Showing 12001 words to 15000 words out of 241571 words

Chapter 5 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14687

takwas, kafin Allah ya kawo shi kin ga na haife su ina da shekaru talatin, gara a kai mishi Yaransa." Duk sai jikinsu yayi sanyi. "Amma me yasa tuntuni baki bukaci haka ba?" "Yo ina nake da yancin yin haka yanxu da nake da Yanci ba gashi nayi ba." Kiran wayar Aunty Rukayya akayi ta kalle Aunty Maryam ta ce . "Kin ganshi nan!" "Sai ki dauka ai!" "Daukar wayar tayi tana faɗin. "Ayya Tafida kayi hakuri mana!" "Ina karamar mara kunyar?" Mika min wayar tayi na saka ta a handsfree. "Ina jinka!" Na fada a dake. "Meye nufinki? Ki zubar min da mutuncina a gari ko me?" Dauke kai nayi gefe nace mishi. "Yo na ga ba mutuncin ne da kai ba, gara na watsar da sauran a titi kowa ya huta!" "Hadiyya!" "Na'am Uban A'isha!" "Akan me zaki sakawa Yata sunan A'isha? Na gaya miki bani da lokacin zuwa ne nayi masu huduba, maza ki biyo su Rukayya su kawo ki gida idan na haka ba raina zai b'aci." Kamar bai ji haushin abin da na fada mishi ba nace mishi. "Na rantse da Allah, ba zan dawo ba kuma na gaya maka kafin na barbad'a da sauran mutuncinka, ka sake ni ma gaya maka!" Tass naji an dauke ni da mari a zafaffe na d'ago kai, Mama ce a tsaye jikinta yana rawa. "Kika ce me?" Ban dawo daga wancan marin ba ta kara min wani sai da naji bana ji sosai. " mama ki gaya min meye zan yi da Aliyu? Me xan yi da zuri'arsa? Mutumin da ya ke kyamar uwarsa? Alhamdulillahi da Ya bani Uwa irin ki da ta tsaya min ta hana ni kuka amma kiyi hakuri na rantse da Allah ko a lahira bana fatan tashi a matsayin matar Aliyu Tafida na gaji da auren shi Gara ki kashe ni da ki ce na koma gidan Aliyu domin ni nasan makara zaki tura ta dauko ni. Duk da ina son Yarana Amma na hakura a kai mishi Yaransa na yafe su, yaji yadda ake ji idan da gayya Hajiya ta tafi ta barshi a tsummar goyo yaji yadda take ji shima ai Ubane kuma yasan Uwarsu tana raye don haka a kai mishi Yaransa, kuma wallahi yana ji ki gaya mishi aurena da shi ƙaddara ce, Mama bana son na bude miki cikina amma gashi yana jina idan karya nake mishi, Aliyu baka ce min idan na gama nayi har sata ko bin maza na ciyar da kaina ba? Ko baka gaya min cewa na tafi wurin Wanda ya aure maka ni ya ciyar dani, ba don kasan kai kafara ba da ka musanta Yaran nan ba naka bane karya ne?..........(Tirkshi 500₦ kawai fa na bukata🤔 domin warware wannan rikata-rikatan)YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


05


Cikin sheshakar kuka na ce mata, "ki gaya min akwai abin da ya fi haka muni saboda kawai Miji baya kaunarka yace ka fita ka bi maza ko kayi sata bai dame shi ba? Mama gasu nan a gaban idanunsu yake cin zarafina sun tab'a dakatar shi? Addu'a nayi tayi ba dare ba rana Allah ya ara min ranar da zan mara ashe cancanci a dafa min ba? Yana ji tunda ya iya cewa ba don shi ya fara tarayya dani ba, da ya ce cikinsu Mufidah ba nashi ba ne, amma babu yadda zai musanta hatta a gaban jama'a da danginsa ya gaya musu idan na gaji da kafata zan tafi tow na bar mishi gidan shi don Allah ku kyale ni na huta." Jikin Mama kamar an watsa mata ruwan sanyi haka ta fita, Aunty Rukayya suka kasa magana kowacce kanta a kasa, kafin suka mike. "A dai yi hakuri kome na duniyar nan dan hakuri ne!" "Da yake a jikin bishiya na fado, Ni yar talaka mara galihu, shi yasa da yayi babu me ce mishi ya daina domin shi d'a ne da Uwa ta haife shi ni kuma mahaukaciya ta haife ni " girgiza kai Maman Ilham tayi tana faɗin. "Ko daya kina da ikon niman hakkinki ma, babu me dakatar dake da nasan haka ne wallahi ba zan fara zuwa ba domin ban isa da wannan abin kunyar ba Ummu Hadiyya Allah ya huci zuciyarki." Daga haka ta ajiye min kuɗi fa ban san nawa ba ne, suka min sallama suka fita. A tsakar gida suka samu Mama tana lissafin an kawo mata wake. "Har kun fito?" Ta tambaye su da sakin fuska. A kunyance Maman Ilham ta ce mata. "Eh Mama, zamu tafi!" "Tow mun gode fa!" Ta musu godiya, abun mamaki yake bawa Aunty Rukayya suka fita dake gulma na cinta ta cewa Aunty Maryam!" "Ban gane yarinyar nan Uwarta kasuwanci kawai take yi ne ko da wani abu?" "Yar kasuwa ce kuma kin san ai muslunta tayi shi yasa bata damu da sauran abubuwan da matan hausawa da kanuri suke ba, ita niman kudi kawai ta iya." "Amma kuma idan har ita ta yi tarbiyyar Ummu Hadiyya da alamu ta samu tarbiyya me kyau tunda har kowa yasan cewa Ummu Hadiyya tana da kirki ta ina Tafida ya rasa na shi tarbiyyar da har ya iya ci mata mutunci kuna gani kun kasa magana!" "Hmmm!" Inji Aunty Maryam da tasan kome domin har gidan take zuwa taci mutuncin Ummu ta ce mata. "Wallahi ki bari kawai, amma abin bai yi dadi ba!" Haka suka isa gidan Babansu domin Tafida yayi kira ya kai goma babu wanda ya ɗauka, yana ganinsu ya mike. "Ina Yarana?" "Ai Gara ka cire rai akan Yaran domin Ummu ta rantse ba zata dawo ba, idan kuma ka nace kaje ka dauki Yaranka ta ce." "Wani irin hauka ne wannan?" Ya fada a harzuke. "Zafin kanka ba zai hana kome ba, abu mafi alkhairi ka sauke girman kai ka nime sulhu babu abin da yake kawo zaman lafiya kamar sulhu." Inji Safiyyudeen. "Akan me zan nime sulhu da ita me na mata?" "Kai zamu tambaya." Kamar ya fasa ihu ya kurawa Safiyyudeen idanu. "Me kake bukata?" "An jima zamu gidansu muje da kayan Barka idan muka je kada ka sake ka b'ata min aikina!" Suna cikin tattaunawa yan party dinsu suka tawo tare da Mr Abdullahi deputy suka iso gidan, aka bude musu babban parlour baki, suka zauna aka fara taya juna murna kafin suka shiga tattaunawa akan abin da ya kawo su. Safiyyudeen yana tare da shi yana kokarin kwantar mishi da hankali, tare da aron bakinsa yana cin albasa har aka gama meeting din suka tafi. Ya kalli Safiyyudeen ya ce mishi. "Deen me yasa ka hanani magana!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ranka a fusace yake, idan aka ja maganar kwamishinonin nan laifin Ummu zai shafe su." Murmushin takaici yayi yana me kwantar da bayanshi a jikin kujeran parlour din ya ce mata. "Na cancanci haka daga Ummu?" Girgiza kai Safiyyudeen yayi yana faɗin. "Ko kaɗan, sai dai itama tayi haka ne domin niman yanci." Kankance idanunshi yayi yana kallon Safiyyudeen. "Dama bata da yanci ne?" "A wurinka fa bata da yanci ita da da baiwa daya ce, sannan duk abinda ya fada baka musu ba shin laifi ne don Ummu ta nime Yanci?" Kurawa juna idanu suka yi. Kafin ya cewa Safiyyudeen. "Na ga ai ba wani abu ba ne ko?" "A wurinka da wurin kowa naka ba wani abu ba ne, amma a wurina da ita wani abu ne, idan da Ummu ta zauna tow tabbas zaka kashe ta ne da takaici domin kuwa akan Yaranka ma zaka kara dagula mata lissafi, amma akan kanta da ta zabi barinka da Yaranka ina ga ya kamata ka fahimci ba kowani mutane bane ake cutar da shi yayi hakuri akwai masu iya shanye kome kamar Ummu tayi hakuri yanzu da tace ba zata hakura ba ya kamata kai ka sauko da kanka!" "Never!" Ya furta kamar zai mangare Deen da yake bashi shawara. Kiran wayar Deen aka yi ya mike yana faɗin. "Zan je na dawo Madam tana niman dan saurayinta." tsaki yayi ya ce mishi. "Banza wawa me rami daya ni biyu ne gare ni!" "Gaskiya kan gara kai ni daya ne idan ta rufe ramin asirina ne zai tonu!" Ya fita yana dariya. "Sai me idan bata dawo ba, ina da wani ramin wallahi kuma a yanzu zan tafi kodumo!" "Aikin kenan Hajiri!" "Yes!" Ya fada yana dariya, a kofar gidan suka hadu da Mahmud, "Har ka iso?" "Eh wallahi!" Suka mikawa juna hannu sannan suka yi sallama. Mahmud ya shiga yana mu Tafida zaune yana kallon wakcyarshi. "Mai girma gwamna da kanshi me aminai biyu ango yar baka mijin yar fara!" Kiran wayarshi aka yi ya dauka ya kara a kunnenshi. "Don Allah don darajar Iyayenka kada ku tasa maganar Ummu!" "Ok Kanin Ubana, Bagwai." Ya kashe wayar, yana murmushi. "Yallabai kana dai sane da ina jiran appointment dina!" Murmushi Tafida yayi yana faɗin. "In sha Allah ina sane da kai!" "Yaushe zamu je ganin Madam da Yara ne?" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Sai na samu lokaci!" "Allah ya kai mu. Haka suka yi ta hira har lokacin sallah yayi, a daren ranar suka nufi gidansu Hadiyya.
*Ummu Hadiyya*
Tunda rana da abin nan ya faru Mama bata kuma min magana ba, nima kuma ban takaleta ba gudun kada samu matsala sai dai naga kamar jikinta yayi sanyi bayan sallah Isha ina shan kunu aka yi sallama daga yadda naji Muryan Baba nasan Tafida yazo don haka na gyara zamana, ina saka hijab mama tana sallah, suka shigo dakin. Dake akwai wadataccen haske da ni suka fara arba, kallo daya nayi musu na dauke kaina. "Sannunku da zuwa Yaya Deen!" "Barka dai mai jego akwai kunun kanwa?" "Eh har da yajin kunu, ya aka ji da Jama'a da hidima!" "Alhamdulillahi!!" Ya fada yana kallon Yaran da aka nad'e su cikin shawal. Sallama Mama tayi suka gaisa sannan ta mike ta basu yaran, sannan ta fita ta kawo musu abinci tuwon laushi da miyar kuka, sai kayan yaji da farfesu. Kunya ya hana tafida nutsiwa kamar ya nutse domin bai zata zai ga Mama a dakin ba, a hankali Deen ya ce. "Ni fa Hajiya Ummu nayi missing abincinki don haka ci zan yi wallahi!" "Bani nayi wannan ba, my Chef My Master ita tayi Mama wannan girkin!" Murmushi yayi ya ja kwanon ya wanke hannunshi kafin ya fara cin tuwon laushi da yaji tuki, sai miyar kuka da yasha namar rago, yana ci yana gyada kai. "Dole na turo Sadika ta dauki course domin na yarda Mama ita karshe ce." Murmushi yayi, kan tafida yana sunkuye ya saka yaran a gaba yana kallonsu. Sai da Deen ya ci ya koshi sannan ya ce mata."gaskiya ba don kada nayi abin kunya ba da nace miki ayi parkinge dinsu zuwa gida ayi min dumame wallahi!" Zungure shi Tafida yayi yana hararanshi. Can aka fara shigowa daki ana gaida Tafida sai da Baba ya fito ya tsawatar domin har makota sun fara shigowa. "Malam Ummu ko nace Hajiya Ummu Hadiyya, nazo ne akan batun taron suna domin yallabai zai tafi umara ibada!" Tab'e baki nayi nace musu. "Ku yi taronku a can family house dinsu ni zan yi nawa anan!" A zafaffe ya d'ago kai yana kallona, nayi kamar ban ganshi ba."amma da kinyi hakuri an hadu anyi ba, zai fi kwanciyar hankali da nutsuwa." "Waye ya aike Ni? Na je gidan tafida nayi suna, wai kawai ka bashi shawara na janye igiyar da aka zarga mishi da ya takura mai don Allah!" Wasa wasa tun karfe takwas muke tukawa har sai da goma tayi bamu cimma matsaya guda ba, na kafe suma sun kafe. "Idan ya dage sai nazo anyi suna ga Yaranshi dama Yaranshi ne ba nawa ba." "Ok ba xan karbi yaran ba, kuma ba zan sake ki ba za ayi sunan yadda kika ce amma ki sani wallahi babu shegen da ya isa raba auren nan zan nuna miki iyakarki a garin nan da ni kike wasan." Wani dan iskan dariya nayi nace mishi. "Ai kuwa sai dai na zauna da aurenka da na koma gidanka mu zuba mu gani Allah ya bamu sa'a." Tun daga ranar kowa ya fahimci ai babu zaman lafiya Mama tayi tayi na koma naki, kowa kai hatta dangin Aliyu sun zo amma na zuba musu idanu suka gama magana nayi murmushi kawai. Haka muka cinye kwanakin har ana jibi suna saniya daya da raguna biyu aka kawo, Ummu Kulsum da Ummu Rooman sun zo, aka ana gobe suna sai ga Hajiya da Kanwarta Umma Yaanah a gidanmu suka sauka. Ta ga Yaran kamar tayi kuka ta kalle ni cikin rarrashi ta ce min. "Allah ya miki albarka, amma a yafewa Babana banki a hukunta shi ba amma kada a ce za a rabu dashi wallahi bai kyauta ba bana bayanshi don Allah kada a rabu da shi." Matar tana da mutunci ba zan iya mata musu ba amma nace mata. "Kiyi hakuri sai na duba yiwuwar zamana dashi." Haka ta hakura har aka yi suna a daren sunan ya turo akan dauke ni da yara suna wani gidan shi aka taa daukar mu hoto, ana gamawa ya karbi tukin motar har mun hau kan hanya ya ce min. "Ke ba kowa ba sai ninkin ake kina batawa mutane rai, na barki dai ki yi wanka idan kuka gama ki dawo dakinki!" Juyawa nayi na kalle shi ina murmushi na ce mishi. "Ina ga ya kamata na gaya maka gaskiya don na lura baka fahimta sosai. Ba xan dawo gidanka ba. Kuma idan kace zaka min dole zan baka mamaki!" A fusace ya ce min . "Allah ya baki sa'a!" "Ai ya bani Uban A'isha Baban Muhammad!" Na fada daidai ya iso kofar gidanmu. "Ni da kai Allah ya bamu sa'a!" Na fada ina kara rungume Yarana, fitowa yayi ya dauki Mufid ina rike da Mufidah har cikin gidan, kada ku dauka wani abin arziki muke yi tsakanina da shi gasawa juna magana muke, domin kuwa ya hau dokin zuciya, har cikin gidan ya shiga anan ya ga Hajiya dauke kai yayi bayan ya gaidata sama sama, Mama tayi mishi nasiha da mishi fatan alkhairi da nuna mishi ya manta wani nauyi da ya kasa saukewa, bai ce kome ba yana zaune ya turo min text. "Ki ce mata tazo ina son ganinta!" Cike da mamaki nake kallon Tafida Mahaifiyarsa ce fa? Innalillahi wa innalihir rajouna! Hadiye kukan da yazo min nayi ina kallon Hajiya cikin tausayi ya saka kai ya fita, "Hajiya tana son ganinki ya ce!" "Tow!" Ya fada cikin sanyin murya sannan ta mike ta bi bayanshi, kuka na saka har da shasheka. "Mama Uwarsa ce fa!" Girgiza kai tayi tana kallona, "Uwar da ta haife shi! Mama Aliyu ya halaka!" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Kul koda wasa uban Yaranki ne addu'a yake bukata." "A'a Mama son rai ne irin nashi, Aliyu son kanshi yayi yawa ba zan iya zama da shi ba, duk me sabawa Iyaye yana tare da fushin Allah........'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


*Assalamualaikum don Allah kada a tura payment ta GTBANK babu network zan saka Opay dina*


06


Madadin Mama ta taya ni jin haushin abin da yayi sai ta koma tana bani laifin da cewa. "Aliyu bai da laifi me yasa ke baki ja shi a jikin kin nuna mishi girma da hakkin Uwa ba? Me yasa baki gaya mishi azabar Allah akan wanda ya watsar da iyayenshi ba? Kawai kina tsammanin Aliyu zai gyaru ne domin yafi kowa? Ke ya kamata ki nuna mishi hanya!" Sake baki nayi ina kallon Mama hala ta manta mazan zamanin yau ba irin mazansu na da ba ne, "Aliyu kamar yaro yake ko nace duk wani namiji kamar yaro yake." Ganin yadda fuskana ya sauya ta ce min. "Bakya jin dadin magana ta ko?" "A'a!" Na fada a sanyaye, Mama bata yarda tayi mana goyon kawai ba, ta ja mu a jikinta sosai.
Cikin hade rai yake wani kaukauda kai tare da kunkuni yana faɗin. "Kin san yanayin da ake ciki kin zo taya?" Yadda zaka fahimci lamarin uwa sai Allah ita ya dace ta tsaya a sama amma ta kaskantar da kanta cikin yanayi na rarrashi ta ce mishi. "Ayya gadanga kusar yaki kayi hakuri, na zo ganin likita ne!" Ta fada da dan rawan jiki. "Tow gaskiya ki koma idan kin ganshi!" Cikin kulawa irin na d'a da uwa ta kalle shi tana faɗin. "Gobe in sha Allah zan koma!" "Anan zaki kwana?" Ya tambaye ta idanunshi bude. "Saboda nan yafi kusa da asibiti ne!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Ki zo mu tafi za a duba ki." "Tow Ummu Hadiyya ta ce zata raka ni!" A yadda ya fahimce ta tana son lallai su tafi da ita Ummu Hadiyya ne, don haka ya barwa kanshi haka matsayin damar da zai sake magana da Ummu ta dawo dakinta. "Tow sai dai mu tafi yau gobe ta same ki a can! Domin ina sauri ne." "Tow bari na dauko kayana!" Ta shiga cikin gidan, can sai gata ta fito tare da Maman Hadiyya, har wurin motar ta rakata, shima cikin girmamawa yake kara godiya wa Mama.


Ina kwance Mama ta shigo, tana faɗin. "Ke ni banga kome da Tafiya yayiwa Mamanshi ba, kece dai mai gurguwar fahimta." Shiru nayi ina me gyara kwanciyar Mufeedah tare da mata addu'a, sannan na kwanta. Washi gari da safe ina farkawa da sakon Tafida na fara cin karo. *Inuwar alli! Mahmud zai zo daukarki!* ban kula shi ba nayi wanka na gyara jikina sosai, sannan na dauko wata English wax na saka me yakuwa, sai babban mayafin da lullube kaina bayan na karya d'an kwali. A hankali na zaro takalmin lefena grey colour da jakarshi kasancewar Mayafina ma grey colour ne. Domin akwai a jikin zanin. A hankali na kalli kaina a mirror dakin, fuskana tayi kyau da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login