Showing 39001 words to 42000 words out of 241571 words

Chapter 14 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14699

aka sallame shi, sai dai har lokacin jikinshi babu kwari, tunda muka dawo gidan yan dubaiyya suke zuwa gaishe shi. Wani abun tashin hankalin shine yadda nake wuni a tsaye bani da ikon zama zai kwala min kira duk da wannan zaman da nake bai saka Tafida cin abincin da xan girka ba, asalima zuwa mishi ake yi Ni kuma nawa haka zan ta girkawa ana cinyewa. Ana haka Sa'adiyya tazo, tunda na ganta na zuba mata idanun, tana zuwa ta amshi ragamar girkin gidan tsakanina dasu idanun. A hankali na lura zaman jinya ya fara wuce gona da iri, domin kusan a dakinshi take kwana, wata safiya ina dakina a kwance naji ana buga kofar gidan, na tashi na je na bude Deen ne da Abba. Kamar na nutse a kasa domin nasan Sa'adiyya tana dakin Tafida. "Abba! Sannunku da zuwa anan kuka kwana? Ku shigo!" Na fada ina jin kamar na saka hannu a kaina nayi ta ihu. "Bari na taso shi!" Na fada ina nufar dakin, ina shiga na same su cikin wani irin yanayi da duk me Imani abin da zai zo ranshi zargi ne, na buga kafarshi ya bude idanu a gajiye. "Ka zo Abba ya zo, sannan ita ta zauna a dakin kada ta fito domin kimarka zata zuba a idanun mahaifinka." Kafin na fita daga dakin, dafe goshi yayi tare da ture Sa'adiyya wallahi bai yi kome da ita ba, duk da Burinta yayi wani abu da ita amma shi bai tab'a ketare iyakar Allah ba yau ma don tace bata da lafiya ne, shi yasa har ta haura gadon ta kwanta a jikinshi. Sannan akwai wani abu da ya kasa ganewa da zaran ta nufe shi da wani shaidanin turarenta yake jin bai da ikon sarrafa kanshi. Jallabiyar shi ya saka ya fito waje, Ni kuma na shiga kitchen na fara aikin ina ta Addu'a Allah yasa kada ta fito don na lura yar iska ce. Dankalin turawa na soya da sauce din kwai, sai garin kunun tsamiya da na dama, na fito da shi parlourn sannan na koma ina daura abincin rana tuwon semo ne miyar kubewa busashe da na hada da miyar kazar nan, nayi kome na kwashe a leda, a ranar Tafida ya fara cin abincina don yaga idanun Abba, sai kallon Deen yake wanda yake murmushi yana faɗin. "Abba ya kamata a dafawa Ummu ta buɗe katon shagon abincin, domin ni dai Allah ya gani yarinyar da zata saka surukarka zata zo koyan girki wurin Ummu." "Safiyyudeen bakina yana kewar abincin Ummu, kai idan ta gama jinyarka, maza ka tura min ita gida domin bakina da cikina suna kewar abincin ta." "Ai Abba ta dawo kenan sai dai ayi hakuri." Haka suka yi ta santi, haka suka ci na zo na kwashe kayan na kai kitchen sannan na dawo na wuce daki nayi wanka na saka kaya, na fito muka kara gaisawa da Abba, shima dakinsa ya wuce yayi wanka tare da zubawa Sa'adiyya warning kada ta fito. Sai wurin karfe uku su Abba suka tafi, ya ja Deen gefe ya gaya mishi abin da yake faruwa. Sake baki Deen yai idanunshi sun yi jajjur. "Idan ka sake hauka ya kwashe ka, ka sake Ummu Hadiyya. In sha Allah zan aureta tunda baka bukatarta a rayuwarka ka sake ta ka ga ikon Allah!" "Deen!" "Eh zan mata da abotarmu, alakarmu zan aure ta a matsayin da duk tazo min kuma zan yanke mu'amala da kai saboda ex-wife dinka ce kada ka ketare min iyakata, sai ka zauna da ƙaruwar da take biyo namiji har gidan aurenshi akan idanun Matarshi, idan da kasan wacece yarinyar nan ko hada numfashi da ita ba zaka yi ba, Aliyu na gaya maka gaskiya ne domin ba zan koma baya ina cin dudduniyarka ba! Ka sani ba iya kanka kake jefawa bala'i ba innocent soul din da kake jefawa masifa shine tashin hankali, Tafida zina ko kusantarta masifa ce balle kuma Allah ya baka mace ta gari da take kara kame kanta, idan da yau duk abinda zaka yi iya kanka zai tsaya da sauki idan ita wani yayi attempt dinta saboda ka kusanci zina kayi mata adalci? " "Amma kasan ban tab'a zina ba ko?" "Taya xan sani bayan ka ajiye mace a dakinka kuna kwana daki daya, ita matarka ta sunna ka mai da ita hoto, kamar yadda kake da lafiya da kuzari haka take da shi kai ba Jahili ba amma kafin jahili jahilci zan gayawa Abbanka yasan irin ukubar da kake ganawa Ummu, tunda kai ka tashi daga sahun mutanen kirki ka koma sahun kasikai azzalumai masu cutar matayensu da danginsu."
"Deen " dakatar da shi yayi yana faɗin. "Ban gama ba, ita yarinya har abada ba zaka tab'a samun biyunta ba, ta rufa maka asiri ta saka ka boye macen da ta zo mata dadiranci sannan kayi tsammanin yarinyar nan har yau bata isa ta baka abinci ka ci ba, Yarinyar da ta rufa maka asiri idan wata ce tona maka asiri zata yi a gaban mahaifinka, amma ta nunawa maka kai mutumin kirki ne abin da ta gani ba zai hana ta rufa maka asiri ba, Ummu Hadiyya mace ce ya kuma me tarbiyyar da ake bukata don Allah idan ba xaka zauna da ita ba da kayi ta bata wahala ka sakota ni zan zauna da ita


Daga haka ya bar shi sake, sai dai yadda ya fadi haka sai yaji ranshi ya b'aci ba fa akan Ummu ba a'a shi kawai babban matsalarshi aibanta Saadi baby da yayi, bayan tafiyarsu ne ya shigo ya dauki abinci ya kai mata dakin, tana murmushi ta ce mishi. "Abba ya tafi ne?" "Eh ki koma gida yau, zaman ya isa haka!" "Ya Ali!" "Nace ki koma gida!" Jin haka yasa ya shiga hada kayanta tana kuka. "a yau xan koma Maiduguri!" Kallon agogon dakin yayi yana shafa kansa. "Zuwa gobe ki wuce!" Sannan ya fita, har dare bai kuma yin wani abu ba asalima ban san ya suka kare ba, washi gari da sassafe naji tana ta kuka tare da surutai, domin cikin dare da na fito na dibi tea saboda muran da yake damuna a parlour na ganshi ya kwanta, na dauke kai nayi kitchen. Ko bayan tafiyarta ban yi abin karyawa da wuri ba, domin nasan iya cikina ne. Sai wurin sha daya na dumama tuwon jiya naci, da rana nayi shinkafa da wake, na ci tare da barin sauran zuwa dare don nasan baya shigowa sai da barcin, haka muka cigaba da rayuwa babu me shiga harkan wani sai dai akwai wata yarinyar me suna Tina da ta dame mu da zuwa, idan tazo tun safe sai ta kai har karfe goma kafin ta tafi, na farko Ita ba musulma ba balle nace ba wani abu. Sai dai dake ban bata fuska ba. Tana zaune zama take a parlour idan yana gida suka yi hira, haka zata gayyato kawayenta sun mai da ni mai girkinsu. Sannan ban isa na ce yau ina ciwo ba domin Tafida da bai da uzuri yanzu sai ya fara fada. A hiransu na fahimci Babanta kusan gwamnati ne, sannan yana da kusanci da shugaban kasa, bayan nan Baban Tina Yana son Tafida musamman da yasan waye Uban Tafida, haka yasa shi kara son shi. Sannan wani abu da ya yarinyar tana da hankali da nutsuwa matsalarta shine yadda ta maida ni mai girkinsu.


Ranar wata Juma'a ina dan wake tazo, tana buga kofa naje na bude mata, "Amarya yau na zo miki da wani abu canka?" Murmushi nayi nace mata. "Kin ga na bar abinci akan wuta shigo!" Har ga Allah na gaji sosai, kamar na gudu gida haka nake ji, kwashe dan waken nayi na zuba a ruwa na karasa sauran jifan. "kin ga wannan wata kawata ce a kamfanin Maggi star, wai za ayi girki na gasa arewa da kudu shine na amsa miki Form!" Kallont nayi bakina sake."kika amsa min?" "Eh mana taya xan biya ki hidimar da kike mana, kin ga har da kyauta na san Amarya You Are the best, kuma abincinki ko uban waye yaci zai sara miki, manyan masu girki ake gayyata shine na gayawa Aliyos yace babu ruwanshi." Murmushi nayi tare da cewa. "Tow bari na gani xan gayawa Alhajinmu!" "Yawwa next week za a kira ku!" Ta mika min takardan yarinyar nan ba karamin kudi ta kashe ba, sai naji kunya ya kama ni. "dubu dari uku kudin shiga gasar!" "Kina tsammanin baki fi karfin haka bane?" "Na gode!" Na fada bayan na ajiye takarda na nufi daki na ji bakiɗaya kunyarta ya ishe ni. Na fito na zuba mata abinci, tana ci dai ga Tafida na shiga kitchen na dauke mishi takardan na ajiye mishi. "Me yasa kika kashe kudinki tina akan inuwar alli, ina ruwan kukun guntaye, don Allah dube ta da kaɗan tafi Mug tsawo!" "Aliyos wannan cin fuska ne." "I'm just joking ne fa!" "Wannan ba joking bane mock dinta kake, maybe a idanunka ne kake kallonta haka, amma tana da mutunci da sanin darajar kowa tunda nake zuwa bata tab'a gajiya da ni ba, sannan ko ya na kawo mutane zasu ji dadin zuwan Please bayan ni kada ka kara cin zarafinta haka, domin ni idan aka min zan iya mutuwa balle ita da haka.bai dame ta ba which mean ta saba da cin fuskarka. Addininku ya bawa mata kariya, ya kuma girmamasu. Sannan ya nuna musu muhimmancin mutanen, kai kana da kirki da mutunci amma Matarka ta wuce tunanin ka, da ce ni ce kai na sameta har abada ba xan yi wasa da damar da na samu ba, ita kamar haske ce a gidanka a lokacin darkness, tana da kirki Please ko ba yanzu ba kada ka taba yarda wani abu ya rabaka da ita don ba zaka tab'a samun kamarta ba" kasa magana yayi yana jin tinah har ta gama suka yi hira ta bar gidan, ina zaune ya d'aga labulen ya watsa min takardun yana faɗin. "Idan ma asiri kike yiwa mutane tow ki daina domin wallahi xan miki ba dad'i....
*Ni jikar na tsalle kwad'o yace. inji Aunty Hadiza 🤣😂 Tafida baka jin magana wallahi asiri kuma dai!*
#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


14


Hadiye yawu nayi ina kallonshi, kafin na ce mishi. "Kayi hakuri idan kace ma kada na shiga gasar zan hakura da shi!" Wani wulakantaccen kallo ya zuba min yana me kara shigowa cikin dakin. "Da kiyi da kada ki yi daya ne a wurina ko a kwalar rigana, ke idan kin son ki tafi tsirara babu abinda ya dame ni." "Na gode!" Na fadi haka tunda na samu wannan damar nayi alkawarin zan yiwa Aliyu biyayya koda kuwa zan rasa rayuwata ne, don na kara gane wasu daman baka tab'a samunsu haka kawai sai ta wani dalili me karfi dalilin kuwa shine auren Tafida, don haka na yarda da cewa Allah yana tare da ni shine wannan damar yazo min, bayan fitar shi na kira Mamana na gaya mata abinda yake faruwa, Abinda ta fara tambayata. "Mijinki ya amince?" "Eh ya amince!" "Tow ki kira Babanshi ki gaya mishi sannan ki gayawa Babanki da Babanku Bulama!" "Tow Mama!" Haka kuwa nayi na gayawa Abba yayi min addu'a sosai, sannan na kira Baba Bulama na gaya mishi, ya tambaye ni Aliyu ya amince nace eh, sannan yayi min addu'a. Can na kira Babana sai da muka yi dogon hira har katina ya kare sai gashi ya kuma kirana. "Babana!" "Na'am Ummuna!" Ya fada yana murmushi. "Dama wani gasar girkin zamani ne aka saya min Form din shine na ce bari na gaya maka ayi min addu'a." "Masha Allah Mijinki ya amince?" "Eh ya amince!" "Tow ya za ayi shi zai na kai ki ko kece xaki na zuwa don nasan ke bakuwa ce a abuja!" "Eh gaskiya yana fita da wuri ni kuma ban san yadda xan na fita ba." "Tow shi kenan zan nime shi muyi magana!" "Tow Baba!" Haka muka yi sallama, bayan Isha ina zaune na ji ana buga kofar gidan, zuwa nayi na bude Sa'adiyya ce, ban yi mamaki ba na bude mata kofar ta shiga tana yatsina fuska. Ban ce mata kome ba, wurin karfe goma ya shigo gidan ina dakina, buga kofar yayi na tashi na buɗe. "Uban waye ya ce ki hada ni da wadancan tsofi ukun!" "Kayi hakuri na gaya musu ne amma ba zan ƙara ba." "Sakarya kawai!" Ya fara tijaran da ya saba, koda yake kwana biyu bai yi ba amma yau kamar jira yake Sa'adiyya ta dirko gidan, haka ya gama ina bashi hakuri yana kara tinzura karshe na makale jikin bango kamar zai dake ni, yana gamawa ya fita. "Ya Aliy!" "Sa'adi yaushe kika zo?" "Dazun nan man!" Washi gari Tina tazo ta amshi Form din ta ga ban cika ba, ware idanu tai tare da cewa. "Aliyos bai cika miki ba ne?" "Eh kin san yana busy!" Amsa tayi ta buɗe jakarta. "Amma naji kamar kina mura!" Na tambaye ta. "Eh jiya nasha ice cream ne!" "Bari na dafa miki ruwan zafi da yar farfesu!" "Amarya bar shi na koshi!" Ya fada tana kallon dakin Tafida da Sa'adiyya ta fito. "Wacece ita?" "Yar uwarsa ce daga Maiduguri!" Dauke kai tayi tana wani haɗe rai. Kitchen na nufa na hada mata kayan kamshi ma dafa mata shayi, sannan akwai sauran nama da yake sayowa na mata farfesu me ruwa ruwa. "Amarya ya kamata ace kina da babban frij, wanda zaki na ajiye kayan abinci. Ba sai kullum za a na girki ba!" "Tow Tina!" Na zauna, ta mika min takardan har ta cike wurin girki ne ta ce min. "Zaki dauki na gargajiya ne domin an fi samun na sa'a akanshi." "Duk wanda kika zab'a min zan amsa!" Ina jin motsin Sa'adiyya a kitchen, har ta gama abin da take ta fito ta wuce dakinshi, dama ya tafi aiki. Kitchen na shiga nayi mana shinkafa da miya sai salat. "Amarya zaki kashe ni da dad'i." Haka muka wuni da dare aka zo daukarta, ta tafi da takardan, weekend bata zo ba duk sai na damu domin tun ranar Alhamis juma'a asabar da lahadi bata zo ba, yammacin Lahadi ina zaune ya shigo dakin yana me tsayawa a kaina. "Ki saka kaya ina jiranki a waje! Kuma kada ki sake ki saka min burma-burman kaya." "Tow!" Na fada sannan na mike, kayana na duba babu wanda yayi yadda yake so, sai kayan dinner da aka min shi bubu ne na saka tare da daura zani akan rigar. Sannan na dauki dan kwalin na kafa dauri. Mayafi fari na saka da takalmi fari saboda lacce din fari ne tas, kwali da man baki na saka fuskana kuwa sama-sama na shafa mishi hoda, na fito. A parlour na same shi da Sa'adi, kwashewa da dariya tayi tana faɗin. "Yau an saka a cuci maza kenan! Don wannan boons din ba naki ba ne!" Yana jin mu bai ce kome ba, haka na tsaya kaina a sunkuye. Domin naga yana shan abu ne da itama shi take sha. Mikewa yayi yana faɗin. "Muje!" Haka na bi bayanshi, abin mamaki a harabar unguwar muka samu Mahmoud ya zo, yana idanunshi kur a kaina. Parking yayi a gefen motar Tafida ya fito yana kallona. "Man ina zaku?" "Kasan yar gidan Mr Kayemi Tina ita ce yau take birthday ta ce na zo mata da wannan abin!" Murmushi Mahmoud yayi ya ce mishi. "Ko na raka ku ne?" "Me zai hana sai ka tawo da Sa'adi!" "Ba dai a motatta ba, domin na tsani yarinyar nan bata da kamun kai!" Ya fada yana hade rai. "Please mana!" Ya fada yana nufar motarshi. "Na gaya miki gaskiya! Ke tauraruwa ce a cikin taurari, haskenki daban yake shi yasa zan biku na kare martabarki kada wasu , su kallar min ke!" Ya fada yana rike da mayafina, kwace mayafin nayi kafin Tafida ya juyo ya ganmu. "Man bari na shiga na mata magana."
Kin yarda nayi mu hada idanu, har na shiga motar, muka bar gidan yadda Tafida yayi ta min kashedi kada na je nayi rawan kai, abubuwa iri-iri babu wanda bai min ba.
**
Lokacin da Mahmoud ya shiga ya samu Sa'adiyya ta shiga dakin Ummu zata saka abu. Kamar ance ya d'aga labulen kawai ya ganta tana niman inda zata saka abin. "Da kuwa naci Ubanki, munafika fito kafin na takaki." Yadda ya hauro mata yasa tayi baya, ya amshe layyar ya jefa a toilet ya tura ruwa. "Yar iska kika sake gobe na same ki a gidan nan sai na baki mamaki, kuma ki shirya mu bi bayansu jaka kawai!" Haka ta fita jikinta a sanyaye, ta shirya suka fita, tasha zagi da harara. Har gidansu Tina.


Lokacin da muka isa ana yiwa Tina kwalliya, janyo ni tayi tana faɗin. "Itama ayi mata amarya ce!" Murmushi nayi kawai,"shine baki gaya min zaki yi bikin Birthday dinki ba!" "Amarya ba zan so kiyi aikin wahala ba!" Ta fada tana murmushi ana gama mata aka yi min kwalliyar dan daidai. Ba yawwa ba hayaniya, a tare muka fito bayan an dauke mu hotuna muka zo wurin Birthday dake mayafina yana kafadana. Idanun Mahmoud yana kaina, duk inda nayi yana bina da idanu. Sa'adiyya abin ya d'aga mata hankali musamman yadda Tina take hada ni da kawayenta, take gaya musu ai ni matar Aliyos ne, haka suka yi ta taya ni murna tare da bani labarin kirkinsa. Haka aka tashi taron wurin karfe goma sha daya, na gaji don ma ban yi sake Sallah ya kwace min ba, don da nace zan yi sallah sake kiran me kwalliyar tayi bayan na idar da sallah ta gyara min fuskana. A hanya muna dawowa yake gasa min magana. Ni dai ban kula shi ba, don barci nake ji. Ban san me ya hau kanshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login