Showing 144001 words to 147000 words out of 241571 words

Chapter 49 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14742

Mufidah!" Yadda ta kira sunana yasa gabana faduwa. "Hmm! Ya jikinki?" "Da sauki Ya Ali Barka da zuwa sannunku!" Ta fada Mamanta kuwa sai wani dauke kai take na bude baki na gaishe ta. "Ina wuni?" Kamar bata ji ba, sai da Yar ta ce mata. "Mammy baki ji tana gaishe dake bane?" "Oho da ni take na zata da ke take?" "Baby muje!" Ya riko hannuna. "Tafida tafiya zaka yi ba ka gaishe Ni ba?" "Akan me xan gaishe ki? Bayan Ummu ta gaishe ki, kika share ta tunda jikinta da sauki ai shi kenan!" Ya riko hannuna muka bar dakin.


*Asiyah*
A matuƙar hasale ta kalli Uwarta. "Meye sunan abinda kika aikata? Kin dauka haka zai samu cikin ruwan sanyi ne? Haka kawai bayan na gama shan azabar samunshi zaki tashi ki lalata min kome, wallahi." Hakuri ta shiga bata."kiyi hakuri haushin yarinyar nake ji, ban kara jin na tsaneta ba sai yanxu da na ganta wata abu kamar inuwar alli, gaskiya dole ki shiga cikin gidan Tafida a damma dake!" Girgiza kai tayi tana cewa. "Itace makullin gidan sau da ita xan shiga cikin gidan, idan babu ita ai ya zama aikin banza."


"Haka ne amma kuma taya kike ganin xan kaunace ta a siyasance, ga tafi dan da girman kai kamar akanshi aka fara zama gwamna. " "Ko da ba akan shi aka fara ba, shi din nawa ne ni daya zan tabbatar da na mallake shi in and out dinsa yadda kowa na shi sai ya biyo bayana.
**
Ummu
Gidan Abba muka isa, zama muka yi yana shan kankana. "Ummu Hadiyya tunda kika koma kika manta da Abbanku!" "A'a Abba!" Yar dariya yayi kafin ya ce min. "Ummu laifi kan muna ta miki, ba wai don ba mu muka haife ki ba, a'a kawai ba yadda zamu yi ne." A hankali gabana ya fara faduwa. "Yarinyar nan Asiyah bata da lafiya, sannan dalilin ciwon shine Mijinki, tana son shi amma ni Na gaya musu gaskiya tuntuni na gaya musu." Kaina a kasa ban iya magana ba amma kuma ai bani za ayiwa kishiyar ba kishiyar Sa'adiyya ce za ayiwa magana!
"Abba ni ai na gaya maka bana sonta akan me zaka ka daura min ita!" "Tsakani da Allah yarinyar nan tana fama da jinya kayi hakuri ka aureta!" Tashi yayi ya bar parlour yana faɗin na same shi a mota. A sanina wasu mazan farin ciki suke idan za a basu damar kara aure sai na kasa fahimtar Tafida, har muka koma gida fushi yake, sannan ya saka an gyara bangaren da Saadiya zata zauna, wani abu da na kara fahimta gara tafida yayi auren yadda kowa iya ruwa fidda kai, kowa tashi ta fishe shi, idan na mallake Tafida ne za a gani idan kuma halinsa ne kowa zai gani, haka yasa na sakawa a raina babu tashin hankali. Bangaren da Saadiya zata zauna aka fara aikin shi domin ya fadawa Abba cewa sai ya gyara wurin, batun Asiyah yarinyar nan tana shan wuya domin yadda ake bada labarin kamar zata mutu haka take ji akan tafida. Shi kuwa ya ce a'a, cikin wannan yanayin aka fara shirin sallah layya, a kwanakin goman zulhajji na hana idanuna barci saboda ina yawan mafarkin Asiyah tana kuka haka yasa naki komawa gaida ta, ina azumin kwanakin kuma kara rub'anya ayyukana. Ranar ina zaune da hantsi, "Ummu!" Naji ana min kiran mafarauta. Gabana ne ya fadi ina fitowa Maman Asiyah ce ta zube akan gwiwarta tana kuka. "Ni taimaka min kada na rasata ki saka Tafida ya aureta don Allah zata iya mutu!" Sake baki nayi na juya xan shiga cikin parlourna sai ji nayi kamar duhu ya lullube min idanuna............
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7645
Ban san me ya faru ba, sai dai tabbas zuciyata tayi min nauyin da na kasa jure kukan Uwar Asiyah lokacin da na farka Hajiya da Mama ne a dakin, tashi xan yi Hajiya tace min. "ki kula Ummu!" Bude idanuna nayi naga dakin da nake, dafe goshina nayi ina kallon sama, na rasa gane me ke damuna, a hankali nake ambaton Allah,ina ji kamar akwai abin da nake bukatar fadar shi amma na kasa, so nake lallai na ji haka ya fita daga bakina amma na kasa fadarshi fashewa da kuka nayi, Mama da tafi kusa da ni ta ce min. "Ummu Hadiyya lafiya?" Girgiza kai nayi nayi ina jin kamar ana daure min zuciyata. "Mama d'aga ni!" Na fada a hankali, "ikon Allah! Tow " Hajiya ta fada tana mikewa, itama zuwa suka yi suka d'aga ni, na zauna ina kuka kamar raina zai fita. "Tow me aka miki?" "Mama ban sani ba amma don Allah ki ce ya aureta!" Na fada ina kuka me motsa rai, tare da dafe kirjina, saboda ji da nake kamar ana hura min zuciyata. "Ummu!" "Don Allah Hajiya, ki saka baki ya auri Asiyah." Kamar zata yi kuka haka take kallona. "Wannan abu bai yi ba." Ta furta sai wurin goma Mama ta bar asibiti, Sagir da ya duba Ni allura yayi min saboda yadda jini na yayi bala'in hawa. Sannan gashi ko magana nayi haki nake, Tafida da yazo ya ga halin da nake ciki Hajiya ta gaya mishi hankalinsa yayi bala'in tashi ya kura min idanun kafin ya ce min. "Me yasa?" Rike hannunshi nayi kamar zai gudu na ce mishi. "Ka aure ta don Allah!" Na fada ina juya kaina tare da dafe kirjina. "Ka aureta!" "Ummu kin san halin da nake ciki zaki kara min damuwa akan damuwa? Ummu Hadiyya!" "Hajiya ki ce ya amince don Allah!" Itama kuka take domin basu tab'a ganina cikin wannan halin ba, sai yayi ta kallona. Wasa wasa Sai gashi na fara ji kamar zan mutu, idan numfashina yayi ta shiga da fita. Haka Sagir da Fadilah suka kwana akaina, washi gari da safe yayi sammakon zuwa ya samu ina ta barci. "Aliyu!" "Na'am Hajiya!" "Ka auri yarinyar! Shine masalaha idan ba haka ba Ummu ce zata ta wahala idan kuma wani abu ya samu yar mutane ba zan iya yafewa kaina ba balle kai, sai kayi kokarin ganin kayi adalci." "Hajiya!" "Sai ka zab'a rayuwarta ko taurin zuciyarka" tashi tayi ta fita ya dawo bakin gadon ya zauna yana shafa kumatuna, bude ido nayi ina murmushi. Gabana ne ya fadi yadda naga yana hade min rai. "Zaka aureta?" "A'a ba zan iya ba! Ki tashi mu cigaba da zamanmu!" Ji nayi kamar ya shake ni, lumshe idanu nake a hankali tun ina iya hango shi har na daina hango shi. A tunaninshi barci nayi, shigowar Sagir ya ce mishi. " ta farka ne?" "Eh ta farka har ta koma ma!" Takowa yayi yana kallon yadda nake kwance, "wani irin komawa, ta sake suma ne fa!" Ya fada yana tab'a hannuna. "Suma kuma?" Fita yayi ya kwalawa nurse Fadilah kira, aka sake rufe kaina. Sai da suka dauki lokaci kafin aka samu na farfaɗo barci yayi gaba da ni.


*Tafida*
A wannan lokacin da Ummu tasan halin da yake ciki ba zata tab'a d'aga mishi hankali ba, ga Mahmoud da ya saka shi a gaba ya gaya mishi inda Deen yake jinya amma yaki karshe kin haduwa da Mahmoud din yaƙe sau uku yana niman izinin ganinshi amma yana hanawa, saboda kawai baya son magana ne, ta gefe guda Yan adawa musamman Alhaji Hamza Goza sun matukar saka shi a gaba, akwai wani abu da matukar baka isa matakin ba gani kake kamar karya ne, zuwa yanzu ya kara hango tashin hankalin da ya kara cusa kansa domin da sauki zama gwamna a wurinshi, sai dai abin da yake kan Gwamna da gwamnati ya sha kanshi, domin kuwa zuwa yanzu duk abinda zai yi sai ya sha kiran manyan mutane.


Lumshe idanunshi yayi a hankali ya bude akan laptop din da yake office dinsa, wayar office dinsa ya dauka ya kira SSG suna gama wayar ya kashe can bayan minti talatin sai ga shi yazo. Zama yayi yana faɗin. "Yallabai!" "A'a ka kirani Aliyu! Kawu!" Inji Tafida. "A'a ai matsayi Allah ya baka!" "Duk da haka dai, kawu dama akan aikin kwangilar nan ne, mutane dayawa suna ta bukatar a basu, kawu kayi aikin gwamnati na tsawon shekaru, shin waye kake ganin za a bashi aikin nan babu matsala!" Shiru SSG yayi kafin ya ce mishi. "ina ga ka bawa Amaan Yusuf Mandara zai fi maka aiki akan sauran, shi yana iya saka dukiyarsu ma ayi daga baya a biya su." "Alhamdulillahi shi kenan, ka hada mana zama da shi." Turo kofar aka yi ya zubawa Mahmoud idanu. "Meye matsalarka da ni nake son ganinka kana hana ni? Nayi kokarin ganin na dauke kai ka gaya min me nayi maka kake hanani ganinka? Wai duk wannan sauyin na meye?" "Kawu jeka!" "Shi kenan!" Ya fita, kallon juna Tafida da Mahmoud suka yi, "zauna!" Zama yayi yana huci. "Meye matsalarka da ni?" Murmushi yayi ya ce mishi. "Babu kome kana da damuwa, aiki ya sha kanmu daga ni har kai bamu da lokacin kanmu, idan nace kullum zamu hadu akwai matsala gara muna haduwa jefi-jefi haka muka shirya da Deen zamu na haduwa idan muka tashi a aiki!" "Da baya nan ni ban cancanci muna haduwa ba ne? Wai ma ina ka kai Deen?" Kai tsaye ya ce mishi. "Wani wurin na daba, yadda rayuwarshi zata tsira." "Tafida me kake nufi da Ni ne? Tafida me kake boye min? Wato ni ne magananne a cikinku kome nawa kun sani ni ban san kome akanku ba!" Girgiza kai Tafida yayi sannan ya ce mishi." Kana da magana, bakinka baya shiru sannan ina kokarin kare Deen ne kada wani abu ya kara samunshi, a lokacin da ta dace yayi murnan Matarshi ta haihu, ko sunan yarshi bai gani aka farmake shi." Taune lips dinsa yayi cike da takaici ya cigaba da jinjina kai yana faɗin. "Ba zan yafewa wanda yayi min wannan abin ba, matuƙar zan ganinshi sai yayi." Murmushin takaici ya kara yi, yana mikewa, "Allah ya kyauta amma ana kan bincike ko?" "Eh nace a cigaba da bincike!" Ya hada kayanshi zai fita. "Zan tafi asibiti Ummu bata da lafiya!" "Tow Allah ya bata lafiya! Nima tafiya xan yi!" A tare suka fito, bakiɗaya jikin Mahmoud wani irin rawa yake, Motarshi ya fada yana jin kamar ba zai iya isa gidanshi ba.


Kiran wani layi yayi yana faɗin, "Ka tabbatar kun nisanta kanku da nigeria, domin gwamna da kanshi ya saka a yi mishi bincike, idan aka kama ku babu ruwana." Ya kashe wayar sannan ya kira wani layi. "Ya ka samu labarin inda ya kai Deen?" "Gaskiya bani da tabbaci amma ina kyautata zaton India ya fara zuwa, kuma a tunanina Deen ya kai asibiti." Murmushi Mahmoud yayi ya ce mishi. "Shi kenan zan san yadda za ayi a nimo kwararru na musamman a tura hoton Deen can, kawai a gama da shi."
**
Jabir Adam
Kallon Tinah yayi yana faɗin. "Aunty babu lokaci, Yallabai Deen ayi ƙoƙarin dauke shi a can!" Ya fada yana cire abu a kunnenshi. "Me yasa!" Kunna mata muryan layin Mahmoud yayi. "Tow me kake tunani?" "A rena musu hankali!" "Tow shi kenan!" Kiran wanda Tafida ya bari yana kula da Deen Tina tayi suka yi magana, ta tanbaye shi ya aikin, ya gaya mata anyi nasara kuma Alhamdulillahi, tun washi gari ya farka. Amma baya asibitin ya tafi masallaci idan ya koma zasu yi magana. Godiya tayi mishi. Sannan ta kashe wayar, tana gayawa Jabir Adam.
**
*Ummu*
Tunda yazo nake ji kamar xan mutu, ganin har lokacin ban bude idanu ba yasa shi riko hannuna. "Me yasa kika min haka?" "Ka tafi ka ji!" "Ina zan je bayan ina da ke!" Hawaye ne ya zubo min nace mishi. "bana da ni, da kana da ni ba zaka tab'a juyawa bukatatta baya ba!" "Ummu! Ki yarda dani wannan ba mafita ba ne, bana son wani abu yayi hurt dinki please!" "Ka tafi gida!" Na fada xan juya mishi baya. Domin na fara haki. "Idan na amince zaki tashi daga jinyar nan?" Kallonshi nake idanuna cike da kwalla shima kuma nashi cike yake da kwallan. "Zan tashi yanzu ma mu tafi gida, xan bika na kwana a gefenka!" Shafa min kai yayi ya ce min. "Ummu kin rame sosai, me yake damunki ne?" "Ina jin wani irin tashin hankali ne daga zuciya ta, sai naji kamar zuciya ta zata fashe so nake kawai ka amince ka ce zaka aureta ko xan daina jin haka!" Kamar ya fashe da kuka ya ce min. "Wani yana cutar da zuciyarki ko?" Girgiza kai nayi ina faɗin.."rashin amincewarka shine yake cutar dani!" Kura min idanun yayi yana jin kamar zai yi kuka yace. "bayan nan akwai wani abu da kike bukata ne?" Hawaye ya zubo min, na dauki hannunshi na daura akan bugun zuciyata. "Ka ji yadda nake ji, ka ji abin da nake ji? Wallahi ji nake kamar kafin gari ya waye zan mutu!" "Me kike so nayi ki daina jin haka!" "Don Allah ka amince itama ta huta, Don Allah Aliyu!" Inji Mama tana bakin kofar dakin. Hawaye ne ya shiga zuba min. "Mama ina jin tsoro ne ne!" "Ba shi bane mafita ka amince muga abinda hali zayi!" Kamar ya fasa ihu ya ce mata.."Mama shi kenan zuwa an jima zan dawo!" Ya mike dafe kirjina nayi da yake wani irin tsalle. Juya kaina nake ina ji kamar zan mutu. "Tunda ba zaka iya taimakawa ba, don Allah ka sake ta." A razane ya kalli Mama. "ka sake ta don Allah, ka sake ta ka dauki abin da kake so." "Mama!" "Bukatar Ummu shine tayi farinciki taya zan ganta cikin wannan yanayin na zuba mata idanun? Ni fa uwa ce!" Ta fada a sanyaye, tari na fara ina rike kirjina. "Zo ka fita mara imani, ka je kada kayi abin da take so, Allah yana.." "Amince !" Ya fada yana zama a bakin gadon, tare da rike kanshi. "Na amince don Allah ku barmu da ita." Ya fada muryanshi yana rawa, juyawa yayi yana faɗin. "Zan aureta yayi miki!" A hankali na zube a wurin, ina jin ihunsu amma ban san me ke faruwa ba, hajiya kuka take tana jin kamar ta cire ciwon ta daurawa kanta, haka yasa ko gida bata zuwa. Addu'a kuwa babu wanda bata mata, sadaka da take na kuɗi da Abinci da take sakawa a dafa a rabawa mutane. Zai saka ka fahimci Hajiya tana mugun son Ummu. "Gaskiya baka da kirki!" "Ya xan yi Sagir!" "Ya kuwa zaka yi! Haka zaka saka idanun akan gidanka Ummu tana buƙatarka."


***
Abba
A gaban Malam Zailani yake zauna, kamar zai yi kuka ya ce mishi. "Alhaji! Aliyu yana kokari mutane ne basu da adalci, idan ka koma ka ce ya amince da bukatarta. Ya amince, auren yana cikin ƙaddaranta, ka bashi hakuri idan yana son ta samu lafiya dole sai ya amince, haka zai saka ta samu sauki da sassauci in sha Allah." "Na rasa yadda zan yi da Tafida!" "Ka kyalesu dta shi mana, Aliyun dai Aliyu ne sannan ba zai tab'a sauyawa daga yadda yake ba, don haka ga gidan shi nan su shigo Allah ya basu sa'a." "Tausayi nake ji kada yarinyar ta kara samun matsala da Aliyu!" "In sha Allah haka ba zai kara faruwa ba! Allah ya shiga lamarinsu........
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7646
Tunda Tafida ya amsa shi kenan, ba a kara ganin Asiyah da Uwarta ba, koda Abba ya ji labarin sun koma Yola bai ce kome ba, da kanshi ya shirya zuwa Yola domin ya ji kome, kuma dama yasan karshen idan suka sami yadda suke so shi kenan, har abada ba zai tab'a barin wani ya cutar da Ummu ba, sai idan baya numfashi. Faruwar abin da kwana hudu ya isa Yola. A lokacin da Turai ta ganshi a gidan ta sha jinin jikinta. Kame kame ta fara yi tana son lallai tayi mishi bayani amma ko inda take bai kalla ba, ya kurbi ruwan goran da Alfah ya mika mishi domin tare suka zo. "Na zo ne nayi miki kashedi! Tunda kika watsar damu ban kara jin ko ganinki bayan rasuwar mahaifina, haka ba laifi ba ne don naji kina zumunci da masu zuwa wurinki!" Murmushi yayi yana kura mata idanu. "Tun kina yarinya nasan halinki, kuma ko ba a gaya min abin da ya faru na nasan zaki aikata kin zata haka kawai nake gefe akan Tafida. Ki gayawa Bokan da yayi aikin ya warware idan kuwa kina son ganin bakinciki ki tambayi Hindu, duk hidimar da tayi sanadiyar rikon Tafida ke babu Allah cikin sha'aninta gata ga Tafida, ba alfahari ba ni nasan Allah ba zai tab'a kunyata ni ba, domin kuwa na yarda da shi." Tunda ya fara magana ta firgita haka yasa shi sake murmushi. "Idan ma baku lalata ba, sharrinku zai dawo kanku!" Daga haka ya bar parlour tare da Alfah. Bayan fitar Abba Asiyah ta fito daga ita sai mini skirt da wani hafvest. Tana kallon Uwarta. "Mammy lafiya?" "Zan tafi wurin bokon nan ne yau din nan ba sai gobe ba!" Rausayar da kai yarinyar tayi tana faɗin. "Me kuma ya rage bayan ya amince zai aure ni!" "Ba shi bane mafita! Ya kara nimo mana hanya da zaki riko hannunshi!" "Kuma dai!" Asiyah ta fada tana saka takalminta. "Hm!" Uwar ta shige dakinta, ta bar Asiyah tana waya da wata kawarta ta zo musu da abar..


Abba ya bar Yola ya dawo gida don dama wuni ce bai da niyyar kwana sai abu na gaba da yayi dangin Mahaifinsu Asiyah da ya tafi wurin niman auren Asiyah a can, duk da mutanen suna da kirki su dai abu daya suka sani sun basu aure idan suka shirya a zo a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login