Showing 102001 words to 105000 words out of 241571 words
Chapter 35 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
kaza ta shigo tana faɗin. "Ke ga wayarki tana ta kara!" Amsa nayi ina faɗin. "Na gode!" "Ni fa ba gudun lamarinki da Tafida nake ba, ke rawan jiki shi rawan jiki, ga shi dama baki yi wani abu na kula da Yaran nan ba, idan ban yi da gaske ba, ciki zaki kara daukowa don haka ki gaya mishi nace sai bayan layya zaki koma dakinki, ki je can naga shegen da zai tab'a min ke! Kafin nan Yaranki sun ƙara wayo wata takwasi zuwa tara tunda yanzu suna da wata biyar ko?" Sai na rasa farin ciki zan yi ko bakincikin sai na tsinci kaina da juyawa na kalli Mama amma kuma ban ce mata kome, watanni uku ban gaba fa mama take magana a kai, sai ban ce kome ba, iya abin da na tsinci kaina da furtawa. "Allah ya saka da alkhairi! Ya baki lafiya da nisan kwana, ya kuma kai ki Umaran ya dawo dake lafiya!" "Amin Ya Allah!" Ban yarda nayi wani farin ciki can ba, na cigaba da aikina. Haka na gama. Ana dabda shan ruwa, koma daki na bawa Yarana nono suka sha, sannan na shiga nayi wanka na gyara su tas, na fito na hada musu madara suna sha suka kwanta, wayata ce tayi ƙara na dauka, ganin bakon number ne yasa na ɗauka na kara a kunnena. "Ummu, ina me kara baki shawara ki amince da bukatata, Ummu yan uwan Tafida ba zasu barki ba." "Deen meye matsalarka da ni ne?" "Ummu! Dalla yi min shiru banza dan iska Dan akuya xan gayawa Tafida na gaji da halinka!" "Kafin nan ki saka Tafida ya sake yaron da ya saka aka kama, domin kuwa abin zai faru ba zai yi kyauta ba." "Barazana kake min ne?"."na gaya miki dai!" Kashe wayar nayi na barshi ina cikin tunanin wani Yaro Tafida yasa aka kama, aka kira sallah, na saka doguwar riga na tadda sallah. Ina zaune a wurin, ina kokarin mikewa na fito na yi bude baki aka dauke wuta, daga yadda aka dauke wutar jikina y bani Tafida tana hanya a gurguje na sha kunun gyada da kosai, bayan minti talatin sai gashi dakin Kawu Gwani na zaune muka kai abincin, shi yana wurin Baba suna tattaunawa. Bayan ya gama ya shiga ya gaida Mama, sannan ya fito don tana mishi godiya ne ya fito yana murmushi. Dakin zauren ya nufa, can na biyo shi da Mufidah da ta farka, ina shiga dakin ana kawo wuta, baya dakin amma ga kamshin turarensa. Juyawar da xan yi na ganshi tsaye a bayan kofar, ya harde hannunshi a kirjinshi. Sunkuyar da kai nayi ina faɗin. "Kazo ka ci kada ya wuce!" Kwaikwayo na yayi yana rufe kofar. Kallonshi nayi da sauri. " ba abincin bane damuwata, ki taimaka bawan Allah!" "Tafida ka rufa min asiri ni na yar iska ba ne!" Jan kumatuna yayi yana faɗin.."tow zauna ki bani na ci sai na tafi kada na lalataki." Haka na cigaba da zuba mishi abinci bayan ya zauna a bayana, juyawa da zan yi na sauka akan cinyarsa da jikinshi. "Ummu Hadiyya karya ni zaki yi?" "Kai ne fa ka zauna a wurin!" "Uwata kin ga abin da akewa Shalelenki ko!" Ya fada yana wasa da Mufidah. Ajiye abincin nayi xan mike ya ajiye Mufidah, ya riko gam. Tare da sakar min wani irin huci me zafi sanyi sanyi, ya matse ni sosai. "Ina kewarki Ummu!" "Kayi hakuri bayan layya tace zan dawo!" "Gaskiya yayi nisa, ina zan kai bukatata!" "Don Allah ka rufa min asiri kada ka ja min magana." Juyar da ni yayi yana kallon fuskata. A hankali ya sumbaci goshina. "Har ga Allah wata uku nan gaba, wallahi zan lalace!" "Tow ya xan maka? Na gaya maka ga abinda ta ce amma ba yarda ba!" Rungume Ni yayi yana shinshinar wuyata, "please a dawo bayan sallah wallahi ba zan iya jiran har bayan babban sallah ba." "Tow kayi yadda kake so shi kenan!" "Yadda nake son haka za ayi!" Ya shiga sumbatar wuyana zuwa kirjina, rike shi nayi na fara faɗin. "Don Allah ka ci abinci!" "Bafa abincin da xan ci!" Ya cigaba da abinda yake, haka kawai nake jin jikina yana wani irin Yummmmm, da sauri na kwace kaina, bai tab'a min abin da yake min yanxu ba, sai na kasa jurewa, bude idanu yayi a kaina. "Ki min adalci ki barni na samu nutsuwa dake!" "Tafida ni ina jin tsoro Mama tace zan iya samun ciki shi yasa ba zan koma ba sai Yarana sun yi kwari!" "Allah ba zan shiga ba na miki alƙawari." Yadda yake lallaba ni da kalamai yasa nayi shiru, tare da kasa cewa kome, domin yadda yaƙe min a da can baya bai tab'a min ba, kuma ni ba zance haka shi ne wani sinadari na musamman a aure sai yanzu da yake biya min karatunsa. Kukan Mufidah ya katse mishi abinda yake yi, ya zuba mata idanun yana faɗin. "Uwata ya zaki min haka? Gaya min laifi nayi da ba a son na huta a jikin Mama?" Kwace kaina nayi na tashi a jikinshi na koma can gefe ina gyara zaman rigana, nayi ina matukar jin kunya. Abincinshi ya a hankali yake ci yana kallona. "Gaskiya wata uku nan gaba yayi min yawa bayan sallah shi ne abin da na yanke!" "Tow ka same ta ka gaya mata ni babu ruwana!" Na zata zai hasala ne, sai na ga ya ce min. "Ummu ina matukar jin kunya mama ba zan iya ce mata haka ba, da Abbana ne ko Hajiyata wallahi sai sun rage, amma ba zan iya kallon Mama nace mata watanni sun min yawa ba, Mama tayi kokari da ta bani ke a karo na biyu, ina tsoron kada wani abu ya faru ta kwace min ke har abada, mutuwa xan yi!" Murmushi nayi kafin na ce . "Ba zaka mutu ba, kawai zaka sha ciwon kai ne!" "Ummu!" Ya kai hannunshi fuskana. "Ki yafe min abin da na miki?" Hannuna na kai saman nashi nace mishi, "Aliyun da na sani ba haka yake ba!" "Ki ce kin yafe min!" "Na yafe maka Daadin yan biyu!" Sai nake ga kamar da can Tafida yana sona kawai iskancinsa ne yasa yake ta tsula min tsiya, haka ya gama cin abincin ya tafi, na raka shi har bakin kofar, ya ce min yana zuwa ne nan kafin Hajiya ta dawo, don a can wurinta da wurin Deen yake cikin abinci har zai tafi na ce mishi. "Ni Ko akwai yaron da ka saka aka kama shi ne?" Kallona yayi kafin ya ce. "Eh wani abu ne!" "Ka sake shi!" "Za a tura shi hannun hukuma!" "Ka sake shi nace, saboda yana cikin mutanen da suka kaad'a kuriar zabarka, babu amfanin rike shi." Murmushi yayi ya ce min. "Zan saka a sake shi, amma kuma dole na tauna aya tsakuwa taji tsoro, waye ya gaya miki!" "Ka tafi sai da safe ka samu kayi sallah tarawee!" Na koma cikin gida, yana barin gidan kofar gidan kiran Deen yayi ya ce mishi. "Taya Ummu tasan da batun yaron nan?" "Ban sani ba wallahi!" Shiru yayi kafin ya ce . "Wani yana niman shiga tsakaninmu kenan!" "A'a ba haka ba ne, maybe an gaya mata ne domin ta roke ka alfarman sake Yaron!" "Ai na gaya maka ba zan waiwaiyi Yaron ba, sai na ga abin da ya faru tsakanina da Ummu, zata kome shi kuma ɗan iska ku ci Ubanshi gobe a mika shi kotu!" "An gama!" Lokacin da ya isa gidan, ya samu yan uwansa da matan yayunsa da matan Sharif wai Sa'adiyya ta hada musu bude baƙi, kallo daya yayi musu ya wuce bangaren shi, Tashi tayi ta biyo shi, wayarshi tana kunne a hankali ya ce mata. "Baki kyauta min ba, naso na sha madaran nan amma kika hanani, me yasa?" Daga can Ummu ta ce mishi. "Saboda kai kato ne, kada ka shanyewa Yarana abincinsu!" "Tow ai ni ma yaro ne, "gaskiya babu adalci a wanann lamarin, duk ranar da kika dawo zamu tafi honeymoon!" "Yarana jarirai ne!" Saadiya Ji tayi kamar an dasata a wurin shi kuwa da bai san tana nan ba, ya ce mata. "Ki gyara min gashinki nan, da wancan wurin sannan na shanun nan a gyara min domin ina nan daram zan dawo fage na!" "Kai ni fa na gaji da kai ka bari dai na tafi na samo wani bazawarin tunda kaima kayi auren!" "Ummu zan fasa miki baki, na gaya miki idan kina son numfashina ya tsaya ki fara kiran saki, zan daujee bakinki nan!"
"Hmm! Ai gaskiya ne!" Jan kofar dakin da aka yi girummmm ya sa shi juyawa, bai ga kowa ba,ya cigaba da sake zantuttukar da yake jin nishsdi akansu, bayan ya gama wayar, ne yayi kamar ana ihu ko kara ne cire babban rigarshi yayi ya fita, Saadiya ya gani tana ta hauka tare da fashe-fashe. "Meye haka?" "Tunda ta fito daga ɓangarenka take wannan abin borin. Murmushi yayi yana faɗin. "Ok tow Allah ya bata sa'a gwamnati bata san asara ba, duk abin da kika fasa ki sani zaki biya shi, su a tunaninsu zai bada hakuri ne sai suka ga wani salon rashin mutunci. "Na san abin da kuke aikatawa kyale ku nayi, don wacce ta fasa abin da tayi niyya ta rena mahaliccinta, Ummu kuwa ku saka ranku ta dawo, wani dan iska ya kara shiga tsakaninmu sai na saka an daure shi har ya mutu, kai wani shegen ya kara shiga harkar Ummu wallahi ko ciki daya muka fito sai na saka an wulakanta min shege, mugun kallo aka mata sai na tozarta mutu, don haka ki gama haukarki Ummu zata dawo wacce kika ji muna waya ita ce zata dawo dakin ta, sannan duk wanda ya san.ya biya wani yaci mutuncin aurena sai na lalata mishi lissafisa." Yadda yake bala'i yasa suka fara daukar kayansu daya bayan daya suna barin wurin dama, ya kalli Maryam cikin masifa da tijaran da ya ajiye kwana biyu ya ce mata. "Wallahi idan kuka tab'a min Uwar Yarana sai na baku mamaki!" Daga haka ya wuce abinsa cikin gidan. Ko yau Baba Nura da yazo daga Damaturu sai da ya gaya mishi kada ya sake ya zama irin Abba da kome za aayi ya tsayawa Matarshi itace shi, kafin ya zama gwamna take tare da shi, sannan ta shanye duk wani abin da yake mata, ya tsaya da gaske ya ga ya bata kariya, kada ya ga kamar abin wasa ne wannan abin da yake faruwa sak abin da aka yiwa MAHAIFIYARSU ce don haka ya tsaya kada yayi saken da zai yi danasani.
*Hajiya*
A kasa me tsarki kuwa bata daina gayawa Allah lamarinta ba, musamman Tafida da Ummu fata take Allah ya daidaita su, idan suka hadu da Abba dariya yake mata ya tsokaneta da cewa. "Idan don Tafida da Ummu ne ki barwa Rabbil Ka'aba, yasan abin da zai yi da alamarinsu!" Murmushi tayi tana faɗin. "Ban sare ba, ina gaya mishi ne domin yasan ban daina rokon rahama da jikai ga Tafida ba." "Allah ya tabbatar da alkhairi!" "Amin Ya Allah!"
**
*Deen*
"Ba zaka gaya min waye ya saka ka ba? Kai ku ci kaniyarshi!" Ganin zasu cigaba da mishi dukar da kullum sai sun mishi kamar jaki. Ya kalli Deen cikin tashin hankali ya ce mishi. "Idan na gaya maka zaka kyale ni?" "Zan kyale ka!" "Da gaske?!" "Eh!" Cikin tashin hankali ya ce mishi. "wasu mutane biyu ne daya Sa'adiyya matar gwamna ce namijin ne ban san waye ba, don Allah ka taimaka min." "Zan kai ka kotu a hukuntaka, idan ka fito zaka min aiki kuma zan tsaya maka kayi karatu ka ji!" Cikin kuka ya ce mishi. "Na gode sosai!" Daga haka aka fitar da shi zuwa office din Yan sanda.
Washi gari aka wuce da shi kotu. Duk abinda ake tuhumi yaron ya amince, don haka aka hukunta shi tare da gargadin na gaba su kiyayye aka tura shi gidan gyaran hali.
***
*Ummu*
Ranar goma sha biyu ga watan Ramadan su Mama suka nufi kasa me tsarki, sai da ta min Gargadi akan na kama kaina kada na sake Tafida yayi min dadin baki, na barshi wani abu ya haɗa mu na hakura akwai gyaran da zata min kada na sake wani abu ya faru don ranta zai b'aci, sannan ga wani tsoro da ya kama ni, don haka na rufawa kaina asiri, bayan na rakota, muna dawowa Tafida ya kira ni. Tsoro yasa na kasa daukar wayar don gani nake kamar Mama tana kallona. Sake kiran wayata yayi na dauka jikina yana rawa. "Me yasa ba zaki dauki wayata ba, Hajiya da Abba gobe zasu dawo!" "Kaga don Allah ka kyale ni, kada ka ja Mama tace ta fasa dawowarmu!" Dariya ya saka yana faɗin. "Ina hanyar zuwa bude wani titi. Deen zai zo ya kawo ki da abin bude bakina." "Tafida masifa kake son jaza min ne? Don Allah ka rufa min asiri!" "Ni kuma ki tona min asiri ina yawo abu a hannu ke zo ki bani hakkina!" "Tafida yaushe ka lalace ban sani ba.......🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
"Innalillahi wainnalihir rajou! Don Allah ka rufa min asiri azumi nake ni ban saba da wannan sabon halin naka ba sai an jima!" Ina jin yana dariyar shakiyanci. "yarinya ki gama kimtsa min kanki na gaya miki, dama Mama ce ta min karan tsaye, yau kuma ki tabbatar tare zamu kwana!" Kashe wayar nayi ina zare idanu. Ba zan iya maganar Tafida da ba, tunda muka dawo sai na kasa kome domin nasan tunda ya ce haka ne tow haka ne na san waye shi akan ra'ayinsa. Shiru nayi ina zare idanu kamar nayi karya.
**
*Asiyah*
"Mummy da gaske Matarshi zata dawo, Wallahi na rasa yadda xan yi domin ni dai yayi min, sannan ba a office dinsa nake aiki ba a tare da wani abokanshi nake aiki. Gaskiya Mummy kiyi wani abu ko ni nayi wani abu!" Ajiyar zuciya Uwar tayi ta kafin ta cewa Asiya ta waya. "Na gaya miki Tafida shu'umi ne, sannan ba zamu tab'a nasara akanshi ba haka kawai sai dai ko idan zamu jaraba makirci shine kawai mafita!" "Kamar ya kenan?" Murmushi Uwar tayi ta waya tana faɗin. "Kwantar da hankalinki, ina yanzu kina gidanshi ne?" "Eh Mummy!" "Shi kenan, ki tunzira matar gidan ta miki wani abu yadda zaki shigo gidan kenan, dole sai mun hau matakala ta kanta yadda zata bamu kofar shigowa gidan!" "Allah Mummy?" "Da gaske nake gaya miki, zaki shiga gidan Tafida kamar yadda shuwa ta shigo da jakar yarta haka kema zaki shigo mishi!" "Wayyo Allah Mummy shi yasa nake sonki, yanzu ki gaya min yadda xan yi?" "Yanzu kafin matar shi ta dawo nake son ke maganarki tayi karfi, idan har muka sake yarinyar ta dawo baki shiga ba tow har abada ba zaki tab'a shiga gidan Tafida, domin yarinyar a shirye take, haka Uwarta ma!" Sannan ta daura yarta akan hanyar da ya dace. Ta kara da cewa , "wawuya ce, tana ganin haka zata haukace ta fara kiranki da sunayen banza, ni kuma zan yi magana a lokacin." Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin. "Na gode sosai Mamana!"
***
Tunda na gama birgima na tashi, saboda yadda Tafida yake gaya min abin da yake bukata na bude baki, na shiga ba baji ba gani, kafin karfe shida na gama. Sannan ka kira Uwani na fara lallabata domin tun shida saura Tafida ya tabbatar min yana hanyar dawowa Maiduguri, Deen zai zo ya kawo ni gidanshi ba na gwamnati ba. Na fara kame-kame. "Babansu Mufidah yace ki tafi ko?" "Eh amma na rasa yadda zan yi! Don Allah ki rufa min asiri, wallahi na rasa yadda xan yi da shi ya dage kuma Mama ta ce." "Wayyo Allah Aunty Baby Allah ya baki irin mijin da nake fata!" Inji Zakiya da ta shigo dakin. "Meye?" "Eh mana domin ya rakashe ya tura keyar Mama Umara" suka kwashe da dariya, fita Uwani tai ta dauki jakar goyanmu ta zuba kayan barcin da nazo dashi kala daya, sai na su Mufidah. "Ba don kada Mama ta zargi wani abu ba da ba hada miki kayanki sai ana gobe zata dawo ki dawo gidan nan, kina da hakuri gaskiya. Irin su Mama ne da a sawun mutanen farko ta fito tow za a sha wahala ita kafin ta fahimci Yesu Almasihu Annabi ne ba dan Allah ba! Maza ki gyara! Aunty Baby kema kamar tsohuwa fisabiilillahi ko irin maganin matan nan ba zaki na sha a boye ba, haba don Allah." Sai gani da zare idanu, ina sosa kai tsaki tayi ta bar dakin, store ta shigo ta dauki kwai da lipton, ta fasa sannan ta jika lipton din, ta matse min tana faɗin. "Lokacin da Ummu Rooman take wanka idan mama ta wuce dakin Baba shegiya mijinta yana zuwa ganinsu zata jika ta sha, idan ta raka shi waje. Yarinyar nan tantiriya ce wallahi Aunty Baby na ga kokarin, yadda Ummu Kulsum tayi ta kashe arna da sunan wanka lokacin da muka je mata kwana biyu. Yadda kuka san me ciwon idanun na fata kyafkyafta idanu. Yarinyar ta bani tsoro da ta mika min kwai na sha. "Zan yi amai!" "Mtseew yar kauye!" Ta kama hancina ta matse tare da dura min ruwan sannan ta dauko lemon tsami rabi ta cusa min a bakina, haka nayi ta taunawa har na hadiye, na wuce ban daki da gudu ina wanke bakina. "Aikin kenan!" Ta fada tana ciro dabino ta fara cire hancinsa, tana jefawa a cikin ruwan zafi. "Aunty Baby wannan sai kin dawo ke da kanki zaki ce Excellency ya bani kujeran aikin hajji!" Fita nayi ina faɗin. "Allah ya kawo miji mu mika ki, kafin ki fara sayar da kayan