Showing 123001 words to 126000 words out of 241571 words
Chapter 42 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
na taimaka mishi yayi wanka, yana fitowa ana shan ruwa, shiga dakin nayi da ruwan dumi da dabino na mika mishi. "Barka da shan ruwa!" "Yawwa Barka dai Ubangiji ya amshi ibadarmu!" "Amin Ya Allah!" Yana daure da towel ya sha ruwa na ciro mishi kayansa, ya saka su sannan ya riko hannuna muka sha ruwa a nutse kafin ya jamu sallah, muna idarwa muka ci abinci kadan sannan ya ja laptop dinsa ya fara aiki har aka yi isha, nan ma ya jamu sallah yana fadin. "Ina da aiki sosai idan kina jin barci ki je ki kwanta zan zo!" "Zan tayaka hira!" Haka muka yi ta hira muka kallon tafsiran malamai, can na kwashi Yaran na basu madara sannan nayi musu wanka na kwantarsu na tofe su da addu'a, na shiga nayi wanka wurin karfe sha daya, kayan barci na saka na shirya jikina sosai sannan na fita parlour na zauna, duk da hankalinsa yana kan aiki amma sai da ya d'ago a gurguje ya zuba min idanun, "Kin iya kashe mutum da shagali!" Ya kashe laptop din, ya bude min hannu, da sauri na nufe shi, ya rungume ni yana faɗin. "Zan saka ki kuka muje daki don na ga nan!" Rufe mishi baki nayi, "ai idan wannan kukan ne yanzu na fara. " Ina mishi wani irin kallo, wanda ban san yaushe na koya ba, Ya Salam Tafida ya tashi kaina a parlour ya goge min duk wani abin da nake ji, ya kuma sani jin lallai a duniyar nan bayan shi babu wani namiji. Haka yasa da kome ya lafa, ya min wayo ya kai ni daki, sannan muka yi wanka sai da ya ga mun kwanta barci yayi gaba da ni, ya dawo ya cigaba da aikinsa. Project ne mai muhimmanci, idan ya bari bai san yaushe zai gama ba, haka yasa shi ƙara mai da hankali, a bangaren Ummu yasan sarai idan ba kashe mata jiki yayi ba, ba zan tab'a tafiya nayi barci ba shi yasa ya min wayo ya sakata ni barci. Da asuba shi ya tashe ni, na tashi ban daki na nufa na wanke baki da alola na amshi tea na sha, ina kallonshi. Kashe min idanun yayi yana d'aga min gira. "ko muje second round ne?" "Hmm" na ce mishi, kallon agogon yayi karfe hudu da minti goma, jin hmm kawai da yayi ba sai ga Malam Ali ya sake turmushe ni a karo na biyu ba, bargon da ya fito da shi domin lullubuwa yana aiki, ya rufa mana, yana zaune a bayana. Yana shan tea din da ya kara hada mana, "Yaushe Mama zata dawo?" "Sallah da kwana hudu!" "Ya kamata na koma gida!" "Ni kuma waye zai kula da ni!" Kwantar da bayana nayi a kirjinshi ina faɗin. "Akwai saadiya!" "Idan kina son muyi fada ki daina kira min wata mace daga Hajiya sai Inna da Mufidah!" "Allah ya huci zuciyarka!" Na fada ina kurban tea. "Hmm!" Shafa mama na yayi yaji suna zubda ruwa. "Ummu don rowa hana ni sha kika fa!" " abincin yaran zan baka fisabiilillahi!" "Ni dai ki bani na sha!" "Zaka mai da ni ruwa ko?" Juyar da ni yayi ya fara sha kamar wani jinjiri. Dakyar na kwace ina jin jikina yana wani irin budewa, lasar wuyana ya fara har zuwa fuskata. "Lokaci yana tafi don Allah ka bari!" "Kiyi!" Sumbatar bakina yayi yana faɗin. "ba xan yi kome ba! Ba zan ketare iyakar Allah ba!" Ya matse ni a kirjinshi, ajiyar zuciya na sauke ina k'amkame shi, bayan an kira sallah na tsayar da cin abinci muka shiga wanka, muna fitowa nafilla muka yi sannan muka jira lokacin sallah yayi, muna sallah har rana ta fito. Kafin muka kwanta, kasancewar ranar Monday ne. Da kanshi ya tashi ya fada ban daki, ina jin motsin shi na mike na ciro mishi kayansa, na shiga haɗa mishi duk wani abu me muhimmanci kafin ya fito na hada kome, yana fitowa na taimaka mishi ya shirya sannan na amshi jakarshi nima na saka doguwar riga na kara shi har bakin motarshi, yana shiga ya d'aga min hannu. Ina shiga cikin gidan na fara aiki kafin sha daya na gama kome, sannan na kwanta. Ina barci wurin sha biyu aka yi ta buga kofar gidan. Bude idanun nayi na saka hijab na fito. Security ne. "Madam kina da baki sun ce su yan uwan His Excellency ne!" Murmushi nayi kafin nace mishi. "Tow su shigo nan da minti Talatin!" Rufe bangaren shi nayi na nufi bangarena da Yarana, sannan na gyara ko ina duk da nasan jiya mun gyara da Jalilah. Bayan minti talatin kuwa na fara jin hayaniyarsu. Ina zaune a parlourna na daura kafa daya akan ɗaya, doguwar Arabia gown ce, pink colour. Fuskata ba yabo fallasa. "Kutumar Uba! Gidan nan na ajiye ki?" Inji Sa'adiyya, murmushi nayi ina faɗin. "Ina kike so ya ajiye ni tow?" Maryam da Rukayya sun kasa magana. "Sai naci Ubanki sai kin gaya min waye ya tsaya miki!" Murmushi na sakar mata ina kallon bakin kofar. "Aliyu Muhammad Jadda Tafida ya tsaya min, ta Ikon Allah Barka da zuwa Mijina hasken rayuwata! Uban Aisha Baban Muhammad!" Cak Saadiya ta tsaya tana kallonshi jikinta yana rawa. "Abin da kika yiwa Asiyah ba a tsawatar miki ba kika zo zaki yiwa Ummu
*ASIYA!*
(Ba fa kowa ka isa ka tab'a ka kwana lafiya ba! Musamman heir din Tafida 😜🏃🏻♀️)
*Shin ko kun san kayan kamshin da kayan zobo tare da duk wani dangin kayan abincin gargajiya da Ummu take amfani yana samuwa ne ta wurin Shaharariyar me kayan kamshi na AIDA spicess! Ina mata yan yayi ina masu abinci na online kayanku ya tsinke a gindin kaba, ga Hajiya Aida special spicess tazo mana da kayan girki na gargajiya da na zama kai Jama'a wata miyar sai a makota! Na gwada sauran ku gwada ina jiranku! Za a iya samun Aida spices ta wanann number:+234 806 968 1068 Whatsp siyan na gari mai da kudi gida! Hajiya ki zama yar gayu me sauki ne amma girkin yan gayu dai da Aida spicess*....🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
Wani irin numfashi ya sauke tare da rufe kofar parlour ina zaune a kujeran har lokacin. "Munafuka kiranshi kika yi? Annamimiya!" Murmushi nayi na ce mata. "Idan kina tsammanin idan da kiranshi nayi, kafin na kashe wayar ina ga da yasa an muku ba daidai ba, amma bani da lokacin kiran shi domin ya tsaya min don nasan ko baya nan babu abinda zaki iya min." Har lokacin yana jan wayar wuta ne da aka hada kayan electric na gidan, "Me xaka yi da shi? Ai babban kuskuren da ta so aikatawa bata aikata ba, kawai ka tattarata ta bar min gidana." Na fada ina mikewa daga kujeran. "Ke jinki wata jar wuya ce? Asirin da kuka yi don mallakanshi in sha Allah sai mun warware, wawuya me dangi arna!" Juyawa nayi kamar zan tanka mata amma na kyaleta, ko don Tafida Maryam ta cancanci na kyaleta, amma kuma zagin ya min zafi. Sai nayi baya kamar zan fadi, ya tare ni yana haɗa Sa'adiyya da bango. "kada ka illatatta kyaleta don Allah!" "Maryam ke da Rukayya mu bar min gidana kafin na saka a muku koran kare!" "Wai ka ji kunya, mune zaka biya mu wahalar da muka maka kana yaro shine bari ka ci zarafinmu, Tafida mun barwa Ummu kai, amma ki sani akwai karshen ki yana nan zuwa yana nan tafe zaki ga abinda zai faru alkadarinki yana nan zai karye wata rana." Haushin ba zai iya dukar Yayunsa ba, kawai ya rufe Sa'adiyya da duka, zuwa nayi na kwantar da Yaran. Na fito suna kokarin janye shi amma yaki barin dukarta sai da na zo na rungume shi ta baya, ina kiran sunanshi da karfi. "Don Allah ka daina dukarta haka, kada ka saka min tsoronka don Allah!" Na fada da karfi ina kara k'amkame shi. Yarda wayar yayi yana me bude musu kofarshi. "Ku fitan min a gida, ko na rufe idanuna na ci zarafinku!" Hanta suka yi waje tana sume, hankalinsu a tashe domin basu zaci tafida zai iya mata kafirin duka haka ba. Juyawa yayi yana kara rungume ni. Na fashe da kuka kamar zan bar jikinshi. "ya isa babu abinda zai faru in sha Allah baki yi kama da matar da xan saka ba, da na dake ki gara na wayi gari hannuna ya rube!" Kuka nake a hankali na d'ago kai ina kallonshi. "abinda Mama take gudu kenan, ko bama gida ɗaya ba zan huta ba!" Shafa kaina yayi yana faɗin. "Zaki huta, nima nasan zaku huta!" Cikin shashekar kuka na kwantar da kaina a kirjinshi. "Ya aka yi kazo?" "Matori ya gaya min ga wasu sun zo zasu shiga, sun ce yan uwana ne su. Na kira wayarki baki d'aga ba, ashe har ya tambaye ki, shine mace maza a kawo ni na san Babu alkhairi a zuwansu." "Don Allah ka daina dukar mace haka zaka kashe ta ne?" Girgixa min kai yayi yana shafa bayana, "ba zan kashe ta ba, sai dai ta cigaba da min haka zata wahala." Har lokacin jikinsa bai daina b'ari ba, zaunar da shi nayi na daura kaina a kafadarshi, "Ina son zama dake har karshen rayuwata!" Damke hannunshi nayi cikin sanyin murya na ce. "Ina fatan daga yanzu har abada ina tare da kai!" Murmushi yayi yana faɗin. "Kiyi hakuri!" "Ya wuce kai zan bawa hakuri an d'agoka daga aikinka!" "Zan koma yanzu!" Haka ya koma bangarenshi ya sauka kaya, na raka shi ya shiga Mota suka koma office. Wunin ranar dakyar nayi shi cikin nutsuwar rai. Daga can gidan Abba ya wuce ya kai ƙara, lokacin da shida ta ga halin da yarta take ciki sai da ta fashe da kuka domin bata zaci haka daga Oga Aliyu ba, wani irin rigima aka yi ta fama da shi a cikin gidan Tafida ya rantse ba zata koma mishi gida na ya gaji da renon tinkiya. Maganar da yayi ta gayawa Shuwa yasata kuka sosai, rigimarsu taki karewa sai da aka kira Hajiya ta tsawatarwa Tafida cikin fushi ya ce mata. "Wallahi ta kara yunkurin tab'a min matata sai na yanke hannunta ku rubuta ku ajiye!" Ya juya ya bar gidan sai da ya dawo gida ya kura Deen yake bashi labarin abinda ya faru me zai yi ban da dariya Deen ya ce mishi. "Muna asibiti an kawo Sadika haihuwa!" "Kai Masha Allah, bari na gayawa Hajiya yanzu!" Ba karamin farinciki ya shiga ba, ya kira Hajiya ya gaya mata. Aiki ya koma amma bakiɗaya sai ya kasa nutsuwa. Can ya kira Ummu "babu wata matsala ko?" "Babu!" "Ummu Hadiyya!" "Na'am!" "Ki kara min hakuri kin ji!" "Akan me zan kara hakuri me kayi min? Ba kai ne matsalata ba, kuma bana fatan ka kara zame min matsala, ka fuskanci al'ummarka kada ka damu da ni, ba ni da matsala a har can!" Kashe wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya.
UMMU
Ina gama waya da shi, sai ga kiran Maryam kin dauka nayi na rufe idanuna, can ta kara kira na dauka. "Ummu ki rubuta mi ajiye sai mun raba ki da Tafida, ki saka a ranki duk abin da ya same ki, mu ne tunda kika mallake mana dan uwa kika sa ya daki matarsa da danginta suka mishi kome!" "Alhamdulillahi tunda na yar kanwar Hajiya ba ce ya daka ai da sauki, Maryam ni ba zan ce zan rama abin da kika min, in sha Allah zaki gani a ƙwaryan cin tuwonki, ai kema gidan wani kike, nima Allah xai aiko masu rama min!" Na kashe wayar, Tafida ba shine matsalata ba, yan uwansa sune damuwata. Bayan na kashe wayar sai ga kiran Mahmoud. Haka yayi ya kiran wayata naki dauka, kira yayi da bakon number na ɗauka. "Kada ki kashe min kira, baki yi mamaki yadda su Rukayya suka zo ba? Kada ki damu ni na gaya musu! Ki kashe aurenki da Tafida zan baki kome na rayuwa zan tabbatar da na nime takarar da ta fi na Tafida domin na baki duk abinda kike so?" "Jahili kazami, fasiki matsiyaci na kasar wuta, in sha Allah Ubangiji yana nan yana maka shiri na musamman, Allah sai ya kunyata ka lokacin da baka zata ba! Mahmoud matukar ina raye zan yi murna da farin cikin ganin ka a wulakance, aurena da kimata da ka so tab'a Allah sai ya kawo masu tab'a naka, Allah sai ya kunyataka Mahmoud Allah ya isa tsakanina da kai, ba zan yafe maka ba albarkan azumin bakina!" Na kashe wayar ina kuka, idan na tuna abun da Mahmoud ya min ji nake kamar na mutu da takaici, yadda Mahmoud ya ga tsiraicina, Allah ka wulakanta shi. Wuni nayi ban daura kome ba,saboda kukan da nake, yana dawowa ya ganin a birkice, ai sai yafini shiga damuwa ya tambaye ni yafi sau goma, tow na goge kome na wayar bakiɗaya na tsani wayata. "Ummu idan aka abinda su rukayya suka miki ne, zan dauki mataki na gaya miki!" "Kaina je ciwo!" "Tashi muje gidan Hajiya mu sha ruwa, na ga yau baki yi kome ba!" Ban sauya kaya ba, haka na fita shima duk abinda nake mishi yau ban yi ba domin haushinsa nake ji, ai shi ya kawo Mahmoud ya wulakanta ni. Hannunshi ya kai zai tab'a ni, ma kauce. Ciki ciki na ce mishi. "Muje don Allah!" Daga haka na wuce sai ya tsaya yana kallon hannunshi kafin ya dunkule hannun. Ya fito ko a mota kin zama kusa da shi nayi ina can gefe hanya. "Gobe zan koma gida kada ka ce min a'a!" "Ummu amma ai ba haka muka yi da ke ba!" Sharrr naji hawaye na zuba min, ban tab'a ganin wanda bai iya jure tashin hankali irin Tafida ba, yadda ya shiga damuwa sai nake jin babu dad'i. Tambaya ta yake na gaya mishi me yayi min wallahi ba zai kara ba, har muka isa gidan Hajiya Hajiya kuka nake, yana rungume da Mufidah muka shiga gidan, tunda hajiya taji karan saren tasan yazo, murmushi ne a fuskarta tana me mana barka da zuwa sai dai ganin yadda nake kuka yasa ta zuba mishi idanu. Zubewa yayi akan gwiwarshi a kasa, "Hajiya ki min tsakani da su Rukayya zasu kashe min auren da na sha azabar dawowarshi Hajiya, ji nake zuciyata tana zafi don Allah Hajiya kiyi wani abu kafin su raba ni da Ummu!" Ya fada yana juya kanshi. Hajiya zuba min idanun tayi kafin tayi murmushi tana faɗin. "Ummuna Hadiyya!" D'ago kai nayi ina kallonta, "kiyi hakuri! Kin ganshi durkushe gabanki, ban san me ya faru ba, amma nasan su rukayya ba zasu raba ki da shi ba, ban ga tsoro akan abin da kika dauka ba, amma naga damuwa akan fuskarki, idan su Rukayya ne basu kara zuwa damunki, kin ji ko?" Gyada kai nayi kaina a kasa na ce mishi. "Ka tashi !" Kallona yayi kafin ya kara matsowa. "Kin hakura ba zaki tafi ba!" A sanyayye na kalle shi kafin na ce mishi. "Babu inda xan je sai ana jibi Mama zata dawo!" Na tashi da sauri na shige dakin Hajiya, murmushi tayi tana karban takwaranta. Zai yi magana ta dakata da shi. "Ka godewa Allah ta san darajar Manya, idan wata ce babu ruwanta da haka nake gaya maka ka samu mace na nunawa sa'a. Ka riketa gam domin ka sake ta subbce maka sai kayi jinyar da tafi ta dawo!"
***
*Asiyah*
Tafiya yankin azaba, shine Hajiya Turai da yarta da kawarta suka yi har wannan lokacin basu isa cikin dajin gyambu ba, sai wurin karfe biyu na rana suka isa dajin wanda tun kafin su isa suke hango alamar bokanci, wani takadaririn shaidani ne zaune wani fili fallau, a saman iska ya tankwashe kafarshi, gefenshi bukka ce a wurin gabanshi kayan tsafi ne gasu nan kamar hauka. "Aliyu Muhammad Jadda Tafida, kika kawo a saka shi ya auri yarki Asiyah, akwai haske bayan kin rasa wanda zai miki aikin nan yau gashi kin zo mana, aiki zai yi nasara amma ba yanzu ba ba yau ba domin ana azumi duk wasu shaidannun da zasu mana aiki suna daure, idan aka gama azumi yau saura kwana goma sha biyu ki dawo da ita. Nayi aikin da zai bata shi amma ku sani aikin nan ba zai kammala ba sai da amincewar matarshi! Ummu Hadiyya." "Matarshi kuwa?" "Ba a tambayata maza juya ku koma inda kuka fito." Haka suka juya hankalinsu a tashe, "kada ku damu tafiyar zata gajarce muku!" Daga haka suka cigaba da tafiya ko minti goma ba su ba, sai gasu a bakin hanyar da suka shiga dajin. Ajiyar zuciya suka sauke sannan suka koma motarsu.
***
Ummu
Har bayan shan ruwa ajiyar zuciya nake saukewa, duk sai ya rasa sukuninsa yayi ta bina da idanu har aka yi bude baki, massalaci ya tafi a can suka hadu da Abubakar, bayan sun su sallah, suka tawo gidan Hajiya tare, anan suka sha ruwa suna hira sama-sama, Hajiya take gaya masa abin da su Maryam suka yi. "Wai ni kam me kake yi da yarinyar nan ne tunda ya tabbatar baka bukatarta?" " A lokacin da narasa nono Shuwa ce ya bani kunu, a lokacin da narasa Uwata ita ce ta ɗauke ni duk da na taso da jin zafin Hajiya, haka bai hana ni ganin girman Hindu ba, tayi min abin da ba kowa yayi min ba, matsalar da aka samu ni ba zata juya ni ba ne, sannan ba zata saka ni nayi abinda ban yi niyya ba. Hindu so take ta kowani kusurwa ta mallake ni, amma Allah ya tsare ni ba tare da na yi kome ba, yarinyarta kuwa naso na zauna da ita watsar da kanta da tayi yasa na jingine ta. A da can baya idanuna