Showing 228001 words to 231000 words out of 411050 words

Chapter 77 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14356

lafiyar da suke zuwa wajen ta na ciki amma bai gan ta ba.

Bai kuma tambayi matan da ya tarar a ɗakin ba da ko alamu basu da nasaba ta jini da ita , dan haka sai ya koma.

kichiɓus suka yi da matar da ya baro a waje ,

," ka same ta....

Da hannu ya dakatar da ita , alamar tayi masa shiru  ya wuce cikin ran sa yana bawa kansa tabbaci babu shakka Khaalty Rahima ce , ita ya gani

Ƙanwar mamar sa ce da kusan tare suka tashi  , tunda ya buɗi ido ya gan ta a gaban iyayen sa kafin daga baya kaddarar da bai san ta mecece ba ta gifta tsakani ta raba su .

Sai dai koma menene yana ganin yazo ƙarshe , zai bi kuma duk hanyar da ta dace domin dai-daita rayuwar iyayen nasa daga walagigi .

Kai tsaye wajen motar sa ya nufa zuciyar sa cike da tunanin hanyoyin da zai bi domin gano haƙiƙanin rayuwar da Khaalty Rahima take tsawon shekarun nan, shin ita ce ko kuwa ba ita bace ?

Khaalty Rahima bata da wata larura da ta shafi ji ko gani , ance wannan kurma ce ??

Tada motar sa yayi , zuciyar sa maƙare da wasi-wasi , wajen Amne yake da burin zuwa a yau ɗin to amma yadda yake jin zuciyar sa a yanzu bai son kome illa ya kaɗaice .

Yana isa gida kai tsaye sashin su Rahima ya nufa saboda yunwa da yake ji tana ƙwaƙular ƴan hanjin sa ,

Da sallama ya shiga falon , idanun sa suka sauƙa akan ta da ta juya baya tsaye a gaban hoton ƴar yarinyar da bai kai ga rarrabewa ɗiyar wacece a tsakanin Hafsa da Zainab ba ?

Zama ya yi akan kujera tare da yin baya da kan sa ya jingina da kujerar

"Rahima idan akwai abinci ki kawo min , idan kuma babu ki dafa min Noddles yanzu ina jin yunwa sosai ki haɗo min da tea .'

Numfashin ta ne yayi sassarfa lokacin da sautin muryar sa ya sauƙa a kunnuwan ta,

shikenan addu'ar ta bata karɓu ba , domin kuwa tunda Rahima ta tabbatar mata da cewa hutu ya zo zai ya koma garin Abuja inda ya koma aiki da zama baki ɗaya tare da matar sa ,

take addu'ar Allah ya raba ganawa a tsakanin su har ya gama hutun sa ya koma .

To sai dai addu'ar ta ta a iya ranakun jiya da shekaranjiya tasirin ta ya tsaya , domin ga shi yau ko azahar bata yi ba Alƙadarin ta ya karye ,

Ita kunyar sa take ji , kunya mai tsanani kuwa , kunyar abunda ta aikata , me zata ce masa ? Da wanne ido zata dube shi , anya duniya da gaskiya ita tana da tsaurin idon sake kallon sa ?

"Rahima baki ji na ?

Satar kallon inda yake Yakaka tayi ta gan shi har yanzu yana yadda yake kan shi a kwance bisa kujerar ya miƙe ƙafafun sa .

Ba tare da ta juyo ba ta kama hanya da ƴar sassarfa da nufin barin wajen tsawar da ya daka mata ya sa ta dakatawa tana jin yadda zuciyar ta ke tsananta bugu .

"Rahima yaushe kika zama haka , marar ɗa'a ? Ni nake yi miki magana kina tafiyar ki ?  Zo nan .

Juyowa tayi a hankali , ta tsugunna a wajen da take , muryar ta tana sarƙewa tace

"Ba-ba Rahima bace ni ce Yaya Dakta .

Tamkar a ire-iren shuɗaɗɗun mafarkan sa da ya saba yi a shekarun baya ya ji sautin muryar ta , dan haka ya buɗe idanun sa da suke lumshe a hankali .

"Rahima zo nan nace "

Ya sake maimaitawa cike da burin son kawar da mummunan tunanin da ya bijiro masa da sautin ta a yau .

Ni ce Yaya dakta ta sake maimaitawa tana kif-kifta ido daga inda take .

A wani irin yanayi ya yunkuro kamar an tunkuɗo shi , ya zauna da kyau lokacin da yake ɗora idanun sa akan ta , da ta sunkui da kai ta ƙi kallon sa illa bakin hijabin ta da take wasa da shi a hannun ta ,

Ita ce ? Me ya dawo da ita ? Me ta zo yi nan ?

"Ke ce wa ?

Ya furta hakan da wata buɗaɗɗiyar murya me amo da ya sa Yakaka yin rau-rau da idanun ta da suka kawo ƙwalla ,

Shiru tayi ,

"Ke ce wa nace ? Me kika zo yi gidan nan ?

,"Ni ce Yakaka ."

  Ta bashi amsa cikin sanyin murya ba domin tana da yaƙinin bai gane ta ba , sai domin yunƙurin ta na ganin ta wanke kan ta .

Miƙewa tsaye yayi yana jin yadda wani irin bacin rai da ya sauƙo masa tun daga tsakar ka yana neman rufe masa idanu , 

"Tashi ki bar gidan nan ," ko kuwa na sa maigadi ya fita da ke , nan da kike gani ",
ya buga ƙafar sa guda a dandaryar falon cikin yi mata nuni ,

"   Ba gidan Karuwai bane , ba kuma gidan giya bane , tashi nace ,"
   Ya kwatsa mata tsawa

  Tsawar da yayi mata bata razana ta ba , bata kuma huda zuciyar ta ba irin kalmar karuwa da gidan giya da danganta ta da su ,

A hankali ta ɗago kan ta , idanun ta suna zubar ƙwalla tace ,

",Yaya Dakta kayi hakuri dan Allah na san nayi kuskure amma wallahi ba karuwanci naje ina yi ba makarant....

,"Shut up,

"Ki tashi ki fita nace ,

ya furta hakan yana kusanto ta da takun ƙafar sa  ,

," Big Bro ,

Ya tsinkayi muryar Rahima daga bayan sa ,

Ƙarasowa tayi tana raba ganin ta a tsakanin su biyun , da sauri ta ƙarasa wajen Yakaka wacce zuwa lokacin kuka take haiƙan , ta ɗago ta tsaye

"Big Bro , Mamar Mama ce fa Yakaka , bata mutu ba , kai ma kayi zaton Fatalwa ce kamar yadda ta tsorata ni da farko ko ? ,

"Rahima ki min shiru ,

yace yana nuna ta da allin ɗan yatsan sa , goshin sa a tattare da mabayyanin ɓacin rai .

,"ke ki tattara ki bar gidan nan yanzu-yanzu , kar ki ƙara minti goma idan ba haka ba kuma zan sa a fitar da ke ,"

Da sassarfa ya bar falon ,

Babu shakka kunya tayi ƙaranci a zamanin da muke ciki , idan banda tsagoron rashin kunya ita wannan yarinyar har tana da ƙarfin guiwar dawowa cikin gidan da ta gudu ta bari ?? Shin da wata alaƙa ta jini ne a tsakanin su bayan taimakon da yayi mata da ta saka masa da tarin butulci ,?

Da har kuma yanzu zata ɗebo ƙafafu ta zo gidan su to a matsayin wa take ? Kuma gurin wa ta zo ?

Har ta gama barikin ne ta gaji ta dawo ? Zaton ta nan matattarar karuwai ne ?  Ko kuwa har auren nasu da uban ƴar ta ta ya ƙare ne ?

Dole ta bar gidan kamar yadda tayi a baya,  tayi nesa da shi da dangin sa domin mumini ai baya sanya hannun sa a ramin Macijiya sau biyu .

Ba zai taɓa saurarar ta ba , ita ɗin zantukan bakin ta ai duk ƙarya ne , da yaudara , kirkin baka ne da ita tare da ladabin banza .

Runtse idon sa yayi yana tura ƙofar sashin sa da ƙarfi , ɓacin ran ganin ta yana sake hauhawa a ran sa hatta yunwar da yake ji tayi ƙaura .

,"Rahima dole na tafi tunda Yaya Dakta ne da kan sa ya kore ni kin manta shi ne ya fara kawo mu ? Dalilin sa muka zo gidan ku Rahima bani da ikon cigaba da zama ,"

Yakaka ta furta hakan tana shiƙar kuka lokacin da take jawo jakankunan kayan ta ,

Kukan ta daga ƙasan ran ta yake , kukan tausayin rayuwar ta tare da nadama ,   ina zata je ? Tun zamantowar su 'yan gudun hijira nan gidan ne kaɗai mafakar da suka tsaya cikin ta ba tare da ƙalubale ya cisgesu ba har sai da ita da ta sanya kafafun ta da kan ta ta bar mafakarta ,

Tayi zaton kome zai zo mata da sauƙi zaton ta zai yi saurin yafe mata , tayi tunanin zai tare ta da yawan ƙaunar nan tare da tausayin da ta san yana gwada mata can baya , har ma tana sanya ran cigaba da samun kulawar sa kamar farkon fari ,

Ashe dama ta riga ta kufce mata , ta riga ta ɗibga kashi a inuwar da ta huta ,

ashe ita ɗin yanzu wulaƙantattace a wajen sa ? Ashe yanzu ita abun kƴamata ce da bata wuce a kore ta ba ? Babu shakka ba'a ɓari a kwashe du , hangen hadarin nesa kuma ya sanya ta damal-malewa cikin kashi .

Ɗauki take nema , so take ta samu wanda zai dube ta ya fahimce ta ba tare da ya aibata ta da laifin da ta riga ta aikata ba ,  ba tare da wani hukunci yayi tsalle kan ta ba sakamakon abunda ta aikata da bai wuce Kaddarar da zata iya hawa kan kowanne ɗan Adam ba .

Malama Maryam ita ce ɗaya jal wacce ta sani da tashin farko bayan sanin laifin da ta aikata ta tausasa mata , a yanzu kuma bata nan , tayi komawar ta garin su tun kwanaki biyu da suka wuce .

Shin Mutane ba za su mata uzuri ba ? Ashe haka halli  'yan adam yake ?? Da wanne zata ji ? Ita kenan haka guguwar Rayuwa zata cigaba da walagigi da ita ? Yanzu ina zata ?

"Kar ki tafi Yakaka  tsaya ina zuwa .

Rahima ta katse ta bata tsaya jiran amsar ta ba ta fita da ɗan gudun ta ,

bata tsaya ba , ta cigaba da jan  baccon ta da yafi ƙarfin kinkimar ta , tana yi tana rera kuka da murya mai ban tausayi .

" Yakaka , Yakaka ki tsaya , kar ki tafi nace ki zo Baba yana ƙiran ki .'

Kanta a ƙasa tana sharar ƙwalla ta shiga falon Prof , da ta tadda shi kamar koyaushe a zaune , muddin zai miƙe tsaye sai da sanda mai ƙarƙo .

Muryar ta tana rawa ta gaida shi , ya amsa yana nazarin ta ,

," Me ya faru zaki bar gida 'yata ,?  meye dalili ?

Muryar ta na rawa tace

"Yaya dakta ne yace na tafi  .

Ya gane wanda take nufi dan haka ya ɗan yi jim cikin ransa yana sake ganin dai-dai kan ƙudirin sa .

"Ki koma ciki , nan gidana ne ba na wasu ba , dan haka babu wanda yake da damar korar ki , kin ji ko ?

',To Baba , nagode ,"

", Madallah ku koma ciki ,'

Bayan tafiyar su ya ɗau wayar sa tare da ƙiran Doctor Hamza wanda tunda ya shiga sashin nasa ya gaza aikata kome illa kai-kawo da yake yi , zuciyar sa na cigaba da tafasa ,

Bayan ajiye wayar sa , sashin Prof ya tasamma , inda ya tarar da shi yana  tsimayen sa , bai saurari gaisuwar da yake yi masa ba , ya fara da tambayar sa fuskar sa na nuna ɓacin rai

"Me yarinyar nan tayi maka zaka kore ta ?

Da sauri ya ɗago kan sa yana duban Baba , a zaton sa yau ta zo , sannan Baba bai ma san da zuwan ta ba , ashe ba haka bane .

Shin ƙarar sa ta kawo ? Babu shakka babu kome a bariki sai darussan da ke koyar da tsaurin ido tare da rashin kunya ,

Shiru yayi , ganin yayi shiru ya sa Prof  sake jefa masa wata tambayar

"Ko kuwa ta aikata wani abu da ba dai-dai bane ? Ko tana kan aikatawa da ta cancanci kora ?

Shiru Doctor Hamza ya sake yi , kai tsaye ba zai ce ga abunda ya hana shi ya ce kome ba , Bazai ce ga dalilin da yasa ya gaza bayyana laifin ta da yake sirri ne a gurin sa wanda yake tunanin a iya tsakanin su biyu yake,  da kuma can inda tayi rayuwar bariki ,

sai dai hankalin sa yafi tafiya akan ya rufawa ƙaryar sa da yayi a baya asiri ne,  sanin da yayi Ƙarya wata mummunar ɗabi'a ce da iyayen su suka wanzu suna hanin su da aikatawa ,

"Idan baka da wani dalili ,kar ka sake korar ta , ita ɗiya mace rauni ne da ita a koyaushe , a kuma ko'ina tana buƙatar matallafi ne cikin rayuwar ta , '

" Wanda daga zarar ta rasa mai tallafar ta zata iya faɗawa kowacce irin mummunar rayuwa  , yan gudun hijira su ma mutane ne kamar kowa walaƙanta su abune marar kyau , ka kiyaye .

"Zan kiyaye Baba ,

***

Yakaka tana komawa cikin gida bayan Rahima ta kama mata kayanta sun mayar su ɗakin da cikin sa suka  zauna ita da Falmata tun farkon zuwan su gidan , muryar ta a ɗan dishe ta ce

  " Rahima yaya Dakta fa yunwa yake ji , da farko da ya shigo yace ki masa girki ,

  Zama Rahima tayi a bakin gado tana ɗan riƙe kanta ,

  "Yakaka wallahi kaina ciwo yake ba kaɗan ba , yau nasha yawo a School ( makaranta ) taimaka ki ɗan dafa masa ko ƴar indomie ce .

Bata ƙarasa zancen ba yakaka ta nufi ƙofa , tana amsawa da "To yanzu zan yi ,"

Bayanta Rahima ta bi da kallo cikin ranta tausayi ne me tarin yawa , Yakaka mai kirki ce kaddarar Rayuwa ce ta faɗa mata ta dalilin raunin Ilmi da wayewar ta .

Ita da aka ce ta dafa indomie sai ga ta ta zage damtse wajen girka lafiyayyar jalloup ɗin Spaghetti da ta sha niƙaƙƙen nama da kayan ɗanɗano , cikin sauri da azama take aikin dan haka bata ɗau ɗogon lokaci ba ta kammala , ta tafasa shayi ( tea ) da ya buƙata ta adana su a mazubi me kyau ta ɗora bisa ɗan faranti ,

Zuwa tayi ta samu Rahima tana bacci , bata son tashin ta domin kar ta ƙara mata ciwon kai .

Dan haka ta fita daga ɗakin ta koma kitchen tayi tsumu a tsaye hankalin ta ya rabu kashi biyu , tunanin Dakta da yace yana jin yunwa da kuma tsoro da take ji na kai masa abincin ,

Tayi tsayuwar kusan mintuna uku ta gaza ɗaukar abincin kafin daga baya ta gyara zaman hijabin ta ta ɗau tiren tare da nufar sashin nasa da ba baƙo bane a wajen ta ,

Cikin sanɗa take tafiya lokacin da ta shiga sashin nasa a yunƙurin ta na son ta shigar masa da abincin ta fita ba tare da ya san ita ta kawo masa ba ,

Ta zo dai-dai ƙofar tayi tiris ganin ƙofar shiga falon nasa a rufe , ajiye tiren tayi , tana tunanin yadda zata yi ?

Wata dabara ce ta faɗo mata , dan haka ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi , tayi wuf ta juya da saurin ta ,

garam !

ta ji tayi karo da mutum .

Da sauri ta ɗago kanta ganin fuskar sa a murtuƙe yana jifanta da mummunan kallo ya sa ta haɗiyar yawun tsoro ,

", Un- um daman Yaya Dakta abincin ne , Un Rahim..

,"Wuce ki bar nan bana so na sake ganin fuskar ki .

Yace da maɗaukakin sauti ,

Sum-sum ta ratsa ta gefen sa da yayi banga-banga yaƙi matsawa tamkar mai shirin jibgar ta ta bar wajen har tana haɗawa da ɗan gudun ta bayan matsanancin bugu da zuciyar ta ke yi .

Sanin darajar abinci ya sa shi ɗaukar abincin da ta kawo masa ya shigar da shi falon nasa ya zauna tare da ajiye ledar da ya sayo abinda zai ɗan ci ,

Dafadukar shinkafa ce irin wacce aka cika mata ƙaƙale da launi ruwan ɗorawa shar ,  da ya taka takanas zuwa shahararren gurin sayar da abinci da ake ji da shi a garin ya sayo .

Loma ɗaya-biyu yayi yaji abincin bai masa yadda yake so ba , sam shinkafar ma bata dahu sosai ba a bakin sa , shi yafi son yaji abinci ya dahu sosai ko shinkafar ce yaji ta suɓut-suɓut tuɓus-ɓus daɗin tauna , ba irin wannan dahuwar ƴan gayun ba,  da yake hasashen rabin shinkafar sai dai ta ƙarasa dahuwa a cikin sa .

Rufe abincin yayi ya ɗan ture gefe , yayi jugum a zaune , yana tunanin matan zamanin gaba kamar nan da shekara hamsin anya za'a iya cin girkin su ? Ko Amne da take ba tsohuwa tukuf ba salon girkinta ya banbanta dana yaran mata irin su Hafsa, zainab ,Rahima a bar batun Safiyya wannan ba abunda tafi ƙwarewa akai irin Kwaɗon ganyen salad da take cin sa kamar me .

Ɗan satar kallon girkin da Yakaka ta kawo yayi ta wutsiyar idon sa , tsaki yayi tunowa da yayi duk kanwar dai ja ce da girkin su Rahima da na wannan da ya raina dahuwar tasa  .

kasa jure yunwar da take sasuƙar sa yayi dan haka cikin yanayin,  ya na iya ?  Ya ɗauko tiren abincin zuwa kan teburin gaban shi ,

Sai dai Yana ɗora ido akan abincin ya haɗiye yawu , da sauri ya ɗau chokali yayi bismillah ,gami da kai lomar farko bakin sa ,

Bai saurara ba cikin nutsuwa ya dinga aikawa hanjinsa haƙƙin sa har sai da yaji cikin sa ya samu dai-dai da buƙatar sa sannan ya sarara , a fili yace

", Alhamdulillah wannan ko wacce irin pasta ce haka Rahima ta dafa ? Wataƙila ta zallar Alkama ce ba surki .

***

Bayan Yakaka ta idar da sallah tayi addu'o'in da ta saba yi duk bayan sallar ta ,

Ta waiga ga Rahima wacce ta farka daga bacci

"Rahima yaya ciwon kan naki ? Kin ji sauƙi ko ?

" Ya ɗan sake ni Yakaka thanks ,

"Yakaka yawan ibadar ki na burgeni ga yawan addu'o'i da kike yi kin fa kusa mintoci ishirin kina addu'a ,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login