Showing 240001 words to 241571 words out of 241571 words
Chapter 81 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
in sha Allah ba zan tab'a barin wani ya wulakanta ki ba!" "Mammy ya san abin da ya faru da ni?" Rungume ta nayi, ina faɗin. "Bashi yake bukata ba, tun bai ganki ba yace yana sonki, idan kin shiga gidansa, zai yi farin ciki da haka. Kema ba yin kanki ba ne! Haka kaddara take." Haka muka yi ta rarrashinta, kafin muka samu kanta. Tafida ya kira Uban yarinyar ya mishi magana, take ya amince dama kamar ya gaji da yarinyar nan, nawa Naziha take ko ashirin bata rufa ba. A can Maidugurin aka daura aure, ni da Iyalina bakiɗaya muka wuce da ita Turkiyya, inda zata zaune da shi kanshi. Kwananmu biyar a can Mama da su Kulsum suka zo da Ummi Hajiya Balkisu, sai Jalilah sai Rabi'atu kanwar Babanta da Deen da Matarshi, wacce ta gaya min rashin jin dadinta akan Tinah da zai auro, na bata hakuri nace ta kwantar da hankalinta zata iya jure kome, kuma Deen ba irin Tafida ba ne, zata ji dadin tinah, kuma na bata hakuri sosai Deen zai kamanta adalci.
Bayan mun bar amarya da ango, mun tattara mun wuce Umara ne har da Mama, sai dai Tafida bai bi mu ba. Ya koma bakin aikinsa. A tafiyar da muka yi kwana goma nayi kacal, na dawo gida domin yadda yayi ta damuna kwana shida a Madina kwana hudu a Makka na barsu. Duk da haka na ji dadin ganinshi. Haka muka cigaba da zamanmu har tsawon wata tara wani azumi ya gaya min Rukayya zata zo, sai da Abba ya gaya min na tattare kayana kada ta min sata, abin tausayi a waya yake gaya min kuma a gabanta. Lokacin da tazo ashe Tafida ne yasa ta zo zasu wuce china da Sharifai ya kawo ta, satinta daya suka tafi za a mata hannun robo, wani lokacin baya gaya min zai yi abu sai yayi idan na tuhume shi ya ce yana da Uwa irin Mama ai ba zai yi shawara da ni ba, kuma haka ne karfi da yaji ya kwace min uwa. Bayan sun dawo daga China watanta biyar, har su Naziha suka da ita da mijin, tayi kyau ga ciki nan, rabo fa. Daga nan muka zo Maiduguri har da Tafida. Kofar gidan Abba an cika ana fadanci, haka ya karbi takardun matasa ya sama musu aikin gwamnati sannan akwai kamfanin da zasu bude da Deen, za a dauki wasu. Har da shagunan Tijjani ma ya kai wasu. Mamanmu kuwa mun tsaya sosai akanta, musamman ni da Tijjani da muke zuba kudi a kanta. Kulsum da Ruman suna bakin ƙoƙarinsu, don ma Tijjani ya basu jari, ni kuma bawa Uwani da Zakiya da za ayi aurenta, Uwani dai Mudan zata aura Zakiya kuwa wani dan Damaturu, an saka sai December, don haka tunda muka koma nake tanadinsu, Maryam da ta ga Naziha ko irin jin dadin nan bata nuna ba, don ma Tijjani bashi da kunya tare tare yake da matarshi kamar kwai. Sonta yake a gaban mu ma tambayarta yake me zata ci me take so, Mama da bata ganin zarau sai ta tsinka, ta taya shi barna kome yi mata take yi. Sau biyu yana kaita wurin Maryam da kuka suke dawowa, amma ana kwana biyu zata koma. A na kudi ne ya fito mata a mutum ya ce mata.."Aunty rigimarku da Aunty Baby daban, ki daina saka min matata kuka, don Allah ya gani ina ganin girmanki na ke ce kika haifi Baby. Bana son na hanata zuwa ne ki ji babu dad'i amma daga yanxu ta haihu ba zata kara zuwa ba." Tunda ya gaya mata haka ta daina damun yarinyar, Ni ce ko mutuwa xan yi ba zata tab'a sona ba.
****
A December aka yi bikin su Uwani, a lokacin da muka koma na ga Tafida ya ɗan fara sauyawa, ban damu kaina ba, na fito mishi mutum idan aure ne yayi abin shi ban yarda da sauyi ba. Addu'a na yarda yana tasiri domin bayan nan na tsaya da addu'a, Allah ya zab'a mana mafi alkhairi a rayuwarmu da shi, karshe auren ya watse. Na rungume shi sosai kada kuce ya sauya dukka idan abin ya motsa yana kan yin shi, amma Alhamdulillahi don yana matuƙar gudun abinda zai tab'a alakarmu, bayan shekara daya aka yi bikin Deen, haka Naziha ta sauka lafiya an samu y'ace aka saka mata sunan Mama..tana yada wanka Mijinta ya kawo min ita kwanansu biyar suka koma dakinta.
Sai da muka shekara biyar cib, sannan na samu cikin Babana, wanda shima yana tare da ni, don ma yana fama da rashin lafiya ga girma, Mama ma ta ajiye aikinta ita da Baba Bulama da sauran kishiyoyinta. Umma ce Yaran duk matan suna gabanta, ba karamin damuwa take ciki ba, domin irin wahalar da suke sha don ma Baba Bulama yana sassauta musu albarkancinmu, ya daina fita kasuwa ni dasu Bakura da Kawu Gwani, da Ahmad babba da Tijjani mun rike gidan, sosai muka cire kishi muka hade kanmu, a gidan Babana ma Sagir ya tsaya kamar shi babana ya haifa.
A gidansu Tafida, girman da bana shi ba ya hau kanshi, kome shine da taimakon Yan uwa irinsu Alfah da Sharifai, Umar. Rukayya ma mijinta ya maida ita bayan ta sami kishiyar da yayi mata. Ita nata da sauki sai dai wani irin abu da yake damunta, ko ta samu kudi lalacewa yake. Haka ta gaya min, nace mata tayi ta sadaka da niyyar ladan a kai ga Hajiya, Allah zai albarkacin rayuwarta, kuma haka tayi ta yi. Hatta sutura sai da yaso fin karfin Rukayya, kafin rahamar Allah ya sauka akanta. Ta fara sana'a sai gashi ana zuwa ana saya. Sai Allah ya jarabceta da Yaronta Khalil da dauke dauke, tayi kuka tayi addu'a, ga niman taimako, sai abin yayi sauki amma tana fama da ciwon abin.
Uwani sai da ta shekara biyar ta haihu itama kamar ni tagwaye mata ta haifa, Tinah itama rabo haihuwarta na biyu kenan, Yarana kan sai Godiyar Ubangiji, Rayyan da Matarshi sun tab'a zuwa ma duk da naji Tafida ya gaya min ai yana aiki da shi ne, amma ban yarda yana kowa min wasu mazan gida ba, haka na hada kan Yarana ina kula dasu.
Hajiya Hindu take kula da Kaltuma da Sa'adiya, Haka ma Asiyah tana samun kulawa sakamakon alkhairin.da nake mata ni da mijina, daga karshe dai ga mijina ya dawo nawa ni daya. Tarbiyyar Yara ba na mu bane mu daya, ina yi Babansu yana ta ni, haka Addu'a ba dare ba rana.
**
A yanzu shekarun mu goma sha daya da aure, kamar bamu ba daga ni har shi kowa hankali ya fara zuwa mana, idan muna hira abin da ya faru sai yi ta dariya. Ga yaranmu Masha Allah, ilimi nutsuwa, sai yan rashin jin da ba za a rasa ba. Da wannan Maryam take yawan gaya min nima sai naji bakin cikin yadda taji, Allah yana kare Yaranta ita dai gata bata ga tsuntsu bata ga tarko, tana yawo kamar mahaukaciya.
Deen da gaske yake tsaye a gidanshi, daga Tinah har Sadiqa, suna tsoron abin da zai fusata shi. Kuma Ammah ta maida su Yaranta ko me ta gani bai mata ba zata ajiye su tai musu nasiha dake Tinah ta muslunta, kuma jin familyn Uwarta manyan malamai ne yasa ba a samu matsala ba. Deen bai banbanta su ba, ya nuna musu dukkansu yana sonsu ya ajiye su. Haka yasa yake yiwa Tafida gorin ba zai iya auren mata biyu ba.
Duk wani rayuwa mai kyau tushen shi Uwa ta gari ce, Hajiya da Mamana sun kafa mana misali sosai don babu ranar da ba zan yiwa Hajiya Addu'a ba. Mamana ina fatan mi rabu lafiya. Burin kowacce uwa yaranta mata su zauna a dakin aurensu da dad'i ko ba dadi, Mama tayi rawan ganin na zauna a gidana da zuciyar mijina, dadin da take fada gashi nan na hango shi, Mijina da duk sauran da muke tare Alhamdulillahi.
***
Yau da yamma makotanmu da na fahimci Yarbawa ne, ana ta biki da hidima, sannan sun gayyaci makota musamman muslmai da muke makota, ana ta hidima nan birthday ake, ba laifi wurin yai kyau. Wasu iyalai naga yan Nijeriya ne, ina zaune abin ka da ka ga dan uwa. Na isa gare su muka gaisa, su biyu ne, dayan tana ta hidimarta sai Mamarsu dayan kuma ta kame, kamar kunya ce ko tsoro ne, sai dai ita Mamarsu yae kano ce. Sai mijinta da yazo daga baya, ina kallon ɗaya yarinyar ta zungure dayan kamar zata yi kuka ita kuwa sai dariya take.
Haka aka taso taron na dawo gida ina gayawa Tafida abin da ya faru dariya yayi ya ce . "Prof AbdulGaffar Akindele Rafiq, Yan naija ne Matarshi yar South Turkiya ce wurdawa ce, shi kuma wanda ake abin domin shi Abu Zar! Ban samu zuwa ba ne aiki yayi yawa." "Na ji dadin ganin yan Nijeriya!" "Ai fa ku haka kuke mata." Ya fada yana dariya.
Duk yadda ka dauki rayuwa haka take zuwa maka, na dauke shi da sauki ya zo min da sauki. Idan na tuna duk abinda ya faru ribar soyayya ce sai naji Alhamdulillahi Ubangiji ya bamu alkhairi, sharrin da yake cikin dare da rana Allah ya kare mu da shi.
Anan na kawo karshen Yar Mace!
Alhamdulillahi.......
___________________________________________
Fatan Alkhairi taku har kullum.
Ramlat A Manga
Mai_Dambu