Showing 105001 words to 108000 words out of 411050 words

Chapter 36 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14389

basu kenan ,

Ga mamakin sa godiya suka dunga sauke masa kwando-kwando tamkar wanda ya basu wurin kwana a ƙuryar gidan sa , hakan ya sa tausayin su ya sake baibaye shi ,"
   Ku dawo da jakar kayan ku ajiye cikin shago na ," kuma ku tabbatar kafin cikar karfe huɗu da rabi kun bar duk inda kuke kun dawo kun amshi kayan ku domin ni karfe huɗu da rabi nake rufe shago ,"

Cikin daɗin rai yakaka ta kawo falmata dai-dai wurin da take zaman barar ta ,'  ta ajiye ta bayan sun gaisa haba-haba da ɗan dattijon da yake sayar da kayan miya a gefen wajen wanda suka tarar da shi yana fidda kayan lambu ɗangin su yakuwa , alehu , zogale , rama da sauran kayan lambu yana shirya su akan ɗan teburin sa ga alama bai jima da isowa ba , har yake jajen kwanaki da dama baya ganin falmata ,"
    Nan suka ce hana su fitowa aka yi daga sansanin su ,"
  
   Falmata ga naira ɗari ki sayi wake da shinkafa da salat ki ci anjima da rana , kar ki ce zaki zauna da yunwa kin san bana so ," kuma kar ki tafi ko'ina , nima ba nisa zan yi ba zagayen kasuwar zan kewaya ko Allah zai sa na samu ko dako ne nayi na ɗan samo mana ƴan kuɗi kin ga ƙarshen kuɗin hannu na ne ɗarin da na baki , bayan ita bamu da ko sisi ki kula da kan ki sosai kin ji kou ?

Naji yakaka
ta furta hakan tana  mai miƙewa tsaye daga kan ɗan dutsen da yakakar ta ajiye ta , gaban ɗan teburin mai kayan miyan ta ƙarasa
   Baba ɗan Allah ko zamu samu chanji ? Tana mai miƙa masa gudan ɗarin ,
    Ƙarɓa yayi , ya bata hansin biyu ,ta ƙarba tare da lalubar hannun yakaka ta danƙa mata gudar hansin ɗaya ,

Idan kin bani duk kuɗin ke kuma da me zaki ci abincin anjima ? Kin fini buƙatar abinci yakaka , ke da baki da lafiya ,kar kiyi aikin wahala da yawa wanda zai sa ki samu matsala , idan kin shiga matsala ni kuma yaya zan yi yakaka ? Dan Allah ki lallaɓa kan ki , kuma ki dawo da wuri ,"

Toh madam falmata
ta furta hakan tana murmushi jin yadda falmata ta zage tana bata umarni kamar dai ita ce babba .

Hanya ta miƙe tana tafe tana raba ido cikin fatan son ganin inda zata ɗan samu wani aiki ta je ta kama ko da ba'a sa ta ba , amma har ta kai kan gadar kasuwar bata ci karo da wani wajen da ake buƙatar ƴan aiki ba , hasalima yanzu ne ƴan kasuwar suke kan buɗe shagunan su , tare da fito da kayayyakin sana'o'in su ,"

Har ta yanke shawarar komawa wurin falmata ta ɗan jira zuwa anjima , sai idanun suka hango mata mattatarar masu niƙa a ƙwarin gadar ,

Sai ta yanke shawarar ta ƙarasa wurin ƙila ta samu aikin yi tun da ta hango wajen a cike ,"

Gangarawa tayi ta sauka wajen , ga mamakin ta masu injinan niƙa ne birjik ta ko'ina a wajen , ƙarar inji kuwa ba'a cewa kome domin ko maganar na kusa da kai baka iya ji sai fa idan yayi ihu ,'

Da gudu ta ga wasu ƴan matasan yara maza da baza su gaza falmata ba sun nufo ta ,"

   Yaya ta niƙa ne ? Ki kawo na kai miki injin mu yau yau muka kai faifan injin washi , laushi luƙui za'a miki ,

Yaya ta injin su mutuwa yake ana cikin niƙa , anjin mu yafi lafiya kuma ga arhar niƙa ,"

Ita dai da ido take bin su da kallo ba sosai take fahimtar su ba , saboda ƙarar injin da ya cika mata kunne ,

Ita ma da ɗan karfi ta amsa musu
   Ba niƙa na kawo ba , aiki nake nema ,
   Haɗa ido yaran suka yi suka kwashe da dariya , suka maimaita
   Wai aiki take nema ?  kut wannan ƴar na'u ce ita ma .

  Juyawa suka yi suka bar ta nan tsaye ba tare da sun bata ansa ba .

Har sun ɗan yi nisa sai kuma ɗayan ya komo ,
aikin tankaɗe dusa kike nema ??
    Batare da ta kai ga fahimtar sa ba ta gyaɗa kai ,
    Zo muje injin abokin yayana jiya sun ɓata da mai yin tankaɗen dusar sa ,
    Da murna yakaka ta bisa a baya har wata ƴar siririyar hanya , bayan ƴar gajerar tafiya suka bullo a wani babban fili faffaɗa , saɓanin injinan da ta tarar a waje waɗannan manyan injina ne girkakku , ƙaran su mai matuƙar karfin gar diri yake a cikin ƙasa ,"

Gaba yaron yayi zuwa wurin wani da yake tsaye a gefen ɗaya daga cikin injinan yana juye hatsi a cikin injin bayan ya gwamtsa shi da ruwa .

A kunne yayi masa maganar yana mai nuna yakaka da ɗan yatsan sa ,"

Bayan sun gama magana ya dawo wurin yakaka ,' 
    Yace wai shi ba zai biya ki ko sisi ba dusar da zaki tara ita ce ladan aikin ki ," kin yadda ?

   Cikin sanyin jiki yakaka ta gyaɗa kan ta , "bata da zaɓi ! Amma cikin ranta tana tababar ta yaya dusa zata zama ladan aikin ta me zata yi da dusa toh ? Ko suna nufin ta ci ??

   Bayan yaron ya faɗa masa amincewar yakaka , da kan sa ya taso ya zo inda take ,
     Keh yane ƴar na'u ? Kin gane ne aikin yana da yawa dan haka zaki samu alheri , ina ga nima har sai kin ware min wani abu a ciki , ya ƙarasa zancen yana kwashewa da wata hautsinannan dariya ,
     Biyo ni na nuna miki aikin ,
Cikin wata babbar rumfa ya kai ta , wacce take cike da mata tsoffafi da ƴan mata irin ta da ma waɗanda suka fita , wasun su a tsaye suke suna faman zirta hatsi , masara , dawa , alkama , a manyan-manyan turamen da suke watse a cikin rumfar , wasu kuma suna zaune a ƙasa suna ta faman bushe abun da suka zirtan , suna tara dusar a buhun gefen su ,"

Wani babban buhun masara da na hatsi ya nuna mata ,"
  Ƴar na'u wannan ne aikin ki yau ake so , kiyi aiki mai kyau dan gaba a neme ki , kuma banda waskiya ai kin gane ?  idan masu shi suka kama ki kin waske musu abun su , suka ciya miki ni babu ruwa na ai kin gane ko ?

  Na gane

Toh ki zo mu je na baki aron faranti dan naga baki da shi , kuma waɗannan ƴan ciki baki baya kwalta ne , ba baki aro zasu yi ba !

Zungui zungui ta bishi a baya ,'

Daka da surfe ba sabon abu bane wurin yakaka , toh bare wannan da zirtawa ne ba surfawa ba , manyan injinan su ke yin surfe ," nan take ta kama wani turmi da ta ga babu kowa akan sa , ta ɗauki wata ɓasgararriyar taɓaryar da take jefe a gefe ta kama aikin ta babu tsayawa hira , to ma wa ta sani a wurin da har zasu yi hira?? Babu !

Kafin la'asar yakaka ta zirce hatsin da masarar tas , ta hau bushe dusar har da gyarawa , la'asar lis ta gama ta tara dusar daban-daban fiye da rabin buhu kowannen su , iyakar gajiya ta gaji , ga yunwa ga kishirwa , nan gefen ɗan buhun ta samu ta zauna tana mayar da numfashi ,  dayawa daga matan sun gama aiyukan su suna zaman hutawa ,'

Ba'a jima ba masu kayan suka zo ɗauka ƙarƙashin jagorancin "ubangidan ta "mai surfen , nan suka duba kayan su ," yakaka ta jawo buhun dusar ta nuna musu ,

  Ɗan saurayin da ya zo ɗaukar kayan ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata ya ce ta haɗa da dusar ta riƙe kamar yadda suka saba ,

Da murnar ta ta sanya hannu biyu ta ƙarbi kuɗin , cikin ran ta tana tambayar kan ta toh ita kuma me zata yi da dusa ? Ina zata kai ta ?

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga wasu dattawan maza da mata sun fara shigowa , da gudu ta ga kowacce mace tana surar buhun dusar ta tana kaiwa gaban su ," wannan tace tata ta masara ce , wannan ta ce ta hatsi , wannan ta dawa , alkama , su kuma suna tambayar kwano nawa ne ?? ko kuma daro nawa ?? Sai ta ga an fara cinikin dusar , ita dai tana tsaye tana bin su da ido cikin son fahimtar abun da suke ,

Kafin kace meye wannan tas mutanen sun gama saye dusar nan har sun fara lodawa a wulbaro ana jide musu , fahimtar da tayi masu sayan dusar ne , ya sa ta janyo nata buhun-hunan ta kawo gaban su ,"

Cikin tsanaki ɗan dattijon yake kallon ta duk alamun gajiya da yunwa sun bayyana a gare ta fatar bakin ta har ta bushe , jikin nan busu-busu da ƙurar dusa ,"

  Kwano nawa ne ƴan mata ?
Nima ban sani baba

Ungo wannan daron hashimu juye ka auna dusar yarinyar nan kwano nawa ne ,"

Tana tsaye aka auna kwano biyar biyar ne , ta masarar da ta geron ,

Kuɗin ki naira ɗari huɗu ne ƴan mata kowanne kwano murtala biyu muke sayan sa idan dusa mai nawi ce irin taki , idan kuwa faya-faya ce naira ishirin da biyar ne kowanne kwano ,

Ɗari biyar ya miƙa mata tare da buhun ta ,'
    Bari na nemo chanji baba ta furta hakan tana jin wani zallar farin ciki kamar tayi tsalle ,"

Ki bar chanji yarinya ki sayi abinci da ruwa ki sha , ki daina zama da yunwa a wannan halin da kike ciki babu kyau , Allah yaye mana talaucin da ya addabi ƙasar mu !

Har ƙasa yakaka ta sunkuya tana jero kalaman godiya kamar zata kwanta ,"

Sauri sauri ta wanke jikin ta tare da ɗaura alwala da ruwan randunan ƙasa da ta gani birjik a filin wajen , ta lura har babban bayan gida ne a wajen wanda ake shiga a yi wanka da kama ruwa bayan an gama aiki ,

Gudu-gudu tayi sallolin ta na azahar da la'asar , ta ninƙe buhun ta ta cusa shi a ɗan wani lungu , ta fito tana kallon rana yadda ta tafi tana gaf da faɗuwa , hankalin ta baki ɗaya yayi kan falmata ,

A haka ta kama hanyar kasuwar busu-busu da ita sai cin karo take da mutane waɗanda su ma suke cikin sauri domin su bar bakin kasuwar ,

A zaune ta tarad da falmata inda ta ajiye ta tayi shiru da ita ta sunkui da kai , mafi yawancin mutanen da suke hada-hadar su a wurin duk sun watse hatta baba mai kayan miya baya nan,"

Cikin sauri ta dafa falmata ,"
   Falmata na dawo ,
Yakaka kin dawo sannu da zuwa , baki gaji sosai ba koh ? Baki yi aikin wahala ba ko ? Kin ci abinci ? Ya jikin naki ?

    Ƴar dariyar ƴake tayi , tana mai jin yadda jiri ke kwasar ta , ƙarfin hali kawai take wurin tsayuwa akan kafafun ta ,

  Falmata tashi mu ƙarasa rumfar da zamu kwana kin san fa mutumin nan cewa yayi kar mu wuce karfe huɗu da rabi , yanzu kuma ina ga kamar biyar ma ta ɗan wuce kin ga kar ya fasa taimakon mu da yace zai yi mu dunga kwana a bakin shagon sa ,:

A tSaye suka tadda shi a gaban rumfar shagon sa sai faman duba agogon hannun sa yake ," ba dan yadda yake jin tausayin yaran ba da tuni yayi tafiyar sa domin a ka'idar sa baya wuce karfe huɗu da rabi a kasuwa , sai ga shi yau har biyar da wajen minti ishirin , cikin ran sa ya aiyana ya ƙara musu mintoci goma idan basu zo ba zai yi tafiyar sa .

Sai gasu sun iso ,
    A gurguje ya ansa gaisuwar su ya shiga shagon sa ya fiddo musu da jakankunan kayan su gami da tabarma mai biyu da kuma wasu robobin abinci da suke rufe guda biyu , sai jakar ruwa ɗaya , yayi musu sallama bayan ya gargaɗe su a Kan su kula da kan su ,"

Ga mamakin yakaka sai ta ga ya sauke  musu jibga-jibgan labulen da aka yi da yadin tamfol duk kusurwa uku na rumfar wanda aka yi domin kare zubar ruwan sama zuwa cikin rumfar ,

kirif suka rufu daga barin idanun mutanen da suke kai kawo ba za'a san ma da mutane a ciki ba idan ba leƙawa aka yi ba , yana daga waje yayi musu sallama akan sai da safe , suka bishi da doguwar addu'a tare da godiya !

Cikin jim daɗin karamcin da yayi musu yakaka ta shimfiɗa musu tabarmar tare da kama hannun falmata ta zaunar da ita a gefen jakar kayan su daga jikin bangon shagon sai lokacin ta lura da ledar mai ɗan girma da take hannun falmatan ,"

Falmata menene wannan a cikin ledar hannun ki ??
   Abincin ki ne yakaka , naga yanzu kin fi son tuwo miyar yakuwa shine na saya miki lokacin da naji baba mai kayan miya yace mai abinci ta kawo mishi , shine nima na bada kuɗi aka kawo miki , na naira ɗari da hamsin ne , ga sauran kuɗin da na samu yau ƙirga ki gani , "ta miƙa mata ledar da ta tara kudin a ciki ,

Da tarin ƙaunar ta da tausayi ta karɓi kuɗin ta kirga su naira ɗari hudu da sittin ne idan aka haɗa da kuɗin abincin da ta saya mata ya zama ɗari shidda da goma , ai kuwa lalle sun samu kuɗi ita ma ga nata naira ɗari bakwai hansin ɗin safe na abincin ta, kuɗin su sun kama dubu ɗaya da ɗari biyu da goma ,"

Falmata nima na nayi aiki na samu kuɗi har ɗari bakwai kin ji su ,

ta ɗora mata kuɗin akan hannun ta , da murna ta shafa kuɗin

kai yakaka amma wallahi mun ji daɗi kin ga sai muyi ta tara kuɗin da zaki dunga zuwa asibiti ana duba lafiyar yaron mu kamar yadda likita ranar ya faɗa ," kuma mu dunga ware ko ɗari ɗaya ne kullum muna ajiyewa dan mu sayi kayan jarirai koh ?

Idon ta cike da ƙwalla ta ce

hakane falmata kin kawo shawara .

Bari na ci abincin yunwa nake ji sosai falmata , ke ma ki ci wanda mutumin nan mai kirki ya bamu ga shi har kwano biyu , ɗayan sai mu bari da safe mu ci koh ?

Ni ban jima sosai da cin abinci ba yau sau biyu na ci abinci na saya da hansin ɗin safen kuma baba mai kayan miya ma ya saya min biski da miyar yakuwa naci ɗazu da la'asar ,' anjima da dare kafin muyi bacci sai mu ci wannan ɗin , yanzu ni sallah nake so nayi ,!

******

Dare ya tsala yakaka ta gaza yin baccin kirki daga ta fara sai ta farka,  sai juyi take yi ta tattake a cikin abun rufuwar ta tayi matashi da jakar kayan ta ,

Ba kome ne ya hana ta bacci ba illa ciwon baya da kai , ga kuma matsanancin tsoron karnuka da take jiyo kukan su kurkusa da inda suke , zuciyar ta sai dakan lugude take ,

A hankali ta zira hannu ta lalubi wurin da falmata ke kwance , wayam ta ji bata nan , sake baza hannun ta tayi , ba shiri ta bankaɗa abun rufuwar ta gami da miƙewa zaune , duhu ne bakikkirin a cikin rumfar har ba'a iya ganin tafin hannun , murya ƙasa-ƙasa ta kira sunan falmata ,"

   Shiru ta ji

Da ɗan ƙarfi ta sake kiran sunan tana mai miƙewa tsaye ,

    Haske ta ga ya ratso rumfar kafin ta ga shigowar falmatan tana lalube , da sauri ta taka ta kamo ta zuwa cikin jikin ta ta riƙe , murya ƙasa-ƙasa tace
   Falmata ina kika je ? Meyasa kika fita ? Ke bakya tsoron dare ne ?

  Yakaka fitsari na ɗan je baya nan nayi ba nisa sosai ba

Meyasa baki tashe ni ba ,? Kar ki sake irin haka , ba a cikin gida muke ba a bakin kasuwa muke bakin titi cikin rumfa , babu kowa sai mu kaɗai !
    Toh ta amsa mata

Daga haka suka kwanta ƙwaƙume da jikin juna ko yaya ɗayan su ya motsa ɗayan zai iya ji ,"

Asubar fari suka tashi suka yi sallah suka ɗan sake kwanciya zuwa lokacin da gari zai ƙarasa wayewa ai kuwa waɓi daddaɗan barci ya kwashe su tare da taimakon sanyin asuba ba su suka farka ba sai da hayaniyar jama'ah da ƙarar motoci ya fara yawa wuraren takwas da rabi ,

  Yakaka mun yi bacci dayawa , cewar falmata
   Mu wanke baki mu ci abincin ALLAH ya sa bai lalace ba , ilai kuwa suna buɗe robar warin lalatatcen wake da shinkafa da miyar ya bigi hancin su ba shiri suka maida murfin ,

Bari na fita na sayo mana abin karyawa me zaki ci ? Fanke ko ƙosai ? Ko doya ko masa ?

Ni kawai duk abinda zaki ci yakaka , ki nuna min wurin da zanje na zubar da abincin nan na wanke masa kwanukan ?

Kwanci tashi suka yi kwanaki a bakin kasuwa suna gudanar da al'amuran su cikin jin dadi , ƴanci tare da walwala , sosai rayuwar da suke yi a bakin kasuwa ta fiye musu duk wata rayuwar da suka taɓa yi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login