amma zan farka naji ya mai da ni sama. "Shiii! Zan koya miki yadda ake gudanar da kome ne! Da zaran kin zama yar hannu ba ki da matsala! Don ma kina da tsafta jikinki bai da wari ko karni!" Kuka na saka mishi haka yayi ta jagwalgwalani, kafin ya kyale ni. "Ya nasan kin ji dadi ko? Nasan kin ji kamar na cigaba!" Tattara kayana nayi na shiga ban daki nayi wanka na fito na kwanta a kasa. Idan nace bana takura ai nayi karya Tafida ya saka min damuwa har sai da ta kai cikin dare bana barci domin yadda zai lallabo ya tashe ni, kai ranar da muka cika kwana uku, zazzaɓin shi ya dawo ina jin bai tashe ni ba sai kakarinsa naji na farka ina me nufarshi. Kunna wutar dakin nayi na ganshi yayi rubda ciki. "Sannu Meke damunka?" "Kina guduna ne fa, shine ciwon ya tashi!" "Ban gane ba?" Na tambaye shi. Nan ya warware min ji nayi kirjina yana dokuwa, kamar zuciyata zata dirko nayi baya. "Me kake nufi? Ni." Dake bukatar shi ce ya manta da kiyayya da kome ya fara kokarin niman abin da zai kara da shi ya min tijara, kasa hakuri nayi na koma can inda nake kwanciya na kashe wutar dakin na kwanta. "Kada ki manta Mala'iku zasu ta tsine miki har gari ya waye domin kin kauracewa shimfidar Mijinki! Sannan zan gayawa Abba ya sani idan na mutu kece!" Kasa magana nayi ina kallon shi a cikin duhu, ya tako kamar wani dan kwayya ya nufe ni. "Kin gani kamar zan mutu kada na.mutu a wannan yanayin!" Banza nayi da shi zan tashi ya riko jelar kitsona ya wuce da ni kan gadon.
Kamar wanda aka cire mishi ciwon ne ko jin yadda nake kuka yasa shi cire hannunshi a jikina, ya koma ya kwanta yana juyi karshe ya tashi ya bude jakarshi ya hadiye wasu magani ba ruwa ya kwanta. Ni dai kwanan zaune nayi. Bayan minti talatin na ji ya fara barci. Nima kwanciyar nayi a wurin, bamu farka ba sai da gari ya waye tas, wani ikon Allah sai gamu manne da juna, bude ido nayi na ganni cikin jikinshi da sauri na tashi zaune ina kokarin ganin na bar shi ya kalle ni a wulakance. "Iskanci zaki min? Ko fyade kika so min?" Hadiye yawun bakina anyi na rasa me zance mishi, a hankali na zare jikina daga nashi na sauka akan gadon na wuce ban daki nayi wanka da alolan shima wanka yayi da alolan ya fito daure da Towel a kugunsa, lokacin har na gama saka kaya. Yau juma'a babu abin da zasu yi sai asabar da Litinin. Don haka ina gama shiryawa na saka abayan zan fita ya ce min. "Ina zaki da safe nan garin akwai ruwa?" "Zan je na karya ne!" "Ki zauna za a kawo dakin!" Ya fada yana saka wandon shi naki yarda mu hada idanu. "Dawo nace!" Haka na dawo na zauna, cire towel yayi yana shirinsa, yana gamawa ya kuna wayarshi nan na ga yana me murmushi. Wayar ya kanga a kunnenshi ya manta da ni bakiɗaya daga yadda yake wayar na fahimci da rukayya yake magana, "Laraba zamu dawo ke kuma kizo juma'a." Kallona yayi ya ce. "Kina kallona kamar mayya ni manyan idanunki nan tsoro suke bani wallahi! Yanzu za a kawo abinci." Sunkuyar da kai nayi ban kula shi ba. Haka aka kawo min abinci har dakin na karya , washi gari asabar muka je taron, Litinin da Talata duk an yi, na dawo da tarin kyautttuka. Na kira Mama da Abba na gaya musu sannan na kira Baba Bulama da Babana na gaya musu. Ranar Laraba muka dawo Alhamis na wuni aiki ranar juma'a, sai ga Rukayya da yaranta biyu. Nayi kokarin koyawa kaina dauke kai akan abinda bai shafe ni ba, kuma Alhamdulillahi Allah ya ba Ni saa domin naki kula iskancin Yaran balle na Uwarsu, yadda ta ga dan uwanta yayi laushi sai da ta xage ni wai na karbi asiri xan mallake musu dan uwa. A hankali fa kome ya fara cabe min abin da ya rage ya dawo, kwananta uku Sa'adiyya tazo sai da naji kamar na kashe kaina don bakinciki domin duk ta inda zasu saka min damuwa suna aikatawa, abu daya na sani zuwa wurin koyarwa tayi tasiri bana ganin abinsu kayana kuwa har na dawo na samu anyi min kaca-kaca da shi. Kwana biyu ban ga Tinah ba sai da tayi kwanan biyar sai gata da wasu kawayenta na amshe shi da farin ciki, na kawo musu abin tabawa. "Iyawo mun zo za ayi bikin wannan kin ganta!" Ta nuna min ita sannan ta cigaba da cewa. "Tana son turaren wuta, da irin wanda kike amfani da shi, sannan za ayi mata cake." "Tow ki gaya mata za a yi amma turaren wuta daga gida zaa kawo kamar na nawa take so?" Tana gayawa kawar tace ita . "Ni ko na dubu dari biyar ne." Kiran Mama nayi muka gaisa na gaya mata, ta kaiwa Ummi wayar na fada mata abin da ake bukata, ai kafin wani lokaci ta turo account na kara mata bayanin ni nawa har da humra da kwalaca, duk aka hada mata aka tura kuɗin, sai lokacin Aunty Rukayya ta fito tana kallonmu,jin muna maganar kuɗi. Sama-sama suka gaisa da Tinah sauran kayan aka bar min aikin. Sannan na raka su. Ita yarinyar da zata yi aure ta bani kyautar dubu hamsin. Na dawo na ajiye a kitchen. Abin mamaki sai gashi tsakanin rukayya da Sa'adiyya ba a san waye ya dauke kudin ba, ni dai ban yi magana ba, na barwa Allah don sune a wahale. Shi ma Tafida ashe a wannan dan yanayin da gidan ya karu sata ake ta mishi dakinsa, wannan lokacin ko bera albarka, sati guda aka.dauka sai ga turare ban yarda na kawo gida ba, Tina ta amsa musu ni kuma na amso kayan da Mama ta hado min na kawo. Haka lokacin bikin yayi muka sha aikin cake da kawo sauran gida, akan idanun Tafida na ajiye a kitchen shima ya shiga dauka aka rasa waye ya dauka. "Ummu!" Ya daka min tsawa, ina sallah ya kara kiran Amir ya ce mishi. Ina sallah, ina idarwa ban yi addu'a ba, na fito . "Ina abin da kika kawo?" "Ai kana gani a kitchen na ajiye!" "Rukayya, Sa'adiyya Ummu tana shigowa dukkanku biyu kun shiga kitchen din wacece ta dauki abin da aka ajiye." Fashewa da kuka Rukayya tayi wai ya daura mata sata, dama ta lura na gama da shi. Abin haushi ban san lokacin da na fara fada ba wanda nasan tunda nake ban tab'a yin shi ba. "Na gaji ban isa na fita ba xan samu an bincike min kayana, ban isa na ajiye za a dauka min. Ranar can dubu hamsin na ajiye saboda dakina ban isa ajiya ba za a bincike min na saka a kitchen haka narasa kudina, Allah ya isa min ban yafe ba, domin hakkina ne gumina ne duk.wanda yaci sai mun tsaya Allah ya karba min abina a ranar da bamu da shi."
"Kudinki yana wurin Umminmu, cake din ma ita ta dauka!" Juyawa Sa'adiyya tayi tana me nufar dakin Tafida ta saka kayana ta fito tana faɗin. "Ni dai babu shegen da zai ajiye abu na dauka ko na dakinka da ake dauka ita Yar uwarka zaka tambaya." Bakiɗaya muka barta a wurin kunya kamar zata nutse, ai kuwa washi gari ya haɗa mata kayanta kudina na wurinta fir taki bani, nima ban mata magana ba. Ashe gurmi ne a aka shirya bayan tafiyarta aka kira shi aka gaya mishi bikin Sharif wanda za ayi shi wata me kamawa....
*SAURA 3 PAGE NA GAMA FREE PAGE! ANZARTA KI BIYA KADA A BAKI LABARI*


500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga number da zaku tura naku payment din : +227 84 50 64 76 Nana A'ishah maradi'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*






*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML*


*Ina mata yan yayi shin ko kun san kayan da Ummu take amfani da shi, yana fitowa ne daga shahararren Shagon nan na R&U Exclusive Kitchen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login