Showing 165001 words to 168000 words out of 411050 words
Chapter 56 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
da ni ,
,"To ," yace yana sauƙe wayar
Cije gefen leben sa yayi , watau dai kome gaskiya ne , ga shi nan duk yadda suka shirya yana faruwa daki-daki , watau har sun yi auren ta turo shi ya zo ya ɗau ƴar sa da ƙanwar ta ,
Zuciyar sa tayi duhu , me na miki da zaki yi wasa da zuciya ta irin haka ? Ashe sakayyar da zaki min kenan ?
Wani irin kishi mai ɗaci yake ji a ran sa , shan alwashi yake daga yanzu bai ƙauna sake jin ko me suna irin nata , bai ƙaunar sake jin duk wani abu da ya shafe ta , bashi da wani sauran uzuri da zai iya bata kariya da shi , ya yarda ya amince ta yaudare shi .
Tada motar yayi a hankali ya hau titi , yana nisawa cikin tunanin mace a yau !
Sojojin nan basu bar su madam saly ba sai da suka sake chasa su yadda ran su ke so ," Ah soja birgimar hankaka ne fa ?
Suka yi ficewar su suka hau motocin su wasu a tsaye a bayan hilux wasu a zamne , suka yi tafiyar su ,"
illahirin gidan a ruɗe yake da kururuwar matan da aka lallasa , sai ɗuruwa ake ganin su ana tambsyar me ya faru ? Me suka yiwa sojoji ?
Ɗan liti wanda muryar sa ta dashe saboda tsabar ƙwarmato , ya dubi madam saly wacce bakin ta ya kumburo yayi suntum sakamakon haƙorin ta ɗaya da ya fita ,"
Cikin dusashiyar muryar sa yace saly fara yau wacce rana ce ? Kuma a wanne wata muke nawa kuma ga watan ??
Da ido kawai madam saly ta bi shi tana jin yadda raɗaɗi yake ratsa tsokar jikin ta ta ko'ina gefe guda ga bakin ta da take ji kamar an cusa garwashi ,"
Ya cigaba ,
Na rantse ki rubuta ki ajiye ido na idon wannan tsinannan yarinyar yagana sai dai uwatta tai naƙudar wata , wai ace kana zaune da makashin ka baka sani ba ? Ashe tuntuni ita ta san ana nan ana shirin far mana da yaƙin basasa ,amma tayi funfurus ta ƙi faɗa mana bare muyi ta kan mu ,ki tsoraci ɗan adam ƙuzazje mai tafiya da ƙafa biyu saly fara ,
wai yanzu ace tsawon lokacin nan ashe shegiyar yarinyar nan mai kama da takanɗa ta san inda yaran nan su yaks suke , shine bata taɓa yunkurin faɗa ba "ko daya ai yake hannun hagu ba baƙon duwawu bane ,"duk jirgi ɗaya ya kwaso su ," to ƙwaranƙwasa ba'a daki bulus ba, farautar ta zan shiga yi ba dare ba rana ," wayyo wayyo ni liti du mazauna na sun yi tsami sun ɗuri ruwa , saly gane min ko dai farfashewa mulamulai na suka yi ?
Ya juyo mata duwawu ,
Kawar da kan ta tayi tana miƙewa da kyar ta nufi cikin gidan tana aiyana irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Yagana , ai ita ba'a zubebeniyar ƙwaryar rashin mutunci da ita mutum ya kwashe ƙalau ,"
*****
Bayan komawar Biyamuradi Youssouf tare da Tafeeda ɗakin hotel , kowannen su shiru yayi yana saƙa cikin zuci ,
Ta bangaren Youssouf abu biyu ne zuwa uku , na farko mutuwar Yakaka da ta girgiza shi ta kuma bashi tsoro , ya wanzu yana tunanin da yanzu shi ne fa ya mutu ? Me zai cewa ubangijin sa akan tarin laifukan da ya wanzu yana aikatawa , tausayin ta yaji yana ninkuwa a ransa , tare da alwashi da yake ɗaukarwa kan sa na wanzuwa yana yi mata addu'a neman gafarar ubangiji har zuwa tsayuwar nasa numfashin ,
Ƙaunar ƴar jaririyar da kafin ɗora idanun sa akan ta suks tsara da shi da tafeeda akan cewa ko abun da aka haifa ya/ta nuna wasu alamu a halittar sa/ta dake nuna cewa nasa ne baza zai amince ya dangantar ɗa/ƴar da cewa jinin sa ba ne , kasancewar ya riga ya faɗawa Tafeeda yakaka ƴar talakawa ce sun san cewa ba wani tsananta binciken su gwajin jini a tsakanin sa da ɗa/ƴar da aka haifa za'a yi ba , dan haka suka tsara zasu barwa yakaka abunda ta haifa amma zasu taimaka mata tsayin daka kamar yadda tun farko Biyamuradi youssouf ya tsara ,
Sai dai fa kome ya sauya ya birkice masa lokacin da ya rungume ƴar sa a ƙirjin sa , ya ɗora idanun sa akan ta kamannin mahaifiyar sa duk suka bayyana kan su a halittar ƴar , ta buɗe idanun ta ta kalle shi , so irin na tsakanin ɗa da iyaye yayi tasirin sa cikin ƙudurar ubangiji , wani irin so mai yawa mai tafe da tausayi da tsantsar zallar ƙauna marar gauraye irin ta iyayen da suke da matuƙar ƙwalafaci da ƙawa zucin ƴaƴan su , suka taso suka lullube zuciya zuwa idanun YARIMA YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE
Yaji zai iya sadauƙar da kome da ya mallaka domin ya tsira da ƴar jaririyar ƴar da tayi rashin ɗumin uwa tun daga ranar zuwan ta duniya , rashin maihaifiya a tare da ita ya kassara illahirin gaɓɓan jikin sa , ji yake ina ma yana nan ranar da ta zo duniya alhalin uwar ta bata tare da ita , da tun daga ranar zai fara gwada mata ƙauna da tattali mai tudu biyu irin na uwar ƙwarai kuma jajirtattcen uba , tausayin ta yake , tausayin da bai taɓa jin yayiwa wani mahaluki irin sa ba , bai ƙi ba ace tun daga ranar haihuwar ta har zuwa lokacin da zata mallaki hankalin kan ta ƙirjin sa ya zama wajen kwanciyar baccin ta , so yake yayi mata rumfa ya zama mamar ta , kuma baban ta , ya zama ya cikace gurbi na duk wani makusanci da yaro zai nema cikin rayuwar sa na ƙuruciya , bai son ta tashi cikin maraici , tunanin hakan kawai na sauke ƙwalla a idanun sa , yana kuma katange tunanin sa daga duk wani ƙalubalen da kasancewar ƴar a rayuwar sa zai iya samarwa ,
kou yanzou baby ta daina kuka ?
Ya tambayi Tafeddah wanda ya rafka tagumi hannu biyu ya zurfafa cikin tunanin yanayin da ya hango da alamomin da suka bayyana kan su ga Yarima daga lokacin da ya ɗora idanun sa kan ƴar jaririyar da a yanzu yake hango alamun zamantowar ta barazana ga farin cikin mutane da dama da suke kewaye da yariman , shi yasan wanene youssouf ,
a lokuta da dama ba sai ya masa bayani ba yake fahimtar abunda ke cikin zuciyar sa , sai dai ya san wannan karon Yarima zai zo da wani Al'amari mai girma muddin ya nuna son ƴar ta tsaya tare da shi cikin rayuwar sa ,
Abunda hakan zai haifar ba abune mai daɗi ba , bai son ko tunawa , yau ace yarima youssouf ya doshi cikin masarauta tare da ɗiyar da ya haifa ba tare da amre ba , al'amura zasu rinchaɓe,
kai ka kawo yake cikin tunanin sa yana son samar da hanyar da zai bi ya dakatar da yunƙurin yarima ya bar ɗiyar nan a inda ya dace ta zauna,
Tunanin sa ya katse lokacin da yaji youssouf ɗin nayi masa magana ɗagowa yayi ya dube shi
Me kake faɗi yarima ban ji ba ?
Ɗiyar nan ko ta daina kuka yanzou ? Wacce iriyar madarar jarirai ake bata ?
Sasarere Tafeeda yayi yana kallon youssouf ,
Anya kou ranka ya dade yarima ba'a bar batun jaririyar nan haka nan ba ?baka gani Allah ne ya doube mu ya kawo hanyar da zamu samu masalaha akan wagga lamari ya kawar da uwar ɗiyar domin mu samu mafita ,"
abun da ni nake gani shine ka bar ɗiyar nan wajen masu riƙon ta tunda ba mu riga mun sanar da wani abu da ya shafi asalin mu ba ga mutanen nan ba, sai mu juya baya mu tahi abun mu ba tare da kowa ya san inda za'a same ka ba , ta iya yiwuwa ka dunga yin aike ta wata hanya mai nisa wadda zai dunga isowa ga ita ɗiyar nan , domin fa ka sani ita wannan ɗiya babbar barazana take a gare mu yarima da ma masarauta baki ɗaya , ko kouwa me kake tounani ne yarima ? Ko kouwa masalaha bata zou mana ba ??
Ya ƙarasa zancen yana kwantar da muryar ganin yadda Youssouf ɗin yake masa wani irin kallo mai karfi dake bayyana ɓacin ran da yake cikin ran sa ,
Tafeeda me kake faɗi haka mai kaushi , kana nufin na bar ɗiya ta jaririya nan nigeria hannun mutanen da ban sani ba ? ƙaƙa kake son rayuwar ƴa ta ta kasance cikin wahala tare da rashin galihu ? Baka tounanin tarihi zai maimaita kan sa ga ɗiya ta , rashin galihu yasa ta faɗa kwatankwacin halin da mahaifiyar ta ta shiga har ya zama silar faɗawar ta halin da ya zama silar samar da wagga ɗiya ? INA SON ƊIYA TA TAFEEDA , DOUNIYA ZATA KASSANCE TARE DA NI , DUK RUNTSI NI AI MAHAIFIN TA ,
A hasale Tafeeda ya miƙe tsaye
Amma ka san ita wagga ɗiya take ba ta halali bace kou ? Ita ɗin baka samar da ita ta tsafatataciyar hanya ba , ita ɗin barazana ce ga martabar iyayen ka da dangin ka baki ɗaya , barazana ce ga hawan ka ƙaragar mulkin masarautar mu , ƙazanta ce ita wacce ya kamata ka ji kunyar bayyana ta ba.....
tsawar da Yarima Youssouf yayi masa ya hana shi ,
Kome zai yanke tsakanin mu idan ka sake touzarta ɗiya ta Tafeeda , ita ɗin batta da laifin kome , ni ai nine za'a hukkunta , ita wagga ɗiya bata tare da dauɗar kome , ita ai abun a tausayawa ce ,
ita ce kaddara ta Tafeeda ina roƙon ka da Allah ka taimaka mouna ni da ɗiya ta , ka tsaya tare da ni bisa lamurran ta ni nasani me tarin laifuka ne , ka duba wnnan ɗiya mai tarin rauni ,
Yarima youssouf ya ƙarasa zance tare da share ƴar siririyar ƙwallar da ta sauko masa ,
So yake ya samu mai taya shi son ɗiyar sa , so yake a bashi karfin guiwar tsaya mata , tafeeda yana da muhimmanci cikin rayuwar sa bai son ya juya masa baya a wannan gaɓar ,
Tare da wani irin yanayi yake kallon sa , bai son tausayin sa da ya fara ji ya rinjaye sa har ya taya shi aikata abunda yasan zai cutar da shi mummunan cutarwa , zai kawo tsaiko akan cigaban rayuwar sa , idan yayi haka shi yasan bai kyauta ba Amintaka bata cika ba, kuma hatta shi fushin iyayen yarima sai ya shafe shi , kai shi fa basshi da ƙwarin guiwar da zai bada goyan baya ga yarima a wannan gaɓar ,"
Yarima idan ka ɗau ɗiya jaririya irin wannan ka tahi da ita zouwa ina ?
Zan yi amre na bada riƙon ta ga maimounatou zata riƙa min ita ,"
Kana da tabbacin ƴar sarkin agades ɗiyan gata irin ta zata yadda tayi maka riƙon ƴa ?
nakan iya haƙourewa dagga amren ta muddin batta riƙon ɗiya ta.
Murmushin takaici tafeeda yayi
kace da maimartaba da hajiya umma , da ƴan uwan ka me ??
Kaddara ta ce ta zou a haka , nasan umma zata fahimce ni ta fahimtar da maimartaba ƴan uwa zasu min uziri da afouwa ,"
wanne irin tanadi kake tounanin maƙiya zasu yi ta hanyar ɗiyar nan su kawo naƙasu cikin rayuwar ka tare da lalata mana sunan masarauta ?
Maƙiyi shi ai kullum maƙiyi ne , shi kuwa jajirtatcen namiji badda maƙiyan sa yake ,
gƴaɗa kai tafeeda yake yana iya hasaso gingimemen rikicin da Toussouf yake neman tsunduma kan sa cikin rayuwa ,
Allah shi badda sa'a yarima
Amine !
yarima ya amsa yana jin daɗin ganin kamar tafeeda ya sauko zai goya masa baya ,
Yaushe zamou kouma ka ga ɗiyar nan ɗan ouwa ?
Gobe iwar hakka na hantse a ƙassa ta ta haihouwa ,
Gobe kake koumawa ɗan ouwa ?
toh zaman me zan yi a nan na baro aiki na ? Gobe da iznin Allah nake koumawa .
Allah shi kaimu ,
Yarima Youssouf yace yana ƙarasawa gaban window ɗakin ya yaye labulen yana kallon rana da tayi yamma take gaf da tafiya ,
Ran sa cike taf da son sake ganin fuskar ɗiyar sa ....!!!
[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Fikra writers association
Mafari .......
Hargitsin Rayuwa .
Umm'muaz
29
TUN RAN GINI RAN ZANE
Washegari da misalin tara na safe , jirgi ya ɗaga da Tafeeda zuwa birnin Lagos inda ta chan zai wuce ƙasar su ,
Dukkanin su shi da Biyamuradi babu mai isashiyar walwala suka yi sallama , alhalin basu kai ga cimma matsaya guda kan matsalar su ba ,
Duk da cewa bangaren youssouf ya ji kaso sittin cikin ɗari na damuwar sa ta tafi , saboda ya bayyana ta ga aminin nasa , ya kuma san Tafeeda zai yi duk yadda zai yi ya ga ya dai-daita kome a gida kafin komawar sa , yanzu babbar matsalar sa ita ce rayuwar ɗiyar sa ,
A daren jiya kwana yayi yana dogon nazari akan yadda zai yi ya ga ya bata ingantatciyar rayuwa ba tare da gurbatatciyar hanyar da aka samar da ita ta zama ƙalulabe a gare ta ba , da mutum yana iya sauya kaddarar sa da a daren na jiya ya juya , ya gyaro hanyar da aka yi ƴar nan ta sa ta zo duniya , amma ya riga ya san bakin Alƙalami ya bushe ,
hakan ya sa ya ɗau ƙuɗirin zai jajirce akan duk wani ƙalubale da shi zai iya cin karo da shi cikin rayuwar sa wajen ganin ya inganta tare da kyautata rayuwar ɗiyar sa ta FARKO a duniya ,"
Tafeeda kuwa ya bar ƙasar ran sa cike taf da tunanin yaya zai yi yaga ya boyewa hajiya umma musabbin shiga damuwar yarima ? Ya zai yi ya boye mata irin mummunan aikin da yarima ya aikata ? Yaya zai boye mata samuwar wata haramtatciyar ɗiya daga tsatson ta ? Kome yana neman kubce masa , shi ya kasance a tsakiya ne , ɗan aike ne shi , sai dai saƙon da zai koma da shi a yau me nawi ne wanda ya fi ƙarfin fitowa daga kan harshen sa ,
Cikin awanni (2) da tashin jirgin su daga Murtala Mohammed International Airport Lagos, Ya samu dira a Diori Hammani International Airport Niamey , duk yadda ya so ya tsaya wajen 'ubbo' su gaisa kamar yadda ya tsara , ya gagara saboda rashin nutsuwar zuci , Allah-Allah ya ke ya samu isa wajen hajiya umma ,"
Jirgin da zai sada shi da Maraɗi kai tsaye ya hau , yana isa gidan su wanka kawai yayi ya sauya kaya ,ko abinci bai duba ba ya yiwa fada tsinke , nan ya nemi iso ga hajiya umma , aka yi masa ba tare da jinkiri ba ,"
Bayan ya gaishe ta yayi shiru yana son samun ƙarfin guiwar faɗin abinda ya shirya ,"
Yayin da ita kuwa hajiya umma baki ɗaya ta tattara hankalin ta gare shi , tana nazarin sa ," ita ta katse shirun da tambayar sa ,'
Yaya kun ka ƙarƙe da yarima ? Shin ya sanar da kai damouwar sa ? Ko kouwa ?
Ƙwarai ranki ya dade yarima ya shaida min basshi da watta damouwa da ta wucce , na rashin aboukiyar zama , inda har ya nouna ra'ayi da zai yiwu ma yana buƙatar a amra masa mataye biyu a rana gouda wanna shine ɗai guda damouwar yarima , sai kouma yace ayi albishir yana nan tafe nan da ƙarshen wata me kamawa, bayan haka yarima yana nan lafiya cikin yanayi mai kyau !
Tafeda ya ƙarasa zancen sa yana sunkui da kai da jin kunyar ƙaryar da ya gilla , wacce rashin mafita ya ja sa ga aikata ta ,"
A take fuskar hajiya umma ta yalwatu da fara'a zuciyar ta ta haskaka , har haƙoran ta suka bayyana ,"
Alhamdulillah , Madallah da kai Tafeeda yaron kirki , tashi maza ka tahi ka sanya a fara shiri tare da gyara ga bangaren da anka gina na wagga ɗiya ƴar mutan agades , zan yi magana da mai martaba akan buƙatar da yarima ya tado da ita , amsa zai isar maka , Madallah da kai ,Madallah !
Godiya Tafeeda yayi tare da miƙewa yana barin shigifar , yana sake ganin dacewar shawarar da ya bayar na aurawa Yarima mataye ganin sa hakan ne mataki na farko na dakile sa daga sake faɗawa cikin wata musibar a gaba , domin ya ƙare nazari kaf rashin aure shine dalili na farko da har ya sa Yarima faɗawa ga zina ,
Yana fatan yadda ya rufa asirin mummunan labarin nan a nan gaban hajiya umma , Youssouf ma ya rufawa kan sa asiri ya bar ɗiyar chan a Nigeria kamar yadda ya faɗa masa , idan kouwa har ya ƙi jin shawarar sa babu shakka jiki magayi ,"duka da ɗanyen kara ," tsuntsun da ya jaa ruwa kuma shi ruwa kan doka , shi dai yayi iya yin sa ,"
Faɗuwa ta zo dai-dai da zama , shine abunda hajiya umma take kitsimawa cikin ran ta , ganin cewa a saukaƙe tare kuma da haɗin kan yarima auren sa da Siyama zai tabbata , kai wannan Al'amari yayi kyau gwanin daɗi , cikar gata da martaba ne ga ɗan nata ya auri mataye biyu a rana gouda