Showing 27001 words to 30000 words out of 411050 words
Chapter 10 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
,( ya tsora ta su )
Ai kuwa koh dakika ɗaya ba'a ƙara ba falmata ta tattara fiye da rabin zanin ta tare da sanya hannayen ta duk biyu tana laluben daga inda ta fi jin damshin fitsarin ta sanya zanen ta tana guza gurin tare da gogewa da dukkanin ƙarfin ta , idanun ta suna zubar kwallar buguwar da raunin ƙafar ta yayi dalilin wurgi da ita da aka yi , "
Da gudu yakaka ta karaso ta sanya hannayen ta biyu ta ɗauke hannun falmatan , " falmata ki bari zaki yaga zanen ki bari na goge ," ba tare da jinkirin kome ba ta warware ɗankwalin kan ta , " tare da sanya guiwar ta a ƙasa ta fara goge wurin ," lokaci guda hawayen da suka taru cikin gurbin idanun ta suka fara sauka , "
Yakaka zan iya gogewa nima dai-dai lokacin da ta kai hannun ta tana lalubar jikin yakakan , " zan iya... Sauran kalmomin bakin ta suka maƙale lokacin da hannuwan ta suka sauka akan lallausan yala-yalan gashin ƴar uwar ta, Yakaka ina ɗankwalin ki ? A gaban namiji kike zaune babu rufin kai ? Kwance ɗankwalin kan ta tayi lokaci guda ta rufawa yakakan a bisa kan ta , cikin sauri kuma ta sake tattara bakin zanen ta tare da cigaba da goge kafet ɗin tun karfin ta ,
Ji yayi idanun sa na son zowa da ruwa , baya raba ɗaya biyu tausayin su ne ya mamaye ransa , sanin da ya yi yana daga cikin mutane masu raunin zuciya ," a hankali ya fara taku har ya ƙaraso cikin office ɗin ,"ba tare da ya dubi fuskar hamza ba ya ce kai ku tashi haka ku tafi abun ku ya isa , nan gaba kuma ku dunga lura da wurare kun ji koh ?
Da sauri yakaka take gyaɗa kai lokaci guda kuma ta fara yi masa godiya ," ɗan gyaɗa kan sa yayi idanun sa yana kan fuskar falma da shatin marin da ta sha ya kwanta rudu-rudu .
Kamo hannun falmata tayi ta ɗago ta lokaci guda kuma ta zare ɗankwalin falmata daga kan ta tare da rufa mata shi daga kan ta zuwa kafaɗun ta,( da yake ɗankwalin na da girma kaɗan )
Yakaka ke da me zaki rufe kai ? Ba tare da ta jira amsar yakakan ba ta ɗaura hannu da nufin sake cire ɗankwalin ta mayar mata ,"dafe hannun falmata yakakan tayi , idanun ta na cigaba da son taro ƙwalla saboda kumburar da taga fuskar kanwar ta yayi , ba tare da tace kome ba ta dora hannun falmatan bisa kan ta , anan falmatan taji jikakken ɗankwalin da yakaka ta ɗaura akan ta wanda ta goge wurin nan da shi ," da sauri falmata ta buɗe baki da niyyar sake cewa wani abun ," katse ta yakaka tayi cikin cewa mu tafi falmata ,"
Taku suka fara yi hannayen su saƙale da na juna ," sun zo dai-dai kofar yakaka ta maida duban ta , kan sa sarƙewa idanun su yayi cikin na juna ," kallon-kallo suka yi na ƴan dakiƙai ,'kowannen su zuciyar sa na bugawa da yanayin da take ciki , "
A bangaren sa haushin su duka biyun ne fal a ran sa! Tare kuma da jin takaicin me ya sa suleiman bai bar shi ya hora waɗan nan gidadawan ba son ran sa ta yadda gaba baza su sake gigin yin ganganci makamancin wanda suka yi a yanzu ba , yayin da wani bangare me rangwamen rinjaye yake jin wani abu me kama da bai fa kyauta ba , musamman a yanzu da ya kalli cikin ƙwarar idanun ta masu ruwan zaiba-zaiba ,sai ya ji wannan yanayin kamar yana sake ƙarfafa acikin ran sa ,! Tsaki ya jaa a lokaci guda yana mai kau da kan sa ,
Ga yakaka kuwa ,' lokacin da take kallon ƙwarar idanun sa baƙar shaida take yi masa tare da jin tsanar sa tana mamaye baki ɗayan zuciyar ta tana jin shine mutum na farko da ta fara tsana a cikin rayuwar ta , sakamakon rashin tausayi ƙarara da ya nuna a gare su uwa uba , shi ɗin ne mutum na farko da ya taɓa lafiyar ƙanwar ta abar ƙaunar ta akan kuskuren da ta aikata shi cikin rashin sani ,ba tare da ya dubi naƙasar da ke tare da ita ba ," ɗauke kan ta tayi lokacin da suke sanya kafafun su domin barin ofishin ,
Baku ji ba ," waiwayowa yakaka tayi lokaci guda tana me jin faɗuwar gaba ," a hankali ya ƙaraso hannun sa a aljihu , zare hannun sa yayi daga aljihun ya fiddo da sabuwar naira dubu ɗaya ," ungo ku sayi hijabi ku dunga sanyawa ," ganin basu ƙarba ba ya sanya yayi ƙasa da hannun sa dai-dai hannun falmata ya taɓa hannun nata da kuɗin cikin buɗe muryar sa yace ,"
Ƙarbi mana ,' duk da cewa falmatan ba gani take ba hakan bai hana ta juya fuskar ta inda take jin hucin numfashin yakaka ba ," da alamun neman izni bisa fuskar ta ,"
Mungode Allah ya saka da Alkhairi amma baza mu karbi kuɗin ka ba a wurin Allah muke neman taimako ta hannun gwamnati muna tunanin gwamnati ke da Alhakin ɗaukar nawin mu ,? Dan haka baza mu ƙarbi kudin ka ba mun gode sosai ," cewar yakaka daga haka ta jaa hannun falmata suka ƙarasa barin wajen.
Ɗan murmushi suleiman yayi lokacin da yake bin bayan su da kallo , lokaci guda yana jin tausayin su yana ratsa shi , gefe guda na ran shi ji yayi kyakyawar tarbiyyar da ya ga alamun ta a tare da su ta burge shi , juyawar sa yayi bayan ya maida kuɗin sa aljihu ,"
Amma wallahi hamza baka kyautawa a wasu lokutan ,abun da kayi ga waɗan nan yaran sam bai kamata ba , baka ganin ƙauyawa ne ? Ya kamata ka dunga rage zafin zuciya tare da tausayawa na ƙasa da kai Dan Allah .
Mts toh uba na idan ka gama min faɗan sai ka fita ka samo Cleaner ya zo ya goge wurin tun da ka sallami masu ɗauke da alhakin gyaran kaji koh waliyyin Allah ?
Yakaka , Falmata wanka kuka yi ne naga jikin ku du a jiƙe haka ? Falmata meya ya same ki haka fuskar ki a kumbure faɗuwa kika yi a banɗakin ?
Ganin sun wuce basu tanka mata ba ya sa yagana bin bayan su tana me sake ƙare musu kallo daga sama har ƙasa ," a ranta kuwa ta fara jin haushin irin halayyar da suke gwada mata a wasu lokutan ,' musamman ma dai falmata ,
Yagana meyasa kike yin ƙarya ? Tun muna yara maman mu ta nusar da mu rashin kyaun faɗar zancen da ba gaskiya ba ,meyasa kika ce mana can wurin banɗaki ne alhalin kin san ba haka bane ? Dubi jikina dubi jikin falmata kuma ki dubi fuskar ta ? Duk sanadin kin faɗa mana zancen da ba gaskiya bane kika jawo mana wannan masifar ya zaki ji idan mu ne muka tura ki cikin haɗari irin haka ,?
Cikin nadama yagana take kallon fuskar yakaka wacce take bayyana tsantsar bacin rai a lokacin da take sanya sauran guntun ruwan da ta ɗibo tana wankewa falmata jikin zanin ta ,"
Kuyi hakuri yakaka na ɗauka banɗaki ne ganin wani mutum ya fito daga ɗakin yana gyara wondon sa da buta riƙe a hannun sa ,
A fusace falmata ta katse ta wacce ta zo har wuya da bacin ran yagana domin ita ce ainahin sanadin faruwar kome ," amma ai yagana cewa kika da farko an gwada miki can wurin ne banɗakin ? Meyasa kike haka tun farkon fara tafiyar mu tare zantukan ki dayawa ba gaskiƴa kike faɗa ba, haka kika ce mana kin san hanyar maiduguri ? Ba domin Allah ya haɗa mu da mutanen dajin nan ba(fulanin da suka taimake su ) da ba mu san halin da zamu shiga ba ," yagana yana da kyau mutum ya dunga faɗin gaskiya kome wuyan ta .
Cikin takaici yagana take kallon falmata wacce take daga zaune idanun ta suna kallon gefe ," tayaya za'a yi ƴar karamar yarinyar da ta girmewa , ta zauna tana gaya mata magana son ran ta ? Tana yi mata tsawa da ihu irin haka kuma ƙarin abun takaicin ma makauniya ce miskiniya ,"
Dakata falmata daga yau sai yau ni ba sa'ar ki bace dan haka kar ki sake cewa zaki min faɗa da tsawa ," meyasa ku da kuka shiga wajen kuka ga ba banɗakin bane ba ku fito ba ,? Koh kuwa ba tare muka zo wurin ba ɗazun nan ? Da dan kawai nayi kuskure zaku hau kaina da faɗa yayar ki tana min ke ma kuma kice zaki min kamar ku kuka kawo ni garin ?
Cikin sanyin jiki yakaka ta bi bayan yagana da kallo wacce bayan ta gama mayar musu da magana ta kaɗa kan ta ta bar wajen ba tare da ta sake ce musu ƙala ba , ta koma nesa da su ta zauna , alamu sun nuna taji haushin faɗa mata laifin ta da suka yi ,
Wanda ita kuma yakaka sam hakan bai mata daɗi ko babu kome cikin kwanaki biyun da suka yi tare da yagana taji daɗin samun ta a matsayin ƙawar da suka shigo sabuwar rayuwar su a tare , kuma ƙwarai yagana tana kokari wurin kyautata musu musamman ma dai falmata ," toh sai dai har ga Allah ita bata son hallayar da ta lura yagana ta na da ita na ƙarya , ba dan kome tayi mata magana ba sai dan tana son yagana ta bar hallayar dan ba hallaya bace mai kyau , duk da haka cikin ran ta ta ƙudurci aniyar bata hakuri tun da ta ga tayi fushi, sam ita baza ta so rabuwar su ba ,ƙwarai take bukatar ƙawa cikin rayuwar ta a yanzu wanda a tun tashin ta bata damu da ƙawaye ba , falmata ita ce ƙawar ta abokiyar wasan ta , amma a yanzu da girma ya hau kan ta ya zama dole ta nemi wata ƙawar bayan falmata da zata dunga taya ta koh da da shawarwari ne domin inganta rayuwar falmatan .
ƙamshin abincin ne ya daki hancin su da ya sa ba shiri yakaka ta bi manyan farantan da aka wuce da su da kallo nan take yawun bakin ta ya tsinke ganin shinkafar da aka wadata kan ta da baƙar miyar da tashin farko ba za'a tantance jar miya ce koh kuwa wacce irin miya bace , amma da yake cikin su ya jima rabon sa da abinci sai abincin yayi kyau matuƙa a idon yakaka ,"
Yakaka ƙamshin abinci nake ji ? Muje mu ci mana koh ba namu bane ? Falmata ta ƙarasa zance tare da haɗiyar yawun da kamshin abincin nan ya sanya shi tsinkewa ,"
Wucewa aka yi da abincin inaga rabawa ake dan naga gashi sai kaiwa ake wuri-wuri ," inaga mu ɗan jira za'a zo kan mu ,"
Miƙewa tsaye yagana tayi tare da ƙarasawa bakin kofar ɗakin da ɗazu ta shiga tayi tambaya wanda yanzu ta ga an shiga da farantan abinci huɗu ,"
Dogarewa tayi daga bakin ƙofar tana ganin yadda matan nan kusan su arba'in da ƴaƴan su ,suka tasamman farantan abincin nan huɗu haiƙan da suke tashin tiririn zafi .
Hannu baka hannun ƙwarya suke auna abincin nan zuwa cikin bakunan su yayin da ƴaƴan su waɗan da wasun su basu wuce ƴan shekaru biyu ba zuwa ƙasa , su ma ba'a bar su a baya ba, kokawa suke da tiren abincin nan wasun su hannu bi-biyu suke jefawa cikin tiren basa koh nuna alamun jin zafin abincin , na bakin su yana komawa ciki sakamakon ƙona musu harcen da abincin ya ke ,
Cikin mintocin da suke ƙasa da biyar babu abincin nan babu alamun sa tamkar dai gonar hatsin da mayunwatan tsuntsaye suka sauka a kai suka tashi , haka kan farantan nan suke babu koh ƙwarar shinkafa ɗai , sai tashin tiririn da har yanzu da suka kammala cin abincin bai kai ga hucewa ba , ƴaƴan su suna ta sanya harce suna tanɗar jikin faranti tamkar zasu haɗa da farantin su lanƙwame .
Sauke ajiyar zuci yagana tayi lokacin da suka haɗa ido huɗu da matar da ta yi mata kwatancen banɗaki a ɗazu "tana ta faman tanɗar yatsun hannun ta lungu da sako tana zura harshe tana zaƙulo duk wata guntuwar miyar da ta rage mata a hannu ," yarinya ke ba anan za ki ci abinci ba ki tafi ta can bayan tantunan da suke farfajiya anan ƴan mata sa'o'in ki suke kiyi sauri ki tafi kar a cinye a bar ki , cewar matar nan da yanzu ta kammala suɗe hannun nata ta goge hannun akan ta .
Ba tare da tace kome ba ta juya gami da kai hangen ta ga harabar wajen can ta hango masu rabon abincin nan sun nufi manyan tantuna biyun da suke haɗe da junan su daga gefe ," da sauri ta ɗiro daga kan dakalin barandar har ta ɗaga kafafun tayi taku biyu sai ta waiwaya karaf suka haɗa idanu da yakaka wacce duk ta bi ta damu da fushin yagana , hakan ya sa duk wani motsin yaganan yake kan idanun ta ,"
Yafitar su tayi da hannu lokaci guda ta buɗe murya ", Yakaka ku zo mu je mu ci abinci a can ," ba tare da ta jira amsar su ba ta ɗaga ƙafafun ta cikin sauri ta nufi tantin da ta ga an kai abincin nan cikin ran ta cike da addu'ar Allah ya sa ba'a riga an fara ci ba .
Da sauri ta ruƙo hannun falmata da jin zancen abincin nan ya sa cikin ta ya sake yin ƙarar yunwa ,
Mu yi sauri mu je falmata !
[6/24, 9:58 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association
*MAFARI......*
( _Hargitsin rayuwa_ )
*umm'muaz*
6
Jugum suka yi a ɗosane tsakankanin matsin ƴan mata sa'o'in su da waɗanda suka fi su , da ma ƙasa da shekarun falmata kaɗan "bayan kammala baɗakalar wawason abincin,.
Yakaka ni fa koh rabin-rabin yunwar da nake ji bata mutu ba ,wannan abincin sam bai isa ga uwar hanji na ba , me zai hana mu nemi wurin sayar da abinci mu sayi wani da kuɗin hannun mu ?
Kiyi hakuri falmata mu jira na dare tun da kin ga yanzu la'asar yayi ,idan yaso da daren sai mu shirya salon cin abinci , tun da kin ga dai yadda muka sha gumurzun kokuwa kafin mu samu ƴan lomomin da yanzu suke cikin mu .
Toh yakaka ,Allah ya kaimu ɗaren .
Cikin wani irin yanayi na tausayawa yagana take kallon yakaka wacce koh lomar abinci ɗaya bata sa cikin bakin ta ba , domin duk kokuwar da ta sha idan ta ɗebo abincin maimakon ta sanya a bakin ta , lalubar hannun ƙanwar ta take ta zuba mata ,
Cikin neman son su shirya bayan ƴar hatsaniyar da ta shiga tsakanin su ,"yakaka ta sakarwa yagana murmushi tare da riƙo hannun ta , mun gode yagana ba domin kin kira mu ba ,"da baza mu samu abincin ba"
Murmushi yagana ta mayar mata ,"babu kome yakaka mun riga mun zama ƴan uwa "
Waiwayawa tayi ga wata budurwar da take zaune kusa da ita "ta ɗuƙufa sosai wurin soka allura da zarewa a jikin hular da take ɗinkawa ",
Dan Allah kawata koh zaki gwada mana banɗaki muna so muyi sallah? Cewar yagana
Ba tare da ta ɗago daga yin ɗinkin da take ba tace ,idan kuka fita kuyi hannun ku na dama ku miƙe sosai zaku tarar da banɗaki a jere amma ku kula hudu daga cikin takwas ɗin basu da kyau duk sun tsage sun farfashe ba'a amfani da su dan gudun su rufta da mutum .
Godiya sosai suka yi mata dai-dai lokacin da suke miƙewa .
Da ido yakaka take bin farfajiyar da take dauke da banɗakunan da kallo cikin wani irin yanayi na tsantsar kyankami domin duk da kasancewar su mutanen ƙauye ," suna da wadatar tsafta basa barin muhallin su cikin dagwalon ƙazanta ,"
Cikin ɗaukewar numfashi falmata tace kai yakaka wannan banɗaki da wari yake da alama babu wadatuwar tsafta , ni dai gwada min inda zan yi alwalar .
Koh kafin ta buɗe baki "yagana ta karaso wurin hannun ta riƙe da manyan gorar ruwan roba wanda mafi akasarin mutanen wurin suke amfani da ita a madadin buta .
Itama turus tayi ganin tsimi-tsimin "bahaya" a farfajiyar wurin wasu an turbuɗe da ƙasa wasu kuwa muraran suke a sarari ƙudaje tare da sauran ƙwari suna sukuwa a kai .
Da sauri ta kawar da kai tare da tsirtar da wani mugun yawun da taji ya taru mata a baki tace ,"yakaka anya wurin nan kuwa ya dace da wajen alwala ? Gaskiya ku zo mu koma
Bata gama rufe baki ba ,"taga wata mata da goyon ƴar ta, ta zo tayi ƴar tsallaƙe ta tsallake tarin kazantar dake wurin tare da shiga ɗaya daga cikin banɗakin wajen ,"cikin ƴan dakikai kuma wata mace ta fito daga ɗayan banɗakin .
Yagana babu yadda zamu yi kin ga kowa dake nan wurin da nan ɗin suke amfani , dan haka muma dole mu bi ayari .
Tana rufe baki ta saki hannun falmata gami da tattare zanen ta , ta tsallaƙa cikin dauke numfashi ta nufi bandakin ,"tare da cewa falmata ki jira ni anan kar ki motsa ",
Bayan sun idar da sallolin da ke kan su da suka yi ta a ɗanɗaryar ƙasar kan baranda ,cikin rashin wadatuwar suturar da zasu suturce jikin su kamar yadda ya kamata a yayin sallar ," duk da daman ba wani sani suke da shi sosai game da ibadar ba .
Tsumu suka yi kowaccen su cikin taɗin zuci ,"
Ƙarar jiniya da tayi musu kama da