Showing 405001 words to 408000 words out of 411050 words

Chapter 136 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14347

Falmata , ki sa a kawo Baby nan ki sa min naji sautin numfashin abunda kika haifa Falmata .

"Ina Baby na ?
Falmata ta cewa Youssouf haka , ɗan murmushi yayi yana jin daɗin yadda ta fara dawowa hankalin ta.

"Riƙe telephoné na amsa miki ɗiyar mu ki ganta Fatima '

Fita yayi sai ga shi ya dawo rungume da jaririyar a hannun sa da shi ma sai yanzu ya ɗauke ta a shirye take tsaf ta sha kayan  sanyi irin na alfarma tayi kyau matuƙar gaya .

Ɗora mata ita yayi a jikin ta bayan ya ɗan ɗago mata gadon sai ya zauna tana jingina da jikin sa daga shi har ita tsurawa jaririyar ido su kayi suna ganin tsananin kamannin ta da Mama kamar lokacin da aka haife ta , marabar su kawai wannan tana da girma kuma tafi Mama gashi bayan hakan za'a ce Mama ce kawai Allah ya dawo musu da ita .

A hankali ta ɗago ta sumbanci kumatun ta dama da hagu da yasa ta motsawa a hankali tana ɗan yamutsa fuska irin na jarirai.

"Yakaka na ɗauke ta ,Yarinya ce mace Mai tsananin kama da Mama , Allah ya dawo mana da Mama Yakaka.

Daga can murmushi mai sauti Yakaka tayi tana jin ƙaunar 'yar da bata kai ga ɗora idanu akan ta ba na samun wajen zama na musamman a cikin ran ta a lokacin ji take kamar tayi tsuntsu ta je ta gan ta ta ɗauke ta ta riƙe a hannun ta ta rungume ta a ƙirjin ta ta gwada mata ƙauna a matsayin ta na uwa a gare ta ba wai Yayar uwa ba kawai ɗiyar Falmata ɗiyar ta ce halak malaƙ .

"Allah ya raya ta Falmata , Allah ya mata Albarka , Yaa Allah yasa ta amfanar da Al'ummar musulmai ajiye wayar ki ɗaga ta ki shayar da ita anjima zan sake ƙiran ki .

"Amin Yakaka .

Daga haka Doctor Hamza ya zare wayar daga kunnen ta ya kashe kafin ya jaa ta cikin jikin sa ya rungume ta tsam suna musayar jin ciwon rashin nasu gudan jinin da suka yi .

Sumbatar goshin ta da Youssouf yayi bai sa ta janye idanun ta daga kallon fuskar 'yar ta ba da take jin wani abun da ya zarce a ƙira shi da So sannan kuma ya wuce ƙauna tasiri yana bin duk wani sarari na ran ta yana dasa wani al'amari mai girma ji take kamar ta tsaga ƙirjin ta ta sa ta .

Wai yau ita Falmata ce take riƙe da 'yar ta ta cikin ta babu shakka Allah shine mafi girman Abun Godiya "Alhamdulillahi Yaa Allah .

Ta furta hakan a sarari tana jin wata ƙwallar farin-ciki na cika mata gurbin ido .

A hankali Youssoufa ya kai hannu yana ɗauke 'yar daga jikin ta bata yi wani yunƙuri ba illa bin su da tayi da ido cikin ran ta bata mamakin yadda ya iya ɗaukar jariri saboda tun akan Mama ta san ya ƙware .

Addu'o'i ya shiga yiwa 'yar sa tsawon mintoci fiye da talatin dan tun Falmata tana kallon su har ta ɗan fara gyangyaɗi .

Hannun sa da ya shafa mata kumatu shi yasa ta buɗe ido da kyakkyawar fuskar sa tayi arba yana mata murmushi kafin sautin  sa ya sauƙa a kunnen ta "Mon Bébé kina ji na ?

A hankali ta gyaɗa masa kai idanun ta cike da baccin gajiya suke lumshewa sai dai kalmar da ya faɗa ya sa ta wara idanun ta da sauri ta dube shi tana son sake jin me ya ce ?

"Wanne Suna kin ka zaɓarwa ɗiyar mu na bar miki zaɓi dan saboda kawai na gwada miki kaɗan dagga farin-cikin da nake ciki.

"Da gaske kake ?
Ta tambaye shi tana narkar da idanun ta cikin nasa .

"Da gaskiya Fatima na bar miki zaɓin sunan ɗiyar mu mai darajja '

" a sa mata Yakaka .

Sautin da ya taso daga ƙasan ran ta ya subto akan laɓɓan ta .

Shiru yayi yana kallon ta kafin yayi magana ta katse shi ta hanyar cigaba da cewa "indai dai har ka bani zaɓi to a sa mata sunan Yakaka Yayata .

"Babu shakka ta cancanta domin kuwa ita ce Mafarin silar haɗuwar sa da Fatima-zahra ba domin ita ba da bai samu Fatima ba bare har ta haifa masa 'yar da yake riƙe da ita yanzu a hannun sa a ƙarshe kuma ita ɗin uwa ce ga 'ya mafi soyuwa a gare shi da har abada baya zaton za'a samu mafiyin ta wajen matsayi a cikin 'ya'ya .....

Tunanin sa bai yanke ba ya juyo yana fuskantar Falmata riƙe da Babyn a hannu yace "Meye Sunan ta na ainashi..?

Cike da zumuɗi Falmata tace "sunan ta Amina.

Bai ce ƙala ba sai ya sake mayar da kai ga yiwa 'yar sa addu'a kafin bayan ɗan gajeren lokaci ya ɗago kan sa yana mai ɗora mata 'yar a jikin ta yace

" Sunan 'yar mu Amina riƙe ta da kyau 'ya ce a gurin ki sannan kuma 'yar uwa.

Da hannuwanta biyu ta rungume ta tana jin yanayin da yafi na ɗazu yana danne ta ta kasa tsayar da hawayen farin-cikin da yake sauƙa fuskar ta kamar yadda ta kasa ɗauke ido daga fuskar Amina .

Haka ma Biyamuradi Youssouf da yake tsaye akan ƙafafun sa hannuwansa duk biyu a zube cikin aljihun sa yana murmushin da yake bayyana haƙoran sa ya kasa janye ganin sa daga kan su kamar yadda yake jin ƙaunar su biyun tana fisgar sa tamkar wanda guguwa ta riska a tsakiyar rairayin hamada .

***

Daga nan ɗakin da Falmata zata cigaba da zama kafin a sallame ta aka kai ta bayan nan Hajiya Umma da har yanzu bata tafi gida ba ta shiga inda suke ta mata sannu sannan ta sake mata addu'a ita da Amina kafin ta bar asibitin .

Sai kuma ta fara amsar waya daga Iyaye da dangin ta na Nigeria har dai zuwa lokacin da likitoci suka buƙaci da a bar ta ta samu hutu mai yawa kar a takura ta.

***

Daga lokacin da Doctor Hamza ya ga har dare yayi bai ji wani labari ba daga iyayen sa sai ya fahimci Sofi ta rufe zancen duk abunda ya faru bata faɗa ba .

Dan haka shi sai ya yanke shawarar sanar da iyayen su da kansa dan haka a daren ranar bayan sallar isha'i ya hada conference call da Baba Prof da Amne da Khaalty Rahima da Momy Kori da shi kan sa Baban Sofi.

Bayan duk ya gaishe su sai ya nemi da su bashi dama zai musu bayani.

Nan ya shiga basu labarin duk yadda kome ya wakana a tsakanin sa da Sofi tun daga farko har ƙarshe .

Kafin ya gama Sallallami da kukan Momy kori tare da Amne ya cika wayar .

Sai da kyar Baba Prof ya sa suka yi shiru domin shi da kansa Baban Sofi ya gaza cewa kome kawai kamar ruwa ya cinye shi saboda tsabar shiga razana da muzanta shi da Sofi tayi.

Ɗan taƙaitatcen Bayani Baa yayi akan lamarin da ɗari-cikin-ɗari ya goyi bayan hukuncin da Hamza ya ɗauka ya ɗora da cewa "tunda har dai abu ya zama da neman aikata kisan kai to babu shakka ba amfanin zaman rabuwar ita tafi dacewa.

Matsanancin kuka Momy Kori ta sa cikin rishin kuka take sanar da su cewa ita har kawo yanzu ma da ake wannan maganar bata ga Sofi da idanun ta ba Sofiya bata zo gida ba to ina ta tafi ?

"Ta tafi ko'ina ma Kori , ina mai tabbatar miki da cewa Safiya ba za ta zo ta zauna min a gida ba domin nima ba zan zauna da mashayiya kuma makashiya ba tunda irin rayuwar da ta zaɓarwa kan ta kenan to tafi duk inda za ta tafi tayi rayuwar ta amma ni dai ban amince ta zo gidana Alhaji ka shaida ni na cire Safiya daga cikin 'ya'yana' ku kuma ina mai baku haƙuri kan abunda ya faru ita yarinyar ma dan Allah a bata haƙuri ita da iyayen ta .

Daga haka Baban Sofi ya yanke ƙiran daga ɓangaren sa .

Duk son kai irin na Momy Kori yau sai ta gaza kare 'yar ta haka tana ji tana gani saki Uku ya tabbata tsakanin Sofi da Hamza sannan kuma dole ta bada haƙuri ga su Amnee da shi kansa Doctor Hamzan da ya rasa gudan jinin sa sannan ta ajiye wayar .

Daga nan suka cigaba da jimantawa tsakanin sa da iyayen sa inda Amnee ta nuna son Yakaka ta zo gida a kula da ita amma tun ma kafin ta gama magana Baba Prof ya nuna rashin amincewar sa hujja da cewa ai shi Hamzan likita ne dan haka zai fi kowa lura da ita dole Amnee ta haƙura ita kuwa Khaalty Rahima daman bata cewa kome sai addu'a kawai tayi ta danne duk wata damuwar ta saboda kara .

Daga nan aka yanke shawarar cewa jibi Amnee da Zainab za su tafi Abujan daga nan su haɗu da hafsa idan sun duba Yakaka da jiki daga nan sai su dawo Kano su wuce Niger gurin Falmata .

Su Hafsa zasu dawo bayan suna Amnee kuma za ta ɗan yi ko da sati biyu ne tana kula da Falmatan .

Kafin kwanaki biyu zance ya gama baza dangi kan abunda Sofi ta aikata na yunƙurin kashe kishiyar ta kuma ta gudu ba'a san inda take ba.

Amnee sun je Abuja tare da direban su a babbar motar da Amnee ta cika kusan rabin ta da kaya .

Sun kwana a gidan Doctor Hamza ta sake rarrashin takwarar ta Yakaka sannan ta bata kayan gyara da tarin wasu turarurruka sannan ta sanar da ita sakon Prof da yace cikin satin nan za'a zo a shirya mata kayan ta a gidan .

daga nan kuma sai suka wuce Maradin Niger da tarin kayan ƙamshi da gyaran jiki tare da kayan jarirai masu kyau da tsada  da Amnee tayi tanadin su musamman domin Falmata da zata haihu kayan gyaran tafiyayyu ne daga Chad .

Can a Maradi suka ga tarba irin ta saraki sai nan-nan ake da su ana sauƙe musu kabbakin arziki.

Daga Zainab har Hafsa sai da suka yi santin kyaun sashin Falmata da irin gatan da ake mata babu abunda yafi burge su irin tarin hadiman da take da su da ko yaya ta motsa sai sun mata sannu girma irin ta sarauta sai gidan sarauta .

Lokacin da Yakaka ta samu labarin cewa jaririya Sunan ta ta ci har sai da tayi kuka dan farin-ciki .

Doctor Hamza ma ya ji daɗi ya kuma musu fatan Allah ya ƙara musu zumunci a ƙarshe yayi alƙawarin daga ya ɗau hutun sa nan da wasu watanni cikin shekara mai zuwa zai kai Yakaka har Niger ta gano takwarar ta .

Ranar suna kuwa Al'umma da suka taru ba'a ce Falmata bata da dangi a Niger ba.

A gurin taron suna dangin suka dunga tsurkun tururuwar zuwa duba Hajiya Mama wacce jinya ta sarƙe ta sakamakon wasu munanan ƙuraje da suke feso mata duk a ƙafafun ta bayan hawan jini da ciwon zuciya da suka mata rubdugu bata ko iya tafiya gaba ɗaya rayuwa ta mata juyin waina a tanda .

Kowa ya fito daga sashin sai yayi gulmar sakayya ce take gani tun daga nan duniya .

Wacce irin ta Maimounatou ɗiyar sarkin Agades ma ta samu sakamakon mutuwa da Mahaifin ta yayi a tun jinyar da ya afkama sanadin mummunan abun kunyan da ta aikata kan yunƙurin kashe Mijinta a halin yanzu kuwa rayuwa ta mata atishawar tsaki batta ga tsuntsu batta ga tarko .

'Yayan Hajiya Mama kansu gaba ɗaya basu da sakewa a cikin taron sunan duk kuwa da cewa sun zo sun kuma kawo kayan jaririya da na uwa irin na alfarma .

Da kaya sai da Falmata ta rasa gurin zuba su tsakanin wanda Mijin ta tayi mata da wanda iyayen sa suka mata da wanda Iyayen ta suka kawo mata da kuma na 'yan uwan sa ga kuma na dangi da abokan arziƙa .

***

Bayan suna da Zainab da Hafsa da zasu koma kayan niƙi-niƙi aka haɗa Su da shi .

Ita kuma Amnee ta zauna kula da Falmata da ta dage tana lura da ita saboda haihuwar da tayi wani ɗam rami na musamman na turara jiki ta sa aka mata a cikin uwarɗakin Falmata kamar yadda al'adar su take su basu cika shan magungunan na mata ba sai gyaran jiki tsaftar sa da ƙyalƙyale fata suka fi bawa muhimmanci .

Gefe guda kuma ita ma Hajja ta dage da nata gyaran irin na matan ƙasar Hausa da su kuma suka fi bawa shan kayan ɗa'a muhimmanci .

Kafin sati biyu Fatar Falmata ta zama kamar bayan tarwaɗa yayin da wani fitinannan ƙamshi ya zauna mata a jiki 'yar kiɓar shayarwa da tayi ta amshi jikin ta sai ta koma kamar irin hamshaƙan matan nan da suke kan ganiyar ƙuciyar su duniya kuma ta juya hasken ta akan su tana haska su .

Bayan cikar sati biyu da kwanaki biyu Amnee ta koma Nigeria inda ta je ta tarar da labari mafi daɗi da Prof ya tare ta da shi kan ya samarwa da ƙanwar sa Rahima Miji .

***

Sheikh Mukhtar ɗaya ne daga cikin jerin ƙannen abokansa da bai yasar da zumunci ba ko bayan mutuwar wansa yake ziyartar sa lokaci zuwa lokaci muddin ya shigo garin Maiduguri daga can ƙasar Saudi-Arabia da yake aiki da zama tare da iyalin sa sama da shekaru ashirin da yayi aure.

Wannan zuwan nasa lokacin da Prof yake tambayar sa iyalin sa yake shaida masa ita matar tasa ta rasu shekarar da wuce .

Prof ya masa ta'aziyya bayan nan ya shawarce shi da kar yayi jinkirin yin wani auren saboda shi aure ibada ne sannan kuma kariya ne .

A lokacin Sheikh Mukhtar ya nuna masa cewa har kawo yanzu dai bai samu matar da ta kwanta masa ba wacce ya yarda da hankalin ta da zai iya danƙa mata amanar tarbiyyar 'ya'yan sa da matar sa ta mutu ta bar masa su huɗu .

Sannu kan hankali cikin dabara irin ta manya Prof ya gabatar masa da Khaalty Rahima cikin sa'a da ganin girman sa Sheikh Mukhtar ya nuna amincewar sa ɗari bisa ɗari muddin dai ita ma ta amince da shi .

Lokacin da aka sanarwa da Khaalty Rahima batun Sheikh Mukhtar bata ƙi ba tunda dai iyayen-goyon ta sun amince ita kuwa me zai ta tayi gardama idan tana da damuwa ɗaya ce ji da tayi ƙasar za ta bari gaba ɗaya ta bar Bulama dan ta sauran 'ya'yan ta mata ta san Allah ya riga ya sanya mata su a hannun nagartattun Mazaje '

Damuwar ta Bulama ne da ya shaƙu da ita fiye da misali sannan babu wani dangin sa na uba da aka samu ɓullowar su har kawo yau duk kuwa da neman da aka ta yi saboda har kawo yau da ake ɗiban shekaru fiye da bakwai da tarwatsa musu gari da 'Yan tawayen Boko Haram suka yi alƙaryar su bata sake kafuwa ba an riga an shafe ta mafi yawan mutanen su kuma sun mutu da take hasashen ciki har da mafiya-yawan dangin Uban su Yakaka da daman ba wani yawa suka cika ba ƙaramar zuri'a ce da su masu gajeran baya .

Duk da ba wai shakkun Bulama zai wahala bane idan har ta bar shi a hannun Amnee sai dai tasirin tsakanin uwa da ɗa ne musamman waɗan da suka shaƙu ya haka raba tsakanin su ba ƙaramin abu bane sai ko Mutuwa .

Ga jin daɗin ta kuma lokacin da suka yi ganawar farko da Sheikh Mukhtar shi da kansa ma ya mata batun riƙon Bulama zai dawo hannun sa daga zarar sun yi aure .

Da yake lamarin ba wai na yara bane cikin satika uku har magana tayi ƙarfi inda nan da satika huɗu mai zuwa za'a ɗaura auren idan ya tashi tafiya nan da watanni biyu ya tafi da Matar sa da ɗan su .

Bayan watanni shida.

Maradi Niger

Siyama tare da Falmata ne tsaye suna Sallama a jikin motar da Biyamuradi Youssoufa yake lafe a ciki yana riƙe da Amina wacce Falmata ta mata laƙabi da ( Ukhtee ) take ƙiran ta haka da kuma sunan ya bi bakin jama'a kowa ma hakan ke ƙiran ta.

Jin Sallamar tasu taƙi yankewa yasa Youssoufa leƙo kan sa yana cewa "Siyama kin ka ce yau aikin rana kin ka tahi yanzou kouwa ga hantsi ta ɗagga ko kouwa kin fara wassa ne da aikin naki ko kouma kin gajiya ne za ki bari dagga farawar ki.?

Da sauri Siyama ta saki hannun Falmata da ta riƙe jin cewa Biyamuradi Youssouf ya  sako maganar aikin da da kyar yarda ta nema ta fara zuwa har sai da Maimartaba ya sa baki yace aikin ta na ceton rai ne sannan tun tasowar ta burin ta ne ta zama likitar haƙora ƙaƙa zai hana ta bayan shi ya san daɗin samun cikar buri a rayuwa tunda shi ma babu wanda ya katse masa nasa burin na zama Babban Soja mai yiwa ƙasar sa hidima .

Ba yadda ya iya haka ya haƙura aka samar mata da aiki a babban asibitin jaha tare da sharaɗin ba ita babu bin sa jaharTahoua sai dai shi zai dunga zuwa kamar yadda suke yi a tun can baya .

Babu jaa Siyama ta amince saboda ranta ya afu ga son taimakon Al'ummar ta itama  lokaci yayi da za ta bayar daga ilmin da Allah ya hore mata falalar sa .

Baya tayi tana jaan mayafin ta ta rufe cikin ta da ya fara girma da yake nuni da nan ba da jimawa ba Ukhtee za ta samu ƙani ko ƙanwa .

"Ƙamnata Allah shi kiyaye mukku hanya hirar mu ba mai yankewa ce ba ina dai sake faɗa miki dan Allah dagga kin koma ecole ki dagewa karatu kiyi zarra ga abokan karatun ki hakan zai zama abun alfahari ne a gare mu.

Falmata tana murmushi ta amsa da "Insha Allah ba zan baki kunya ba Docteur Siyama nan da wassu 'yan shekaru ƙamnar ki zata zama diplômée.

"Allah shi badda sa'a ƙamna ta.

"Amin .

ta amsa tana shigewa Mota direba ya jaa suna barin gidan , Falmata ta waigo tana miƙa hannu domin ɗaukar Ukhtee da take ta tsalle

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login