Showing 204001 words to 207000 words out of 241571 words
Chapter 69 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
tsorace, Oga Hakim da ta gani bata san lokacin da ta zube a kasa ba, tana me faɗin. "Ka rufa min asiri nayi laifi ka!" "Ni laifinki bai bata min rai ba kamar yadda Mijinki yayi ta soka min zagi yana cin zarafina. Ke kin san waye ni me yasa kika tab'a min kayana? Kin san akan wannan kudin zan iya kashe kowa me yasa kika tab'a tab'a min kayana?" "Kayi hakuri Oga Hakim wallahi son zuciya ce!" "Na yarda son zuciya ce amma ni ban san da haka ba, je ki zan duba abin da ya dace!" Haka ta mike kamar tayi kuka, amma bai kulata ba. "Hakim Yarinyar nan tayi danasani!" "Ni ba ita bace matsalar Mijinta zan koyawa hankali daga kaina ya daina zagin kowa yadda ya so!" "Gaskiya ban ji dadin abin da yayi ba, amma yarinyar ta yi kuskure tace zata dawo da kome!" "Bana yafe cin mutuncin da hakkina da ace na wani ne bai zai dame ni ba, duk inda aka shiga aka fita sai na hukuntasu itama dalilin tab'a min kayana." MD zai kara magana ya d'aga mishi hannu. "Ya isa haka! Idan dai ba so kake na zargi wani abu ba!" "A'a Hakim wallahi ba haka ba ne!" Daga haka yayi shiru. Shima ya juya tare da barin office din.
**
Maryam
Yayi ƙoƙarin kyautatawa Maryam amma gani take kamar baya son bata kudade, in fact su gani suke tunda ya zama gwamna ya kamata ace yana musu wadaka da kudi, haka yasa ta nime Abubakar ta kai mishi kukan abinda yake faruwa. Murmushi yayi yana faɗin. "Kina tsammanin ke daya kike cike da haushin haka? Nima nan ina jin zafin haka, balle ke don haka ki daina b'ata rai akan abin da baki da yadda zaki yi!" Zata bude bakinta wayarta tayi kara rukayya ce. "Ruky ina kike?" "Ba ita ba ce, yar uwanki tana hannun HQ na yan sanda idan kina son sanin me tayi muna jiranki!"
"Innalillahi wainnalihir rajou! Tana ina yanzu?" "Na gaya miki tana Headquarter na Police!" Mikewa tayi tana faɗin. "Gamu nan zuwa!" Kallon Abubakar tayi tana faɗin. "Rukayya ce tana hannun yan sanda dai? Eh baka ji bane;" ai kusan a tare suka fita da shi, kamar yadda ya gaya mata tana Headquarter haka suka same ta, tayi wani laushi. Fashewa da matsanancin kuka tayi, tana faɗin. "Na gaya musu ni yayar gwamna ce suka ce min karya nake, wallahi na gaya musu amma suka ki!" Kallon Abubakar Maryam tayi ta ce mishi. "Ka kira dan iska!" Ko minti ɗaya bai yi ba, ya dauka suka gaisa da juna kafin ya gaya mishi halin da suke ciki, kashe wayar yayi can sai ga Commissioner of police, yana zuwa ya mikawa Abubakar hannu suka shige cikin office dinsa. Magana yayi aka kawo file dinta. "Alhaji Abubakar kayi hakuri, babu wanda ya yarda cewa yar uwar Yallabai ce idan ba haka ba ai ba me riketa. Sannan maganar gaskiya laifi tai na sata, ana ta nimanta amma bata yarda ta bayyana kanta ba, sai shekaranjiya aka same ta, gata na nan mun tambaye ta ina ta kai abin da ta ɗauka amma taki magana balle har a san yadda za ayi." Kallon takaici Maryam tayi mata tana faɗin. "Ke dai kin yi asara, me kika dauka kuma? Bayan kayan auren da kika diba bai miki ba, me kika kara diba?" "Wallahi ban debi kome ba." Marinta Abubakar yayi yana faɗin. "Don Ubanki zaki fada ko sai mun barki nan?" "Yana bayan gidanmu, na hak'a rami na saka!" Takaici ya rufesu bakiɗaya. "A gaskiya ba don mai girma Gwamna ne ya kira ba, da sai mun kaita kotu domin ta bawa hukuma wahala, amma ta kiyaye gaba!" Haka ya umarci yan sanda suka tafi har bayan gidanta aka hak'a ramin sai ga kuɗin da sun tashi kan miliyan goma, da sarka da yan kunnen gwal. A ina ta samo su, shine Tambayar da Abubakar ya mata. "Biki naje shine na kwana a can wallahi ba zan kara ba!" "Rukayya satarki ta fara yawa , da kika yiwa Ummu cewa muka yi karya ce. Ashe lokaci na zuwa da zaki dauko wanda ya ci Uban wanda kika yi" shiru tayi tana kuka, ita Maryam takaici ya hanata magana, haka suka amshi belinta sannan suka fito. "Ina zamu kaita?" "Nasiru ya ce ko na fito kada na koma gidansa, ya sake ni ga shaidar sakin nan!" Zare idanu suka yi, "Akan me?" "Saboda yan sanda sun kama shi kafin suka sake shi aka kama ni, bana tunanin ma zai yarda na kusanci Yarana." "Amma dai kin yi asara, wallahi kin b'ata wayonki!" Daga haka suka wuce gidan Tafida, sun samu ya dawo, yana ɓangaren Asiyah, wacce ya kawo mata wata babbar mace kullum da yamma tana zuwa koya mata karatu. Wucewa bangaren Hajiya suka yi Abubakar ya wuce abinsa domin yana jin babu dad'i akan samun Tafida, yayi alƙawarin sai ya saka Tafida ya rasa kome, su dawo kamar yadda suke da. Ya zama matsiyaci irinsu, sunan da ake kiranshi yayi vanishing a manta da an tab'a wani mai sunanshi ma. Murmushi yayi yana kara tuna yadda kome zai tafi idan yayi nasara.
Sai da yaci abincin da ya samu sun girka da matar, yadda ya gansu ba laifi tana samun nutsuwa duk da ko wancan satin, sai da yayi ƙoƙarin ganin likitan ƙwaƙwalwa, akan shaye-shayen da take don sau biyu yana samunta a zube a banɗaki haka yasa ya kira Falmata ta hada shi da wani likitan yazo ya dubata, sannan suka sake zuwa asibitin aka mata gwaji. Kallonta yayi yarinyar bakiɗaya rayuwarta a nakashe yake, kama daga tarbiyyarta zuwa lafiyarta ta samu na kasu sosai, domin a binciken da aka yi akanta akwai wani kari da ya fito mata, saboda shaye-shayen da tayi ta yi a baya, ya haifar mata da tsirowan wannan karin a kanta, shi yasa ta fadi har sau biyu sakamakon girmanshi sannan jini baya samun damar wucewa. Mikewa matar da take koya mata abubuwa tayi tana faɗin. "Hajiya zan tafi!" "Allah Mama zaku tafi!" Ta fada tana kallonta. "Eh xan tafi kin san ana zuwa karatu da yamma!" "Shi kenan!" Ta mike tare da nufar dakinta, ta dauko kudi ta samu Tafida yana mata tambayoyi tana amsawa. Kafin ta raka mata, "ke ina Tafida!" Abin da tsohuwar yar kwaya kallon Maryam tayi, kafin ta ce mata. "Sandar kiwon da kika bani ya b'ata!" "Ke!" Ta bangaje ta, jiri ne ya kwashi Asiyah ta tafi zata fadi, Matar da take koya mata karatu ta riketa. "Yau sau biyu kika kokarin fadi baki da lafiya ne!" Kallon Maryam tayi tana faɗin. "Bani da lokacinki Maryam! Muje Mama!" Ta fada tana share jinin da ya zubo a hancinta. "Jini ne fa a hancinki!" Ta fada a rude!, "ki cewa Matori ya kai ki gida!" Ta juya a hankali, Maryam zata kara kai mata hannu, Security da take tsaron lafiyarta ta rike hannun Maryam. "Madam ki kiyayye kanki!" Ta fada tana shiga tsakaninsu. "Idan naki fa!" "Helin kyaleta!" Inji Asiyah tana rike kanta da yake mata bala'in ciwo. Ɗaya security din ce ta zo ta rike Asiyah har parlournta, kallonsu Tafida yayi yana jiran karin bayani. "Hajiya Maryam ce ta" "Jeki helin!" Ta fada tana kwantar da kanta a kafadarshi. "Ya Aliyu! Kayi kokarin ka dawo da Aunty Baby! Kana sonta, kana buƙatarta, don Allah ka dawo da ita." Ta fada tana gyara kwantar da kanta. "Ummu ba zata dawo ba, domin tayi fushi sosai." "Zata dawo!" Janyo kanta yayi zuwa cinyanshi yana wasa da gashinta. A hankali tayi yunkurin mikewa, ya d'aga ta. Tissue paper ya dauko ya saka mata a hancinta. "Ina ji a jikina kamar zan tafi ne, gashi ban gyara alakata da Allah ba, idan na mutu a wannan yanayin Allah ba zai yafe min ba ko?" Wani abu yaji ya tsaya mishi a rai, murmushi yayi yana faɗin. "Zamu je ganin Hajiya ina ganin kema zaki ga likita!" Shafa fuskarshi take a hankali, tana mishi wani abu, a yau sai yake jin shi cikakken d'a namiji, domin kome na shi ya taso mishi kamar da lokacin Ummu. Sai dai yadda yake jin kyamarta yasa shi maza ya rike hannunta. "Kyamata kake ji ko?" Ta fada tana jin hawaye na zuba mata. "Ban ga laifinka ba." Hade bakinshi yayi da nata, duk da yadda yake jin zuciyarshi. Asalin kyamarta yake ji, kamar zai yi amai. Janye jikinshi yayi yana sauke numfashi. Ita kuwa tayi lumo a kujeran. _Tunda ka gano gaskiya akanta me yasa lallai sai ka zauna da ita? Ka sake ta kada ka kara aikata irin kuskuren da kayi a baya, zargi yana lalata aure abin da yasa Ummu ba zata dawo gare ka ba kenan, don kome gaskiyarta wata rana sai ka zarge ta_ kalaman Deen kenan da yake yawo kanshi. Lumshe idanunshi yayi kafin ya cire kyamar ya rungume ta. Saboda yadda take kuka sosai. Ba karamin tab'a mishi rai yake ba, yana buƙatar mace kuma macen ma Ummu Hadiyya, amma taki ta fahimci yadda yake bibiyarta. A hankali kome ya warware tare da haifar da wani irin nishadi a yanayin da bai tab'a kawowa zai tsinci kanshi a ciki ba, yanayin ya tafi da lissafinsa yayinda ya warware wasu lissafin, barci me nauyi ne ya dauke su. Bude, duk da babu Ummu a rayuwarshi yanzu sai dai ya yarda kusantar barna da yayi a baya,.Allah ya hukuntashi da Sa'adiyya da Asiya, sai dai the worst part shine Asiyah tana bukatar kulawar at any cost, kiran sallah Magariba yasa shi bude idanun tana kwance a jikinshi, hancinta yana bleeding, amma a haka take barci ko ya ta sauke numfashi sai jinin ya zubo. "Asiee!" Ya fada a hankali, bude idanunta tayi tana kallonshi. "Na zata Ummu zaka kira?" Ta fada tana share hancinta da bayan hannunta. "Kana bukatar Ummu." "Baki ga kina zubda jini ba ne?" Dariya tayi tana faɗin. "Ba wani abu bane fa, abin da nayi ne na ke girba kana tsammanin Allah zai bar wanda ya zalunci wani ne? Kasan me? Kai na musamman ne, i'm sorry to say amma kai a cikin maza na musamman ne. Kasan me? Idan aka wayi gari bana raye ka rike Ummu da daraja, idan har ƙaddara zata kara hadaku, ka sota sama da yadda kake sonta yanzu. Ka tsaya mata yadda ba zata yi kuka ba. Ummu Hadiyya mutuniyar kirki ce, tana kuma da kirki. Nasan cewa wani abu ne me muhimmanci ya faru a tsakaninku ka zama Adali a cikin lamarinta, Yan uwanka kuwa ba san me zance ba amma tabbas ka san yadda zaka yi da su, domin ko ka dawo da Ummu." D'ago kanta yayi yana faɗin. "Ina son Ummu! Amma na cutar da Ummu sosai, a yanxu na hakura da Ummu ba wai don bana sonta ba, kawai don ina jin kunyar sake niman Ummu nake. Da ina da uzuri tabbas da Ummu bata bar rayuwata ba, na san nayi laifi amma Ummu ta tafi kenan sai dai na bada labarin na tab'a auren Ummu......
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7666
Girgiza kai tayi tana faɗin. "A'a haka ba zai yiwu ba. Lokacin sallah ya gota mana." Kasa magana yayi ya rungumi kanta, da yake kirjinshi, yana faɗin. "Na gode sosai!" Ya fada yana mikewa da ita, suka wuce dakinta ban dakin suka nufa suka yi wanka, sannan suka fito ya saka kayanshi da kanshi ya jasu sallah, bayan sun idar da sallah ta kawo littafanta, yana jin ana buga Kofar entry dinta amma ya dauke hankalinta da karatun Alqur'ani, yadda take tana tuntube, kuma ta nace. "Aliyu!!" Maryam ta shiga kwala mishi kira, Allah ya gani Maryam tana cikin ƙaddaranshi ta addabe shi ta hana shi sakat.. d'ago kai tayi tana kallonshi. "Kina jin tsoro ne?" Gyada kai tayi domin har yau bata manta dukar da Saadiya ta mata ba, Allah ya gani Asiyah tausayi take bashi, idan ya cire abin da tayiwa Ummu, amma yarinyar tana da sanyi sosai. Sauke ajiyar zuciya yayi ya shafa fuskarta. "Ki jira ni yanzu zan zo!" Ya mike ya fita, ya samu ana shan dagga da Maryam. "Ku kyaleta!" Ya fada yana me ratsa tsakanin jami'an tsaron. Ya kura mata idanu babu wasa a fuskarshi. "Me kike bukata?" Yadda ya tsare gida yasa bakiɗaya ta gigice, ta rasa me zata ce mishi. "Amma mun dawo ya !" "Ni nace ki dawo min da ita ne? Maryam!" Ya gyara tsayuwarshi ya cigaba da cewa. "Ki saka kai ko bar min part ko nayi miki ba dad'i, ina danne zuciyata a kanku kada ku fusata ni!" Ya juya zai shiga ta ce mishi. "Amma ya kamata ka san abin da ya faru!" "Bana bukatar sai na ji, idan kika kara damuna sai na baki mamaki!" Ya wuce ciki, parlourn ya same ta, tana ta fama da karatun. Kallonshi tayi kamar zata yi kuka ta ce mishi. "Ya Aliyu! Na kasa ganewa ba." Shiru yayi ya kara maimaita mata, har sau uku sannan suka cigaba a tare. "Me zaki ci?" "Zan ci abincin dazun!" "A'a ki saka kaya da face mask, zamu tafi cin abinci ne." Ware idanu tayi tana faɗin. "Ki shirya bayan Isha zamu tafi!" "Ok !" Ta fada tana me nufar dakinta, fita yayi zuwa part dinsa ya shirya sai da yayi alola kafin ya wuce wurinta, sallah suka yi, sannan suka shirya, yana gaba tana biye dashi. Har wurin motar da ya samu an ajiye mishi. Sai da ta shiga, ta zauna sannan ya shiga ya zauna. A hankali yake jan motar. "Don Allah ka kai ni gidansu Aunty Baby!" "A'a ba zaki ba!" "Kai kace zaka min duk abin da na roke ka? Yanzu na roke ka don Allah!" Shiru yayi mata, sannan ya cigaba da tukinsa, yana kallon hanya kafin suka isa gidan cin da babu kowa an sallami kowa, a tare suka shiga manajan gidan ya karɓe su da wasu staff din gidan, aka kai su wurin cin abincin. Aka fara hidima dasu, ana ta kawo musu abinci. Kallon yadda take daukar hoton abincin a waya ba. Shi a wannan yanayin Ummu ce kawai take yawo a kanshi, domin har yau baya jin akwai macen da zai mata irin son da yakewa Ummu, Ummu wata aba ce na da bazai ina mantawa da ita ba. "Bar ɗaukar hoton nan ki ci abincin!" "Tow!" Ajiye wayar tayi tana me fara cin abincin, a hankali ta fara cin abincin, yana kallonta, har ta ci sosai kafin ta d'ago kai tana murmushi. "Ka ga yadda nake cin abincin ko? Kayi hakuri." "Ai saboda ki ci na saya miki!" "Kai fa!" "Na koshi!" Cire Hannunta tayi tana faɗin. "nima na koshi!" Ta fada tana goge yatsunta. "Ok ki huta sai mu koma!" Haka ta jingina da kujeran tana ta wasa da wayarta, lokaci zuwa lokaci tana d'ago kai tana kallonshi, shi kuwa hankalinsa yana kan wayarshi da yake turawa Deen sako. Shima turo mishi yayi yana mishi dariya. "Mu gani kana hira da budurwa ce!" Ta leka, hoton Deen ta gani akan profile dinsa. Sosa Kai tayi tana faɗin. "Sorry!" Murmushi yayi ya ce mata. "Muje!" Bata yarda ta kalle shi ba, saboda abin da tayi sai kunya ya ishe ta. Har inda motar su take suka rako su. Manajen sai godiya yake yana har suka bar gidan abincin. A hankali yake tuki yana kallon yadda take sauke numfashi, kanta ta kai jikin window tana shaƙar iska. "Zauna da kyau!" Gyada zaman tayi tana faɗin. "Wani lokacin muna son Abu amma haka muke sadaukar dashi, ba don mun so ba!" "Kiyi shiru!" Yana kallon hanya, unguwar Ummu ta nufa. Kallonshi tayi tana faɗin. "Ina zamu!" Bai bata amsa ba, har kofar gidan. "Ki shiga!" "Zata karbe ni kuwa?" Hararanta tayi yana faɗin. "Yadda kika sani zuwa sai kin wuce mun je!" Tura baki tayi tana faɗin. "Don ka samu xan gyarawa soyayyarku hanya!" Ta fada tana fita daga motar, dafe goshinsa yayi yana kallon yadda take nufar gidan. Allah yasa kada zuwanta ya haifar da wani abu mara kyau, domin yasan yanzu sai Ummu ta fishi daukar zafi.
*Ummu*
Ina kwance hira Uwani suke da Mama, ina jin su amma ban tanka musu ba kasancewar kwana garin ana zafi. Muna tsakar gida muna shan iska. "Assalamualaikum!" "Waalaikumunsalam!" Muka amsa mata, domin duhun da yake wurin, sai haske farin wuta. "Ina wuninku!" "Lafiya!" Na gano Asiyah ce, haka yasa nayi mamakin zuwanta. "Maman Mufidah tana nan kuwa?" "Me kike bukata wani asirin kika kawo ki min!" Na fada ina haska mata touching wayata, kare fuskarta tayi tana faɗin. "Don Allah ki saurare ni!" "Malama bar mana gida bana son ganinki, kafin a sake min wani asirin." "Aunty Baby kiyi hakuri ki saurare ta!" Inji Kulsum, "akan me zan saurare ta? Gaya min me ye laifina da zata min asiri?" "Amma tace ki saurare ta mana!" "Mama matar Tafida ce!" "Na sani wani abu ne?" Yadda tayi maganar sai naji na kasa mata musu. Zama tayi a kujeran tsuguno. "Babu wanda baya kuskuren, kullum akan kuskure muke kuma muna masu kaskantar da kai da rokon Allah ya yafe mana, Aunty Baby ke mace kuwa? Taya zaki zubar da kayan yakin da kika fara? Waye ya zai gyara miku sauran aikin da kika fara? Na sani da ciwo amma kuma kada ki juya mishi baya yana bukatar ki a rayuwarsa, yayi kuskure kuma Allah ya yafe mana, kiyi hakuri Aunty Baby. Tafida yayi kuskure, amma mu mu fishi laifi domin bamu gane irin gwagwarmayar da muka yi ba burin mu kawai mushi cikin gidanki!" Duk sai naji raina ya ƙara b'aci. "Kice har ya gaya miki abin da ya faru? Tow maza ki fita min kafin nayi miki rashin mutunci!" Yadda na fusata yasa Mama rike hannuna. "Baki da hankali ne? Ko an gaya miki." Sallamar Aliyu