Showing 291001 words to 294000 words out of 411050 words
Chapter 98 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
can ko gidan shi mariƙin nasu bata sani ba , ana gudun kar ta ɓata ko ta shiga wani mawuyacin hali kuma a can , da naji haka sai nace to fa nima zama bai kamani ba tare zamu tafi , to kaga shirin nan da nayi ma na tafiyar ne ga kayana ma can na haɗa su gu ɗaya .
Bayan ya gama sauraron Hajja da tayi shiru tana tsumayen iznin sa , sai yace ,
" hakka ma shawarace mai kyaou Hajja , to idan hakka ne ku taho na sauƙe ku ga tasha na sanya kou a mota , nima sai na tai gida ,
"Amma Hajja doumin Allah dagga kun cimma gida kun tadda Fatima ki sanar min ta téléphone , sabadda na san halin da kuke ciki a can , duk da nima ba da jimmawa ba zan tai can Nigeria ɗin , kuma a nan sojin mu zasu yi bakin ƙoƙari wajen duba hanyar da ita Fatima zasu bi , sai dai kouma idan har ta ɓarauniyar hanya ta daban zasu ɓulla yanzou fatan mu dai yana ga Fatima ta cimma gida lahia .
" to babu laifi Babban soja ai sai mu tafi ɗin , Allah dai ya sassauta wannan lamari , bari na ƙira ita Yakaka ,
Mota ɗaya suka tarar wacce zata tafi Kano kai tsaye daga Niamey dan haka Youssouf ya biya musu gidan baya na motar su biyu rak da daman mutum ɗaya suka tarar a gaban motar dan haka nan take aka shiga neman direba ya zo kuɗin kujerun mota sun kammala ,
Laluba aljihunsa yayi ya fiddo kuɗaɗen ciki da baki ɗaya CFA ne , mayar da su aljihunsa yayi saboda sanin da yayi daga sun bar shiyar ƙasar su ba zasu musu wani amfani na sosai ba , ya zaro wallet ɗin sa da dalolin Amurka ke ciki a miƙe , ya matsa kusa da gilashin motar da yake sauƙe ta sashin da Yakaka take ,
Ba tare da ya dubi fuskar ta ba yake miƙa mata kuɗin da bai riga ya ƙirga ya san adadinsu ba ,
Yakaka wacce tunda ta shiga motar ta ɗauke kai daga barin kallon sashin da yake tsaye , amma tana ankare da shi ta kuma ga tsayuwar sa akanta yana miƙa mata ƙudi , bata son sake kallon fuskarsa ne dan haka taƙi ɗago kanta ,
Hajja wacce take raba ganinta a tsakanin su biyun , ta ɗan zunguri Yakaka ,
"Babba uwar Mama , Babban soja yana baki saƙo ,
Da wani irin yanayi na gargaɗi a fuskarta ta kafe Hajja da idanunta da suke da kaifin kallo masu kamar gilashi ,
Galala Hajja tayi tana mayar mata da martanin kallonta , sai kuma ta muskuɗa ,tana cewa
"Ajabba inji kanurai, o ni hauwa'u ,
sai kawai ta maida ganinta can gefe tana kyeɓe baki .
A hankali Youssouf ya zura hannunsa kaɗan ta cikin motar ya sauƙe mata kuɗaɗen akan cinyarta yana cewa "Hajja Allah shi kiyaye muku hanya don Allah Hajja duk yadda lamari ya kassance muku ki jisheni ,
" Amin Amin Babban soja , da yardar Allah zan sanar da kai duk yadda ake ciki , kaima kuma Allah ya tsare maka hanya , mungode , mungode sosai Allah shi yiwa rayuwa Albarka .
"Amin Hajja nima nagoude , yace yana kama hanyar barin wajen ,
Yakaka wacce tunda ya ajiye mata ƙuɗin ta runtse idanunta tana tuno da lokaci na farko a haɗuwarsu , yadda ya ajiye mata kuɗin da ya sayi martabarta da su akan cinyarta ya haka ,
Hannunta ta kai tana ture kuɗin da ya ajiye mata a yau zuciyarta cike take da rauni mai tarin yawa , sanin da tayi a yanzu Youssouf ya haramta a gareta , ta kuma Haramtawa kanta shi koda kuwa babu ran Falmata .
Tashin ƙugin motar su yazo dai-dai da sauƙar hawaye a idanunta , haƙiƙa so gaskiya ne , so halitta ce da Allah yake sarƙawa a tsakanin zuciyoyin bayin sa domin ya samar da Salama a tsakanin ƴan Adam , yafiya , haƙuri tare da tsusayawa tafe suke a cikin so na domin Allah ,
Babu shakka Youssouf shine mutum ɗaya da Allah ya ɗarsa mata son shi tun bata san menene so da kansa ba , ta kuma so shi ba domin kome da ya mallaka ko ya taɓa mallaka mata ba , cikin rashin sanin ta jarrabawa ce Allah yayi mata kan soyayyar sa ,
Tun ranar da ta san laifin da Youssouf yayi mata kan Yaudarar ta da yayi ya ɓata mata rayuwa bata taɓa jin tsanar sa tsana irin ta ƙiyayayya ba , sai dai ta ji tsanar shi bisa ga laifin da tasan ya aikata mata, take kuma neman yadda zata yi ta hukunta shi domin ta goge wannan tsanar da tayi masa a dalilin laifin sa ,
Dawowa da tayi ta tarar ya auri Falmata , ya rugurguza mata zuciya , lamarin ya girgiza ta fiye da duk wani abu da ta taɓa cin karo da shi cikin rayuwarta ,
Tashin hankalin da ta hango tare da Youssouf lokacin da tayi tattaki ta same shi take masa togaciyar ya saki Falmata , tare da tirjiyar da yayi mata sun shaida tare da bata tabbacin cewa Youssouf yana son Falmata , so kuma mai tarin yawa , abunda ya kassara mata duk wani karsashin ta , ya kuma ƙara mata hau-hawar ɓacin rai ,zuciyar ta ta shiga tuhumar ta kan yaya zai yi mata haka ?
Rana ta farko da ta san da tabbatuwar cikin jikin Falmata sai ta ji ta tsani kanta tana kuma tir da zuciyarta da ta gagara yakice shi baki ɗaya daga cikinta , alhalin tuntuni ya zama mallakin ƙanwar ta ,
A yau saƙo-da-lungu take bi tana zaƙulo duk wani ɓurɓushi na son sa tana zarewa daga cikin ranta , duk wani gurgun tunani ko hasashen da ta dunga yi a baya na zasu dawo suyi rayuwa tare da ita da shi da ɗiyar su har ma su haifi wasu ƴa'ƴan , yana zagwanyewa tare da gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta , ta rabu da Youssouf da sunan so kamar yadda Allah ya rabata da Mama ,
Youssouf ba nata bane , ya taɓa zama nata ne kaɗai akan shimfiɗar da shaitan ya shimfiɗa musu .
Youssouf na Falmata ne tare da ƴa'ƴan da zasu haifa nan gaba da kuma sauran matansa ,
Takurewa tayi a jikin ƙofar motar tamkar zata tsaga ta koma ciki saboda wani irin zogi da zuciyarta ke yi , babu shakka cikin sadauƙarwar soyayya ta gaskiya akwai ciwo mai tsanani .
***
Ya juya tare da tarin tausayinta cikin ransa , yaso ko da sau ɗaya ta bashi dama ya nemi yafiyar ta bisa ga laifin da shi yasan ya aikata mata , har abada ita ai uwa ce ga ɗiyar sa mafi soyuwa a gare shi , bai so ba suka sake yin rabuwa makamanciyar ta farko ,
A shekaru da girma gami da hankali nashi irin na cikakken Namiji , ba sai ita ko wani ya taɓa faɗa masa cewa tana son shi ba so kuwa mai tarin yawa da shi yake iya hango shi a kwance cikin idanunta ɓaro-ɓaro koyaushe ta dube shi ,
Sai dai shi da ita dukkanin su sun faɗa ne ga jarabawar rayuwa , kuma shi bai mata so irin na auratayya ko kaɗan , sai dai yana tausayawa mata sanin yadda ciwon so yake ,ga wanda duk Allah ya jarabta .
gefe guda kuma yana jinjina Yakanah irin tata da bata taɓa furta masa kalmar so a gaban sa ba ko sau ɗaya , ta kuma yi ƙoƙarin dannewa ta ɓoye hatta ga shi kansa bata yadda cikin saninta ta nuna abunda ke binne cikin ranta ba , bare kuma ga ƙaunarta da yasan abadan baza ta taɓa bari ta fahimata , daga ƙasan ransa ya furta "Madallah da ƙarƙƙarfar kyakkyawar zuciyar da take iya danne tasirin So , ƙwarai ita ɗin ai jaruma ce . "
Ƙarfe uku na ranar ta yi masa a cikin Masarautar su inda ya tafi kai tsaye ga fada ya kai gaisuwa gurin Maimartaba wanda ya amsa masa fuskarsa ba yabo babu fallasa , sai dai saɓanin baya da idan har ya shigo fada ƙirarin da manyan fadawa da kansu ke yi masa har ya tashi , yau dai shiru babu wanda ya kambama shi da ƙirarin sai fa dogarai da suke tsaye daga bakin-fada .
Shiru yayi kansa a sunkui yana jiran Maimartaba yayi masa umarnin dawowa daga gefensa kusa kamar yadda ya saba a koyaushe , sai dai har ya kusan mintoci ishirin a zaune maimartaba bai sake duban sa ba , dan haka ya miƙe yana mai sallama da Maimartaba da sauran jama'a da suka amsa a sama-sama ,
Idanunsa suka kai inda yake mazauninsa ada kusa da ƙafafun Maimartaba , karaf suka haɗa ido da Mammadou da yake zaune a gurbin sa , wanda yake jifan sa da wani ɗan guntun murmushin ƙeta , ɗauke kansa yana ƙarasa barin Fadar .
A sanyaye ya taka yana yana nufar ciki sashin Hajiya Umma , a hanya babu abunda ya sauya na yadda bayu ke zubewa gaishe sa , sai dai yana lure da wani irin kallo da wasun su ke binsa da shi wasu kuma yana iya jiyo ƙus-ƙus ɗin su daga ya gota .
Ita ɗaya ya tarar da ita a falonta na ƙurya da yawanci sai zata yi ganawa ta sirri take shigarsa ,
Zama yayi a gabanta yana mai sunkui da kai cike da ladabin da yake halayyar sa ya gaishe ta , muryarta babu amo sosai ta amsa gaisuwar sa ,
Shiru ya ɗan gitta kafin da murya mai kaushi tace da shi ,
" Ina kouma itta ɗiyar da kake amren ?
Shiru yayi kaɗan kafin ya ce
" sun tai ga ƙasar su baki ɗaya ,
Sake tsare shi da ido tayi , duk kuwa da ta ɗan yi farin-ciki da cewa da yayi "sun koma ƙasar su , sai ta ɗora da cewa " ka sau amren ta ko kuwa ?
Shiru yayi cikin fargaba , yana tsoron kadda ta tilasta shi ya saki Fatima , wani sashi na zuciyar sa ya ji yana gargaɗin sa daga sake yin ƙarya ,
wani busasshen yawu ya haɗiye , ya ɗago da kansa ya dube ta , a hankali ya mayar da kansa ƙasa kafin yace ,
"Ban sau amrenta ba sun tai gida ne kafin al'amura su dai-daita anan ,
"Youssouf ,
Hajiya Umma ta ƙira sunan sa , a tsorace ya amsa "Na'am Umma , zuciyarsa tana mai tsananta bugu yauce rana ta farko a iyakacin sanin sa da ta taɓa ƙiran sunan sa kai tsaye .
" na maka oumarni ka sau amren ɗiyar nan ka aika mata da shikan ta can zouwa ga ƙasar su , muddin kana ƙamnar da na yafe ma kouma Mahaifinka shi maka afouwa , idan kouwa ka ƙi bin umarni na Youssoufa , shiru tayi bata ƙarasa ba ,
sai dai ya fahimcin munin abunda ka iya biyo baya ganin yadda ɓacin rai ya ƙara hauhawa a kan fuskar ta bayan ta kawar da kai daga barin duban sa ,
Gumi ne ya shiga keto masa kota'ina cikin jikin sa , ya sanya hannun sa yana share zufar goshinsa ,
Muryarsa can ciki yace , " Na amshi oumarnin ki Umma, ki yafe min bissa ga kuskuren da na aikata .
Muryar ta da ɗan sassauci tace , " Laifin ka ga Allah kayi ka nemi Yafiyar sa , doumin shi mai yawan afouwa ne ga bayinsa , sannan ka kyautata tuban ka , ni kam abou ɗai nake so kayi shine sakin auren ɗiyar nan idan kayi hakka shikenan .
Shiru yayi baice kome ba , saboda zallar tashin hankalin da yake ciki , duk wata ƙafa ta isar da saƙo a jikinsa jinya take da amsar umarnin Hajiya Umma .
Ganin yadda ya zamto tamkar wanda aka zarewa lakka a gabanta yasa tayi gyaran murya tana mai ƙarfafa zuciyarta daga tausayi irin na tsakanin ɗa da mahaifiya daya soma mamayarta , musamman kasancewarsa mafi soyuwa a gareta cikin 'ya'ya ,
" ka tashi ka tai ga matanka bayan ka tanadi kyawawan kalmomin da za ka yi amfani da su wajen tausasa zuciyar su doumin laifin ka mai nawi ne a wajen su .
Kamar jira yake tace ya tafi , sai ya miƙe a hankali bayan ya mata bankwana ya fito daga falon , baya sanin takamaimai ina yake jefa ƙafarsa ya nufi shiyar gidan sa ,
Sashin Siyama ya tasarwa ba tare da ya haƙiƙance meye zai je ya sanar da ita ba ,
Da shigar sa Yumna ta taso da gudunta daga inda take wasa a tsakiyar falon da tarin kayan wasanta ,
Da sauri ya sunkuya ya ɗauke ta yana matse ta a cikin jikin sa kewar Mama marar adadi na taso masa ,
"Papa ,
ta ƙira shi da ƴar muryar ta ,
"Yumna , ya amsa yana ɗora idanunsa akan Siyama da ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take kishingiɗe Rakiya na mata tausar ƙafafunta ,
Da sauri Rakiya ta miƙa gaisuwar ta kafin ta bar falon zuwa can waje sashin su na ma'aikata ,
A hankali Siyama ta tako gaban sa bayan ta ƙirkiro wani guntun murmushi akan furskar ta ,
"Sannu da zouwa Biyamuradi, da fatan ka iske mou lafiya ?
Tana ƙarasowa ta kama hannun sa guda , kafin ta cigaba da cewa ,
" Mu tai kayi wanka Baban Yumna kafin a samar da abinda zaka taɓa ,
Yanayin rashin kuzari bai bar shi ba ya bi bayanta zuwa sama ɗakinsa ,
Bayan ya yi wanka ya shirya , cigaba yayi da zama akan kujerar ɗakin ya zurfafa cikin tunanin umarnin Hajiya umma , da kowacce daƙiƙa guda tashin hankalinsa daɗuwa yake , gefe guda ga rashin sanin takamaimai halin da ita kanta Fatima ke ciki tare da ɗiyansa dake maƙale a marar ta ,
Ƙarar wayar sa ya sanya shi janye tagumin da yayi ya ɗau wayar ganin mai ƙiran nasa daya daga cikin manyan kwamandojin sojin su ne na yankin Diffa ,
Magana suka sake yi kan tsaron da zasu daɗa a tsakanin boda saboda motar da take ɗauke da matarsa da zasu bi ta Boda zuwa Nigeria , bayan ya gama wayar da bai ɗau lokaci yana yi ba ya ajiye wayar a gefe yana baya da kan shi ya ɗora kan bisa allon kujerar ya ɗora dogayen ƙafafunsa akan ɗan teburin gilashi da yake gaban sa ,
Idanun sa ya runtse yana jin yadda kansa ya ke sara masa musamman ta goshin sa ,
Siyama wacce ta ji shirun sa yayi yawa bayan ga abinci ta haɗa masa a shiyar cin abincin su , sai ta miƙe ta hau saman , cikin ranta kuwa ƙoƙari take tayi aiki da shawarwarin da Rakiya ta bata na danne kishinta daga barin bayyana shi a sarari ,
Tana murɗa ƙofar ɗakin ta hango shi a kujerar ya dafe kan sa da hannunsa guda , wani irin yanayi na zallar tausayi da ake samu ga abunda ake ƙauna ta gaskiya , shine ya tsigar mata , babu shakka a tun shigowarsa ta fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki .
Bai ji shigowarta ba har zuwa zaman ta a gefen sa , sai da ya ji hannunta mai tsananin taushi ta ɗora akan nashi hannun da ya dafe goshinsa da shi ta janye shi ,
"Baban Mama , ta ƙira sa , ɗas ! Zuciyarsa ta buga da jin sunan Mama da ta masa inkiya da shi da Falmata kaɗai ke ƙiransa da sunan , sai ya dawo da ganin sa kanta ,bayan ya gyara zamansa yana jin wani irin yanayi mai tasari matuƙa ,
"Baban Mama ina miƙa ta'aziyyata kan rashin da muka yi na ɗiyar mou , Allah shi jikan Mama shi sa ta ceto mou .
Sai tayi shiru tana neman dai-daita nutsuwar zuciyar ta daga tarin baƙin-cikin da yake bijiro mata na zallar kishin Falmata , ta ɗora da cewa ,
" Ina ƙamnata Fatima ? Da fatan ka baro ta lahia ?
Da wani irin yanayi ya matse hannunta dake cikin nasa , cikin muryar dake cike da rauni yace
" nagoude sai dai a halin yanzou Fatima ta gudou ta barni zuwa kan hanya mai matuƙar haɗari , Hajiya Umma kuma ta min oumarni na sau amren Fatima , ki min addu'a Siyama lamura agareni sun tsaurara , kowa ba shi fahimta ta bisa jarabawa ta rayuwa .
Ƙwalla ta ji sun tara mata a ido , tunda take bata taɓa ganin Biyamuradi cikin halin ɗimuwa tare da rauni makamancin haka ba , sai fa yau ta dalilin ɗiya Mace , babu shakka wagga ɗiya Fatima ta kai ayi gangamin tafiya kallon ta .
Gagara cewa kome tayi illa kanta da ta kwantar bisa ɓarin jikinsa , cikin tausayin kai tace , " kayi haƙouri da ikon Allah lamura zasu dai-daita maka a tsakanin hakka nayi Alƙawarin taya ka da addu'a , Allah shi dawo maka da Fatima-zahra .
Hannunsa duk biyu ya sa yana rungumeta tsam a jikin sa , ransa cike taf da ƙauna ta musamman gami da ƙarin ganin ƙimar ta a idanunsa , babu shakka shi masoyi na gaskiya abun riƙo da hannu biyu ne .
" Nagoude ƙamnata kouma Matata , ya furta hakan yana sumbatar kan ta ,
Idanunta ta runtse da hakan ya bawa ƙwallar dake cike a gurbin idanunta damar zubowa , tana sauƙa akan kirjin sa .
Kanta take tausayawa yadda zuciyarta ta afu ga son maso wani irin haka , ta san zafi da raɗaɗin rashin abun so dan haka take tausaya masa babu shakka ita bata da makaman yaƙin tunkarar ko wacece wannan Fatima da ake ta ƙiƙi-ƙaƙa akan ta da