Showing 222001 words to 225000 words out of 241571 words
Chapter 75 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
nasan halinsa
-- A wata uku da rasuwar Hajiya su Maryam suka gane wani bangaren da Hajiya ta ta rufe musu, domin dai abincin da zasu ci sai da ya gagare, da gatansu a garin Maiduguri amma abincin da zasu ci ya gagare su, sannan wani babban tashin hankalin shima Abubakar ɗin garin son zuciya sun tabka wani rashin mutunci inda suka kwashi kudin da zasu yi rubda ciki akai, kawai sai gashi an kama su kuma aka sallame shi, Deen ne ya tsaya akan case din domin Tafida da Abba sun ce babu ruwansu, Umar da ya rike Allah cikin lamarinsa sai gashi yana.ta samun nutsuwa da nasara akan aikinsa, yayinda tafida ya kara mishi wani hanya ya tafi Japan akan kasuwancin karo, Tafida ya zuba musu idanun ya kuma rungumi abin da yake nashi.
Yau muna zaune a parlourn, Asie ta shigo tana kallona. "Don Allah dubi yadda kika koma? Kamar wata mage tashi akan cinyar Yayana na kwantar da kaina." "Asie kyaleta don Allah cikin yana juya mata ne!" Zama tayi kusa da shi, tana tambayar shi. "Haihuwa ce? Na shirya kaya mu tafi asibitin? Yaushe ne EDD dinki?" "Barta haka ta huta mana!" Shiru tayi sai kuma ta mike tayi gaba kamae zata fita sai ta dawo ta ce mishi.."Ta fada nakuda ne?" Daga shi har ita suka kara cusa min takaici na ce mata. "Zaki saka kiraren kafafunki, ki bar min parlourn ko sai kora ki da pillow!" Na fada ina kallonta. "Allah ya baki hakuri!" Ta zauna kamar zata yi kuka, "ina ma da ni ce." Ta fada tana hararata. "Sai kin fi kowa raki." Tura baki tayi tana hararan Tafida. "Ina kai ne ka k'i min ciki ina da nima ina ta tutturawa." Bashi ba har ni sai da muka fashe da dariya, domin wallahi Asie mahaukaciya. "Tow kai me yasa ba zaka mata ciki ba, gashi nan tana tafiya bata tutturawa." "Bana son shiga wannan maganar" ya kafe ta da idanu. "Tow me na kallona!" "Ashe kin gane ina kallonki!" "Tow me kake son nace!" "Addu'a nake miki Allah ya baki haihuwar!" "Amin amma kasan ba zan iya haihuwa ba ai, na fada ne kawai don raha!" "Na sani nima bance ki fadi kome ba, Allah ya baki lafiya sai Ummu ta kara miki da new Baby." Murmushi tayi tana faɗin. "Da zan yi nisan kwana!" "Tashi ki tafi ki cigaba da bawa su Mufida labarin yadda zaki mutu kafin lokacin yayi!" "Aunty Baby ki ce ya daina korata." "Tow kema ki daina maganar nan mana!" "Ya Aliyu ka ce ta daina bin bayanka!" Dariya abin ya bani kamar wata yarinya kowa ya mata magana idan bai mata ba zata kawo karanshi. Haka muka cigaba da hiran kiranshi aka yi a waya ya dauka, fuskarshi ce ta sauya ya kallemu. "Duk wanda ya sake suka shigo min gidana, sai ya rasa aikinsa na rufe shi." Daga can aka ce Yes Sir! Kallonshi nayi, kamar zan yi magana sai na fasa ko jiya mun yi maganar da Fanna tace sai kiranta Maryam take tana cewa ta dibo mata abinci, basu da abinda zasu a cikin wata uku kawai sun sayar da kayansu da gadon da Hajiya ta bar musu. Shiru Asiyah tayi ganin yadda ya fusata, tsoro ya sata dawowa gefena, kaina a cinyarsa. Sai tab'a ni take ina ji naki kulata. "Hakkinsu ne ka basu abinda kake da shi!" "Inji waye?" "In Allah da Manzonsa!" Na fada a zafaffe, zuba min idanun yayi yana mamakin yadda na fusata. "Ba zan bada ba!" "Zaka bada fa, don ni tun jiya na hada musu kayan abinci, a samu Kwamishinan jin kai da walwala ya basu ka tambayi Deen na gaya mishi saura a tura musu ne!" "Me yasa? Tow banyi niyya ba!" "Ai ban basu da niyyarka ba, na basu da niyyar Allah ta bawa Asiyah lafiya ne. Sai kuma da niyyar na sauka lafiya!" Sake baki yayi yana kallona, abin mamaki ya bashi yadda na tsaya ina ta fada sai abin ya bashi haushi ya bar mana parlourn yana mita, kallona tayi tana me dawowa gabana ta ce min.." Yayi fushi fa!" Dariya nayi na ce mata. "Zai huce ma!" Tayi shiru kafin ta sake matsowa ta ce min. "Me yasa kika yi haka kin san ranshi zai b'aci!" "Saboda wasiyyar Hajiya ce!" Gyada kai tayi tana faɗin. "Gaskiya ne abin a duba ne!" Wani lokacin kamar me wayo dai tayi abin sai ya dame ta, ashe fitan shi kiran Deen yayi cikin masifa da tijara yayi ta bala'i akan me zai munafunce shi! Dariya Deen yayi ya ce mishi. "Ka godewa Allah da ka samu irin Ummu wife material, idan ka fahimci kanka ba zaka na ihu akan abinda Ummu tayi ba, katse wayar!" Ya kashe yana shiru.
A bangarensu Maryam an kawo kayan abincin, amma Rukayya ta kwashe rabi tayi gidan Dillaliya da shi, domin dai ta saba da kashe kudi da na sata da nata, kuma kafin tafida ya cire subsidy din da yake basu, ba karamin wasa da kudi take ba, haka yasa ta saba da kashe kudi, kuma ko kafin Zaman shi gwamna Tafida ya bauta musu. Bayan sun bar gidan Tafidan suka dawo nan tsakaninsu da Abubakar abin karya wane! Idan aka basu ba ankara basu sai kuma gobe, a da can abincin yana nan jibge sai yadda ya musu, a lokacin su dafa su bawa Hajiya ma tashin hankali ne, musamman ita Maryam kome Fanna take yi, kowa yasan yadda ciwon sugar yake da baya son kome, amma haka zata shiga kitchen ta dafa abinda ranta yake so ta zuba wa Hajiya, idan Tafida yazi ya gani zai magana Hajiya rike shi take tana girgiza kai ta ce mishi. "Uwa tana haifar yara goma ta kula da su, amma a cikin goman nan Allah yana iya cire daya da ba zata ba ya kyautata mata sauran taran tana kulawa dasu saboda dayan nan da ta tallafeta." Sai ya rasa yadda zai yi, yasa zuwa ya samu anyi abincin da ya dace a zuba ganye haka zata ki zubawa, idan Fanna tayi magana ta fara masifa tace tafita son Uwarta ne? Haka zata yi ta masifa tana zagin Fanna. Ita kan bata magana sai dai tayi shiru. Yau gashi an wayi gari abincin da zasu ci ya fi karfinsu, kamar su yi sata gara ma Rukayya tana fita yawonta, taci abinci. Ita kuma Maryam bata fita sai kunci da yake damunta. Ranar da ta samu Abubakar a gida ya rufe idanun yayi mata rashin mutuncin akan bai sakata kashe aurenta ba, shi ba Tafida ba ne da zai na musu barin kudi, shima yanzu nima yake. Ya kuma gaya mata har wurin Abba ya je ya saka baki a dawo da shi aikinsa yayi mishi koran kare, amma zai sami Hanyar da zai koma bakin aikinsa, sai yayiwa Tafida sanadin da ba zai kara sha'awar siyasa ba. Dake mugunta da hassada ya ginu a ransu, haka suke ta kullawa. Amma Allah baya basu nasara, ba don kome ba, Tafida ya samu albarkan Uwarshi, shi ne bai samu gatan da suka samu, amma shi ya dace da rabuwa da uwa lafiya, Hajiya har ta mutu tana jin zafin rashin zuwan Abubakar ya duba ta ko lokacin da suka bar kasar ita take kiranshi ta tambaye shi ya suke, wai shi ya kullaci Hajiya akan me zata zauna a wurin Tafida saboda don ya zama gwamna, wannan bai isa ba haka tana jinyar nan basu tab'a kiranta ba, ita din dai zata bisu har gara Umar kullum zai kira, su gaisa shi yasa tana rasuwa kamar wnada aka gaya mishi ya kira Tafida yana tambayar shi. Ina Hajiya yana jin kamar wani abu ya same ta, ya gaya mishi ai ta rasu, kuka riris yayi. Sauran duk sun ji mutuwar amma bai wani dame su ba, domin suna ganin kamar don basu da abin duniya Hajiya ta tare a jikin Tafida idan ta tafi sai tafida ya bita da abin duniyar, yadda Maryam take fada kenan, ta fifita Aliyu sai su bita da abin duniyar ita ba don Allah ya ce yiwa iyaye addu'a ba, wallahi da ba zata yiwa Hajiya ba domin kiri-kiri ta banzatar da rayuwarsu ta rungume Sabira da Tafida. Abin yana masifar bata mata rai ai suma Yaranta ne sai dai bata san darajar da Allah yiwa wanda zai rungume uwa a lokacin da take gab da komawa ga Mahaliccinta ba, bata san falalar da Allah yayiwa wanda ya kyautatawa wanda ya rabu da uwarsa lafiya ba, ko nace basu sani ba basu sani ba suna da yawo da bulayi amma tabbas asara da tab'ewa ta tabbata akan wanda ya wofatar da mahaifiyarshi, boni ya tabbata ga wanda yayi wasa da iyayenshi, zai kasance mara daraja da albarka da sun san yadda tafida ta rabu da hajiya lafiya da sun ta kwad'a kansu da kasa suna kuka. Amma ina idanunsu ya rufe da kishi da hassada gani suke kamar zasu kashe kome basu domin ganin bayan Tafida.
--
Lokacin da ta dawo domin Fanna ta kirata ta gaya mata an kawo kayan abincin, tasan halin Rukayya duk da hankalinta ya tashe yake amma tasan idan ta kara jinkiri Rukayya zata iya salwatar da abincin haka yasa akan lokaci ta isa sai dai ta makara domin kuwa Rukayya ta kwashe kashi saba'in cikin dari na abincin ta sayar, sannan ita kanta bata san inda ta kai kudin ba, domin ta dawo gida da kudi. Bata san cewa Dillaliyar da ta kaiwa abincin ta saka danta yana sane ya biyota ya kwashe kudin, sai nima take tana fadin. "Wallahi kudin nan ta bani har dubu dari da goma amma kamar tsafi ya zube!" Kuma ai dama a kudin aka bata ba, rufa ido ne aka mata sannan takardun kudin da aka bata yaron ya biyota ya sace bata sani ba, wannan abin ya ƙara fusata Maryam ta fita cikin fushi ta dauko katako ta shiga dukan Rukayya kamar zata kashe ta, abu goma da ashirin ya same ta domin Ubansu Naziha ya kirata yana ta fada da zaginta yau kwana uku kenan an nemi Naziha an rasa wannan tashin hankalin da me yayi.kama haka suke ta yawon niman inda take babu labarinta, dab zata dawo ne aka kira su wai ga naziha an kaita asibiti, daga hotel din da aka kaita, abin babu dadin ji, domin kuwa yarinya karama ta hadu da iftula'in rayuwa, na farko an bata kwayar da fitar da ita hayacinta, haka bai isa ba sai da suka dauki hotonta tsirara suka bari a wayarta tare da barazanar idan wani abu ya faru sai sun fitar da videon, duk da mata ne dukkansu amma asibitin sun tabbatar da an tab'a jikinta, domin gabanta kamar an saka reza an yanyankata don kuwa ta hadu da yan iskan mata ne, suka mata rashin mutunci, kuma ba kome ba ne ja janyo haka sai yadda Uban ya watsar da su,babu abincin babu kulawa tunda uwar gidan gifan dake itama sakarya ce. Shima Uban ai matar da ya aura yar iska ce domin sanadinta Yarinyar da babu ruwanta ta hadu da yan iskan kawayenta, suka ja ta zuwa hotel din da cewa zasu bata kuɗi kawai abu zasu yi da ita, wannan tashin hankalin Maryam ta gani ya kara fusatatta, yasa ta rufe Rukayya da duka kamar jaka. Ai kuwa ihun Rukayya ya janyo makota aka zo aka kwace ta a hannun Maryam taci bugu, ta shige daki ta rufe kanta, tana faɗin.."tabbas Ummu ce, wallahi ba zan yarda ba, yadda aka lalata min Yarinyata sai lalata miki naki yar wallahi baki isa na Ummu kece kika yiwa Naziha asiri!" Haka take ta fada tana kuka domin tayi imanin cewa Ummu ce zata mata haka, kaf duniya bata da abokiyar gaba kamar Ummu. Don haka sai ta dauki mataki akan Ummu domin Ummu ce zata mata haka.
Rukayya fa sai da Abubakar ya kira Umar aka kaita asibiti domin ta mata jahilin dukar da ko motsi bata yi, sai da ta sha ruwa na tsawon kwana uku, a lokacin labarin ya isa kunnen Tafida ko ta kansu bai bi ba.
A can asibitin da Naziha take, har yau bata farka ba, domin kwayar tayi mata karfi......74
Hankalin Maryam yayi bala'in tashi, idan ta tuna Naziha. Haka tayita zirga-zirga akan Naziha sai da ta kwashe kwana goma kafin ta farka, duk da kakarta ce akanta itama ganin bata farka ba, Yaranta mata suka zugata ta bar asibitin da cewa ba zata yi jinyar yar kwaya ba, tana addu'a bayan ta idar da Allah Naziha ta farka. Kallon Mamanta tayi tana lumshe idanu tana son ta tuna abinda ya faru. A hankali ta tashi zaune, sai lokacin Maryam ta lura. "Naziha?" Kallon Mamanta tayi, tana lumshe idanu tana budewa. "Ya jikinki naki? Bari na kira likita." Haka ta fita can sai ga su tare da likita da nurse, aka duba ta, ya mata tambayoyi ta amsa mishi. Sannan ya kalli Maryam ya ce mata. "Alhamdulillahi, ki bata abinci ta don ta dawo hayacinta!" "Tow na gode sosai!" Godiya tayi ta mishi kamar ta kwanta a kasa, bayan ya fita ta dauki kwano tana faɗin. "Naziha muje kiyi wanka da alola!" Sauka tayi a gadon suka shiga ban daki, ta haɗa mata ruwa. "Ko na miki ne?" "A'a xan iya!" Ta fada tana tsaye tana kallon ruwan. Bata san yadda zata ce ba amma tausayin Naziha ya cika ranta, haka ta fito ta kira Baban Nazihan ta gaya mishi, ta farka ta buga kofar tace mata."bari na nimo miki abinci!" "Hm!" Ta ce mata, sannan ta fita a ban dakin kuwa kuka yarinyar ta fashe mai karfi, yunwa, duka, azaba suka kaita wannan abin. An hanata makaranta balle tana samun sauki don tasan idan ta je gidan Uncle Tafida Aunty Ummu ba zata hanata abin da zata ci ba, shima Uncle ba zai kore ta ba. Amma Kakarsu ta hana su don kada wani ya ji tausayinsu ya taimaka musu. Amma dake an shirya wannan lamarin kai tsaye aunty Dayyiba ta aike ta hotel wurin kawayenta. A hotel din. Tayi kuka sosai, kanta a sunkuye tana kallon ruwan hawaye na zuba mata. Aunty Dayyiba ce da kawayenta. Ja da baya tayi tare da durkusawa jikinta yana bala'in rawa. Dariyar da suka hadu suna yi yasa ta ji kanta ya fara juyawa kafin su kai hannun jikinta, ta zube a bandakin ta suma. Lokacin da Maryam ta dawo ta ji shiru buga kofar tayi amma shiru kara bugawa tayi, amma babu amsa kawai tana buɗe kofar ta hangota kwance. Hankalinta a tashe ta saka mata kaya, ta fito da ita ta fita, sannan ta kira likita. Suma sun y mamakin amma kasancewar kwayar bata gama barinta ba, shi ne dalilin sumanta. A hankali suka gama kome sannan suka fita, ita kan ta ga Jarabawa. Halin da take ciki babu bukatar tayi kuka, tasan Naziha yarinyar kirki ce, bata da wannan yanayin da zata lalace har haka ba. Sai dai idan asirin da Ummu tayi mata ne, matsuyaciya ita ce zata mata asirin. Zata rama ba zata tab'a barin abin ya tafi a haka ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru.
***
Ummu
Tunda Fanna ta gaya min halin da Naziha take ciki domin Maryam tana gaya mata kome, sai dai ta boye min cewa ni Maryam take zargi da nayiwa Naziha asiri, bana son ina samun matsala da Tafida akan yan uwansa ne haka yasa na share zancen amma na kira Mama na gaya mata, kamar yadda na zata matar nan balbale ni tayi da fada tana faɗin. "Ban yarda ki je ba, domin zata iya miki wani abu babu wanda zai bu bayanki!" "Amma ai jinya ce ta wuce kome, kuma ko ba kome ai abin da ya faru ya riga da ya wuce don Allah ki yi hakuri!" Yadda ta yanko min wani katon ashar yasa na rufawa kaina asiri nima dai da saka kaina Uku goro a miya. A hankali na kashe wayar, sannan na kira Fanna. "Ki kai musu abinci asibitin!" "Kin san an sallami Rukayya! " "Me ya same ta itama?" "Wai Maryam ya buge ta da katako!" "Allah kadiran a lamanya sha'u! Tow tana ina ita;" "tana gidansu!" "Yanzu sai ki kaiwa su Maryam! Don kin ga ban ji labarin ba sai jiya da kike gaya min, na zata Tafida ya gaya miki!" "Ba zai gaya min ba domin zai ce na cika shiga abinda bai dame su ba!" Shigowar Asiyah yasa muka yi shiru, kamar wacce Tafida ya sakata zaman yar lekan asirinmu duk abinda ya tambaye ta sai ta faɗa, wani lokaci kamar na mangareta. "Gulmar wa kuke?" "Bamu kira sunanki ba;" inji Fanna, "tow ai kun huta!" Ta fada tana zama a gefena, muka cigaba da wani hiran, Fanna ta barmu ta wuce ta dauki abincin ta fita. "Ina zata?" "Gidan Abba!" Daga haka nayi shiru domin ta fini kwakwa.
Bayan Magariba muna cin abincin da shi, sai kallonshi nake har ya tsargu. "Ummu ci abinci mana!" "Na koshi ne!" "Tow me kike so?" "Asibiti zamu je duba Naziha." A harzuke ya d'ago kai yana kallona. "Fatan Hajiya ce, ni kuma ba zan gushe ba sai na iya yina!" Na fada ina cin abincin. "Au dama shine kika saka Fanna ta kai abincin?" D'ago kai nayi na harari Asiyah. "Kiyi hakuri tambayana yayi!" "Sam baki da wayo!" "Kiyi hakuri!" Haka na cigaba da cin abincin. "Babu inda zan je idan zaku Bismillah." "Hmm zaka je wallahi!" Na fada ina kallon cikin idanunshi. "Ummu!" "Meye matsalarka da yan uwanka? Me yasa ta kowani fuska ba zaka fahimci yadda kake kara nisanta ni da kwanciyar hankali ba? Kai kasan kuskuren da kake aikatawa kuwa? Idan baku yafiya da afwa gaya min taya duniyar zata zauna lafiya ce maka aka yi wayonka ne ya baka damar zama cikin amincin Allah? Idan kana son nisan kwana da kyakkyawan karshe ka rike zumuncin kada ka ga don ina tare da