Showing 51001 words to 54000 words out of 411050 words
Chapter 18 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
gami da kai hannu ya kashe ac tare da kai hannu ya murɗa ɗan mukullin motar sa ,"
A firgice ta matsa daga jikin motar tayi baya tare da juyowa ta fuskanto motar tana mai sake takurewa saboda azabar sanyin da take ji ,"
Sai dai saɓanin ɗazu yanzu fuskar ta ta ɗan sake daga tsananin bacin ran da take nunawa hakan kuwa baya rasa nasaba da fahimtar da tayi cewa ya taimake ta ne , ya ceto ta daga hatsari a saboda bayan ruwan ya fara tsagaitawa ne babbar kwatamin ta baƴyana , wanda hakan ya sa ta fahimci taimakon da ya sake yi mata a karo na biyu ,
Baya yayi da motar sa ya karya kan motar ya hau titi sosai , sai a lokacin ya kallo in da take suka haɗa ido ,"
Da sauri kowannen su ya ɗauke kan sa ya jaa motar da matukar karfi wanda hakan ya sa ruwan da ke kwance kan titin ya sake fallatsuwa mata a jikin ta ,.
Tsayuwa ta cigaba da yi tana mai fuskantar titin tare da jin wani sabon tashin hankalin rashin ganin alamun mutane a bakin titin da zuwa yanzu ta fahimci ta nan suka shigo unguwar sai dai lokacin da suka zo wurin cike yake ta ko'ina da jama'a tare da rumfunan saye da sayarwar su na wucin gadi ,
yanzu kuwa babu jama'ar babu rumfunan su hakan ya sa baza ma ta iya tantance dai-dai wurin da suka bar falmatan ba
Da gudu ta tsallaka titin tayi diri-diri cikin rashin sanin takamaimai bangaren da zata nufa hagu koh dama , da sauri ta fara bin bangarenta na dama wanda ta nan suka bar falmatan sai da ta dangana har karshe ta je ta tarar da roundabout "shataletale" bata ga koh alamun falmatan ba , kai mutane ma tsilla tsilla take cin karo da su suma kuma duk hanya ɗaya suke bi , sai kuma tsirarun motocin da suke wucewa da gudu suna watsa mata ruwan kan titin ,
Dawowa da baya ta sake yi da nufin nufar bangaren hagu sai dai wannan karon ta sauya salon neman ,domin dagewa tayi tana buɗe murya tana kwalla kiran sunan falmata ,bata damu da kallon da tsirarun mutanen da take yin taho mugama da su suke yi mata ba , burin ta koh ita bata ga falmata ba falmatan ta ji muryar ta ta amsa mata ,"
Nasan kun gaji , nasan kun min uxuri ,nasan kun tsumaye ni , nasan ya kamata na baku yafi haka , toh amma yanayi ne ya zo da haka ,ina fatan zaku ƙara hakuri , kuyi fata daga yau babu sauran dogon jira , wanda nima nake fatan haka .
Inaso mu shawarta zaku dunga hakurin ganin posting sau ɗaya koh biyu a sati amma da dogon jadawali mai ɗauke da kimanin kalmomi dubu takwas zuwa tara / koh kuwa zaku fi son gajeran jadawali a kullum ,mai ɗauke da kimanin kalmomi dubu ɗaya zuwa biyu ? ???
Ina jiran ra'ayoyin ku , yadda kuke so haka za'a yi insha Allah
#son so
#fikrh
#umm'muaz
[10/3, 2:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Fikrah writers association.
MAFARI .........
( Hargitsin Rayuwa. )....
umm'muaz
13
Tuki Hamza yake cikin rashin kuzari wanda ba domin kan titin shal yake babu kowa ba a sakamakon gudun da kowa yayi , da tabbas babu abunda zai hana ya samu tukuicin zagi daga wurin sauran direbobi saboda sam ya gaza yin sauri , zuciyar sa taƙi aminta da ya tafi ya bar ta cikin halin da take ciki , wani sashi na zuciyar na son sanin me ma ya kai ta wannan unguwar wacce take cike da hatsari .?
Gangarawa yayi gefen titin ya tsaya dai-dai lokacin da tunanin abun da zai iya samun ta marar kyau idan har dare yayi mata a wannan unguwar ya gitta masa , da hakan ya sa ba shiri ya karya kan motar ya juya batare da la'akarin ba akan hannun da yakamata ya juya bane .
Wannan shine karo na biyar da take safaa-da-marwaa a bakin babban titin tana mai kwalla kiran sunan falmata , wanda zuwa yanzu da ta kawo tsakiyar hanyar ta ji juya ya fara kwasar ta a sakamakon muguwar yunwa da kishirwa gami da tsantsar sanyin da yake ratsa bargo da kasusuwan ta ta jikin jiƙaƙkun kayan ta da iska ta fara busar da su ,
Ba shiri ta dira guwowin ta duk biyu a ƙasa tare da sake fashewa da wani matsanancin kukan da baya fitowa sosai a sakamakon kwalla kiran da take ya fara dusar da karfin muryar ta .
Kuka take bilhakki tana kiran sunan falmatan a hankali cikin ƙaramar murya ,"
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Allahgammama falmata are3 nyi baa maa range3 kindaa dikkin3 baa ," (Dan Allah falmata ki dawo idan babu ke bazan iya rayuwa ba )
Ƙarasa bajewa tayi daɓas a cikin guntun ruwan da yake wajen idanun ta na fara ganin bibbiyu ,
Daf da ita ta bayan ta ya zo yayi birki , kallon ta yayi ya ɗauke kai gami da matsa mata hon ,
Taji ƙarar motar sarai a daf da ita amma bata yi wani alamu na motsawa ba hasalima wani ɗan guntun tunani ne ya gifta mata na ina ma da motar nan zata take ta ta mutu ita ma kamar yadda mahaifin su ya mutu take kuma hasashen mahaifiyar su da sauran kannen ta ciki har da mafi soyuwa a gareta "falmata" duk sun riga sun mutu sun bar ta ," tunanin hakan da tayi ya sa ta sake muskuɗawa ta matsa kan titi sosai yadda zata bawa motar da ta taho damar bi ta kan ta ,"
Wani dogon tsaki ya saki ganin yadda ta rarrafo ta hau kan titi a maimakon ta taso ta zo su tafi kamar yadda yake nufi ,
Balle murfin motar yayi ya fito laɓɓan bakin sa suna furta kalmar "sokuwar banza ƴar kauye ",
Tsayuwa yayi a kan ta ya zuba mata ido yana nazarin ta cikin tantamar samuwar cikakken hankali a gareta , gefe guda na zuciyar sa na yaba kyaun dogayen fararen yatsun kafafu da na hannayen ta da suke zara-zara kuma fasalin yatsun hannayen nata kamar an feƙe fansiri haka suke da ɗan tsini ta saman su , gwanin ɗaukar hankali duk da ɗauɗa da maikon miya da suka bata su .
Tsayuwar sa akan ta bai sa ta ɗago kan ta da ta ɗora bisa hannayen ta dake kan guwaowin ta ba wanda hakan ya bata ɗamar dunkulewa guri guda tana jiran motar tayi awon gaba da ita ,"
Ganin taƙi ɗago kan nata ya sanya ransa sake ɗugunzuma ganin sa tana neman ɓata masa lokaci alhalin shi taimakon ta kawai yake son yi wanda har zuwa yanzu ya rasa dalilin da ya sa yake son taimaka mata ,"
Ke duba bana son wawanci ki taso na mayar da ke sansanin ku tun kafin dare yayi miki anan karnuka su yagalgala ki ,
Hamza ke furta hakan yana yi yana yamutsa fuska tamkar an sanya shi yin maganar a dole ,"
Har illa yau dai yakaka taƙi ɗago kan ta taƙi cewa koh uffan duk da cewa ta gane shi ,a ranta kuwa ta gama yankewa kan ta shawara a dalilin zancen karnai da ta ji ya ambata wanda take taji hanyar mutuwar ta mafi sauki shine kawai ta kwana a nan wurin domin tana da tabbacin idan har tayi ido biyu da karnuka a sulusin dare babu abun da zai hana jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciyar ta su tsinke ta mutu nan take ," tunanin hakan ya sa ta sake gyara kwanciyar kan ta ta maida fuskar ta zuwa ɗayan bangaren cikin sallamawa.
Wanda hakan ya bawa hamza damar ganin fuskar ta da jijiyoyin kan ta daga goshin ta da na gefe-gefen idanun ta suka taso raɗa-raɗa koraye shar "kasancewar ta fara sol "
Firgita yayi da ganin ta a haka wanda a take ya fahimci rangwamen lafiya a gare ta kasancewar sa cikakken likita kuma kwararre wanda gwamnatin jaha ta amince da shi har ya zama ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da marasa lafiyan dake sansanin ƴan gudun hijira .
Sunkuyawa yayi a gaban ta gami da kai hannu ya taɓa goshin ta ," a ɗan tsorace ta ɗago da idanun ta da suka ƙanƙance gami da sake zurmawa ciki ainahin launin su na zaiba-zaiba kamar gilashi suka bayyana tar ,"
Da sauri ya janye idanun sa daga cikin nata sakamakon ji da yayi kamar akwai wani ɗigo dake sashi cikin wani yanayi tun daga ƙasan ruhin sa a tare da idanun yarinyar .
Ya janye hannun sa tare da miƙewa ya tsaya ,"
Baki da lafiya , ki taso mu tafi na mayar da ke sansanin ku a duba ki a baki magani zaman ki anan hatsari ne ,"
Kin ji koh ?
Jin ta sake yin shiru a karo na biyu ya sa shi shafa sumar kan sa cikin gundura da halin ta ,"gefe guda na ran shi yana mamakin kan sa ta yadda ya damu har yake rarrashin ƴar gudun hijirar da bai san ma daga wanne ƙauye take ba.
Ke idan baza ki tashi ba zan cicciɓe ki koh da bakya so na kai ki saboda hakki na ne na kula da lafiyar ku , ( haka kou ? naga alama 😂 )
Ji da tayi yace zai ɗauke ta ya sa ta miƙewa tsaye batare da ta bari sun sake haɗa ido ba , ta nufi cigaba da tafiya ,
Idan kika sake kika sake taku biyu da waɗannan ramammun siraran kafafun naki zan ɗaga ki sama na jefa ki cikin mota ,"idan ya so ki karye ma ke kika sani doluwa kawai , "dan ma kin samu ina sauke hakki na na taimakon ki da Allah ya ɗora min shine zaki dunga min iskanci da reni ,???
Tare da rashin jin dadi danganta ta da yayi da mai reni ta koma da baya ta tsaya a jikin motar ,' tana mai riƙe kan ta da hannu bibbiyu wanda yake masifar yi mata ciwo tamkar zai faɗo ,"
Da sauri ya buɗe mata murfin motar
Shiga muje ! ?
Tafiyar kurame ita ta biyo bayan gudun da hamza yake shararawa akan titunan da babu wani wadatar motoci , cikin mintuna goma sha biyu ya karaso bakin sansanin nasu ,"
Sauke gilashin motar yayi gami da gaisawa da sojojin da suke gadin sansanin da hakan ya sanya yakaka ɗago kan ta da tun da ta shiga cikin motar yake sunkuye ,"
Karaf ta sauke kwarar idanun ta akan ta tana tsugunne a tsakiya tana fuskantar duk wanda zai shigo sansanin ,"daga inda take tana hango yadda take rawar sanyi da jikakkun kayan jikin ta ,"
Wani irin numfashi ta sauke mai tafe da nishin jin daɗi bata yi wani jinkiri ba ta fara tura murfin kofar da kokarin ɓalla ta ta fita ,'cikin sautin da yake bayyana tsantsar murna da farin cikin ta take jera kiran sunan ƙanwar ta ta ,"
Falmata nah !
Falmata nah !
Mayar da duban sa yayi inda yaga idanun ta suna kallo ,' yamutsa fuska yayi tamakar ya ga kashi ,"domin haushin yakaka da yake ji kaɗan ne akan irin tsanar da yayi wa falmata.
Ke dallah ki nutsu kar ki ballamin murfin mota ," ke da baki da lafiya ina zaki fita da gudu ki je ??
Tun kafin ya rufe baki ta amsa masa cikin siririyar muryar ta da take gauraye da sautin farin cikin da ya gaza boyuwa har akan siririyar fuskar ta da siraran laɓɓan ta suke ɗauke da dariyar da har ya bayyana gajejjerun hakoran ta irin na ƴar uwar ta ,"
Na warke wallahi na warke falmata na ashe ta dawo bata mutu ba ,"bata ɓata ba dan Allah ka buɗe min kofa naje wajen ta wallahi na daina jin kowwane ciwo a jikina .
Shagala yayi wurin sauraran sassanyar muryar ta da koh kaɗan bata tare da hayaniya uwa uba ɗan bakin ta da yake bayyana baki sidik ɗin dasashin ta da ya kawatu kwarai akan farar fuskar ta ,"
Jijjiga kofar tayi da ɗan karfi cikin nuna alamun ƙosawa
Dan Allah ka buɗe min !
Cikin sanyi jiki da sabon yanayin da yake ji yana ratsa kowanne sashi na zuciyar sa ya miƙa hannu a kasalance ya matsa ɗan mubuɗin kofar ta bude , fit ta fita a guje har tana koƙarin faɗuwa ,"
Takun gudun kafafun ta shi ya fara isowa ga kunnuwan ta kafin taji sautin muryar ta ,"
Zuruf ta miƙe tsaye ita ma tana ambaton sunan ta ," tare da nufar inda take jiyo tahowar ta ,"
Kyakyawar runguma suka yi wa juna zuciyoyin su suna masu cika da farin cikin ganin junan su cikin koshin lafiya bayan taraddadi tare da zullumin da kowaccen su ta shiga na tunanin rasa ƴar uwar ta ,"
Hannu bibbiyu yakaka ta tallafo fuskar falmata ," da take dariya
Falmata ya akayi kika dawo ? Waye ya dawo da ke ? Meyasa baki jira ni ba a wurin kamar yadda muka yi yarjejeniya? falmata kin tayar min da hankali dan Allah nan gaba kar ki sake tafiya wani waje mai nisa ki barni ,"
Yakaka nima ba'a son raina na matsa daga gurin da kuka ajiyeni ba , bom ne ya tashi yakaka , duk mutane suka dunga gudu ," kowa yana neman wajen tsira ," na rasa yadda zan yi , inaso naje inda kuke ban san wajen ba kuma bani da ido bare nima na gudu , Allah ne ya taimaka min , wannan mutumin da kuka ajiye ni a gefen rumfar sa shi ya kama hannu na ya kawo ni tasha , da nufin mu nemi ƴan uwa na tun da na gaya masa kuna kurkusa da wajen ya san za ku zo tasha ," sai dai wajen minti talatin babu wanda ya zo daga cikin ku ga gaf ake da fara ruwa , har ya yanke shawarar zai tafi da ni gidan sa , sai naji muryar "Kolo" tana kiran suna na , nayi murna sosai domin a tsorace nake ina ta kuka ,"
Na tambayi kolo ina kuke ke da yagana ta tabbatar min da kuna tare kuma zaku dawo ," sai dai hankali na bai kwanta ba tun da muka dawo na kasa zama ina tsoron kar ku ɓata yakaka ku kasa gane sansanin mu ,"zuciya ta baza ta jure rashin ki ba yakaka ", domin bani da kowa bayan Alllah sai ke yakaka ,"
ta ƙarashe zancen ta tana mai kai hannunwan ta ta ɗaura akan na yakakan da take tallafe da kumatun ta ta zubawa ƴar kewayayyiyar fuskar kanwar ta ta idanu," kamar yadda fararen idanun kanwar ta ta ma suke fes akan fuskar ta tamkar dai tana kallon ta ,"
Murmushi tayi tana mai sake jin yadda zuciyar ta take narkewa da ƙaunar ƙanwar ta ,gefe guda tana sake jin zuciyar ta tana ƙarfi da ɗaukar ƙudirin zamantowa GARKUWA ga falmata ..!!
********
Kai kawo yake yi a gaban gungun zaratan sojojin cikin matsancin bacin rai yake magana da maɗaukakiyar murya ,"
Matsayin mu na jami'an tsaro ba shi ne zai bamu damar cin zarafin Al'umma tare da mayar da rayukan su ba a bakin kome ba ," ba'a bamu kaki da makamai domin naɗa mu jagorancin zalinci ga fararen hula ba ," sai domin mu basu kariya da tsaro tare da kwato musu hakkokin su ," sai dai yadda kuka tafiyar da mutanen ƙaramin ƙauyen da yake tsakanin yankin difa da birnin maiduguri ya sha banban da rantsuwar kare martabar jama'ah da muka yi ," labari ya zo min na yadda kuka ci zarafin mutanen ƙauyen ta hanyar yi musu kisan kiyashi ƙona dukiyoyin su da yi wa matan su fyaɗe dan kawai an sanar da mu akwai ƴan tawayen boko haram daga cikin su , ni a matsayina na shugaban rundunar ku ba haka na tura ku kuyi ba ,"gwamnati ba mutanen ƙasa ta turo mu mu yaka ba face ƴan tawayen boko haram ,
ɗan tsagaitawa yayi yana mayar da numfashi ,"
Wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zaku hau kan mutanen gari da kisa a zuwan kuna yakar ƴan tawayen boko haram .
Jaan kafafu suka yi suka buɗa gami da ƙamewa su sara masa da hakan yake nuni da sun karbi umarnin sa ,"
Shigewa yayi cikin ɗaya daga cikin manyan tantunan da suke kakkafe a sararin faffaɗan filin da yake cikin daji sosai daga gefen birnin na maiduguri .
Zama yayi a bakin ƙatuwar katifar da take yashe cikin tantin gami da kama kan sa da hannu biyu , wani iri yake jin kan nasa yayi masa matuƙar nawi kamar ba nasa ba , ga zuciyar sa da tayi wani irin cunkushewa sam sam ba ya jin sa dai-dai da ya riga ya danganta abubuwan da yake ji da rashin shan abar sa "Burkutu" har na tsawon kwanaki biyu yau ana yinin na uku ,
Miƙewa yayi ya nufi wurin da jakankunan sa ke jibge ya jawo ɗaya daga cikin su gami da buɗe ta sai ga tarin kwalaben giya sumfuri daban daban da yayi guzurin su, ɗaukar ɗaya daga cikin kwalbaben yayi ya riƙe a hannun sa yana jujjuya ta ,"
Kwarai yana da bukatar son ya sha giya sai dai shi sam ba giyar ba turawa yake sha ba , hasalima idan ya shs giyar turawa bikita masa jiki take yayi ta haraswa tare da matsanancin ciwon kai ," giyar gargajiya ta burkutu ita ce abar shan sa .
Mayar da kwalbar giyar yayi cikin sauran ƴan uwan ta gami da rufe jakar yana me miƙewa cikin ransa yana jin ya zama dole ya nemo burkutu duk inda take idan har yana so ya iya cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali ya kuma gabatar da aikin da