Showing 45001 words to 48000 words out of 241571 words

Chapter 16 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14700

muna dawowa muka samu Tinah, murna kamar zai yi yaya ta kawo min kaya ne , wai ashe ta tafi Dubai ne sai gata da kaya niki-niki, tsaki yayi yana faɗin. "Tina kina bata yarinyar nan da kyauta fa,.ni bani da halin yi mata abinda kuke mata ke friend dinki!" "Aliyos ba zaka gane ba ne, Ummu tana da kirki shi yasa bana jin zan iya samun abu ban bata ba." Dogayen riguna kala uku sai takalma heel , masu kyau kafa hudu da jakunansu. Sai wani Musulmin lace me kyau kala biyu, "Gashi kin zo muna azumi me zan miki?" "Tafiya xan yi idan za a sha ruwa xan zo!" Haka na rakata ina ta godiya, har zata shiga Mota ta ce min. "Akwai wata yar ghana tana sayar da mai da sabulu xan karba miki." Dariya nayi nace mata "a'a bana son bleaching!" "No ba zai kara miki haske ba amma zai gyara miki fata!" "Tow shi kenan amma zamu tafi Umara duk da bai gaya min lokacin ba!" "Zan kawo miki an jima! Ni dai turaren Maiduguri nake so ga gidan ki nan mutum ya rasa wani irin kamshi yake yi!" "Kai Tina zan a kawo miki!" Haka muka yi sallama ta tafi,na shiga aiki kamar kafafuna zasu yanke. Ana shan ruwa Tina ta kawo min kayan na ciro mata kula masu kyau na zuba abinci a ciki ta tafi da su don saurayinta ya kawo ta, an fara azumi da kwana bakwai muka bar Nigeria zuwa Saudiyya. Lokacin da na ganni a dakin Ka'aba sai da nayi kuka nayi kuka nayi farinciki nayi addu'a na kai kuka na wurin Allah. Sai da aka sha ruwa na koma hotel dinmu, hmm Tafida tunda muka yi wanka muka tafi harami ban kara ganinshi ba, wasa gaske sai da muka sati Daya na ganshi tare da Sa'adiyya. Kallo daya nayi musu na dauke kai, ko ya sha jinin jikinshi ne, da asuba lokacin Sahoor sai gashi. Sau daya na kalli inda yake na kauda kai. Koda muka yi Sahoor kowa kama gabanshi yayi, na nufi masallaci, shi kuma yana me budar hotel din da ya sauya dukkanmu a nan haramin muke, haka ma da muka tafi Madina, sau na ganshi sai na dauke kaina, lokacin da naje rauhda. Anan ne naji kuka ya zo min, na tafi gaban Kabarin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, na zauna cikin kuka nace. "Ya Rasulullahi, ka sauke dukkanin sakonka ka yanta mu daga duhu zuwa haske ka cire mana rigar jahilci ka saka mana naka me haske da kamshi, Ya Rasulullahi kace muyiwa Mazajenmu biyayya su kuma su riƙe mu da adalci Ya Rasulullah na kawo kukana gare ka." Ban sani ba ko damuwar Tafida da ne yasa nake surutai ko bakinciki ne yasa nake jin kamar ban isa kome ba,amma zamana a rauhda yasa ni jin sauki da kuma surutai da nayi tayi sai naji kamar na yantu na samu sauki a zuciyata, na roki Allah ya cire min tashin hankali da damuwar Tafida. Har muka gama umara, sannan muka yi sayayya wanda ana jibi zamu bar maka yazo ya watsa min kudi na kalle shi nayi murmushi tare da cewa. "Ni bana bukata, ita wacce ka dauko ka kai mata ta fini bukatarshi ita tana jiran naka ne ni wanda iyaye suka bani ya ishe ni!" Ware idanu yayi tare da shigowa dakin zai hayayako min nace mishi."ina azumi bana faɗa!" Ina fadar haka ya dakata. "ina dakin Allah bana son na tafi na bar zunubi, kaima ina maka fatan shiryar Allah. Domin ka b'ata da yawa." Na fada ina me shigewa ban daki, wanka nayi tare da alola na fita nayi sayayya a kantin da naje sayayya, nayi ta sayan kananun kaya, Allah ya taimaka ina dan iya fahimtar larabci saboda mun yi tajewid, haka na gama sayyana lafiya lau na fito. Har nuna ni larabawa ke yi wai sun sha mamaki da nake iya fahimtar larabci da kuma kokarin da nayi. Turare na sayawa Abba biyu Babana biyu. baba bulama biyu sai Hajiya Kaltuma da Hajiya Salamatu, sai Maman Tafida da na saya mata kaya itama, ina dawowa na same shi a bakin kofar dakina. "Ga kudin nan Abba ya turo na baki wai na kayan sallah ki ne!" Saka hannu nayi na amsa ina faɗin. "Allah ya ƙara mishi lafiya da nisan kwana!" Na shige abina ina me rufe kofar, zama nayi ina nazarin kudin nan idan na canza shi Maman Tafida ya dace na bawa tai ko jari da shi ne gaskiya matar tana bukatar taimako sosai. Ranar da muka bar Makka muka wuce jidda, ina kallon tsiyarsu. Jirgin Maiduguri muka hau amma zai sauke mutane a Kano, haka muka bar kasar cike da kewarshi. Mun isa Kano, daga nan ban kara ganin Sa'adiyya ba, murmushi nayi domin naga sai lokacin ya nutsu da bai da nutsuwa bakiɗaya, haka muka taso bayan mun sha ruwa muka iso Maiduguri Deen yazo ya dauko mu, sai tsiya yake mana wai mu gaya mishi gaskiya ko mun dauko dan Makka da Madinah ne! Ni dai ban ce kome ba, ban san wani irin mutum ne Tafida ba, amma bai iya boyewa Deen matsalarshi. Domin anan ma gaya mishi yayi tare da Sa'adiyya suka tafi Umaran, bayan sallah nan zai gabatar da ita a wurin Alhaji . "Yayi kyau ai, amma ka sani yadda ka saba lalata da ita a waje idan ka shiga cikin gidan ya." "Bana son iskanci wallahi ban tab'a wuce gona da iri ba, iya kata." Sai juyawa muka haɗa idanun ganin murmushin da yake kan fuskana ina sauraron karatun Alqur'ani, domin akwai earpies, shiru yayi yana faɗin."ashe tana jin abu ne!"
"In sha Allah sai Allah ya saka mata!" Kafin mu isa gida sunyi fada kaca-kaca kamar zasu daku,. Har cikin gidan Deen ya dauka min kaya, ina jin yana faɗin. "Muje na ajiye miki zan tafi wurin budurwata!" "Kai ba zaka ɗauka min kayana ba!" "Saboda tsine min Ammah tayi?" "Hmm Dan iska!" "Ni bana wuce iyakar Allah!" Ya fada yana shigar da kayanmu, ni kuma na wuce cikin gida, dakin Inna na fara shiga ina faɗin. "Hajiya Innata gani nan!" "Ummu kai ne kazo!" "Eh nice Innata!" "Sannunka Yaron nan Ummu sannu da zuwa!" " yawa Inna! Da fatan an sha ruwa lafiya, mun same ku lafiya?" "Alhamdulillahi, ya Tafida take?" Murmushi nayi ina faɗin. "Duk muna Lafiya!" Sannan na mata sallama na wuce wurin Hajiya Salamatu na gaidata, ta ji dadi sosai. Ina fita na shiga dakin Hajiya Kaltuma, Uwar dakina nan na bararraje muka sha hira kafin na wuce wurin Abba, wasa wasa zai da muka share awa biyu hiran da nasiha yake min. Sannan nayi mishi sai da safe na.dawo bangarena. Dakina da gidan na ga an share min shi tas an goge an gyara ko ina, wanka nayi da ruwa me dumi ina fitowa nayi sallah Magariba da Isha na bi lafiyar gado, da zan yi sahur nayi wani mafarki me ban Mamki, Tafida ne ruwa yake tafiya da shi Ikon Allah hajiyarsu tayi kokarin janyo shi amma ina ruwan yaci karfinsa, ban san ya aka yi na fada ruwn ba na shakka wuyarshi, amma wasu mata da bansan su ba suka hanamu fita, wani katon maciji ya fasa kai yana bude baki, ganin haka yasa nayi ta jan Tafida amma Macijin nan yana bin mu, duk wanda ya nufe mu xan ga macijin nan ya nufe shi baki bude da wannan tashin hankali na farka jikina yana rawa. Ban daki na shiga nayi alola sannan na nufi parlour yana zaune shi da Sa'adiyya, ban yi mamaki ba don naga yana cin abinci, sai hira suke abin su zuwana Umaran nan na koyo shan shayi na fito da dauke da kofin tea domin jiya bayan dawowa na daga cikin gidan Deen ya buga mana kofa ya bashi yace. "Kai bawa Ummu na ta ne!" Don har da Nama yana zuwa ya ajiye min a bakin kofar, wani ikon Allah ban tab'a jin nayi magana akan Abinda yake min ba, haka kwanaki suka zo suka wuce , aka zo bikin sallah nayi abinci na kai, anyi sallah da kwana biyu kamar an bashi ina kwance a dogon kujera ya shigo yana faɗin. "Idan kin gadama ki shirya muje ki ga yan gidanku!" "Da gaske?" Na tambaye shi, "Ni abokin wasanki ne?" Yadda yayi min maganar na fahimci babu wasa da sauri na shiga daki sai ga Ni dauke da katon akwati, na tsarabarsu dama na cirewa Abba da na yan gidan, sannan na daura laffaya. Ina jan akwatin haka muka fita, a waje muka samu Deen ashe har da shi gaban motar ya shiga, "Ummu inji Ammah wai ta gode, abincin sallah sai sun cinye suka hanani. Gashi ko abokaina ban yi musu kome ba, don Allah na kawo cefenen ki musu girki wancan yarinyar ba zata iya fitar dani kunya ba!" "Ka turo ta mana muyi tare sai kace mata tazo na tayata babu dad'i tana matar da zaka aura amma ce ka kawo min abincin da zaka ba abokanka, sannan gasu Jalila ba zaka basu su maka ba?" "Ammah zata min sinasir, Jalila me ta iya ban da iyayi." "Shi kenan!" Na fada ina dariya, haka muka isa gidanmu, Wayyo dadi tunda muka shiga cikin gidan, na nufi parlour Baba na gaishe shi tare da Tafida, sannan na wuce wurin bangaren Ummi na gaida ta ita da Umma kafin na wuce bangaren mu, ina shiga na ga irin kallon da Tafida yake yiwa bangaren mu, kamar ya ga kashi. Mama kuwa sai hidima take mishi, Deen sai godiya yake mata. A yau nakara jin wani irin tsanar Tafida, domin babu dan da za a yiwa iyayenshi haka ya ji dadi. Ko ruwa bai sha ba ashe bani daya abin ya dama ba,.har da Deen. Suna gama gaisawa ya fita Deen ya zauna yaci abinda aka ajiye musu, ya ce mata. "Mamanmu ni fa zan tafi da kayan dadin nan wallahi!" " za a zuba maka ka tafi da shi!" Nan ya sake narkewa da murna, ita kanta Mama ta ji dadin Deen domin ta fahimci abokin Aliyu ne na amana. Bayan ya gama ya fita nima muka yi ta hira, na tura mata tsaraban ina mata bayani, ta amsa tayi godiya ta kuma ce zata raba gobe in sha Allah, "maza tashi ku tafi Allah ya miki albarka." "Amin Mamana " haka ta zuba min kayan ciye-ciye, na fito da shi, anan take gaya min ai Uwani ta tafi sallah gida , nayi fatan Allah ya dawo da ita lafiya haka muka bar gidan, tun a mota Deen yake faɗin. "Ummu Mamana ta ce min zata baki kayan dadina!" "Da dai kayi hakuri muje gida na diba maka!" "A'a gudun kada a sake samun dan fashin da yake juye nama ya kuma juye min kayan dadina ne wallahi ba zan yarda ba!" Ashe ya gaya mishi ya juye min nama, mutum sam babu sirri koda yake na lura tsakaninsu su biyun nan babu sirri suna gayawa juna kome, idan ka cire Mahmoud da basu irin wannan maganar da shi. Koda muka dawo na diba mishi nashi ya tafi, na bari a kitchen ina fitowa na samu ya dibo ya zuba a flat suna ci da Sa'adiyya sai santi take. Washi gari na kara kiran Mama na gaya mata ina son turaren wuta zan kaiwa Tina da yan uwanta da kawayenta, ta ce zata saya min a wurin Ummi. Kwana biyu Abba ya ce na shirya Tafida zai kai ni Biu.


Haka na roki Hajiya Kaltuma ta bani aron Nabila muka shiga kasuwa nayiwa Babana sayayya, muka yi cin-cin da cake. Sai nama wanda Abba ya bamu na sallah na soya na saka rabi a firji domin a zaman shekara kusan daya na gano lagon Tafida yana son nama kamar yayi hauka, zai iya cin nama da bread ya sha ruwa ya koshi, don haka na saka mishi wani a langa tsirara. Da kanshi da rakiyar Deen ya kai ni har kofar gidanmu, wannan karon an karbe shi a matsayin d'a ne da zai tafi ba karamin hidima aka mishi ba, Babana har kudin mai ya bashi ya mishi alkawarin zai saka a kawo ni har gida, haka kuwa aka yi na kwana biyu a garin Biu, mahaifina da danginsa kamar su lashe ni domin duk abinda na kawo ya saka an rabawa dangi kaf sai kaɗan Mamawo ta ajiye mishi, nima da zan dawo kamar wacce nace musu bani da kayan abinci, kuka, kubewa busashe, barkono, albasa, daddawa, garin kunu me kyau, kai tsaraba sai da aka cika min bayan mota da shi, kaji kuwa yanka min su aka yo aka gyara aka fasa ƙanƙara a kai, domin nace dambu zan yi. Mun iso da la'asar ban huta ba na hada wuta na daura dambu. Ya kwana washi gari na tuke shi tass. Alhaji ya kara turo min da nama danye yace na soyawa Tafida, haka na dafa na soya shi cikin langa tsirara, Mama tayi min cin-cin da kayan ciye-ciye sosai domin wannan karon mota zamu bi, sai da na gyara gidana na cirewa yan gidan tsarabansu ana gobe zamu tafi da dare Aunty Rukayya ta zo, ina jin yana gayawa mata shi ya gaji da bin shi da zan yi yayi magana Abba ya fara faɗa. Shine ta shigo dakin ina zaune da littafin addu'a. "Ummu Hadiyya ki gayawa Abba ba zaki bishi ba, don ai wannan takura ne ke baki ji kunya ki bishi ba." D'ago kai nayi na kalleta kafin nace mata. "Aunty Rukayya ke me zai hana ki samu Abban da kanki!" "Ni sa'anki ne?" "A'a na gaya miki abin da ba zaki iya ba tow nima ba zan iya ba, ba haka aka koya min ba, ba a nuna min musu da babba ba!"


Fita tayi jikinta a sake, can ya shigo.ya fara zagina ina ga Sa'adiyya tana parlourn don naji muryanta Aunty Rukayya tana bata labarin har ya gama ban d'ago kai na kalle shi ba, yana fita na rufe kofata. Jin Muryan Deen yasa ni fita muka gaisa nace mishi. "Don Allah ina son magana da kai idan da hali!" "Ok!" Ya tashi muka fita waje mika mishi kudi nayi nace mishi. "Don Allah ga number Mamanshi ka tura mata kudin nan, " "ke kika yi niyya ko tambayarki tayi?" Murmushi nayi nace mishi, "Bata tambaye ni ba idan ka canza a tura mata don Allah!" "Allah ya tsare gabanki da bayanki, lallai na yarda akwai abinda Abba ya hango ne." Amsa yayi ya saka a aljuhun shi, koda ya koma ciki share shi Tafida yayi wai akan ya kula ni hala, shi kuwa dan ya kular da shi sai dariya yake irin na niman fada.. da fada suka rabu, washi gari muka bar Maiduguri da assuban fari ana kiran assalatu, wannan dawowar da nayi abuja ya saka ni jin na tsani kome na duniyar nan, ya sakani cikin tsoro da wani irin fargaba. Domin kuwa Tafida ya barni ina rayuwa kamar bani da yanci.


Tunda muka dawo Mahmoud ya saka ni a gaba ko a ina ya samu numberta kullum sako kullum kiran waya, idan nayi blocking dinsa zai kuma kirana da wani layin. Tun ina daurewa har wata rana kira Deen ina kuka na gaya mishi Mahmoud ya dame ni, don Allah ya saka baki Tafida ya sake ni, har abuja Deen.yazo Ashe ya nimo Mahmoud ne ya mishi dan banza duka, ina wannan bai ishe Mahmoud ba sai da ya saka Tafida ya dawo dashi gidan wai da sunan jinya...............Babban al'amari ne....


500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


16


Tunda Mahmoud ya dawo gidan da jinya, na shiga wani irin takura wanda tunda nake ban tab'a ganin irinsa ba, dama gidan daki biyu kuma kowanne da bandaki a cikinsa sai ban daki a parlour haka yasa ko su tinah a ban dakin waje suke yin uzurinsu, ni kuma ina dakina shi ma Tafida haka, sannan a yan kwanakin nan ina fita taron kafin Onga haka yasa bani da lokacin da zan huta sai asbar da lahadi, wanda bakiɗaya Mahmoud zama yake a parlour har na kasa fita, idan na fita kitchen duk motsina idanunshi yana kaina, wuraren Kirsimeti, Tina ta dawo daga course din da ta tafi, tunda tazo na karanci fuskarta ganin Mahmoud bai mata. Bata nuna min ba har ta tafi.
Washi gari
Tafida yana office dinsa ta shiga Hannunta harde a kirjinta. "Aliyu Tafida!" "Yes My Love sannu da zuwa zauna." "No tambaya daya nazo maka zuwa biyu!" D'ago kai yayi ya zuba mata idanun ta sake murmushi. "Meye alakarka da gayen nan da yake gidanka?" "Abokina ne tun na yaranta!" "Babu kada blood related da shi?" "Ko daya na gaya miki tare muka taso?" "Kai muslumin kwarai ne kuwa?" Kura mata idanu yayi cikin gajiya da maganarta. "Ban fahimta ba?" Ya tambaye ta. "Addinin Musulunci ya ce ka ƙare darajar Matarka da kimarta, sannan kada ku bari waɗanda basu da related daku su zauna a cikin gidajenku, gujewa haduwar Baligi da baliga, a Suratu Nur da Suratu Nisa'i Allah ya rarrabe hukunce-hukunce akan matayenku da Yaranku da Yan uwanku mata da yan uwan Iyayenku mata da maza haka ne?" Zama tai a kujeran office din tana murmushi ganin yadda yake zaro idanu. "Sannan na ga wasu daga Islamic scholar irin Malik, Abuhanifa, Bukhari da Muslim sun kawo hadisai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, akan matayenku da abokan." "Tinah go to the point, ki daina dukar Tanti bayan ga jaki." "Last abinda na gani a wani hadisin wani mutum ya zo wurin Manzon Allah yake gaya mishi yafi kowa kishi." "Tina na gaji gaya min me fitar da ni a musulunci? Da kike tambaya ta anya ni Muslim ne?"
"Wancan gayen da ka bari a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login