Showing 81001 words to 84000 words out of 241571 words

Chapter 28 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14737

me kai karar Tafida. Domin idan ta fara da Abba tafida na zuwa Abba ya mishi magana zai fusata. Tana komawa bangarenta ta kira Saadiyyah, ta gaya mata duk rintsi kada su tawo Najeriya bata fusata Tafida ba. Ita kuma yayi mata alkawarin haka zai faru. Shirin da Shuwa take ba karamin shiri bane don haka ta kira Rukayya domin tasan ita ce zata fi bata haɗin kai, don haka tayi amfani da ita ta kirata da sunan ranar da Tafida zai dawo ta zo su yi abinci, dake bata da lissafi Allah ya zuba mata kwadiya, don ko Maryam bata gayawa gudun kada maryam ta mata faɗa, haka ta ki faɗa. Aikuwa Ana gobe zasu dawo Shuwa da kanta ta shiga bangaren Saadiyyah ta gyara mata, sannan ta koma bangaren Ummu da tasan dole ta nan sai fara shigowa, haka yasa ya turara bangaren tas. Da kyakkyawar shirinta, haka kuwa ya faru tun a jidda ta fara mishi tijara, bai kulata ba domin burinsa kawai ya isa ya nufi wurin Ummu da Yaransa. Don haka yaki yarda ya amsa mata domin kada ta yarda ta fusata shi lokaci zuwa lokaci yana murmushi, don na karamin dad'i yake ji ba, koda suka bar Saudiya a jirgi ma magana take gaya mishi. Har su iso garin Maiduguri Allah yasa sun iso da dare, don haka ba tare da ya damu ba ya kalli Mahmoud ya ce mishi. "Ka wuce da ita gida! Ni zan tafi ganin Ummu!" Ya kan wasu akwatina guda biyu. "Tow na zata gida zaka wuce!" Wani shu'umin murmushi dariya Sa'adiyya tayi, tana faɗin. "Allah yasa rawan kan da ake yi akan Ummu ya koma upside down" banza yayi mata bai yarda ya kula ta ba zai shiga motar Deen ta ce mishi. "Da alamu dai gudu abin kunyar da aka aikata yasa ana ƙoƙarin rufa-rufa, waye ya sani ko yaran ba jininka ba ne!" Cak ya tsaya kamar an dasa shi a wurin ya kasa gaba ya kasa baya. "Waye ya sani ko bayan kai akwai mata yi tunda ai kafin kai akwai wani a gidansu da yake sonta!" Ta shige motar da gudu, wani irin tafasa ranshi yake tunda ya shiga motar, jikinshi yake kyarma, asalin yarinyar ta san spot din da ya dace ta buga ta koma buga yadda ya dace, "wuce da ni gida na ci Uban Yarinyar nan." "Kayi hakuri ka fara kai musu kayan!" "Wuce da ni gidan kawai!" Yasan yadda ya fusata nan, ba zai saurare shi ba, don haka bai yarda ya kai shi gidan ba, ya wuce da shi gidan Malam Zailani. Ai kuwa yayi ta fada kamar zai daki Deen yaki kuma fitowa, Malam da kanshi ya tawo har wurin motar. "Aliyu!" "Sannu Malam!" "Allah ya tayaka riko tunda ba zaka samu shigowa ba, ina jiranka Allah ya tsare hanya." Bai ce kome ba shi dai burinsa ya isa gidan, Deen bai ji dadi ba haka ya ja motar ya bar gidan Malam. Har ga Allah Malam Zailani tausayin Tafida yake ji, domin zuciyarshi ita ce matsalarshi. Lokacin da suka isa ko parking Deen bai gama ba, ya fita daga motar ya nufi bangaren Shuwa don yasan Sa'adiyya tana can, yana shiga cikin fusata ya shiga kwallo da Sa'adiyya, yadda yake dukanta zaka ɗauka Allah ne ya aiko shi yana faɗin. "Ke din banza karuwan banza kin isa ki kama kafar Ummu yarinyar da ta kare rayuwarta da mutuncinta zaki zaga. Ke karuwa da maza suka gama hawa da sauka akanki zaki zagar min.mata da tafiki daraja." Bai damu ihun da Shuwa take ba ya mata duka har yana ture shuwa. Sannan ya bar bangaren jikinshi yana wani irin rawa domin bai tab'a jin fushi irin na yau ba, riko hannunshi Abba yayi kamar zai yi kuka ya kai shi parlourn shi ya ajiye shi tare da bashi ruwa, yana.sha yana haki domin babu abin da ya mishi kamar sheganta mishi Yaranshi a duniya bai da sama da su. Gumsar ruwan sanyi Inna tai ta fesa mishi, ya sauke wata ajiyar zuciya me karfi a kai akai. "Tafida!" D'ago kai yayi yana kallon Abba kafin ya ce mishi. "Yaushe Ummu zata dawo?" "Sai lokacin da kayi hankali ka koyi sanin darajar iyaye da Macen aurenka, ku zama shaida na raba Aliyu Tafida da Ummu sai ranar da yayi hankali!" Ya juya ya koma dakinshi, ya rufe kofar ya zauna a bakin gadon shi. Baya son yayiwa Tafida kuka amma tabbas deeply inside dinsa yana jin rauni a ranshi dama haka Ummu tayi hakuri da shi. Waye ya sani ko har dukanta yayi Allah Sarki Yar Mutane. Kiran Malam Zailani yayi ya gaya mishi a hankali yake kuka kamar karamin Yaro ya ce mishi. "Malam Tafida yana son fin karfina ji nake kamar na mutu da takaici,na rasa yadda zan yi da shi." "Alhaji Muhammad kenan, ka daina kukan nan kada ya tab'a shi!" "Ba shi nakewa kuka ba." "Kada ka damu, ka godewa Allah yadda ya tsaya a haka bai zama wanda zai na janyo maka magana daga waje ba, zan zamu cigaba da addu'a." Rarrashin abba Malam Zailani yayi, sannan suka yi sallama. Dakyar Deen ya saka shi a gaba har bangaren Ummu ya kwanta yana jin kamar zuciyarshi zata buga musamman yadda Abba ya haramta mishi maganar Ummu! A daren bayan tafiyar Deen ya kira Ummu Hadiyya, "ki kira Abba ki ce zaki dawo gidana!" Dariya tayi tana faɗin. "Allah Sarki Malam Tafida, da fatan ka dawo gida lafiya! Ai kai yanxu yayana ne don haka babu maganar dawowa!" "Ummu me yasa ba zaki dawo dakinki?" "Saboda bana son aurenka bana sonka bana kaunar na bude idanunka, Tafida bana sonka bana son aurenka ka rabu da ni na samu Lafiya!" "Naji amma ki gaya min me yasa kika tsane ni?" "Kai baka san dalilin tsanarka ba, ba kasan dalilin da yar baka mummunar me siffar goron bobo ta tsane ka ba, ka manta dalilin da yar Mace yar matsiyata. Yar mace me sayar da tuwo a kofar gidansu ba.." kamar zai fasa ihu ya ce mata. "Dama kina rike da wadannan kalaman na zata ya wuce tunda between ni dake ba wani abu ba ne don an samu ire-iren waɗannan stuffs din shine kike ta threating din kike wani d'aga min kai, Ummu ki cigaba da zama da aurena tunda ba zaki dawo ba, kina nufin ni Aliyu Muhammad Jadda Tafida na kira ki ina baki hakuri tow baki isa ba, har yau baki kai macen da zan bude bakina na baki hakuri, ki zauna a gidanku ." "Ba zaka tab'a sauyawa ba, ina bakincikin rashin samawa Yarana Uba na gari, na fada rayuwarka Idan ka gadama ka cigaba da rike auren har ranar da zaka ji labarin na mutu sai kayi murna, ba zaka sauya ba ba zaka tab'a sauyawa ba!" Ta fada tana jan hancinta. Kashe wayar tayi ya bi wayar da idanun, bai san lokacin da ya maka wayar da kasa ba ya mike tare da nufar dakinsa.
*Ummu Hadiyya!*
Ni a tunina da lissafina Tafida zai sauya ashe ba haka ba ne, domin bai sauya ba kuma babu al'amar zai sauya. Kowa damuwarshi na koma dakina amma basu san Tafida ba, hawaye ne ya zuba min, na share da bayan hannuna shigowa Mama tayi da ta kawo min namar da Baba ya kawo. Ganin yadda nake kuka yasa ta zama tana faɗin. "Kuka kuma?" A yadda tayi maganar a tausashe yasa ni na sake fashewa da kuka na kalleta cikin kuka na ce mata. "Don Allah ki bar ni na koma wurin Babana!" Kallona tayi bata iya magana ba, "wani abu ne ya faru?" "Kawai zan tafi nesa da nan ne!" "Kun yi fada da shi ne?" Cikin sheshakar kuka na ce mata. "Don Allah kada ki ce min na koma ki ni na koma can wurin Babana!" Yadda nake rokonta yasa ta kasa magana, bakiɗaya. "Me ya faru?" "Kawai na gaji ne na gaji na gaji wallahi gawata zaki gani na gaji na kai matakin da bana son kome sai nutsuwa!" Murmushi tayi tana faɗin. "Dakinki ne wurin da zaki huta, ki koma dakinki ki kara sa yakin da kika fara!" "Me yasa ba zaki gane halin da nake ciki ba, me yasa kike ƙoƙarin ganin ko zan cutu sai na koma ga Tafida? Mama Tafida ba mutum ba ne, ni ba zan iya gyara shi ba, don Allah ki bar ni na tafi!" Yadda nake kuka har da jan zuciya. Bakiɗaya ji nayi zuciyata tana zafi, tashi tayi ta bar ni a dakin. Bayan fitarta ko minti talatin bata yi ba sai ga sakonshi.
_Idan kina burin na sake ki ne ki auri Mutumin gidanku, kin yi kuskure ba zan tab'a sake ki ba har abada gara na ga mutuwata da naga aurenki da wani mara kunya don ina bin ki shine zaki rena ni! Don haka ki zauna har ki rube!_


Hawaye ne ya zubo min kamar an bude pampo, a daren na kira Mudan. "Aunty Baby lafiya?" "Ana kiran sallah farko ka zo don Allah zamu yi tafiya ne!" "Aunty Baby lafiya kuwa!" "Kayi min alƙawarin haka!" Ina cikin wayar Baba Bulama ya shigo shi da Mama, kashe wayar nayi suka rufe ni da fada kafin suka daura da nasiha, kafin suka kira Babana, shima ya nuna min b'acin ranshi. Ashe bayan ya turo min sakon shine Tafida ya kira Babana ya gaya mishi ni da Abbanshi mun hade mishi kai, shi kuma Babana ya kira Baba Bulama ya ce maza na koma dakina. Daren ranar ban iya barci ba, domin ji nake kamar zan mutu kafin gari ya waye. A daren na hada kayanmu ni da Yarana, na saka Babban jaka sannan tun cikin daren na kira shi na bashi kayanmu, asubar fari muka bar Maiduguri, bayan na ajiye musu wayata, Bauchi na saka ya kai ni, ya juya duk yadda yaso ya fahimci halin da nake ci naki, domin sai karfe sha biyu muka shiga Bauchi. Kai tsaye na wuce inda motar da yake zuwa Lagos, don na fahimci Mudan ba zai tafi ba, haka na je na samu ana kiran motar Lagos da ya fito daga Yola,ina zaune har ya iso na biya kudin Abuja, Mudan yana nan ina sane don yaki tafiya. Haka motarmu ya tashi, ya fito yayi ta bin mu kafin ya juya ya koma Maiduguri. Number Tinah da na dauka a takarda na duba, Ban tab'a sanin Yan biyuna suna da farin jini ba, sai da mutanen motar suka yi ta daukarsu wannan ya dauka wannan ya mikawa wannan, har muka isa jos, Yaran suna hannun mutane, ni dai addu'a nake tofa musu. Bayan mun huta karfe shida na dare bayan nayi sallah muka bar Jos, karfe sha biyu muka isa Abuja, dare yayi don haka a tashan na zauna aka bani wani daki da aka tara kaya, sai a lokacin nake jin me yasa na bar gida, dakyar yarana suka yi barci. Kiran sallah farko nayi sallah asuba, sannan na fito na amshi aron wayar wani mutum na kira Tinah. Har wayar ta yanke bata dauka ba, na sake kiranta a karo na uku ta dauka tana faɗin. "Waye ne? A daren nan!" "Gari ya waye yan mata, ki saka a zo a dauke ni don Allah kada ki fadawa kowa daga Maiduguri!" "Ummu kece!"
"Eh nice!" "A'a gani nan zuwa a wani tasha kike?" Na tambayi mutum na gaya mata. "Gani nan ki jirani Please!" Kashe wayar tayi, wurin karfe shida da rabi sai gata da kiran waya ta iso,amsar Yaran tayi tana me rungumar Mufidah tayi tana faɗin. "Ummu!" Sai hawaye sharrr, cikin kuka nace mata. "Babu wnada ya damu da ni, n bar Tafida na huta amma ban huta ba, Tinah ya zan yi." "Shiga Mota muje!" Ta saka yaran a baya, sannan ta dawo ta saka kayanmu, muka bar tashan bayan ta bawa mutumin da ya bani aron waya dubu biyar, yayi ta godiya. Ganin yadda nake kuka sosai, taka motar take da mugun gudu, ranta yana sosuwa. "Gaskiya har yanzu Northeast basu fahimci Muslunci kamar yadda Annabinsu kawo da hukunce-hukuncen addini akan aure da kuma pillar da zasu rike auren! Ana." Shiru tayi tana jin zafi tasan wannan da kasar turawa ne da tuni an bindige auren, tsaki tayi yafi sau uku. "Yaranki masu kyau da haduwa!" Ni dai kuka na cigaba da yi ban kuma amsa mata ba, koda muka isa gidansu ruwan wanka ta hada min, nayi wanka tayiwa Yaran, ta shirya su tana faɗin. "gaskiya yaran nan sun girman fa!".....
#Mai_Dambu🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


Tea ta hada min me kauri, da soyayyen kwai da bread ta kawo min dakin, na sha kaɗan na ajiye na wanke bakina na zo na kwanta, a madadin barci sai naji hankalina yayi bala'in tashi, kamar nayi kuka na tashi zaune. Shigowa Tina tayi tana faɗin, "na zata kin kwanta ne? Ashe kina zaune har yanzu!" "Hankalina ne ya koma gida sai nake ganin kamar ban kyauta ba!" Murmushi tayi tana faɗin. "Eh da haka gaskiya amma kuma ki daina jin ba dad'i akan yancin kai! Tunda ba cin kai bane ki danne zuciyarki na wani lokaci ne zaki saba, kasancewar baki saba da barin Mama ba ne ban da aure!" Yadda take gaya min kalmomin masu kwantar da hankali yasa na iya rike zuciyata amma tabbas ban tab'a nisa da gida ba. Haka yasa na kwanta barci yayi gaba da ni. Ta rage mana karfin ac ta fita. Cikin fushi ta nemi wuri ta zauna tana jin kamar ta kama Tafida tayi ta caka kan dan banza da kasa, gayen nan bai da mutunci ko na kwandala.
**
*BAYA DA KURAA.*


Barin Ummu gidan Mama bata sani ba, domin kuwa tana can bangaren Baba Bulama, sai ya tafi masallaci mace take dawowa bangarenta. Haka ya faru da Mama itama Baba Bulama yana tafiya massalaci, ta fito itama ta nufi bangarenta, sai tana shiga dakin Baba Ummu babu Yaranta, gabanta ne ya fadi don tasan Ummu Hadiyya guduwa tayi hala biu ta wuce, don haka ta share bata kuma bin zancen Ummu ba ai tasan duk inda zata ce ba bai wuce wurin Babanta, ban daki ta shiga tayi alola tazo ta gabatar da sallah, tana idarwa wayar Ummu da yake dauke da apps na islamic calendar, ya fara kiran sallah, ware idanu tayi tana sake addu'ar da take. Ta nufi gadon tana me ɗaukar wayar "tabbas wayar Ummu ce!" Rasa nutsuwa tayi ta gagara zama, ta nufi bangaren Baba Bulama, haka ya dawo daga massalaci ya same tana zarya a cikin parlourn shi. "Lafiya Hadiza?" "Ummu Hadiyya tana gudu! Domin da wurin Ubanta ta tafi ba zata bar min wayarta ba, barin wayarta yana nufin ta tafin kenan kamar yadda ta fada zata tafi idan na ce dole ta koma Innalillahi wainnalihir rajouna! Ya Allah na tuba." Zube akan kujeran parlour, da tasan da gaske Ummu take ba zata cigaba da takura mata ba, "bari na gama na kira Alhaji Kabiru!" Haka kuwa ya kira Baban Ummu ya gaya tambaye shi ko Ummu Hadiyya tazo, ya ce bata zo ba, amma zai ta zuba idanun jiranta. Abu kamar wasa sai ga shi har rana tayi, babu labarin Ummu Hadiyya. Biu ma Babanta har gidan yan uwansa ya bincika ko ta sauka a can, wurin karfe uku na yamma Baba Bulama ya kira Alhaji Muhammad Jadda ya gaya mishi halin da ake ciki, da wani irin damuwa ya amsa. "Kuma bata tafi da wayarta ba?" "Gashi nan babu wani abu da ta bari na alamar tana nan kusa, don ta kwashe kayanta da na yaranta, ina ga akan maganar da muka yi fa Yaron nan Aliyu ne, muka ci ta koma shine ya bar gidan, Alhaji don Allah ka fahimce ni, a dakatar da maganar komen tunda ka ga lokacin da aka nemi auren bata bada matsala ba, yanzu kuwa ya dace mu mata adalci mu barta don kanta kada muce zamu tirsassa mata a haifi d'a mara idanun!" "In sha Allah, ba zai kara magana ba. Ummu tayi kokari tunda tayi wannan fushi dole mu bata lokaci ta huce don kanta." Haka aka bar maganar ko Tafida bai sani ba, kuma ko da wasa bai gayawa wani halin da ake ciki ba. Domin yana son Tafida ya fuskanci al'umma, amma hankalin kowa ya tashi, Abba ya kira Malam Zailani ya gaya mishi ya ce ya bashi lokaci, bai kuma kiran shi ba sai wurin karfe goma na dare, ya kira Abba yana murmushi. "Ku kyaleta ta huta, in sha Allah tana cikin kyakkyawar hannu babu abin da zai faru, zata dawo idan lokacin yayi, ayi ta hakuri." Abu kamar wasa Ummu ta b'ace a garin Maiduguri babu ita babu labarinta, Mudan bai yarda yaje gidansu Ummu ba, sannan itama Mama ta roki Baba Bulama ya bar maganar akan Ummu tafiya tayi, haka kuwa ranar Alhamis Ummu ta bar gidan, washi gari Juma'a Tafida ya kama aiki tare da gayyatar masu ruwa da tsaki na jahar, suka yi meeting washi gari asabar ma meeting suka ayi, ranar lahadi ya dawo gidan gwamnati shi daya, sai da ya samu nutsuwa ya kira Ummu. Amma bata dauka asalima Mama ce ke daukar kiran, take ya shiga wasi-wasi ba dai lamarin ya kai Mama ta kwace wayar Ummu ba, murmushi yayi yana kara godewa Allah da ya bashi suruka irin Mama, yasan zai yi wahala bata dawo da ummu ba don ya lura da Mama irin iyayen da can baya ne, wani fadaddar murmushi yana kara jin kaunar kanshi da kuma samun Mama da yayi tana sonshi. Sai dai kuma da ya kara kiran wayar ita ce dai ta dauka, yaso ya tambaye ta ama sai ya tsinci kansa da jin nauyinta, haka ya gama kame-kame ya kashe wayar, ranar Monday da safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login